Showing 21001 words to 24000 words out of 51041 words
Chapter 8 - HAMSHAƘIYA-UWA-_3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
ya lalata rayuwar Azima. Aure za su yi amma yana son ya lallaba ya lalata auren ta hayar kwanciya da ida. Wai shi baya jin kunya ne sam? Wannan ce rana ta farko da na ki fita gurin saka musu abinci domin kowa na gidan haushi yake bani. Na kwanta na rufa.
A falo Hajiya ta kalli agogo "Me yake faruwa matarka bata fito ta zuba mana abin karyawa ba?" Yace Zazzbi ne ya rufe ta bari in zuba mana. Na shiga dakin tana kunshe cikin bargo.
Hajiya ta yi dan murmushi sannan tace Allah sarki, kishi kumallon mata. Dazu nake fada mata maganar aurenku da ya karato shi ne abinda ya sa ta a dumuwa. Shamaki yace Ai da kunrabu da ita baku fada mata ba. Hajiya tace "Ai hakki ne kowa a fita hakin shi, ba zai kyautu a rufe mata ba ba adalci bane. Amma yanzu in abin ya sauka bazata kuklaci kowa ba. Shamaki yace to yanzu ta san kwanakin kenan.? Hajiya tace ta sani harma na bata zabi in tana son komwa gidan da za a kai Azima ne shikenan sai ta koma." Shamaki Yace zai fi kyau ta zauna nan ga ki sannan ga yaran nan suna sun saba da ita.
Hajiya tace zabinta shine adalcin ta, kar ma ka nuna mata kasan munyi wannan zancan bare ka ce zaka bata wata shawara, nace ta yi shawara a gurin da take da aminci. Yace bazan yi maganar ba.
In takaici da bakin ciki suka hadunmin guri daya sai na yi wani dan baccin wahala kafin in samu zuciya ta ta sauka. Dan haka yanzun ma baccin ne. Lokacin da na farka shabiyu ta gota, na tabbatar Shamaki ya fita kasuwa. Na yi wanka sannan na fita falon Hajiya. Hankalinta ya dauku ga TV na zauna ina yi mata sannu. Ta waiwayo ta dube ni. "Kin fito ashe baki hi sadi ba?" Nace lafiyata lau Hajiya bacci ne ya dan sace ni, kuma sai be tashe ni ba ya fita. Hajiya tace baki saba bacci a irin wannan lokacin ba, in ba Zazzbi bane to maganar da zu ki ka sawa zuciyarki damuwa kenan? " Nace Kai haba ta yaya zan damu bayan na sani tuni. Hajiya tace to na dai fada miki run kwanaki karki dagawa kanki hankali akan abinda babu fashi. Yanzu ma sun fita tare da Azima din zai aje ta gidan maman Nana domin za su fara yi mata gyaran jiji. Sun fita tare? Na tambayi Hajiya da sauri, tace "Ayya karki damu fa, wata rana a gidanta zai kwana, ya kamata ki sawa zuciyarki salama. Nace Hajiya kina da tabbacin can sukaje? Ba ina zargi bane amma a kalla su yi aure mai tsarki. Fuskar Hajiya ta canza "Me kike nufi kenan zargi zaki jefa wa auren su? Nace a a ba zargi zanyi ba a yi hakuri. Na tashi na shige daki. Hajiya ta dinga juya maganar Baby, kodai yarinyar nan ta san wani abu ne game da Azima da kuma Shamaki. Ta dakko wayarta ta kira layin Azima, ta daga. Tace kina ina? Tace gidan Maman Nana ta ma fita bata sameta ba. Hajiya tace ina Shamaki?"Azima ta ya wuce kasuwa. Hajiya ta kira Maman Nana suka gaisa tace tana "Kina Vida ne? "Maman Nana tace ina gida Ina jiran Shamaki yace zai kawo Azima gashi har mai bata magungunan ta iso. Hajiya tace suna hanya..
Da sauri ta kira Shamaki tace ka kai kasuwa ne? Ina son Zuma ne. Yace e na kai zaki aiko direba ne ko kuwa har in zan dawo in taho da shi? Tace a bari har in zata dawo. Sai da kira Hassan ta ce Shamaki ya kara so? " Yace a a bai iso ba. Tin saga nan Hajiya ta san akwai matsala.. Ta mike tsaye zumbur kalaman Baby suka fara zuwa mata a kai. Ba ina zargi bane amma a kalla su yi aure mai tsarki! Hajiya ta koma ta zauna ranta ya ba ci. Ta kuma Kiran wayar Shamaki Ya daga tare da fadin an kawo zum.. "Dakatar da wasan kwaikwayon haka. Kar ku sake ku aikata wani abu ka dawo yanzun nan, na san a inda ku ke kuma nasan me kuke shirin aikatawa. Minti shabiyar na baku ku dawo.! " Ta kashe wayar.
