Showing 3001 words to 6000 words out of 51041 words

Chapter 2 - HAMSHAƘIYA-UWA-_3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

05 Jul 2024

6858

Hajiya bata da matsala da haka, in kina so ma zaki iya bari sai sun tafi Ummara sai ki yi yadda ki ke so." Na kalli Baba Juma tabbas tana min wani irin kallo mai kama da shurin jeki ki mutu.

Muka ?arasa wani ?aton store narke da shinkafa 'yar gwamnatin ga taliya da makaroni Suger Indomie da sauran kayan abinci na azumi.

Na kalla nace ta??i gaskiya in wannan aikin yana cikin jarabawar Hajiya ba shakka dole a fa?i.

Muka dawo ni dai ranar haka na yini ina nazari
Na ?auki waya na kira mijina Shamaki ya ?aga cikin sauri yace "Menene yi magana meeting zan shiga yanzu." Nace to dan Allah ina son magana da kai in ka fito. "Ki kira ni ?arfe Shidda na yamma." Bai jira amsa ta ba ya kashe wayar.

Na ce kai nima fa ina da uwa,duk Duniya ita ce take min son da ba wanda ya ke min makamancin shi, dan haka ita ce zata bani mafita kamar yadda ya ke tutuyar ta shi uwar tana sama mishi mafita.

Na ?aga waya na kira Umma, Muka gaisa nace Umma dama wani yanayi na samu kaina ina bu?atar wanda zai tsaya min har komai ya yi kyau "To kuwa wake gare ki bayan mu Baby?" Ta katse ni. "Menene fa?a min. Na kwashe komai na sanar wa Umma sannan na tsaya sauraron ta. Tace abu na farko yanzun ki je ki samu Hajiya ki ce abaki list na mutanen da za su amfana da wannan zakkar in ta baki sai mu sake yin magana."

Na zo bayan la'asar na samu Hajiya tana kallo na zauna na gaishe ta,sannan nace Hajiya dama list za a bani na wa?anda aka saba baiwa wannan taimakon. Hajiya ta ?ago ta dune ni kamar zata yi magana sai kuma ta kauda kai, sannan ta ?aga wani fayal ta ciro wata doguwar takarda mai ?auke da sunaye a jere tace "Gashi." Na amsa,nannan na nace yawwa Hajiya dama su wa?annan ku?in na cikin... Ta ?aga min hannu duk yadda ki ke bu?ata haka zaki yi abida ya sa na baki list ?innan saboda kin tambaya ne,da baki tambaya ba bazan baki ba."

Na ce To na gane. Na koma ?aki ina me alfahari da uwata na zauna na duba list mutum ?ari harda uku. Na kalli ku?in aka durowar gefen gado na, nace gashi ku?in na mutum ishirin ne.
Naira miliyan biyu ne ta riga ta raba ku?in bare ince a rage su yadda kowa zai samu. Na sake duba takardar sosai ko a kwai sunayen da zanga anyi musu alama amma bangani ba,na kuma kiran Umma na fa?a mata ga halin da ake ciki.

Tace "To abinda za ki yi ?o?ari ki gano shine wa?anda za a baiwa wannan dubu ?ari ?arin domin tabbas na wasu ne daban kuma ana ha?a musu da kayan abinci sauran mutanan kuwa sai ki kira su tunda akwai suna da kuma lambar waya sannan ki tabbatar ba ki ba wani naki ko mu wannan kayan abinci da ku?i ba."

Nace Haba Umma hauka ake, duk yadda za ayi dole in cire muku kuma,shirme kenan zan yi cewa fa aka yi duk yadda nayi daidai, banda ma tsoron Allah harni sai na ?auki kashi ?aya. Umma tace "Baki da hankali, ko ?wayar gero kar ki sake ki aiko mana da shi. Ki bi list ?in da ta baki, abinda za kiyi kawai shine ki ki fara da kiran lambar farko kiji waye a haka sai ki ware wa?an da zaki ba ku?in, amma ki bari sai ranar lahadi tunda kince baya fita da wuri." Nace to zan yi haka amma zan kira su kafin ranar in sanar musu

