Showing 12001 words to 15000 words out of 51041 words
Chapter 5 - HAMSHAƘIYA-UWA-_3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
saki murmushi nace Allah ya saka masa da alkhairi, kuma sam bai fa?a ba. Da?i ya lullu?e ni, take wani son shi ya ?aru a zuciya ta.
Tsakar gida muka shinfi?a tabarma aka baje muka zube kayan da na kawo. Abba ya shigo muka gaidasa cikin murna yana ta sawa Shamaki albarka da ni. Yara masu shigo da lemo suka gama Umma ta basu ?ai ?ai suka tafi suna murna.
direba ya tambaya ?arfe nawa zai dawo ? Nace ba sai ya dawo ba Shamakin ne zai zo mu tafi.
Nan Umma ta shiga rabon lemo Jafar da Habu suna mi?awa ma?ota, tana cewa kowa dai ya lasa, domin duk wanda ya ci shi ka?ai tofa shi ka?ai zai mutu. Muka sa dariya. Jamila tace Umma in ka ba wasu tare zaku mutu? Umma tace "Ba haka ake nufi ba, abin nufi shine zaku mutu ne da ladan abinda ka bayar, in kuwa ka ci kai ka?ai tofa babu maganar wani lada da zai bika kabari." Ni kai na sai yanzu na san ma'anar wannan Hausar. Nace gaskiya ne. Allah ya bamu ikon aikata alkhairi. Gidansu Zuhra kuwa sai aka kai katan ?aya. Sai kuma ake ta shigowa godiya, nasan da biyu ne dan a ganni kuma aga me na kawo. Umma dai sai ta koma duk wanda ya shigo sai ta basu cincin da naman da na zo da shi.
Muka baje munata hira ina yi wa Umma mitar su Jamila basu zo min ba. Jamila tace Abba ya hana mu kuma ga aikin gida. Umma Tace "Yaran gidan masu ni?a wa?anda su ka yi miki biki wai sunzo an hana su shiga." Nace basu fa?a muku bane lamba ta kawai duk wanda zai zo zai kar?a, ya kirani ya fa?a min cewa zai zo. Shikenan in fa?awa masu gadi. Duk wanda yazo zasu tambaye shi ne, gun wa kazo ko ka fa?a in sukace tasan zaka zo kace e, to zasu ce ka kirata a waya yanzu zata kira mu. In kuma kace bata sani ba,, kai tsaye zasu ce ka wuce ka tafi hazaka shiga ba. Umma t ace "To in kana da shi ne sai da tsaro rayuwar babu tabbas kana bacci wasu suna yi maka minshari."
Haka dai muka yita hira, sannan na tashi na shiga ma?ota da 'yan uwa muka gaisa tsofaffi da ?ananan yara su na bai wa goron salla ta. Shamaki ya kirani muna ?ofar na'isa ni da Jamila gidan wata ?anwar Abba. Yace sai dare zai zo mu tafi na yi murna. Har hankali na ya tashi ko dai sun shirya da wata ne za su ha?u, sai kuma na tuna yana Azumi. Take na sauke ajiyar zuciya tare da fa?in to sai ka zo. Zan je gidan wasu 'yan uwan mu a Fage. Yace "Dama kuna da 'yan 'uwa a Fage ne?" Nace E mana, ya ce "Shikenan gaida su. Ko in turo miki direba ya kai ku bana son matata a kekenapep?" Nace barshi kawai babban ba?o. Yace 'To don Allah ki ?auki shata karki caku?u da mutane kuma daka kike ke ka?ai wani ya taya min mata ya zata budurwa ce. Nace ni da Jamila ne dama ko ni ?aya ce drop zan ?auka. Muka yi sallama akan sai ya zo. Jamila ta dube ni. Ke kuma ina ki ka samu dangi a Fage? Nace ke dai muje kya gansu.
