Showing 123001 words to 126000 words out of 136333 words
sannan ta aiwatar da abinda Malamin ya sata sannan ta shiga mota ta dauki hanya,a ranar ta dawo kusan dare ma ta nemi jirgi ta tafi kudu,can ma haka ta kashe kudi mutumin yace idan ya karya sai ta kwanta doguwar jinya,tace ba komai aka karya asirin.
Kawu ne ya kira sunan Iman ku tafi gida to kawai Inshaallah zai karye,Annoor ya mike kawai ya fita Yana takunsa na zaratan matasa,Iman ta bishi kamar kurame ba Wanda ke kula wani,haka driver ya Maida su gida,suna shiga Palo ya rike hannun Iman ya fisgota idanuwansa cikin nata" haka kawai kamar zai dake ta" ya furta da izinin wa kika fita kika je Office dina? Iman tace da Izinin kaina da kaina,naje din fitar tawa ai tayi amfani tunda gashi nan da naje ai tattabeka akeyi dama kullum,haba shi yasa Dan hutun amarci ma kaki yi,Ina da operation yau,jibi Ina da wani marar lafiya critical condition,critical condition ashe Maryam ce take baka critical condition a jikinka, maimakon nayi aure nayi kiba kullum sai ramewa nake yi Ina Dan wuya sabo da halinka,auren zumunci ko tsiya a dake ka a hanaka kuka,Annoor Yana ta kallonta sai masifa take shi da ta yiwa laifi ta bishi Office ba izinin sa.
Sai da ta gama tace Kuma wlh baka isa ka min kishiya ba,babu kishiya sai dai ka sake ni,haka kawai da me zanji,ko tarihina ya isa ka tausaya min,ai dai ko da asiri to shima Yana iske hali,dama wa yasan me kake yi in ka fita,wasu likitoci wani tsoron Allah ne da ku dama,in ka fita dama haka kake yi da ma'aikatanka idan bakwa yi ta ya zaka bari ta dinga tabaka direct.
Annoor sai da ya bari ta gama sannan yace Iman ni kike fadawa haka? ae din Kai matsa can ko Dan ka rainani nima fa shegiyar kaina ce,dariya yayi kawai yace to Mama Iman zo ki dake ni mana kawai.
Iman sama ta haura da sauri,zama yayi a rantsatsen palon nasu Wanda ya gaji da haduwa ba abinda yake sai kamshi,kwanciya yayi Yana dafe kansa da yake Masa ciwo,Iman bata sake fitowa ba sai da ta Dade Sannan ta fito sanye da guntuwar gown wacce da kadan ta wuce mazaunanta,Yana kwance ya lumshe Ido yaji taku ya Dan bude idonsa kadan,Iman ce ta wuce tana tafiyarta tana latsa waya,idonsa ya lumshe da sauri yace Annoor ba kayan aiki namijin hotiho ga Abu amma ba dama,yanzu ko tabawa nayi shike nan kadarina ya karye Kuma,Bai san an karya asirin ba yaki yarda ya taba Iman,Inda yake tazo zata zauna tace matsa ko na zauna a kanka,tashi yayi ta zauna ya kwanta tare da dora kansa a cinyarta,gashinsa ta shafa tace ya jikin? yace Ina ruwanki ba tafiyarki kika yi ba,dariya tayi tace to kayi hakuri haushi naji, kawai kin rainani sabo da ba abinda nake iya tsinana miki,wanne irin ba abinda kake tsinana min?