Da safe da naje gaida Hajiya bayan na gaishe su har zan mi?e sai tace "Ranar yaushe za ki yi rabon zakka?" Na sunkuyar da kai nace ranar Lahadi. Tace "Nan da kwana hudu kenan me yasa ki ka kai shi har wannan kwanakin?"
Nace ina son in gano suwa za a ba wannan ku?in ne. Ta ?an yi jim sannan tace shike nan Allah ya taimaka. Shamaki ya matso kusa da kunne na "Jiya me ki ka sha ne na yi miki tashin duniyar nan amma ki ka kasa tashi?" Na rage murya nace na yi shaye shaye jiya irin su ruwa da lemo.muka sa dariya.
Nace na jira ka har kusan ?aya baka shigo ba,bacci mai nauyi ne kawai. Yace "Dama maganar da kika ce za mu yi ce na so in tashe ki." Da gefen ido na kalli Hajiya kuma na gane hankalinta yana gurinmu. Nace ba fa wani abu bane,kawai ina so ne inji muryar ka, ko zanji sanyi a zuciya ta. Yace "Zafi ta yi a lokacin?" Nace ?unar sonka ba. Ya ?an kai min dukan wasa,yace Me wayo zaki fa?a min gaskiya bari in shigo. Na tashi na koma ciki.
Na ?auki takardar ina ?ara kallon ta. A fili nace banda Hajiya ta so wahalar da ni, ai da sai tace kawai da sai ta fa?a min cewa ku?inna wane da wane ne.

Na kira lambar farko Na miji ya ?auka kuma da alama dattijo ne. Muka gaisa, nace daga gidan Alhaji Baita ne don Allah da wa nake magana? Sai aka ce "Da liman ne mai jan salla a masallacin gidan. Nace to ranar Lahadi za ka kar?i sa?o. Yace to Allah ya kai mu."

Bayan mun gama waya nace ina ruwa na Allah duk wanda yake sahun farko shi zan ba ku?i kuma in ha?a masa da abinci.

Na kira na biyu shima na tambaya kamar yadda na yi na farko. Akace wacece baki gane da wa ki ke magana ba? Nace Matar Shamaki ce. Sai yace auto Babanku ne ?anin Hajiya. Nace Baba ranar Lahadi za a bada sa?o, yace to "yar nan mu zamu zo mu kar?a? Nace Baba ya ake yi muku ne kawowa ake yi ko ku ke zuwa? Yace "To shekarun baya dai can kafin rabon ya koma hannun matan Shamaki direba ke kawo wa Bama sanin cewa za a bamu amma daga baya sai ace mu zo mu kar?a."
Cikin zumu?i nace acan baya ?in me ake baku ne Baba? Yace "A can baya dai dubu dari da buhun shinkafa da suga da gero. Nace to Baba bana ma ba sai ka zo ba, za a kawo maka kamar yadda ka lissafa. Yace to Allah ya yi albarka. Nace Ameen yace akwai wani ?anenmu a ?auye shi an daina bashi ma gaba ?aya,kuma da har shi Hajiya ke bamu. Nace to za 'a bashi ya zo ranar lahadi ko shima kauyen ake kai masa da? Yace A'a gidan yake zuwa. Nace to.
Wato ashe dai lissafin Umma haka ne da nayi ta bin lambar har shi na ?auyen nan na samu lambar ?ansa, sannan sai ga su Juma na kira ta ?aga tana cewa wacece? Na ?auki murya nace Baba Juma ce tace e, sai kawai na kashe domin na gane. Munan duk makusantan su ne '?angaren Alhaji Baita da ita Hajiya Zeena, sannan 'yan aiki.
Bayan na gama da ishirin ?in nan sai na koma in gano sauran me za a basu, nace irin dai wancan tsarin zan bi innaji a bakin mutum ?aya shike nan.

Na kira wayar na ishirin da ?aya. Muka gaisa mace ce, nace an kirata ne daga gidan Alhaji Baita,tace to Hajiya ce ina yini,ta sake gaida ni cikin girmamawa. Nace na san kin sani zakkar abinci ce ko? Tace e nace me ake baku ki fa?a min gaskiya domin akwai wa?anda za a soke sunan su in sun fa?i ba daidai ba.

Tace tsakani da Allah da dai can ana bamu shinkafa gero sai suga mu biyu buhu ?aya ni da wata itama 'yar uwarmu ce, kuma ana bamu taliya. Nace kuma 'yan uwan Hajiya ne? Tace a a mun yi aiki shekarun baya can tare da Hajiya Gwamma mahaifiyar Alhaji Baita lokacin muna ?ananan yara, shine Hajiya Zeena ta ri?e al?awari ake bamu, duk shekara sai anzo har gida an kar?i lamba. Amma 'yan shekarun nan gero ake bamu da shinkafa. Wannan lambar ki ce? Tace ta jika ta ce. Nace ku zo ranar Lahadi tace sai dai in turo jikata Dan ni sai bakin da kunne ba ido ba ?afa, Nace Kaka ya sunan jikar ta ?i? Tace "Mairamu zan turo ita mijin ya mutu ya bar ta da 'ya'ya." Nace ki fa?a mata in tazo tace tana son ganin matar Shamaki. Tace to zan fa?a mata, inaha Allahu 'yar nan ke ce matar Shamaki ?in?" Nace E ni ce Kaka. Tace Ikon Allah ?annan tun yana goye rabon da in gashi. Na yi dariya muka yi sallama. Haka nayi ta kira ina sanar da su suzo ranar Lahadi har na gaji na yi makin ?in inda na tsaya.

