Showing 114001 words to 117000 words out of 136333 words

Chapter 39 - TANTIRIYA A GIDAN YARI BOOK2 By asma baffa

08 Jul 2024

9543

abin bana jinsa a na asibiti ne Iman doctor ne ni,a gwada dai tukun idan baiyi ba sai a nemi maganin gargajiya sannan mu dage da karatun Qur'ani da Nafeela muyi ta addua.

Tashi tayi tace haba mace bata tsoron namiji daren farko Ina mutum a Nan,Ina namiji ai yau na tashi Ina Jin tsoronka shine gaskiya,Annoor Yana dariya yace au bakya tsorona yanzu? Iman tace akan me Ina dalilin Jin tsoronka,wlh sai na rama gorin da ka dinga yi min ni ba budurwa bace ai gashi Nan kaima ka hadu da jarabawa,Annoor yace Sanyi na dauka a jikinki ranar first night kece kika shafa min lalura,dariya tayi tace ko kaikayi ban taba ji ba a down Dina,yace ai ana yi yayi shuru bazai nuna ba, Infection kika shafa min,nidai in ba a jikinki na dauka ba a Ina zan dauka, kyau har kyau ciki duk Infection kin cuceni da yanzu Ina shagali kin cinye kaza a banza,wlh girki zaki fara yanzu zan fito nace kar a kawo abinci ba uwar da kika min mene na kawo miki abinci,Iman tana dariya tace Kaine ya kamata kayi aikin yanzu ko bude Maka nayi sadaka baza ka iya ba,hannu na ma ya isheka ka kawo gaskiya na hadu da yawa ni hannuna ma Oga ya taba kawowa yake gaskiya Allah ya min baiwa,Annoor yace zan gwada akan wata zan rike hannun wata naji zan kawo,Iman tace zaka fara ko Dan Allah karka yi nidai,Annoor a ransa yace ya zama wajibi na nemi wata na rike hannunta naji,tunawa yayi da Maryam mayyarsa a wajen aiki yace yawwa ga ballagaza tana kawo kanta yau zanje Office zan rike naji,sannan naje na rike Debora itama,wata Likita ce Debora tana mugun son Annoor,Yana tunaninsa Iman ta shiga tayi wanka da brush ta fito ya shiga,kafin ya fito ta shirya tayi Sallah sannan ta tsara kwalliyarta cikin dakakkiyar shadda pink,dinki na zamani ta hadu tayi kyau ba karamin kyau ta zuba ba,ta fito Palo tana taku dai dai tana kallon gidanta sai ga Rahma da Nabeela sun kawo breakfast lafiyayye,dinginshin karya ta fara tana yatsina tace kamar nasan zaku zo na fito.

Rahma har da dariya tace gogan ko an sake farke Inda aka dinke ne,Nabeela tace ai nasan za a rina an saci zanin mahaukaciya,Iman tace bana son wulakanci wato da uwata kuke an saci zanin Uwata sai ta fara kuka,Nabeela tace yau na shiga uku wallahi ba Dake nake ba Karin magana ce Kuma na manta ma Mamanki bata da lafiya,kiyi hakuri Iman,Rahma tace rabu da Yar iska dake ake mu muka miki laifi daga anyi Karin magana bisa kuskure,in zaki shagwabarki kiyiwa Ango shi ya miki laifi ba mu ba,sanda ake tabaki ba dadi kike ji ba,Iman tace banji dadi ba ni,Rahma tace ni nasan dadin fa yarinya Dan Romance din nan ana min shi ba abinda zaki gaya min sai dai sex ke an miki tuntuni.
Nabeela tace ni kuwa Ina nan Ina fama da nawa a jike,Iman ta bude Abincin ta gani,tace Kai bayin Allah ya akaji da taya Umma Habiba kishi?

