Showing 27001 words to 30000 words out of 51041 words
Chapter 10 - HAMSHAƘIYA-UWA-_3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
na ga bakya kiba sam, har yanzu kina nan firit sai dai fatar ki ta goge kin murje alamu hutu." Nace haka kowa ke cewa, Ummana har cewa ta yi wai ko zan dinga yin madarar waken suya tana saurin gina jiki. Nace mata muna cin abubuwan gina jiki sosai, kila dai ni haka nake. Amma shi fa bai damu da kibar ba, domin bai taba min maganar ba. Tace zan baki wasu kwayoyi na gargajiya ne 'yan waje za su fidda miki shef ki yi kyau. Nace ta bani. Ranar na yini munsha hira irin wadda bamu taba yi ba, na kuma sake fahimtar wasu abubuwa game da su.
Sai karfe hudu na dawo ga turaruka ga kayan gyara na mata duk ta hada ni da su.
Hajiya ta sa anyi girki na musamman ana kiran sallar magriba sai ga Azima ta kwankwaso tare da sallama na gyarawa Hajiya gurin salla. Na amsa Hajiya ta shiga alwala. Azima ta min wani kallo sannan ta kama kujera ta zauna. Hajiya ta fito sai naga ta bi Azima da kallo cikin mamaki . Azima ta sakko ta rusuna ta gaida Hajiya. Ta amsa, sannan tace "Me ki ka zo yi? " Azima Tace shine ya ce wai mutaho bazai iya barina ni kadai a can ba. Hajiya ta kalle ni. Da wutsiyar ido na lura Hajiya ta kalle ni, kila tana son ta ga ya na dauki abin, ni kuwa na yi kamar banji su ba, na kalli Hajiya nace, bari in shiga inyi salla. Hajiya tace "Azima kin gaida 'yar uwar taking? " Azima ta ce mun gaisa. Na yi murmushi lallai yarinyar nan makira ce ko a ina muka gaisa.
Na shiga daki ina tambayar kai na me yasa zai ce ta zo nan? Tsabar ya raina min wayo, dan tsabar sone ko me? Bayan da yana gidan ta hatta Hajiya sai daya daga mata kafa, amma bari muga ikon Allah.
Ban fito ba sai da nayi wanka na saka riga da siket na atamfa na daura dankwali na zubo da gashin kaina a kafada. Ina zuwa sai na samu tana zuba musu abinci. Kamar in juya amma sai na fasa, na shiga na ce sannunku. Duk suka amsa har Azima, sai na kasa zama na nufi kicin duk da cewa babu abinda zan dauka a can din. Juma tana goge goge tace "Uwar dakina wani abin ki ke so? " Nace yau bana jin cin abinci, me zan samu ne mai dan romo? Tace da akwai kayan ciki a freezer ko a dumama ne, kuma naga da kina ta zakwadin cin farar shinkafar nan" . Nace ji nayi kuma duk ta fice min a zuciyata.
Ta dakko ta zuba nace ta barshi haka, tace shima dai ki ce "Dantabawa zaki yi ne kenan? , Ta matso wai kuma me yarinyar nan ta zo yi?" Nace wa fa? Tace Azima mana. " Nace ita da gidansu. Baba Juma tace "Ko gidansu ne ba an aurar da ita ba, ki bi a hankali dai yarinyar nan tana da makirci, nifa ba a banza ki ka ga ina shakkar ta ba, ta iya hada zance taje ta fadawa Hajiya abinda ba a yi ba. Hajiya ta hau kai ta zauna daram. Sai dai in anyi a gabanta. Nace Allah ya kyauta amma ni ban dauki wannan a bakin komai ba, domin ta yi min kadan a kishiya. Juma tace "Na raba ki da wannan tunanin ba karami a kishi zage damtse ki karbi mijinki dan hakin da ka raina shi ke tsole maka ido, amma fa kar ki tsorata, ki fiddo da wannan wayon naki ki yi amfani da shi a matsayin ki na uwargida ki rike kambun ki gam.
Nace ina godiya Baba Juma zan kula. Na fito da kayan ciki a plate, suka bini da kallo, su duka ukun har kaman in tambaya ko lafiya? Amma sai na share na zauna a gurin da nafi zama a kan kafet. Sam ba dadin abinda nake ci nake ji ba, amma bani da yadda zanyi domin bana son su gane halin da nake ciki.