????????????
Ni dai a daki in kai mari in kai gwauro na kasa sanin tabbas sun tafi yin shshanci ne lokacin ya yi da ya kamata inyi magana da Shamaki ya sani cewa na fa san me ya ke ciki. Na zauna ina magana ni da kai na. Ina tambayar kai na da wane lokacin ya kama in masa magana? Me ya kamata in fada masa? Kuma a fusace zanje masa ko ta ruwan sanyi?
Wata zuciyar tace duk wata matsala ta duniya ana iya warware ta ne ta hanyar masalaha haka malamin mu ya fadamana. To in har haka ne zan biyo ta hanyar masalaha, kuma zan fada masa na san duk wani abu da yake aikatawa, kuma zamuyi magana da daddare.
Shamaki ya kalli Azima yace an samu matsala. Azima ta aje Jakarta a kan durowar gefen tangamemen gadon dakin Hotel din. Tace me ya faru? Yace Hajiya tace muje yanzu. Azima zaro ido tace na shiga uku Yaya Shamaki ya akayi Hajiya ta gane ne? Shamaki ya ce yadda ta yi ta kiranmu na tabbatar tana son ta fahinci wani abu ne. Azima tace yanzu ya za a yi kenan? Ya ce zuwa zamuyi illar daya ce karyar da muka yi mata. Azima tace ina zargin matarka ko ta san wani abu fa. Ya dube ta da sauri. "So nawa zan fada miki cewa ki daina saka matata a cikin damuwarmu? " Ta yi shiru ya dauki makullin mota ya fice, ta ja tsaki wannan shegiyar matar ta sa natsane ta zan iya kashe ta in har zan samu dama. A mota ta same shi ta shiga. Ta dube shi Yaya Allah ya baka hakuri. Ya dube ta, abinda ki ka iya kenan anjima kuma sai ki sake kiran sunanta, bayan ita da zaki auran mata miji ko kallo baki ishe ta ba. " Tace ai ni ta auran wa mijina. Ya taka wani uban birki zaki fita Yanzun nan a motar nan sai dai ki koma a ta haya.
Azima ta taba baki, babu damar ta yi masa magana tasan akan wannan figigiyar zai iya aikata komai.
Azima ta shiga cikin gida kai tsaye zata wuce sasan su. Hajiya tace zonan. Azima ta dawo kai a kasa tace ki je dakina.
Hajiya ta kulle kofa, tana kallo Azima ki fada min gaskiyar inda ki ka je, ko kuma in kashe ki a nan, iya kacin dai
a sanar cewa kin mutu aje a binne abar banza kowa ya huta. Azima cikin firgici tace, ba inda mukaje mun biya ne ta gurin siyan Icecream zai sayawa yara. Hajiya tadan yi shiru kodai zargin su ta ke yi. Amma dai bari ta kara latsawa. tace "Ba can kuka je ba, har hoton ku an turo min lokacin da ku ke fitowa daga mota ku ka shiga dakin Hotel. Azima ta gigice cikin firgici tace Hajiya Shine wanda yace muje Hotel tun da ya biya sadakina. "Shi wa? "Hajiya ta katseta. Yaya Shamaki mana. Hajiya ta daka mata tsawa "Ki rufe min baki makira, kece wadda ki ka ja ra'ayinsa, bayan na roke shi ya amince ya aureki a haka babu kimar shine sai kin gwada masa cewa ke 'yar barikice.
To me kuka aikata a inda kukaje? Tace zuwanmu ke nan kika kira wallahi namu yi komai ba. Haushi ya sa Hajiya daukar robar turaren wuta ta bugawa Azima a goshi. Har kina iya fada miki min haka kin zubda kanki mara daraja kawai.
