Showing 48001 words to 51000 words out of 51041 words

Chapter 17 - HAMSHAƘIYA-UWA-_3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

05 Jul 2024

6861

karaka ni ance kana da baki. Muka fito yana fada min cewa "Da yawa matan da muke nema awaje ba su kai matanmu na gida komai ba, wata sai ka gama bukatar ka kana kallonta sai kaji duk ranka ya baci." Nace ga zunubi kuna yawo da shi. Daidai lokacin mun sakko kasa bakin da ke jiran shi har kashi biyu, nace masa kawai ka koma bari in tafi. Yace "A a, ya dube su suka gaisa, yace barin raka Madam Ya kalli Hassan yace wanda suka fara zuwa ka kai su sama. Su Hassan suka ce Anty sai anjima. Nace to sai anjima.

Muka fito yace kina cewa in barki ta yaya zan barki a kasuwar nan ba sai wani ya nemi ya miki magana ba, a haka ma ina jin kar wani ya kalle ki.

Haka na isa gida cikin kwanciyar hankali sai gajiya. suna gidan kitso na shantake muna ta hira da Umma nake yi mata zancan gida. Atake ta kira Abba yace ginda yana kasuwa har yanzu sannan kuma na can bayansa shima yana kasuwa mai na gefe ba zai saida ba. Nace to in na koma gida Tac za muyi maganar da shi. Nima nayo kitso da lalle . Umma ta soya wa su Meema gyada mai gishiri sun ce suna so a saya musu su ci, shine ta auno kwano tace sa kwana biyu suna ci.

Tunmuna hanya naji zuciyata natashi nayi mugunci. Muna isa gida kuwa sai amai kamar zan amayar da hanjin cikina.
Kafin washe gari duk na yi zuru zuru. Mukaje Asuibiti da safe bayan gwaje-gwaje aka gano ina da shigar cikin sati daya.

Murna a gurin Shamaki nace kamar ba ga yaran nan muna da su ba. Yace Baby Haihuwa ita ce ribar Soyayya sai dai in ba a samu ba,sai a hakura.
Washe gari ya tashi da azumi a she wai bakance ya yi zai yi azumi bakwai in Allah ya ba ni ciki. Haka muka taru ina jinya yana Azumi, amai kuwa arana sai inyi sau goma. Ban samu dan sauki ba sai da na yi wata biyu.


Ummara da zamutafi har da yara duka Azima ce dai yaki yace ai yaje da ita. Na kada na raya amma yaki. Sannan a wadan da ya biya mawa har da kawaye Hajiya kamar Hajiya Zaliha da kuma wata Hajiya Zainab wadan da ni na bashi shawara. Nace yana da kyau ka girmama 'Yan uwan da kawaye na mahaifiyarka.

Bayan mundawo lafiya na ga kula da riritawa ni da yarana. cikina har ya soma girma lokacin tuni Shamaki ya saye wannan gidan ya hada da na bayan shi aka bige wa su Umma a nan ana ginawa.

Duk da ina da ciki Shamaki bai daina makale min ba, Wai har nafi lokacin da bani da ciki komai a gurin sa. To duk da ina da ciki ban zauna ragwaf ba. Kitso kunshi, gyaran jiki bana wasa tun da na gane shi din dan kwalliya son gayu ne. Abinda na rage sha shine kayan mata, sai irin su zuma kayan marmari da romon farfesu sai madarar shanu.


Cikin haka haihuwa ta riske ni cikin dare, ranar ba a gurina yake ba. Da yake Umma tace min ana yin juyin wata kuma kuma dama Edd dina bai kai ba, dan haka na daure na cije. Aikuwa haka na kwana ina juyi ana kiran sallar farko kan jariri ya danno bashiri na danna lambar Shamaki na dai ji tana ringing ina nishi sai ganin shi na yi da gudu. Ya kamani nace kan jariri ya turo amma ina ganin zan mutune. Yace "A a zaki haihu lafiya bari a kira likitanmu. Ya kira likita ya fada masa cewa kan Baby ya fito. Likita yace a kwantar da ita, rigingine zai turo Nurse . Haka dai likitan ke fadin ga yadda za a yi cikin yardar Allah sai wani nishi ya taho wanda na sa araina cewa mutuwa ce rai na ne zai fita, ina yi ina salati sai wani yunkuri ya zo min na rike Shamaki gam sai fitar da mukaji gaba daya da mahaifa. Lokacin da Nurse ta iso Baby na cikin bargo likita ya gayawa Shamaki yadda zamu yanke cibiyar, du munyi faca faca cikin jini. Nurse tace "Ikon Allah yau naga wata haihuwa a kan gado. To me aka haifa? Muka kalli juna, nace ina ganin mace ce ta zo ta bude ta duba gaban yaron ta ce ai namiji ne. Dasau Shamaki ya ciro shi yana dubawa, yace da gaske ne amma sam bamu lura ba, domin a hoto mace ce. Shamaki ya yi hamdalar godiya ga Allah.