Ba fa haka bane kawai kishi nake yi Kuma kasan ya zama dole tunda Ina sonka,haka dai kika ce amma ni nasan kawai Dan ba abinda nake baki ne,ba haka bane haba Beb ta shafo gemunsa tana murmushi,kanta ta duko a hankali tare da Dora lips dinta Saman nasa ta shiga tsotsa tace yau fyade zanwa mutum ko Banana tayi aiki ko kar tayi dole ma tayi,dariya yayi ba shiri yace Allah sarki Sweetener tana rashin lafiya, amma fa kina kiss din nan ta mike so take ta kawo nasan baza ta Kara 1mnt ba sai ta kawo,Iman ta mike tace bari na kawo Maka fruits" ta mike ta shige kitchen ta fito dauke da bowl ta kawo Masa gabansa da fork spoon a ciki suka fara aikin Shan fruits din,tace me zan dafa ne yau? Yace komai da nake ci ai kin sani in ma baza ki dafa bama a fadawa Rahma ta kawo mana daga gida,ko nayi mana order, Iman tace zan iya mana,Kitchen ta shiga ta dora girkin,miyar jajjage tayi da kifi sannan ta dafa musu farar shinkafa ta hada couslow tayi lafiyayyen zobo ta tafasa da bawon Abarba da kayan kamshi,bayan ya huce tayi blending Banana ta juye a ciki ta zuba sugar yayi mugun dadi ga amfani a Jikin Dan Adam ta shirya a dining sannan ta ganshi ya fito da alama wanka yayi cikin t-shirt fara me gajeren hannu da 3qutr yayi kyau matuka sai kamshi yake,gabansa ta karaso tana murmushi ta furta kayi kyau,Hugging dinta yayi gaba daya a jikinsa tare da furta I love you" da shagwaba tace Maryam din fa? shuru ya mata,sharewa tayi tace abinci Yana jiranka ta ja Masa kujera ya zauna tare da serving dinsa,ta zubawa kanta ta zauna itama,yau baza ki bani a bakin ba? Maryam ta baka,taci gaba da cin abincinta kamar ba itace tayi maganar ba,Murmushi yayi ya fara cin abinsa Yana kallonta,dakogowa tayi suka hada Ido, baki ta murguda Masa ta janye idonta daga cikin nasa.
Bayan su Annoor sun tafi Abba shi dai tafiya yayi,Yana zuwa gida ya samu Yar Inna ta cakare cikin Leshi fari yaji doguwar riga ta tsege dauri sai kace matar wani Gomna ta zauna a Palo tana gogewa Hashimu kayan sawa,sau tari kayansa marasa nauyi ita take wankewa ta goge masa,Kubra ta daure fuska da gaske take fushi da Hashimu,Abba ya kalleta yace kinyi a banza fushi da Hashimu aikin banza kenan,kamar baki sanni ba haba Yar Inna,na tuba nace bazan sake ba,yau wurin sati guda ko daki bama hadawa har sai yara sun gane,na gaji zan fadawa Mohsin.
Da sauri Kubra tace ka fadawa Mohsin Kuma? ae mana shi ya miki fada ai Kinga kinji kunya danki ya miki fada,Yar karamar yarsa ya dauka wacce take zama yanzu Yana mata wasa yace yarinya Yaya kike jiye min kamshin Yar Inna Yana nan ko kuwa ta daina sawa,ni nasan ta daina saka turaren yanzu tunda bama kwana tare dama Dan na yaba ake sawa to bani Ina zata saka,Yar Inna saura kadan tayi dariya ta daure tace Allah ya kiyaye na fasa shafa turare ni dama badan kai nake sawa ba.
Abba yaci gaba da yiwa yarsa rawa tana dariya yarinya yace ke kadai yanzu kike kula nononki ko Yar nan? Dariya Kubra tayi tace ajiye min 'Yata karka lalata min ita,wayar Yar Inna ce tayi Kara" Hashimu ya duba yaga Naila,daga kiran yayi,Naila tace Abba" yace Na'am"gaisawa suka yi tace Ina Umma fa? Yace gata tana fushi,ai fushi take dani mun Kai sati a haka taki hakura,Kubra tana ji bata kulasu ba,Naila tace Abba zata hakura ne,yace Abu yaki ci yaki cinyewa,ka Murda kambunka kawai Abba cewar Naila'' wanne kambu nake da shi Naila ni ba champion ba,ita ce take da Kambun ai,Bata wayar to,Abba ya mikawa Kubra ta karba,Naila tace Umma Ina yini'' ta amsa da lfy ya gida ya mijin naki? Lafiya Alhmdllh,lafiya dai ko? Naila tace dama shawara zaki bani Gani nayi kamar Spark