Na maida kaina ga kallo TV amma inzaka yankani bansan me ake fada ba. Hankali na yana kan su, duk sun yi tsit, sai ma na ji zuciyata ta zargi ko dai yi da ni suke yi da nazo suka yi shiru sai karan cokulan abincin su, ita ma Azima sai cin nata take yi.
Na gama Juma ta zo tana tattara kwanuka. Na ce Hajiya zan shafa maki magani da wuri yau domin ina son inyi bacci da wuri. Shamaki ya kalle ni, yau dai kinsan a nan nake." Na kalle shi, har yanzu haushi yake bani, nace Au gashi ban gyara maka dakin ba." Na kalli Azima nace ko zaki gyara masa? Da sauri ta ce" To" Zata mike Hajiya tace "Jimana. " Ta kalli Azima zauna mana." Azima ta kalle Shamaki. Ya ce baki ji me tace ba? " Ta zauna nikam share su na yi, dama latsawa nayi domin da sun barta taje bansan wane irin hali zan samu kaina ba. Hajiya da Shamaki suka kama lissafin kasuwanci su. Na shafawa Hajiya magani sannan nayi musu sallama.
Ina shiga dakin na tsaya ina kallon ta yadda zan fara, domin tun ranar da ya bar gidan ban shiga dakin ba shi kuma yana shiga in ya zo duk ya birkita ko ina. Na gama kwashe kayan wanki na gyara durowa, sannan na koma gado na canza zanin na kunna borna ta turaren wuta. Na fito falo da nufin in tafi daki na, turus na yi ganin su zaune shi da ita a falon....
.....
Wani takaici ya zomin iya wuya, narasa me ya kamata in yi. Na tako ta gabansu zan wuce, yace "Baby zo." Yi nayi kamar banji me yake fadi ba, na wuce har na kai bakin kofa ya taso da sauri, wai ina magana kina jina Baby? " Na kalle shi, nace me zanyi kuma bayan na gama gyara muku gadon.? Yace "Kina da matsala ni ba maganar gyaran gado bace, zanyi magana da ku ne ke da ita, ya kama hannuna muje ki zauna." Ma bishi fuska daure cikan fushi da tsananin kishi. Ya zauna a mazaunin shi da ya taso, ya zaunar da ni kusa da shi,. ta dube ni, ta taba baki. Sai na gyara zama a kusa da shi din, ita dama ta zauna ne akan
Kujerar da ta ke daf da tashi. Ya kalle "Dan jawabi zanyi muku ba mai yawa ba,
Ya kalli Azima yace "Azima da ke zan fara magana, ina son ki sa hankalin ki ki kuma san wacece Baby a gurin ki bana son fitina ki rike ta kamar yayarki., ina nufin ki yi mata biyayya. Ya dube ni, ke kuma hakuri zan baki, ina mai kuma baki hakuri a karo na ba adadi. Nasan cewa ba sai na fada miki cewa ki zaune lafiya da ita ba domin nasan zakiyi haka, Allah ya hada kanku a zauna lafiya. "
Duk da ina jin haushin sa naji dadin jawabin na shi sosai. Har na rage jin haushin sa. Ya sake kallonta "Ki tashi kije ki kwanta kuma in har ki ka sake na ganki online cikin dare ranki zai baci." Ta mike ta nufi hanyar Bedroom, yace "Ina za kije? Kina da gurin kwana anan ne? " Tace Ina zanje to? Yace dakin ki na da mana. " Ta zaro ido ka san haka ne ya baka barni na kwana a gidana ba ka ce sai na biyo ka! Yace "Dan iska ne ni da zan barki ke daya a gidan kimin jaye jaye." Na zaro ido don mamaki ina kallon shi na kalle ta ta turo baki ta fice.
Na kalle shi, kasan ma a'nar abinda ka fada kuwa? Yace na sani mana inhar kin fahimta to nufiana ke nan." Nace Kana zarginta fa kenan.Kuma in har haka ne to ka tafka kuskure, domin an hana zargi a cikin aure. Yace "Ai ba wai maganar zargi bane, zata iya janyo min wani kato gida. " Nace Ta taba kawo wani ne a tsawon kwanakin nan bakwai da ku ka yi? Yace bata kawo kowa ba amma bazan samu kwanciyar hankali ba zan fadawa Hajiya cewa ta bamu Tabawa ko Juma domin a saka mata ido, kin san Allah bana iya fita da wuri, in na fita din ma Allah-Allah nake in koma, sai ina ji a zuciya ta kamar zan samu wani a gidan tunda ita dai ballagaza ce." Yanzu na sake fahimtar cewaLallai kuskure ne babba ki yarda namiji ya rike koda hannun ki kafin aure domin zai tafi yana zargin ki cewa kowa ya zo zaki iya ba shi hannunki ya rike.Ya katse min tunani da fadin. "Menene ki ka yi shiru abinda na fada har zuciyata na fada miki.