Washe gari sai da na gama komai mijina ya fita sannan na koma na ?ora, zuwa washe gari duk na gama sanar da kowa.

Ranar asabar na idar da sallar azahar ina kan sallaya ina danna waya na ga ansani a wani group na duba admin ?in sai na ga wata 'yar ajinmu ce ta boko Basira Ashiru na sake duba sunan group ?in sai naga an saka Gandu 2019 nace la group ?in 'yan makaranta, gaskiya na ji da?in domin za a sada zumunci.

Wayar gida ta katse min tunani da ?ara, na san Hajiya ce, na daga na gaishe ta. Ta amsa, sannan tace, "Kina ji na ko?Ki fito ga wa?anda zasu taya ki aikin gobe sun zo, ki zo ki basu Umarni yadda za su miki aikin." Nace To. Na samu maza majiya ?arfi su biyar. Suka gaishe ni cikin girmamawa har naji kunya. Hajiya tace ki je ki basu abinda za suyi su fara tun yanzu, bana son sai gobe a cika mana gida kamar kasuwa fatan kuma ki fidda tsarin da wani ba zai amsa so biyu ba. Nace Insha Allahu.

Na dube su nace muje can gurin da kayan abincin suke. Suka fita dan su zagaya. Dama da hijabi na na fito sai na koma ciki na ?akko takardar sannan na ?akko wata takardar da biro na dawo na bi ta kicin na ce da Baba Juma ta zo muje...
????????
?Na nuna musu abincin nace ina son su ware min buhun shinkafa guda tamanin, ko wanne su saka taliya da makaroni da gero sannan ina son su ware min suga buhu arba'in. sannan su cire min ashirin, shima su ware su sa taliya da makaroni da gero da buhun suga in sun gama ina son su fa?awa Juma ta sanar da ni.

Juma ta kalle ni. 'yar nan jiran su zan har su gama kafin in koma ciki?"
Nace kije za su sanar da ke in sun gama.
Tace "Ko da dai bari in tsaya in yi gadi domin kar ace ba wani buhun lissafi ya sha banban." ?ayan ciki yace tsohuwa nan da ki ka ganmu duk ciki babu ?arawo, da sana'ar mu inda halin mu ke nan Hajiya ba za ta ce Alhaji ya turo mu ba, duk shekara mune ke yin wannan aiki. Kuma ko a kasuwa mu ne 'yan dakon kayayyakin Zeena. Tace to naji Allah ya baku ha?uri amma dai ina nan sai kun gama. Na tafi ina dariya. Nace Baba Juma ho!

Ina sako ?afa falon Hajiya naji tana waya dan haka na dawo na tsaya tsam ji nayi tana fa?in. "Saurara kiji Aminiyata, ni dai na gama yanke nawa hukunci kuma dai kinsan dole duk yadda na dama a gidannan dole kowa ya sha shi haka,har yanzu ina kan bakana in yarinyar nan ta fa?i jarabawar nan ba zan ji nauyin sawa a sake ta ba. Duk ba wanda ya san dalilina. Ta?an yi shiru tana sauraron wancan ?angaren sai ta yi murmushi mai sauti. Tace "Ya za 'ayi in da?awa cikina wu?a to kinsan halin kishi watarana ai gora mata zata yi,ban bari ta san maganar Azima ba,ita ma Juma na ja mata kunne shikuwa ai ba yadda zai yi duk da bashi bane ai dole ya aureta a haka. Ina ba so nake kimata ta ragu ba na gama cika baki ta ba?an ?asa a ido ai ba yadda za a yi in fidda wannan zancan. Yanzu tunanin da nake kar inyi tafiyar nan ta ke sa ?afa tana fita ta ?ara ?akko min wata maganar ko iyayen ta fa banbari sun ji maganar ba, na cika baki akanta da yawa sai gashi ta kunyata ni. Abin ya min ciwo da yawa." Ta yi shiru tana sauraro sai tace "Haba Hajiya Zaliha ki na yi kamar baki sanni ba ne, ai ba batun jarabawa akan Azima me zan jaraba kuma baya ta riga ta fa?i warwas na fa?a masa dai ya zauna da ita 'yar uwarsa kuma matar sa, banda a gidana take abinnan ya faru wallahi ke kinsan ni sarai bazan ta?a bari ya aureta ba."
Ta kuma yin shiru can tace Ke kinsan itama akwai maatu?ar wahala ta tsallake ta wannan jarabawar ko ta tsallake komai ba zata iya tsallake ta ?arshe ba, har zuwa yau ni ka?ai na san dalilin jarabawar, shi kuma dole ya sake ta, domin dai shekara guda in suka kwashe kinsan lokacin namiji ya fara gajiya da mace, yadda ya saki sauran ko a jikin sa haka ita ma zai mata. Da?i na ?aya ita ko cikin har yanzu shiru. Amma na kula ita wannan har yanzu bai kawo min ?arar ta ba,duk da hakan baya cikin sharuddan jarabawa ta amma dole in bata makin su." Sai ?aran ?aya wayar ya shigo na ji tace Hajiya Zaliha sai mun sake magana bari in ?aga wata wayar.