ya juya min baya,Dariya Umma tayi,tace me yayi Kuma,Naila tace to tsakani da Allah Umma yau 3days bai kwalbe ba,dariya Naila ta bawa Kubra sosai,tace me yake yi to,tace daga Office sai bacci,in ya dawo da wuri da wuri ma laptop yake sawa a gaba da takardu ya dinga fama sai ya Kai dare sosai har sai nayi bacci,Kuma a rana sai yaje state biyu uku kullum aiki,gaskiya na gaji ni zamuyi fada da shi,Kubra tace ke yanzu Baki gane aiki ne ya Masa yawa ba,aiki ne ya taso Masa baki san Maza ba kenan,kika San me ya taso Masa ya sashi hakan
Koma ba aiki bane ai ba kullum ake kwana a gado ba,dole watarana a samu canji,ki daina damun kanki,abinda kike dai karki fasa Kuma ki koyi juriya a ko wanne hali kika tsinci kanki kiyi hakuri,bare ma aiki ne yasa shi,duk bake kike cinye kudin nasa ba,Naila tace har watana nawa da zan cinye kudinsa kin Kai dai wata biyar ko shida tunda cikin Beauty gashi ya fito ma,Naila tace uhm to shike nan Umma zan jure,Ina Hidaya? ta tafi lalle gobe za a kaita gidan miji,Kiwa mijinki godiya dubu dari biyar ya bamu,duk da Nabeel din ya zuba komai na kayan daki sai da ya Bada kudi,abinda muke so aka Kara siya mata,Baki ga gidan Hidaya ba Mashaallah yayi gida na gaske,Kinga kayan ciki du na kasar waje,kitchen ne ba a zuba abubuwa da yawa ba amma duk mun siya an zuba mata komai,zan tura miki ta Whatsapp ki Gani,Naila tace Alhmdllh ai ta turo min Lefenta gaskiya sunyi,Umma tace ai mu sai godiya ga Allah ta ko Ina rufa mana asiri Allah yake Naila tace ai kuwa Alhmdllh.
Gobe karfe nawa za a kaita? 5pm suka ce zasu zo daukan Amarya gidanta kusa da gidan Iman Inda Annoor yake,Naila tace shike nan tayi Kawa sai su zauna lafiya kar a dinga kishin faccalanci kishin banza mijin kowa daban amma mata suna kishi, Inshaallah baza suyi ba,Allah yasa cewar Naila tana cewa Umma Dan Allah ki daina fushi da Abba kiyi hakuri,ke Ina ruwanki bana son rashin kunya fa ai dama kunfi sonshi,Naila tace mudai Dan Allah a yafe masa Yar Innar Abba....tana fadar haka ta kashe wayar tasan Umma yanzu sai ta zageta.
Wayar ta kalla tace Naila wlh bata da kunya,Abba yace sabo da ta baki hakuri dan Allah kawo min abincina ki ta fushinki,Yar Inna ta mike taje ta kawo Masa abincin,ya bude flask din yace ya naga jullof? tace ae ai tunda naji kana son Alala na fasa yi tunda haushinka nake ji,Abba yace to bazan ci shinkafar ba ni,tace baza Kaci ba? Yace ae bazan ci ba Allah yasa na iya girkin bare ayi min yanga,Abba ya mike ya dauki showel din Baby ya Goyata Charas a bayansa sannan ya mike ya shiga kitchen,ya dora girkinsa,Yar Inna tana kallonsa yana aikinsa,kitchen din ta shiga ta sauke tukunyar,yace mene haka zan Sumar dake,dariya tayi ba shiri tasan ta Ina zai iya ko Marinta ma bare sumarwa,tace dan Allah kayi hakuri kazo kaci abincin nan nawa,Abba yace sai dai kici abinki ni kya min iyayi akan abinci,sabo da Allah mutum yayi ta fushi yaki ci yaki cinyewa,ya dauki tukunyarsa ya Maida saman gas,tace Dan Allah kayi hakuri Kaci wannan,yace wlh bazan ci ba na rantse in ma baza ki bari na dafa ba sai naje na siya,ni ba fushi nayi ba kawai bana son jullof dinne,to me zaka ci? Indomie da kwai zan dafa,to ka bari zan dafa Maka,haka ya hakura ya barta ta dafa Masa,gaf da magriba su Hidaya suka dawo daga lalle tare da Zarah,Abba yace kuzo naga lallen Nan,suka nuna Masa yace gaskiya ta iya Amarya kar fa kisa Ango idonsa ya fado,dariya suka yi,Yace to sai kuje kuyi wanka,Yau Abba Yana zamansa sai ga Yar Inna ta kawo kanta tazo dakinsa ta kwanta,yace kin dawo kenan,tace ae na dawo ko na tafi? Abba yace a'a ni na isa Yar Inna guda.