Gidan gidan sama ne irin tsohon ginin nan na cikin Fage. Muka shiga cikin gidan benan tamkar sai fa?o ?asa, muka yi sallama. Wadda ta zo karbar zakkar nan ce,tana ?o?arin hura gawayi. Ta taso da sauri ta tare mu tana fa?in Hajiya sannunku da zuwa.Muka amsa,tace "Kunzo gurin tsohuwa ne ko?" Nace Gurin ta muka zo. Tace tana sama muje in kai ku?" Muka shiga saman kamar zai fa?o nake ji.
Tana kwance akan wata tsohuwar katifa tayi fale fale cikin tsummuna.sai dai da alamu ana kula da ita in aka yi la'akari da ?akin fes yana ?amshin turaren tsike, sannan kayan jikinta da tsummunan duk suna wanke fes. Ta shimfi?a mana tabarma a gaban tsohuwar tace mata Hajiya ce wadda ta bamu zakka yazo ta gaishe ki. Tsohuwar ta ?an ta?ar?ara ta tashi tana ?an tari ?utul ?utul. Irin na tsufa. Nayi mamakin yadda na ganta a waya kuwa muryar tar kamar matashiya. Nace sannu Kaka. Tace "Sannu yarinya sannu da zuwa, matar Shamakin ce kokuwa dai cikin yayun nasa ne? Domin ba muryar Zeena bace, ina ti?e da muryar Zeena Zeena adon kyawawa maganar cikin ?asaita ta ke yin ta. Tana lafiya dai ko?"
Nace lafiya lau Kaka, matar Shamaki ce ni, na zo in gaishe ki gaisuwar salla, sannan mu?anyi hira irin ta jika da kaka in samu tarihi iyayena su Hajiya Zeena. Jikarta ta yi 'yar dariya tace kun kuwa same shi, domin ko mu radda abin ya motsa muna shan hirar gidan Alhaji Baita. Tsohuwa ta yi kaki ta ?auki wani ?an gwangwani ta tofa a ciki, sannan tace "To yarinya me ki ke son ki sani?" Nace. Hajiya tarihi nake som ji na Hajiya Gwamma. Tace "Allah sarki Duniya labari Gwamma da ke Hajiya uwar Ali Baita. Jikata duk inda ki ke neman mace mai kirki da mutunci in kika samu Gwamma zance ya ?are. Hatta "yan aikin gidan Hajiya Gwamma suna zuwa aikin hajji. Ni nan banje ba,amma mai gidana yaje saboda shine direbanta kuma ita ce ta ha?a aurena da shi. Nace masha Allahu. To kinsan lokacin da aka yi auren Ali Baita kenan? Na tambaye ta. Tace sani kai, a gidan fa muke zaune da mai gidana. Na gyara zama nace ashe kinsan lokacin da aka auro Hajiya Zeena. Tace "?warai kuwa, Ni ce nan aka fara baiwa Zeena a matsayin mai dafa mata abinci, aka maidani kicin ?inta. Jikata ban ta?a ganin soyayya ko jin labarin soyayya irinta Zeena da mijinta Ali Baita ba, kirarin da yake yi mata kullum shine Zeena adon kyawawa. Gata da gayu ban ta?a ganin mace 'yar gayu mai kula da miji tare da tattalinsa kamar wannan baiwar Allah ba.
Ta sake yin ?an tarin ta sannan taci gaba da fa?in "Biyayya kuwa kinga.Ta ?aga yatsun hannunta tana lissafi. Kiga ita ce ke girkawa Hajiya Gwamma abinci daga ranar da likita ya ce ta daina cin farin magi.
Sannan masu aiki a lokacin nan mutum tara ne har ni goma, amma Hajiya Zeena ita ce ke yiwa Hajiya Gwamma gyaran ?aki ta fidda mata kayan wankin ta shirya mata gogaggu a durowar ta. Komai Hajiya Gwamma ta ke so Zeena ta ke yi wa magana.