Nayi tsam jikina duk ya yi sanyi ba shakka ba zan tsallake tarkon Hajiya ba, gashi ina son mijina tunda shi har zuwa yanzu banda maganar neman matan shi bani da wata matsala da shi. Ba dama in wuce, dole in bari ta ?anyi nisa a wannan wayar, sai in fito kar ta gane cewa ni ?in nayi mata la?e.

Da alamu suna magana da Shamaki ne aka batun tafiyar su,dan haka sai kawai na fito sai da na zo kusa da ita sannan nayi mata sannu, da kai ta amsa na wuce ?akina.

Sukuti na yi a kan gado yanzu zamu rabu da Shamaki da gaske! A fili na furta gaskiya bazan iya ba, ya yi min al?awari ba so ?aya ba, amma ya kamata inke tuna masa da wannan alkawarin da ya ?aukar min akai akai.

Kamar awa ?aya da shigowa ta ?aki na kira shi,ya ?aga na soma ?an kukan shagwa?a yace "Wai me akayi ne kuma zaki ?aga min hankali?" Nace Dan Allah wai zaka sake ni? Yace "Injiwa kuma?"

Nace bacci na yi yanzu sai na yi mafarki wai Hajiya tace sai ka sake ni.

Yace "To na sake ki ?in a cikin mafarkin na ki?" Nace 'a 'a kana ta bata ha?uri ne sai tace me yasa zaka yi mata gardama shine kace ka ?aukar min al?awari tun kafin aurenmu har ka fara tuna mata girman al?awari, shine ta ce ta janye. Sai naji ya sauke ajiyar zuciya,yace ba abinda zai sa in sake ki Baby." Nace Al?awari yace "Al?awari."

Sai kusan ?arfe biyar Juma ta zo tace sun gama na fito naje na gani yadda nace haka suka yi, abin al ajab sai gashi wani abu guda ?aya bai rage ba, wannan ya tabbatar min haka rabon nan ya ke. Nace dube su nace ku menene sallamar ku? Suka ce sai abinda aka bamu. Nace to ku zagaya mu ha?u a gurin Hajiya. Na tsugunna agabanta nace sun gama menene sallamar su? Hajiya ta dube ni, wannan baya cikin huruminki in dai sun gama miki aiki to ki turo min sunan.

Nami?e dai-dai lokacin da suke shigowa.
Su Juma su uku ne mata masu aiki a gida da haka na basu ku?in su sannan na nuna musu kashin da za su ?auka wato mai suga buhu ?aya. Juma tace 'yannan kin gaji Hajiya, wannan shine rabon da Hajiya ta ke bamu kafin zuwan matan Shamaki, insha Allahu zaki lashe jarabawar ki, ke ce mandiya matar gida, jinki ya fi ganin ki,ga ki ?arama sai tarin basira. Ta yi ?asa da murya 'yata saboda jin da?i zan miki wani taimako guda ?aya,kina jina?" Na tattara hankali na gare ta. Tace" ranar ?arshe ta jarabawar ki da baki Hajiya zata yi muku tambayoyi anan duk wata ?ullaliya ta ke, ina son ki tabbatar kin san waye Shamaki kafin wannan rana."

Wannan gudunmawa ta ce nima zuwa gare ki,amma karki tambaye ni waye Shamaki domin bansani ba, kar ki kar ki tambaye ni wanda zai sanar da ke." Na yi shiru ina mamakin irin wannan abu, ni ko lokacin da na yi karance karance ban ta?a dubo irin wannan almarar ba. Tace kin ji mamaki ko? To kar ki tsaya mamaki kiyi ?o?ari ki samu wannan bayani. Ta wuce na bita da kallo a fili nace kai jama'a Ni kuma irin tawa ?addarar ke nan.
Washe gari tun bakwai na fito bayan mun gaisa da Hajiya nace zan fita gurin rabon nan in sake bin sunayen in tabbatar kowa ya samu kashin sa. Tace min, hakan yana da kyau, Juma ta fa?a min abinda aka basu Allah ya saka da alkhari. Na sunkuyar da kai nace Hajiya ku za a yi wa godiya, Allah ya sa a ?auka a gidan Aljanna. Tace "Ameen, amma me yasa ki ka ha?awa su Juma da ku?i? Nace to ni dai a ganina su makusanta ne,kuma duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login