Fita ki jira hukunci na. Azima ta dafe goshinta sannan ta fice da sauri. Hajiya ta zauna bakin gado tana maida numfashi ta rasa wane irin tunani ya kamata ta yi. Shamaki yana zaune a falo, duk da karfi irin na Ac amma bai daina zufa ba. Fargaba yake yi, in Hajiya ta fito bai san abinda zai fada mata ba. Fitowar Azima a guje ta nufi dakinta da gudu, Abinda zai sa Hajiya ta shiga dakinta ba a lokacin bacci ba yana da girma. Tana sako kafa falo suka hada ido. Ta juya zuwa daki, baya bukatar sai ta fada masa cewa ya biyota.
Ya aje hula kan kujera ya fada dakin cikin fargaba.
Kafin ya gama gano ina Hajiya take tuni ya ji saukar tafi a kuncinsa dau. Hajiya ta aje masa. Cikin mamaki ya dafe kuncin ya sunkuyar da kai. Yaudai karya ta kare,. Shamaki ya furta a zuciyar sa. Hajiya ta soma magana a hasale. "Nayi mamakin ka sosai Shamaki Na dauka cewa duk wani uzri da nake yi maka zai sa ka gane cewa ina yi maka karane kawai, nasan abinda ka ke ciki nasan kaine ka yiwa Azima ciki. Kuma shiyasa nace kaine zaka aure ta. Taimako daya Allah ya yi maka dana fada maka baka min gardama ba. Wa zan kaiwa ita ka gama kwakuleta.
Nasan kana bin mata meke damunka ne? To ina son ka bude kunne da kyau ka jini. Bayan la'asar za a daura muku aure yau din nan in ya so sai kuje duk inda zakuje.
Sannan matarka ta soma gano cewa kana bin mata, saura ka yi sakaci har ka bata tabbaci. Shamaki ya kasa dago
kai ya kalli Hajiya, kunya ta ishe shi. Tabbas ya kai makura tunda har Hajiya ta sa hannu ta zabga masa mari, abinda bai taba fuskanta ba a iya tsawon rayuwar sa. Hawaye wanda bai san ko na menene ba suka soma kwaranya daga idanun shi, ya zube kasa ya kama kafafunta. Na san cewa a yau na kai ki makura. Ki yafe min insha Allahu bazan sake ba. Ta zauna a bakin gado ita ma ta soma zubar da Hawaye, yau da mahaifinka zai dawo Duniya zai yi bakin cikin ganin ko jin cewa kai dansa daya jal kana aikata laifi irin Zina harda ta cin amana a cikin gida. Kana da dama ta yin mata har hudu kana da karfin rike mace dubu me ka ke lake ne a wajen matan banza? "
Yace na daina Hajiya wallahi naji kunya da yawa, ina yin dana sani sosai.
Ni ina can bansani ba, ya fice. Lokacin da na fito tamkar wani abu bai faru ba domin banga komai ba. Hajiya tana mazau nin ta na yi mata sannu na shiga kicin domin gabatar da abincin rana.
Juma tace "Uwar dakina me yake faruwa a gidan ne? "Nace wani abu ki ka gani? Tace Uban dakina Shamaki yaudai ya fusata Hajiya da rana suka rufe kofa suna tattaunawa, sannan wannan yarinyar Azima sai gata da kuka. Nace Juma bansan komai ba, suda basa gidan? Juma tace "To sundawo nace amma bai shigo gurinmu ba. Tace to bandai sani ba, amma Allah yasa inga Annabi haka yadda na ganshi." Na tsaya ina kallon Juma ta ce, "Hajiya dai cin zarafin su ta yi, domin yadda na ga yarinyar nan kamar ma kuka ta ke yi.
Na sauke ajiyar zuciya kila maganata ta yi tasiri na ayyana a zuciya. Nace ke to ina ruwan ki Juma, kince bakya gulma amma dai kina sa ido. Tace "A a "yannan karki yi min mummunar fahimta.
Bayan an idar da la'asar sai naga kawu ya shigo da wasu maza, da goro da kuma dabino. Na tashi na basu guri ina zaton an saka rana ne.
Da dare na samu Hajiya da Shamaki kamar yadda na saba amma shi kamar yana ta dan dari-dari. Yau Ni kai na ya kasa kallo na. Hajiya tace in shafa mata magani da wuri yau zata sha magani ta kwanta. Nace Hajiya bakijin dadi
ne? Tace yau kam jikina ya yi nauyi zan kwanata da wuri. shima ya yi mata sannu kafin ya dauki carbinta ya bi bayan ta. Na koma dakinsa ina jiran zuwan shi.