Rahma tace Kawu wai harda shi aka daura aure Kai namiji sai a barshi wlh tausayi Umma take bani,Iman tace har ga Allah banji dadi ba,Nabeela tace nima haka wlh ban so ba,wannan abokin nasa ne ya zuga shi Abba,Iman tace shi Kuma fa mata Daya ce da shi jal ya kasa karawa tun auren fari, ke in kika ga matar nan yanda take ji da shi kamar yarinya Bata Jin kunya,dole ya kasa Kara aure sai abinda tace,Nabeela tace sai kace ta Masa asiri duk Inda ya Zauna Yar Inna,Yar Inna" suna dariya,Rahma tace wai Nan Sunan love ne Yana birgeni wlh Abba nan tab madaurin auren Iman, ya yanke sadaki da yawa yace Kuma sai idan baza a aura a haka ba a bar Iman ta Shekare a gida bazai daura ba,Suna ta dariya Iman tace yasa nayi tsada fa,Rahma tace muma a bashi ya daura namu ko zamu yi tsada.

Annoor ne ya fito ya Sha uban wanka ya zuba Gezna dark Arsh yana sheki da kamshi kamar yau za a daura auren,Rahma tace Ango an Sha Mai,yace me ya kawo ku gidan Amarya da safe haka,zuwa muka yi in ta kasa tashi muyi gashi,murmushi yayi yace gulmace ta kawo ku dama,Iman tace kyale su Sweet,Rahma tace Inye lallai ya tashi daga Yaya? Iman tace ae Ina Ango Nabeel? Yana can a wajen Kawu yace shi bai yarda ba wlh a kawo Masa Amaryarsa,Kuma tana Abuja gidan yayarta ance sai nan da sati wai Abuja zai tafi shi,Kawu yace Kai Nabeel dama haka kake? Yace ae shi jiya bai iya bacci ba,Kuma ance sai nan da sati biyu za a kai Masa Amarya sai kace zai zauce wlh ya hana kowa sukuni da zancen Amarya Hidaya,ga yarinya a waya Yar wannan yarinyar sai hure Masa kunne take da kalamai,Annoor yayi dariya yace ku daina ganin laifinsa,Iman abincin ta zubawa Annoor ta hada Masa tea da dai su chips da kwai,suka karya su Rahma suka ce su sun karya amma da suka rage sai suka cinye ragowar suka ce kar ayi asara suka tattara kwanikan suka musu sallama suka tafi,Iman tace ku kawo na rana fa,suka ce to.
Kwanciya tayi a Jikin Annoor tana tumurmusa shi,masifar son jiki ne da Ita,Yana so ya fita yaje Office yayi gwaji amma ta hanashi wai tsoro take ji,yace da me gadi fa da komai Yar aiki ma za a kawo miki soon,tace nidai baza ka fita ba.
Bacci tayi a haka bata sani ba ya lallaba ya kaita bedroom Saman bed ya kwantar da ita ya fice nufinsa kafin ta tashi ya dawo ma.

Asibitinsa ya wuce direct,Maryam tana ganinsa ta taho da sauri tace Sir Allah ya sanya Alkhairi amma yau kazo Office kamar ba Ango ba,fuska ya bata Yana amsa gaisuwar mutane yace Ina ruwanki,ki daina shiga safga ta yaja Kwafa,amma duk da haka ta bishi Office tana goge masa kujera,hannunta ya ruko sosai,ta tsaya tana kallonsa da mamaki,ta zaci ya fara sonta harda sakin Murmushi ta jefar da duster din Dake hannunta ta rungume shi sosai,da Iman ce tayi haka da tuni ya kawo,ko baya Jin Feeling ta yi Masa haka to sai ya kawo amma shuru kake ji,har tsayawa yayi ta sake rungume shi amma shuru bai kawo ba,Maryam tunaninta tayi nasara Yana janye jikinsa ya karkashe ta da Mari har biyu, ya hankada ta waje yace mayya wacce Bata San darajar kanta ba, jaka mahaukaciya fasika ya kulle kofarsa,Maryam tace wato dai baya so na idonta ya ciko da kwalla tana shafa kumatunta ta koma wajen Marasa lafiya tace dole sai ya Soni wlh.