Zuwa Safiya mun yi fes ni da dana. Muna zaune da Azima sai ga Maman Umar da murnar ta, Abban su ya zo. Kafin wani lokacin gida ya cika da dangi har su Ummanaphora. Tawaje na Juma dama ita ce ta wanke min dana nima ta yi min wanka ta gashe ni ras. Harda kuka wai ta so ace Hajiya ta ga wannan rana. Shamaki ya shigo anan dai aka yi wa dan huduba da Aliyu. Ko wa fadi ya ke dan sak Shamaki.

Shima nace baza ayi taron suna ba. Shamaki ya ce sam ai wannan namiji ne ya san cewa Hajiya ma tana can tana tare da farin ciki. Azima tace "Anty na san saboda ni ki ke yi, wallahi ba komai ki bari a yi, tunda haihuwar Safna ai mutuwar Hajiya tana sabuwa.

Haka dai na hakura dan dole na. Aka yi taron suna a Zeena Event Maganar ga yu ko samun wata gudunmawa kauyanci ne. Tunda Shamaki Gayyata ya yi wadda baiyi ba a bikinmu ba. Manyan mutane kuwa ba a magana harda Gwamna mai ci a wannan lokacin. Ranar na kara sanin waye Shamaki a kasar nan. Jariri har da mota ya samu ba a maganar chaki na kudi.

Naci gaba da wankana cikin kwanciyar hankali sai lokacin na soma kiba namurnure na yi kyau. Ina mamaki idan na kalli madubi, na nemi kasusuwana na rasa na zama Hamshakiya matar manya. Shamaki ya taso ni a gaba saina amshi girki ni kuma
Maman Iman ta zigani tace kar in koma sai na gyara jikina. dan haka na dukufa gyara ciki da wajen. Rannan dai ya gaji ya shigo yace "Baby wai saura kwana nawa ki yi arba'in din nan ne? " Nace sati daya jal ya rage. yace "To ranar za a daura min aure nagaji." Na zaro ido tare da fadin wasa ka ke. Yace "Da kamar bazan karba ba, Hajiya Zaliha ta bani yarta Na ima. Nace kana ba'a ne. Yace "Wallahi." Na mike tsaye da sauri. Kuma ka karba ka yarda?" Yace to ke me kika gani? Na taba baki nace ina ruwa na bayan sai da ku ka gama shawara sannan zaka ce me nagani. Na tashi na fice abina.

Ranar na fara yin fushi maitsanai da Shamaki. Dama Azima ce ke da girki dan haka na asali.ban leka dakinsa ba duk da ina zuwa in taya shi wasu Lissafe lissafe. Shima naga ya share ni bai zo ba, nace mu zuba. Ina bacci na yi mafarkin Hajiya ko dan na kwanta da tunanin maganganunta. Wai tazo tana ce min ina rokon ki rike amanar da na baki ki cika all.kawarin da ki ka dauka.
......
Ki yi masa sassauci a hukunci. Da safe abin ya tsaya min a raina. Duk sanshi da Junior daga masallaci sai ya zo ya tashe shi amma yauv bai shigo ba. Bayan yara sun tafi makaranta na je dakin sa. Juma ta kai abin kari Azima tana zuba masa. Muka gaisa da Azima na gashe shi ya amsa amma ko kallo ban ishe shi ba. Na juya ina mamaki wane laifi na yi mai zafi haka.

Washe gari na amshi girki bai dawo gidan ba har tara mutumin da a gida ya ke yin magariba. Dama ranar ban kira shi ba, shima dama ya daina kirana tunda ya fara fushi, muda sai mu yi waya so biyar a rana. Na dauki waya na kira shi ya daga bai yi magana ba. Nace Ina ka tsaya? Yace "Da sakon ki a hannu na ne? Nace E mana kai kanka ai amana ne a gurina maganar aure ce dan Allah ka daina min wadannan dabi'un ka yi aurenka shike nani? Yace "Ba shike nan ba hakkina da aka hani fa? Nace kai da za a daura maka aure me zaka yi da ni? Kawai dai ka dawo gida. Yace ina hanya daga zance nake. Duk daukana wasa ne sai gashi ya tabbatar domin a gaba na ta kira shi tana tambayar ya zo gida lafiya.