" Nace Amma dai Babban bako tsakani da Allah kai ka yaudareta kuka yi ta sharafin ku kai da ita, yanzu kuma sai ka ke zarginta? Yace ta yaya bazan zarge ta ba, kaddara ni nazo nace mata ina son muna fita sai kawai ta yarda mu fita? Ta yaya zuciya ta zata nutsu dan na aureta, da aurena sai wani ya ganta ya taya ta sallama mishi. In kece zaki bini Ko fuskar da zan taba yatsanki ban gani ba lokacin da nake zuwa gurin ki. " Nace to ai ita yarinya ce karama kuma banda haka tana sonka zata so ta faranta maka rai. Yace "To kema ai kina sona sai dai ki kirani ka tambaya ta da gaske zaka aure ni? Ina jin kamar zan mutu in ka fasa aure na." Ya yi maganar cikin kwaikwayon muryata da tsokana. Na dan kai masa dukan wasa ma ina fadin its dai yaudararta kayi. Yace "Ke Lauyar ta ce shike nan amma dai har abada bazan iya bata amana ba tunda taci amanar kanta ma."
Nace itama ai haka taza kalleka a yadda ka ke kallon ta. Ya kamani ya mike tsaye don Allah ki bar maganar ta muje ki biya basukan da ke kanki kema din.
Abin mamaki Shamaki kamar wanda ya dawo daga tafiya, sai kace ba daga gidan amarya ya dawo ba.
Da safe kamar yadda muka saba haka komai ya tafi normal.
Na kuma gane Azima bata da wata martaba a gurin shi dan haka sai na sauke duk wani fushina na rungume mijina. Haka kuma wannan mummunar dabi a ta bibiyar wayar sa na nake yi ban fasa ba, haka kuma ban daina ganin takaici ba, domin har yanzu da neman matan sa.
Zuwa yanzu kuma na gama koyon duk nau'in na girkin da Hajiya ta ke so. Na kuma karbe girkinata a hannun Juma, har nama na fahimci tafi jin dadin nawa, tunda ga su Juma za ta kirani tace in sada mata abu kaza.
Yaran gidan nayi nasarar janyo su zuwa jikina, ta hanyar yin ruwa da tsaki ga bukatun su tare da jure amsar korafinsu da kuma yin sulhu tsakanin su, har ya zama in sun kai wa Hajiya kara zata ce ku tafin gurin Mommy ku.
Haka nan su Juma sun na janye su ta hanyar nuna musu cewa duk daya muke da su, da kuma girmama su.Duk ranar da Shamaki ba ya gidan Azima to fa a dakinta na da zata kwana. Tun ina dariya kunsan halin kishi har na zo ina jin tausayin ta. Domin gaba daya Shamaki baya ganin kima ko darajar 'Azima.
Wata ranar lahadi na shigo falon Hajiya dan zuwa kicin muyi aikin abincin rana, sai na sha mamaki ganin Shamaki turus a gaban Hajiya ga Maman Umar zaune. Na gaida Maman Umar sannan nan na kalli Shamaki ransa a bace yake, Nace sannu da zuwa. Hannu kawai ya daga min. Hajiya kuma bata daina maganar da ta ke yi ba wai dan ganina. Na tsinci tana fadin " Na gama magana ya rage naka gidanka ne kuma matar ka ce duk abinda ka ga dama kuma zaka iya yi amma ni a nan na tsaya. " Na nufi kicin cikin faduwar gaba ko a kaina akeyin maganar na fara lissafi yanzu dai watana shidda a gidan Hajiya bare ince ko wa a dina ne ya iso a mugun yanayi, wato banci nasara ba.