Annoor zama yayi Yana ta tunanin kansa sai ya fito ya shiga Office din Debora tana ganinsa tace yau Oga da kansa a Office dina wow tana murna tazo ta fada jikinsa ta rungume shi harda shafa Masa kirji itama ya kwashe minti yafi biyar a haka ba abinda yayi baiji komai ba bare ma ya kawo,amma Iman dama yasan Yana da feeling a jikinta ko ya ta rabe shi tun Yana da lafiya ma sai yaji shock amma wannan shuru ba komai,jikinsa ya fisge ya dinga balbalin masifa wa Debora ya fice Yana zage zage ya koma gida,ya samu kuwa bata tashi ba,Umma Habiba ya kira ya gaida ta,ya gaida Jauro ma sannan ya kira Mamansa suka gaisa yace gaskiya shi baiji dadin ba Dan me zata auri Kawu ai an ciwa Umma Habiba fuska,Maman Annoor tace to bani da zabi ne wlh ya dade Yana bina,halacci da yayi min Bai cancanci nace bana sonsa ba,ita Kuma matar data rike miki yaro ta rainar miki shi har ya girma fa? ta zauna Dake kamar kawarta Kun zama kawaye ma sannan kizo ki aurar mata miji,Mama tace ni kaina ban so haka ba amma Allah yayi bani da zabi zanje na bata hakuri,ba ki kyauta ba dai gaskiya koma mene bai dace ba babu tsari Kuma.
Mama tace to kuyi hakuri na auri mijin uwarku nima bada so na ba,Annoor ya kashe wayarsa kawai.

A gefen Iman ya kwanta wani sha'awarta ta taso Masa dama tun da can Yana Jin hakan game da Iman,amma ko ya taba ta bai kawowa yanzu kuwa yasan Yana rungumeta shike nan,Iman ce ta bude idonta a hankali ta ganshi kwance a gabanta Yana ta faman kallonta,jikinsa ta koma ta makalkale shi,Ido ya lumshe kafin kace me ya fara shidewa sai kawowa ,Iman tana jinsa ta gane tayi kamar bata gane ba,tashi yayi ya zuba tagumi,tace ko Ruqiyya za a Maka ne wannan wanne masifa ce ne haka,yace Dan Allah ku kaini ayi min Ruqiyyar nan nima naga abin nan bana lafiya bane.
Nasan yanda zamuyi kana ji yau zan bude ma kana Jin feeling karka tabani Nima bazan taba ka ba,zan bude ma wajen shagali kawai ka shiga a haka mu gani,yace tab ai Ina taba wajen da Sweetener ta shike nan na kawo Kuma,Iman ta zaro ido tace kar na Kuma ji wlh kace Sweetener Ina ta isa a kirata da Sweetener banji dadinta ba ka dinga asarar kiranta da Sweetener sai ka bari ka warke tukun,Annoor Yana dariya yace harda gori Iman tace ai Ina Maka da sauki wlh akan ni abinda kayi min akan ka shole dani ka dinga fada min magana iri iri,da ace ramawa zanyi kuka zaka yi nan gaba,dariya yayi yace Kuma ba wahala naji sha'awarki dole fa na Tara likitoci gaskiya,tace shi ya kamata dai.

Naila ana ta gyara Amarya Hidaya tana ta kashe mata kudi,Hidaya har ta canja kuwa tayi Yar kibar sabo da maganin Kaka,ga magungunan Naila tayi Yar bulbul tayi kyau ta Kara haske tana kamshi,Spark yace ke ya naga Amarya tana kiba ne karfa ku bata Sha ka fashe kullum ta dawwama ashan magani,Naila tace maganin kaka ne wlh ba ruwana ni dai,Yace to da sauki sauki,kar a Bata komai na kibar Nan please tunda tayi aure zata yi ne inshaallah ai yarinya ce,in ta fara jin Hallare ko Ina zai bude,Naila tace dama wai Hidaya tace mijinta ya matsu a kaita ya hanata sakewa wai ta koma gida ko yazo,Spark yace yazo mana ga part guda na basu ya Mori abarsa ai mu indai harka ce ta Bado yazo akwai wajen cinsa a gidan nan,Naila tayi dariya tace na hanashi nace zata taho ma da kyar ya yarda fa hmm ba kunya ba komai.