Jauro yau gidan Amarya zai kwana,tana gidansa tare da Habiba uwar gida har dare Jauro yace taso muje na ajiye ki a gida,Habiba tace sai da safe dai Malam,Jauro harda cewa ban taba kwana a gidan wani ba sai yau ki gafarce ni Habiba,Habiba tace kaji da shi in zaka tafi ka tafi dai,fitowa suka yi da Amarya zasu tafi,Haidar,Nabeel,Rahma da Nabeela suna Palo Jauro ya fito ko kunya yace sai da safen ku,Haidar yace bye Kawu,Nabeel ya fara boye dariya,Rahma tace Kawu sai gobe azo dai a duba lafiyar mu,Kawu yace sabo da rashin Imani Rahma in kuka ganni gobe kuce to da matsala,ya juya ya tafi" ita dai Amarya tuni ta fice kunya take ji.
Suna tafiya Nabeel yace yau Kawu za aci sabon balangu,suka kwashe da dariya,Haidar yace kaima ai gobe ne dai zaka ci naka balangun,Nabeel yace irin na karamar Dabba kuwa,Haidar yace to wlh karni zaiyi,yace Dan uwarka ba na kamar Dabbar turawa taji kiwo me Mai,kaga maiko zata yi,to zaka ce na karamar Dabba namanta in banda yauki da karni me zaiyi,Nabeel yace uhm nidai nayi shuru yara na wajen.
Rahma tace sai da ka gama sannan kace muna wajen.
Chika ce da Misam suke hayaniya su kadai sun cika Palo ka rantse Baki suka yi,kamar yara sai wasa suke kala kala suna dariya,Yana zaune Chika ta haye Saman kafadunsa dokin wuyansa,Mima ce tayi sallama tare da shigowa ciki,Chika tashi tayi gata da wasu shegun guntayen kaya a jikinta,bum short da riga,ba kunya ce da su duk da haka dai taga ai uwarsa ce sannu da zuwa ta furta tace bari nazo ta juya ta haura sama da sauri,abin mamaki Mima bata ce komai ba,sai ma cewa tayi Kuna ta kaya kaya wlh na zaci bakin yara kuka yi jibi Palo yanda kuka Masa pillows din kujeru duk a kasa,ai lokacinku ne kuyi.
Misam ya mike tare da zama yace Ina yini Mima,ta amsa da fara'a tace tunda kayi fushi baza kazo ba gashi na sake zuwa ni,uwa ai bata fushi da danta,kiyi hakuri zanzo ne,ba wani zaka zo tun yaushe kake fadar Hakan ka kasa zuwa,ance haushi kaji munce ba bikinka muke ba na Rafeeq muke yi,Misam yace ni dan Baku yi bikina ba sai naji haushi kawai,Mima tace Gani nayi kai da Rafeeq ai duk daya,Misam yace yanzu ba kwace haka mana" koma mene ya wuce Mima,ya gida kwana biyu banga su Arham ba,sun samu shinkafa ai dole ka daina ganinsu,Misam yace Papa yaki dawowa dai,Mima harda hawaye tace abinda ya dameni kenan Misam,shine a gabana,Dan Allah ku roke shi ya dawo dan Allah,Misam yace to munyi munyi yaki ya ma daina daga wayar mu,Mima tace yau ni na shiga uku Kuma a rayuwa,kiyi hakuri zai huce ne,sai yaushe sabo da Allah sai yaushe? cewar Mima tana hawaye,da kyar Misam ya lallashe ta tayi shuru ta goge hawayenta,tace ni nace Masa wlh na tuba ko me yake so yanzu zan canja hali Kuma zan gyara Kuskurena Inshaallah,idan ma ya Kara auren ya taho da matar mu zauna tare,Zai hakura Inshaallah cewar Misam.