Lallai fushi ba nawa bane. Na dake nace ka fadawa Azima domin ita zaka yi wa kishiya ba ni ba. Yace "In fada mata itace zata biya min sadaki? Nace Hakkinta ne ta sani,
yanzu sauran kwana nawa daurin auren? Yace ba a tsaida ba ni dai ina so da wurine sabosa gaskiya a takure nake. Nace Ta kura kamar yaya baga baga Azima ba. Yaja tsaki tare da fadin bana gane mata gaskiya ke kinsani ke kadai ce me maganin matsalata, kin bani mamaki dan kin haihu kike gudu Baby bayan nasan kin warke, banda kullum sai na roki Allah ya yafe miki da yanzu ki na cikin tsinuwar mala'iku."
Nace na gode da ka yafe min.
Yace yauma hakura zanyi kenan? Nace kasan Allah tsoro nake kar in kuma samun ciki domin har al 'adata ta dawo. Yace ki samu mana ke zaki sai min ragon suna? Nace jikina wahalar da zan sha ga baby.
Yaga dai da alamun bazan yarda ba. sai naga ya tashi ya shiga ciki. Jim kadan ya fito sanye da kananan kaya yaki kyau kamar wani matashin saurayi. Ya dauki wayoyi da makullin mota yace " Mu kwana lafiya. Nace bangane ba, har zai yi magana sai kuma ya fasa ya fita. Na tashi da sauri na bishi ya nufi mota. Na dawo na goya Junior na dauki makullin mota ta na dauki wayata da mayafi na fito har ya harba motarsa a gate na nufi tawa na dauka nima na bi bayanshi. Na kalli agogon shadaya na dare. Ina ta binsa na dan bada tazara kar ya ganni har muka isa wani Katafaren gini wanda na tabbata Hotel kafin in karasa ya shige, nima ina zuwa na amshi number na shige. Naje mota ta kusa da tashi. Ina zuwa Reaseption nace akwai wanda na zo gunsa Aliyu yanzu a shigo. Sai naga sun kalli juna. Suka ce ya sunana na fada musu suka rubuta suka ce bari a kira shi a waya. Jim kadan wani ya ce bari ya rakani. Muna kwankwasa kofar ya bude sai ya zaro ido alamun mamaki, yace me ki ka zo yi? Na zata Ashanti ce wadda mukayi waya zata zo ta same ni wai ya ki ke son in ne Baby kin tauye min halas na taho neman haram shime kun biyo n. Nace wacece Ashanti? Yace ki shigo mana. Me ya sa kika fito da wannan daren? Kin zo kin bata min shirina." Hawayen da bansan ko na menene ba suka soma zubowa. Na kwance ya ro na shinfide shi a kan kujera na soma cire kayan jikina ina jifa da su, na cire tas na nufi gadon na kwanta. Yazo ya zauna duk ya gigice. Gaskiya na dauki alhakin Shamaki domin har kuka ya min akan kar in kara yi masa irin wannan horon. Amma fa nima na gayawa yan garinmu. Yarona kuma sai Allah ya dora masa bacci.
sai da Asbashi bacci ya dauke ni. Bai tashe ni ba, cikin bacci na ji ana shamin Mama ashe wai Junior ne ya tashi shine ya zo yana bashi nono. Na tashi da sauri nace banyi wanka ba ba a ba yaro nono jiki da najasa. Yace ban sani ba. Nashiga wanka na fito nayi salla sannan na dauke shi. yace "Baby inje in dakko mana kaya mu dan kwana biyu a nan? Nace kasuwar fa? Yace Hutu zan bata. Nace yarana fa? Yace me zai cinye su? Ga Rahin ga su Juma. Nace to Azima kuma fa ai zamu shiga girkinta. Yace "Kai! Wannan Azima tana takura min fa, Allah ni na kalle shi. sai ya ce "Tom shike nan mu kara kwana daya shike nan? Bani da mafita dole na ce to amma in kaje gidan ka hadani da Juma zanyi mata magana. Yace "Ba damuwa duk yadda ki ka ce haka za ayi." Nace ka fada min kuma wace ce Ashanti? Yace ga ki nan ai nasan zaki biyo ni dama ba wata Ashanti kawai wayo na yi miki." Na yi Murmushi har na ji dadi. Da mota ta ya tafi. Nace kai namiji ma dai sai abarshi. Yana shiga Juma ta tare shi Uban daki na lafiya Ina 'yarnan ta shige ne na juye ruwan zafi bata ba dalilinta dan ma baya nan. Yace gata a waya za ku yi magana. Muka gaisa tace ga ruwan zafi an juye. Nace nayi wata yar tafiya sai gobe zan dawo, ayi komai yadda ya kamata sannan a kula min da yaran nan a lallashe su musamman Anisa yar Mommy na san sai ta yi rigima. Abinda babu a tambayi Azima zan kira ta a waya. Tace to ba komai amma dai lafiya ko? Nace lafiya lau tace to acan za kiyi wankan kinsan haihuwar fari sai an kula.Ya amshi wayar yana fadin Juma wane kuma wanka ai ta gama wanka. Juma ta bishi da kallo baki bude tana fadin ikon Allah Uban daki Haihuwar farice fa lokacin mu arba'in biyu ake yi. Ya shige dakina yana fadin dama Juma ta zigaki ko? Ina dariya nace ba ruwan Baba Juma. Na fada masa duk abinda nake bukata ya dakko min shima ya dakko nashi ya shiga gurin Azima ya fada mata zai yi tafiya. Sanan ya sa Bala direba ya kai shi sai ya bar motata a gida. Haka muka yi gayu cikin kaya masu kyau da yaronmu muka sauka gurin cin abinci na Hotel din muka ci sannan yace mufita. Ni ke tuki shi kuma yana rike da yaro muka yita yawo guraren shakatawa sannanmu kaje gurin cin abincin mutanen kasar Labanon. Sannan mukayi siyayya muka dawo Hotel Muka yi salla muka sha Soyayya muka sake fita. Shamaki yana ta kokarin nuna min irin son daya ke min kuma yana lallashi na da in yarda mu fita kasahen ketare acan ne akwai guraren shakatawa. Nace Zamu fita ka bari sai na yaye wannan yaron don mu barshi a gida. Yace dashi zamuje ke dai ki yarda kawai. Nace mu tafi har Azima da kuma yaranmu. Yace an fasa. Haka dai rayuwa ta ci gaba. Hajiya Zaliha tana ta turo masa yarta. Na gaji nace muje a ne mi auren nan dai ko na huta ni suke ta zagi wai na hana.Yace Baby ke kin sani ke kadai nake so dubi Azima hakuri ta ke yi dadi, dan Allah kada ki kawo maganar wata, nacc barta ta shigo. Rana daya na kwashi yara da shi muka je gidan Hajiya Zalihar. Ta shiga zare ido muka gaisa nace zance muka rako Dady taje yana jiran ta awaje.Mamaki ya kama Hajiya Zaliha da kunya. Na'ima ta fita gunsa muka ta shi muka yi mata sllama muka fita. A mota suke nace ku fito ku bamu guri ko? Suka fito na dura ya'yana muka shige amma kishi hankalina yana gurin su. Na fito nace hirar ta isa haka zo muje na kalle ta nace sai anjima, Shima yace mata sai anjima na tura shi mazaunin direba nace kai zaka tuka yanzu. Ta saki baki tana kallonmu Ni dai tun daga wannan zanca ban sake jin maganar ba. Na san dai na sha tsinuwa.
Su Umma suka tare a gidansu ya keru, na canzawa su Jamila makaranta. Gashi su Umma suna cikin jerin masu zuwa aikin Hajji bana har sun yi passport komai abin shi a wa.