Mummy tagumi tayi a Palonta,tana tunanin Baseeru,ita yanzu ba Wanda take so sama da Baseeru gashi ya saketa,gata jarabarta ta motsa ba Baseeru ta rasa Inda zata sa kanta,ita kadai take magana tace Ashe Baseeru dadi ne da shi ban sani ba,ta kwanta tana matse cinyoyi tana kiran Baseeru,tace Ina ma laifin ya min saki daya ko biyu da yanzu ai ko kudi ne biyansa zanyi ya Maida ni muci gaba,son zuciya ya ja min,gashi gidan yari na jirana ni kuwa ko guduwa zanyi ne gaskiya ya kamata na gudu,Nan take Mima ta hau hada jakarta ta kaya a daren ta shiga motarta ta bar gari ba Wanda yasan ta tafi sai takarda ta rubuta ta ajiyewa Spark a Saman kujera ta ajiye wayoyinta a palon ta cika rigarta da iska.

Malama tun bata Saba da jarabar Rafeeq ba har ta Saba ma ita ta hakura biye Masa take,tana wanka ya shugo bedroom din yaji karar ruwa kayansa ya tube ya shiga ciki,tana wanka ya saki shower ya wanke mata kumfar jikinta sannan ya manna ta a jikinsa,tace yanzu wankan zamu sake? yace ae yeah kema kin sani...











AsmaBaffa
[2/2, 8:18 PM] AsmaBaffa: 🏫TANTIRIYA🏫
A GIDAN YARI

BOOK 2
~YARAN JAURO~

91-95

Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM


PAGE NAKI NE
Anty Nurse Zaria


Rafeeq harda wani basarwa shi ga me gida,sun tsunduma a duniyar Nishadi kawai suka dinga Jin Door bell tana Kara ta cika ko Ina,Ikhram bata ji bama tsabar tayi Nisa Rafeeq ne yaji,tsaki ya ja yace yanzu haka mayun yaran Nan ne su Arham,fitowa yayi ya bude kofa a fusace sai yaga Naila tare da Hidaya,murmushi yayi yace wai kece dama thank God ma kece shike nan wuce ki zauna wanka take ki jira zata fito bari na fada mata,Naila tace to ya haura sama Yana zuwa Ikhram tace waye yace Naila ce ma ashe ai ta San kan garin rabu da ita sai na idar na sauke farali,Ikhram tace ka bari sai dare Please sai tace mun mata wulakanci,Naila ce fa baza ta ce ba tasan komai Yar duniya ce da kike Ganinta da gidanta kika je baza ta fito ba sai sun gama,wa yace tazo gidan Amarya.

Su Naila suna zaune Ango da Amarya shuru shuru basu fito ba,Hidaya tace Anya zasu fito kuwa ko dai ko dai abin akeyi,Naila tace zai wuce shine sai an fito ace mana wanka ake yi,kema kwana Nan zaki fara Hidaya bari a kaiki gidan Nabeel,Hidaya harda rufe Ido tace nidai ba ruwana bazan yarda ba tsoro ma nake ji,Naila tace zaki cuci kanki kuwa mu muna gefe muna Jin dadinmu gwara ma ki yarda yarinya,mu ganshi mijin naki na sake kallonsa na gani ko zan gane kalar tasa Hallaren kin San fa ni me maganin gargajiya ce ato idan kubewa ce shike nan,Hidaya ta nunawa Naila hoton Nabeel,Naila tace ahh da alama doguwa ce kin tsallake rijiya da baya.

Suna ta hira abinsu sai da aka kwashe lokaci me tsawo sannan Ikhram ta fito ta Sha wanka cikin material tana kamshi,tace na Dade ko? Ina shiga wanka yace min kunzo,Hidaya tace ai fa mun ga alama,Naila tace Kun dai kwalbe kar a wani yi mana alaye,Ikhram dariya tayi ta mike ta kawo musu kayan motsa baki,tace Naila ya kamata ki bawa Nabeel matarsa wannan wanne Abu ne,Naila tace gobe zasu tafi fa sallama na kawo su dama su Zarah suna gidan Chika su Spark ya tafi da su tun rana,sun Dade suna hira sannan Rafeeq ya fito sanye da jallabiya Yana kamshi yace ba dai tafiya ba? Naila tace ae tafiya zamuyi Baby kar su koma gidan banyi girki ba,Rafeeq yace uhm kaji masoya,dariya suka yi tare da raka Naila suka shiga mota,Rafeeq ya bawa Hidaya 10k,Ikhram ta bata turaruka da kayan gyara Bado.