Zeena ga kyauta dangin Hajiya Gwamma kuwa duk wadda ta zo gidan tamkar ta bata ranta dan nuna ?auna, ko daga ?auye mace ta zo ba ruwan ta zata jata jika ta cika ta da alheri, sannan tana taimakawa mijinta da abinda ya shafi harkokin kasuwanci sa tunda ita ma layin tane. In ta?aice miki cikin hikima da basira da wayo dan tana da dan bazan wayo.
saida ta mallake zuciyar kowa na gidan da ?auna da mutumci ta maida dangin shi tamkar nata. Ta ?an yi shiru tana maida numfashi. Sannan ta ?ora. Rashin samun haihuwa shine ?alubalen Ali da Zeena. Hajiya Gwamma ce ke kwantar musu da hankali tana fa?a musu tsawon shekarun da ta share kafin ta haifi shi Ali.
Cikin haka sai Allah ya amshi rayuwar mahaifin Zeena."
Nace tsohuwa ban katse ki ba,duk wannan labarin lokacin shi Alhaji Baita baya raye?
Tace "Yaushe rabon shi da Duniya a wannan lokacin? Ya rasu tuni Ali ya ci gado mai yawa, ance a yankin nan namu na ba?ar fata in an samu na ?aya to kuwa Ali ne na biyu a dukiya dai." Ta sake numfasawa tace "Kina jin wannan ta?i ko 'yannan Zeena ta rungumi gadon ta cancakat ta dan?awa Ali,shi kuma da ya tashi sai ya gina mata gidajan mai, ai duk gidan mai da kika ga ansaka Shinkafi to na Zeena ne a wancan lokacin ban san yanzu ba.
Sai kuma wani abin mamaki da zan fa?a Miki yanzu. Mutuwar mahaifin Zeena sai ya tona wani sirri wanda shi Ali da Zeena suke ?oyewa . Ashe dai Zeena ba a Budurwa Ali Baita ya aure ta ba." Kuna jina jin wannan zance?" Na kasa magana saboda tsabar mamaki,yaya ma za a yi haka, ko dai tsohuwar nan takanta ya fara juye wa ne?. Hajiya ta ?an fa?a min wani abu daga cikin daren farkonta. Amma sai na yi shiru domin inji ?arshen zance.
Tace duk munsha mamaki a ranar da Ali Baita ya shigo da yara mata guda hu?u ya gabatar da su ga Hajiya Gwamma a matsayin yaran da Zeena ta haifa da wani miji kafin ha?uwar su da Ali.Wai ya ?oye mata ne saboda kar ta hana shi auren Zeena a matsayin shi na saurayi.
Hajiya Gwamma ta girgiza da wannan ba?on lamari harta nuna fushin ta ga Ali da Zeena wadda ta ?oye kanta tun daga ranar da Ali ya kwaso yaran daga Shinkafi.
Hajiya Gwamma ta daina cin abincin da Zeena ke dafa mata, ta fa?awa Uwar gandu da Tabawa tace su fa?awa Zeena ta daina yi mata girki domin ta daina ci.
Ina falon Zeena lokacin da Ali Baita ke lallashin Zeena wadda ta ha?a kayanta da kuma 'ya'yanta tana ro?on ya sawwa?a mata auren shi zata koma Zamfara da yaranta."
Nice na je na fa?awa Hajiya Gwamma halin da a take ciki. Da kanta ta taso zuwa falon ta ce in tafi da yaran sasanta. Zeena ta zube a gaban Hajiya Gwamma tana kuka.