Juma wadda na samu suna kuskus da Tabawa ta kalle ni, tace "Yawwa Uwar dakina, dama dai ina ta fatan ki fito domin kiji wani mugun labari, ni dai ina ganin lokacin barin aikina a gidan nan ya zo. na zaro ido cikin fargaba. Me zai sa ki bar inda ki ke samun abinci Baba Juma? Tace wai gidan yarinyar nan za a maida ni wannan marakunyar Azima. Ni kuma da in koma gurinta gara in hakura da aikin kawai gaba daya. " Nace A a Baba Juma, ki fara zuwa ki ga kamun ludayin zaman Idan kinga ba dama to sai ki zo ki fadawa Hajiya . Tace "To kin kawo shawara kema, zan gwada in gani, amma dai na san wajibi ne ta bata min rai Indai wannan yarinyar ce." Nace Ki kwada haka. Juma ta ce wai wani abu ta ke yi wai shi ko tintam irin na wayar nan ana rawa gashinan malamai suna ta wa''azin abin ba kyau ashe yarinyar nan tana yi. Tun a gidan nan. Hajiya bata sani ba. " Nace Tiktok ki ke nufi? Juma ta ce "Yawwa shifa." Na saki baki wai ina kallon Juma. Hajiya dai ta samu kalubale a gidanta. Ya yi da take ganin wasu ba su iya tarbiyya ba sai gashi
A gidanta karkashin tarbiyyar ta Allah ya jarabce ta. Juma tace wai Maman Umarce ta gani a wayar ta, shine ta zo
ta sanar da Hajiya shine mitin din gaggawa ya tashi, aka kira Shamaki yana kasuwa. Nace Allah ya kyau ta.
Ranar a gurina ya ke dan haka Juma ta hada kayanta ta koma gidan, Shamaki ya je ya amshe wayar Azima ya taho da ita. Ni dai naga waya a kan durowar sa ban yi magana ba. Da kanshi yace "Kinsan wannan wayar? Nace bansan ta ba. Yace "Ta Azima ce. " Nace wata ka canza mata ke nan Allah ya sanya alkhari. Yace,, " In canza mata waya saboda itace wa,? Kinsan yarinyar nan wai Tiktok ta ke yi a she?" Nace Haba dai! Kai to kana ina? Yace "Humm na sha mamaki ta jima tana rawa da waka, a Tiktok ba mu sani ba tunda ba mai lokacin kallon shi s ciknmu, na dai sata dai ta goge, sannan na rufe account din, shine kuma na amshe wayar. An tura mata Juma. Nace Aiiah ya basu zaman lafiya amma da ka barta da wayar ta.
Nikam ina kewar Juma aiki zai mana yawa yanzu. Yace "Na san in Hajiya ta lura dole zata samar da mafita. Nace Allah ya sa angane da wuri sai a hanata. Yace "Wannan yarinyar ce zata hanu, nifa in fada miki yarinyar nan tsoro take bani, tunda akayi auren nan kullum cikin nadama nake. " Nace duk kai ka ja wa kanka da baka tabata ba, na tabbatar Hajiya baza tace sai ka aure ta ba in har baka sonta. Ya shafa kai, Baby ke dai ki bar sharrin shedan, kinsan Allah ni bazance miki ga yadda aka yi ba amma ita takawo kanta har dakina. " Nace Sauran fa? " Yace "Su wa? " Nace kana nufin akanta ka fara Newman mata kuma daga ita baka neman wata? Ya dan daburce, sannan yace ni bana neman kowa." Nace Kaima yanzu kana son yin karya wanda kuma kasan ba al'adar gidannan bace.
Ya ce "To Yanzu da ki ka tsara ni me ki ke son in fada miki ne Baby? "Nace Abinda ke birge ka a jikin matan wanda ni bani da shi. Kasan me ke bani mamaki da kai, in na kalle ka sai inga wai ta yaya ka ke gane mace "yar iska kuma har ka tinkare ta gabanka gadi ki yi magana ku yi ciniki sannan ka dauke ta kuje ku kebe, bakasan ta ba, baka san ko tana dauke da wani ciwo ba, yadda tsaftar jikinta ma take duk baka da tabbaci.
Kunya tasa ya kasa kallo na kuma ya kasa magana. Nace to wai Tun tsawo wane lokacin ka fara irin wannan karfin halin? Cikin tsawa ya ce, "Ke! Har sai da na firgita, yace kina da hankali kuwa? Kin dame ni fa, an fada miki mu ne mike zuwa mucewa mata muna son su? Ni nan da kika ganni mace ce tafara lalata ni, ita ce ta kawo min kanta har na san amfanin mace a gurin da