Su ma su Zarah sun samo kudi suka dawo da tsaraba iri iri Spark ya kaisu ya kashe musu kudi,har Hidaya aka siyowa nata,Spark Yana rike da Hannun Aslam suka shugo,Naila tace sannunku da dawowa yanzu muka dawo muma,kayan suka hau nunawa Naila suna Murna,Spark tuni ya wuce sama Yana wanka,su Naila suna ta kallo.

Mima ce ta fito ta samu Arham Yana kallo tace Kai wai ka daina zuwa school ne? Arham yace tun yaushe Nima na gudu daga aikin Soja bazan iya ba wlh ai ni yanzu a online nake karasa degree na aure zanyi ni bazan tsaya bautawa kasar da bata da alqibla ba,ai tunda aka balla min kafa da kyar na tashi na cika rigata da Iska Nima,yanzu Papa Bai da magaji kowa ya gudu sai Junior shima Yana sanin ciwon kansa zai arce wannan bakar azaba haka,Mima tace to tashi na aikeka gidan Mummy tun jiya nake kiran wayarta tana ta ringing ba a dagawa je ka gano min lafiya take kuwa,kayi sauri kafin magriba tayi,ya mike yace to dama a shirye yake cikin kana nan kaya sai ya wuce kawai.
Yana zuwa ya iske gida a bude ba kowa,me gadin ma babu,ciki ya shiga a hankali Yana sallama ya samu wayoyinta a Saman kujera da takarda a gefe.

Arham takardar ya dauka ya fara dubawa a hankali yaga ta rubuta
Spark dana ka sanarwa Yan uwana ni na gudu Inda baza ku sake Ganina ba,Allah ya gani nasan prison za a kaini karshe,bazan iya zaman gidan yari ba,kuyi hakuri da rashina na shiga duniya,idan da rabo Allah ya hada mu watarana,Ina me baku hakuri da hukuncin da na yanke,ka sanar da Yan uwana Ina musu fatan Alkhairi,ga wayoyina nan na barsu kar ma ku neme ni baza ku ganni ba nayi nisa yanzu haka Ina hanya.

Arham Yana gama karantawa ya kira Mima ya sanar mata komai yace Mima Yar uwarki dai ta arce tace kuyi hakuri da ita ta shiga duniya,Mima tace ban gane ba,yace bari na zo gida ki gani,Spark ya kira yace babarka ta gudu fa ta bar gari tace baza ku sake Ganinta ba,kazo gidan Mummy gidanku kazo ka gani yanzu,Spark bai bata lokaci ba ya iso gidan.

Takarda Arham ya nuna Masa,Spark ya karba ya karanta,Yana gamawa yace shike nan naci gadon gidan da sauran kadarori,dama gado ance jeka Inda ba a sonka,wani can sai yazo yaci gadonka,Arham yace au haka zaka ce ma uwar taka guda to Nima a bani Daya motar ladan bincike dole a San min ganima,Allah yasa ta bar gwalagwalai da shike nan ni na samu jarin aure,Spark yace baza fa ta wuce tayi hanyar Lagos ba,bari ka gani,Arham yace Dan Allah kyaleta muyi rabon gado Ina ruwanmu tunda Kai baka yi dacen uwa ba,Allah yasa ma kana da Naila ta karbi Duty tuni,Spark yace wlh kuwa na saki nonon uwa na kama na mata Kai muje baza tayi 24hrs ba zan sa a dawo da ita.

Spark ya kira wayar sojoji ya basu sanarwa da number motar da tafi da ita da komai na motar da hoton Mummy yace kar ta kwana a dawo da ita gida,Sojoji suka bazama kamar za a kamo shugaban Yan ta'adda,can Hanyar Lagos suka tsinci Mummy goslow ya riketa,dama sojojin gaba aka yiwa waya aka basu sanarwa,babu bata lokaci suka saka Mummy a motar su suka dawo da ita Abuja.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login