Hajiya Gwamma tace Zeena na yi fushi da ke fushi mai tsanani, ban ta?a tsammanin cewa ?arya ne alaye ne baki ?auke ni a matsayin Uwa ba, sai wannan karon. Kinsani Sunnar gidan nan ce ba a yin ?arya, me yasa ke da Ali ku ka yimin ?arya, me yasa da akayi auren baku zo kun fayyace min komai ba? Kenan ni muguwa ce kuka ?auke ni wadda bansan ina yake min ciwo ba. Bansan ?addara ba,ko da ni bansan r¨¤?a?in soyayya ba lokacin da aka aura ?aura min ubanka amma ai ina jin labarin masoyan ko. Dan haka ni na kar?i yaran zan ri?e su, domin nasan cewa a can ?in suna hannun masu aiki ne da mahaifin ki, kasancewar tun bayan rasuwar mahaifiyar ki bai sake aure ba. Ta girgiza kai, ina son kusani cewa ba ku ka?ai kuka iya shayar da mamaki ba, zan baku nawa kusha yanzu.
Ina son kusan wani abu,duk wata uwa Hamsha?iya bata zama karabiti mai yara da yawa ma bare ni mai ?ara rak." Tsohuwa ta mufasa sannan tace,
Kunsan abinda yasa na nemi guri na zauna bayan na kai yaran sasan Hajiya na dawo? Nace a a. tsohuwa ta ci gaba da fa?in.
Kalaman Hajiya sun firgita ni lokacin da tace. Zeena kin auri Alhaji Uzairu wanda ya kasance shine mai kula da dukiyar mahaifin ki, kuma ya ha?a aure ne saboda yarda da yayi cewa ko bayan ransa zai kula da ku da kuma dukiyar ku.
Bayan ya ga cewa ya same ki, har kin haifa mishi yara sai ya fara shirya yadda zai ga bayan mahaifinki domin ya mallaki dukiyar sa. Asirin sa ya tonu ne lokacin da ?aya daga cikin ma'aikatan da yake tunanin ya ha?a baki da su ya tona shi ya sanar da mahaifin ki abinda ke faruwa kuma ya ro?i kar yasha duk wata fura da wani zai bashi. Dan haka tuni Mahaifin ki ya sanar da jami'an tsaro suka zo cikin farin kaya suka kamashi dumu dumu da furar da ya kawo Office ?in Alhajinki. Bayan bincike an gano cewa guba mai kisan mumm?e aka sawa mahaifin ki wanda zai ?auki tsawon wata uku yana jinya kafin ya mutu.
An kashe auranku a kotu ne lokacin da al?ali ya iza ?eyar shi zuwa gidan kaso.
Ta dubi Zeena wadda ta cika da mamaki tace, duk da ni banyi karatun zamani ba,na tabbata ni ba jahilan bace. Kuma in har Uwa takai uwa dole tasan duk wani shigi da fici na ?anta. Sannan duk tsanani karki yi ?arya tana zubar da kima kuma tana saka aji kunya kamar dai yanzu gashi ke da mijinki.
Hajiya Gwamma zata juya Zeena ta tashi da sauri ta zube a gaban Hajiya tana neman gafara. shima ya zo ya zube. Tace ku ki ro?i Allah gafara. Kunsan wani abu?
Ko masu aikin gidan su dai sunga yara amma basu san yaran Zeena bane ,sai ni da mai gidana wanda shima ni ce na sanar da shi.
Hajiya Gwamma ta yarda da ni matu?a amma duk da haka sai da ta jamin kunne tace matsawar zancan ya fita to kuwa ni ce, dan haka na ja baki na nayi gum. Aka kai yara makaranta da sunan Ali Baita.
Gwamma ita ce ta ri?e yaran nan tamkar kakarsu.
An samu tsawon lokaci kafin aka samu cikin Shamaki. Fa?in gatan da Zeena ta samu kanta a ciki ma ai ?auyanci ne a gurin Hajiya Gwamma .
Nace tsohuwa Kina nufin Aliyu Shamaki shine kadai ?an Ali Baita?
Tace ?warai kuwa, duk wata dukiya ta shamaki ce, sai ta Zeena wadda bata fi cikin cokali ba in aka karata da ta Shamaki."
Nace to kuma kin ci gaba da zama da Zeena ne bayan Hajiya Gwamma ta rasu? Tsohuwa tace 'Ai Shamaki bai rufa wata uku ba ciwo suga ya tasarwa Hajiya Gwamma aka fita da ita ?asar waje, ashe dai tafiyar kenan.