Sai da nayi addu a sannan na dauki tsinken gwajin na shiga bandaki bayan nayi fitsari ciki roba sai na tsoma. Take ya gwada min cewa ina da ciki. Na fashe da kuka sai na fita da gudu zuwa dakin Shamaki. Ya baje yana kallo kwallo, naje fa masa tsiken ina fadin shike nan ka yi min ciki ga jaririn yaro ka huta. Ya tashi da sauri ya rungume ni wai da gaske?Allah na gode maka sai muje gurin likita ya bamu shawara yadda zamu kula da Junior da kuma cikinmu. Na gama mana komai ranar talata jirginmu zai tashi zamuje Istanbul daga can kasashe goma zamuje. Na bude baki zan yi magana ya sa yatsa ya rufe min tare da fadin mun gama magana da Azima ta yarda. Yara zasu koma gidan Maman Umar har mudawo.

Alhamdulillah!
*ALHMDLLH, ALHMDLLH Allah Nagode maka daka bani ikon kammala littafin nan lafiya, Allah ka yafe min kurakuran dake ciki, Allah ka bamu ikon amfani da darussan dake ciki.*

*Masoya makaranta littafin HAMSHAKIYAR UWA Nagode da ha?urin bibiyar labarin da kuka yi, wa?anda na ?atawa a cikin ku ina ro?on su yafe min,?an Adam ajizine amma banida nufin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login