Chika ce ta fito cikin doguwar rigar material ta fito ta durkusa ta gaida Mima ta amsa Kuma harda sakin fuska,Chika tana ta mamaki a ranta ta mike ta shiga kitchen tana cewa shike nan naci banza,rashin kunyar da nayi mata kafin na auri Danta naci banza,naci banza...naci banza...naci banza....tana yi da Waka harda rawa,a hankali ta leko da kanta tana kallon Mima da Misam suna Hira ta cunowa Mima baki tace naci banza a hankali yanda ba me ji,ta washe baki tana dariya marar sauti tace Kai wallahi naci banza tayi hankali,na gaisheta ta amsa harda fara'a,kitchen ta dawo gaba daya ta shirya abinci da na Sha ta shirya a dining ta fito tace Mima ga Abinci
Mima ba a wuce tayi yanzu tace kawo min nan ni yanzu Dining table bai dameni ba,Chika ta kunshe dariyarta tayi sauri ta juya baya ta saki dariyarta marar sauti ta gama ta maze ta juyo ta kwaso kayan abinci ta kawo gabanta duka,tace duka ni kadai haka mene da mene haka yaran nan ku daina Almubazzaranci Dan Allah,Misam yace kayan mijinta ne fa Allah ya hore Masa Kuma Ina gari ba yaji nayi ba Mima ai dole tayi girke girke,Mima tace to Allah ya Bada lafiyar ci wato ni ka fadawa magana ko Misam ba komai,yace Kai Mima ni na isa na fadawa uwata magana yi hakuri,ya bude mata taga dambun nama,Taga farfesun kaji,ga wata fried rice ga couslow sai kayan Sha,Allah sarki Uwa sai ta tuna su Arham dinta,su suna zuwa suci basa tunawa da ita amma ita tana Gani su ta tuno,tace bazan ci ba ni,yarana suna can tuwo suka ci Ina zan sa dadi a gaba naci,Misam sai ta bashi tausayi sosai yace Allah sarki Uwa wlh duk Wanda baibi uwa ba dole ya shiga wuta,yace to kici naki ki koshi sai a Baki nasu,Mima tace to da dai yafi,ta zauna taci abincinta ta koshi,Sannan Misam ya kira Chika kitchen yace Ina abincina tace gashi,yace to sai wanne? tace sai na me gadi Dana ajiye Masa,yace hada duka ki zubawa Mima karki rage komai,har lemon da kika hada komai da aka yi a bata du,tace har dambun Naman Yana da yawa fa yace bata duka ki juye mata,tace to Allah yasa dai Papa ya dawo haka Dan Allah kuce ta canja ya dawo kar ya shiga hakkinsu,Misam ya tsaya a bayanta kamar kwarto tana aiki Yana faman shashafe mata mazaunai"to ka bari na gama mana,yace Ina zan iya ni fa kin San Ina kunnawa to ba sauki a bani a huta kawai ni Dan wutar ciki ne.
Dariya Chika tayi tace Rafeeq na tuna wlh Ikhram kamar handbag duk Inda zaije suna tare,Misam yayi dariya yace wannan ban taba sanin maye bane sai rannan,Spark ya dauki masifa aiki a Office wai shine Sakataren sa,in yaje to Inshaallah sai Ikhram taje tare yake tafiya da ita,ba uwar da yake sai soyayya,Spark zaiyi baki wlh har suka zo suna ta knocking yaki magana gashi ya sawa kofar key,yasa Spark yayi loosing contract din Kuma zai samu kudi masu yawa,Spark ranar tab kinga bala'in da yayi badan Allah ya kaini ba da Sunan Rafeeq korarre sai dai ya koma shawarmar sa.
Shine suka canja salo yanzu idan yaje Office 1:30pm Ikhram zata hado basket guda na abinci ta taho ta kawo idan ta kawo abincin to sai an tashi zata tafi,shiga goma fita goma tana ciki mayya itama,karki ce wata uwa suke a ciki ba wai sex suke ba daga Dan Tabesting sai Hira da kallon juna,Rafeeq bai ki ta zauna a gabansa ba ya sata a gaba ya dinga kallo har dare,Chika tana ta dariya ta hadawa Mima abincin komai a flasks masu kyau ta shirya mata a katuwar Leda wacce zata dauke ta kawo mata,Misam ya dauki kayan yace