Sai gawa aka dawo da ita. Zeena ta yi kuka kamar zata yi me har sai da aka yo mata rubutun dangana tasha sannan ta ha?ura. Ni kuma da suka gina sabon gida za su tashi sai suka saya mana wannan gidan,a wancan lokacin gida irin wannan sai wane da wane muka dawo. Sai saidai muje muyi aiki lokacin mai gidana ya fara tsufa sai aka kawo sabon direba kuma ta canza wasu masu girki domin nima lokacin girma ya fara shiga kuma ga yara amma dai ina zuwa in yini domin tana son ina zauna kusa da ita kasancewar tana da son labarai. Daga baya kuma sai larurar ido ta kamani, sun kashe min ku?i amma haka na rasa idanun, sai na hakura da zuwa, Ali Baita shine ya budewa mai gidan nan kati a nan ?ofar gidan muka ci gaba da ri?e kanmu amma Zakka ta fidda kai da ta azumi baya wuce mu har ya rasu Hajiya Zeena bata dai na ba. Sai shekarun nan ne ma aka canza to Gara wannan karon an baku komai da ake bamu.
To kinji."
Nace Lallai Hajiya Zeena ita ma tana da kirki kamar surukar ta.. Tace "?warai banbanci su ka?an ne, ita wannan Zeena tana da zafi sosai kuma tana da iko da yawa koda dai mako ance sun shafi sarauta acan garin na su."
Na ce me yasa ake kiran Shamaki da wannan sunan mai makon sunan su na gado wato Aliyu?
.......
*Assalamualaikum*
*Naga addu'o'inku game da sace man waya da akayi, nagode??*
Tsohuwa Ta ce bani kofin can insha ruwa, ina Maryama ta zo ta kawo muku ruwan kuma."
Jamila ta ce yanzu muka sharuwa . Tsohuwa tace, , "Nima karambani ne 'yannan, nasani gidan Zeena ko masu aiki basa shan ruwa dan awo sai na roba." Ta daga ta sha sosai har ta dan kware, muka tsaya muna yo mata sannu. Tace "Me ki ke tambaya ne? "Nace game da sunan Shamaki.
Ta ce "Anyi haka. Yadda Zeena ta fada min tace Ya samu sunan ne daga asalin mahaifin su acan Sudan Wato shi Baita shine babban yaron sarki kuma duk babban dan sarki to Shamaki ne kuma yana dai dai da Hakimi. Sai Ana ganin shi taro ne bai dace a bashi Shamaki ba. Ya za a ce Sarki yana ji dashi harma ya kasa boye soyayyar sa, har taja aka fara neman rayuwar sa. Sarki ya kira malamai su yi masa istihara akan wannan matsalar,
baki uku ya hadu daga malamai daban daban akan cewa mafi alkhairi shine ya bar garin domin kuwa taurarinsai masu haske suna nesa. Sannan hadari yana kusa da shi.
Haka suka ba Sarki shawara ya nesanta shi daga garin, ya hada shi da amintattu suka kawo shi kasarnan suka juya suka barshi da guzurin shi." todai . Kinji inda ya samo sunan Shamaki. Ali Bauta da Zeena ai suje can kasar a wata shekara.
Kuma sunga dangin su dawo suna yaba karbar da suka samu haka kuma sun zo a rasuwar Ali Baita
Na Kali Jamila nace kinji kuma. Da alamu dai in zamu kwana ba zan daina jin sabbin abubuwa daga bakin tsohuwar nan ba. Tsohuwa tace "Kwarai kuwa. " Nace to wai Kaka Kina gidan Shamaki ya zama saurayi?
Tace "Yana dan makaranta lokacin da na bar gidan ana zancan za a fiddashi kasar waje." Na kada kai, da alamu dai bata da wata masaniya akan Shamaki sosai.
Nace Na gode Kaka dajin Wannan labari na bude