Suna shiga Hajiya ta hau gado ta zauna ya dakko mata magani ya mika mata, ta amsa ya bata ruwa ta sha. Ta kalle shi, "Yinin yau da bakin cikin ka na yi shi. Amma na yafe maka, ina son ka roki Allah ya yafe maka. Yace na gode Hajiya insha Allahu zan roke shi kuma har abada na daina.
Tace Allah ya sa haka. Tun lokacin da na fahimci cewa kana bin mata na baka dama ka yi mata hudu kuma bani da zabi ka zabo mace ba ta shi'awa ba wadda ka ke so kuma ka ke kauna. Ka auri yarinyar nan domin kana son ta na tabbatar kana son ta amma me yasa ka ke fita waje neman mata? "
Yace ki yafe ni Hajiya amma ba kamar yadda ki ka zata ba ne. Bani da sauran abin cewa dai amma ina neman yafiyar ki insha Allahu, ban taba jan kunya kamar yau ba a duniya.
Hajiya tace ya wuce, gata can a daki yanzu kam matarka ce duk abinda ku ka ga dama kuje ku yi, sannan ka gyara inda zaka sakara ba wani taron biki da za ayi, na baka sati daya ku tare bana bukatar zama da Azima a gidan nan. Sannan ka sani yin adalci a tsakanin matanka shine abu mafi mahimmaci da ya kamata ka maida hankali a kai.
Yace insha Allahu. Yanzu dai bansan yaya zan fuskaci Baby da maganar auren nan ba. Hajiya tace wannan ya rage na ka, duk a baya ni ce nike fada mata wannan karon sai ka fada mata.
Ta bishi da kallo, banda soyayyar da da uwa wadda Allah ne ya dora min da tuni na fita a sabgarka.
Ka tafi zanyi bacci.
Ya shigo dakin jiki ba karfi Ina kwance ina kallon TV, na bishi da kallo ya cire kayan jikinsa ya fada bandaki. Ya yi wanka ya fito, ina ta share shi wai ni irin ya tambayi dalili sai mu zauna a zube magana, amma sai naga shi bama ta ni yake yi ba. Ya hau gado ta kwanata kamar dai nima share ni ya ke yi. Na kalle shi ina mamaki. Nace ka tashi zamu yi magana dama kai nake jira. Yace a yau ba wata magana da zan yi da zai yiwu da sai kawai ki tafi dakin ki. "
Gaba ya fadi, nace ni kake Kira? " Ya ce to kwanata amma ki min shiru ina son inyi wani nazari ne. Ban kuma magana ba, na tashi na fice daga dakin na nufi daki na.
Na sha kuka a daren naga bazai kaini ba na dauro alwala. Akan sallayar na kwan bayan nayi ta salla na gaji na zame na kama bacci.
Washe gari na nufi gaida Hajiya amma bata falo, lallai akwai damuwa jiya ta kwanta bata jin dadi. Na nufi dakinta. Tana cikin bargo sai fuskar Shamaki yana zaune a bakin gadon yana waya da likita. Na isa na durkusa a bakin gadon nace Hajiya ya jikin tace da sauki bacci na kasa yi a jiya gashi dai har yanzu.. " Nace Allah ya baki lafiya Hajiya. Tace ameen. Likita ya zo jinin Hajiya ya hau da yawa, ya zuba mata allurai a cikin ruwan da ya sa mata. Ba a jima ba bacci ya yi gaba da ita.
Shamaki ya kalle ni fuska ta a daura yace Baby jiya kin yi fushi ko? Na zura mishi ido ya ci gaba. Kiyi hakuri ni kaina ina da magana amma Hajiya bata jin dadi shine dalili. Bari ta samu sauki sai mu y maganar.
??????
A ranar dai Hajiya daki ta yini Shamaki ma sai azahar ya fita kasuwa, ni kuma na yini da Hajiya a daki saboda baccin bai yi tsawo ba ta farka. Na bata fura ta sha, sai kayan marmari da na matsa mata ta ci. Har zuciya ta ji nake kamar in baiwa Hajiya lafiya.
Lokacin shan magani ya yi na bata. Lokacin salla na yi mata alwala ta yi salla tana daga kan gado.
Shamaki kunsan duk minti goma sai ya kira waya ya ji batun jikin.
Yace min ko ya fadawa su maman Umar ne. Nace a a karya daga masu hankali ka barsu. Hajiya da ke kwance tana jin mu sai ta daga. Nace ya fada musu, ta girgiza kai alamun a a.
Umma ta kira ni, nake fada mata jikin Hajiya tace Allah ya sawake, sannan tace akwai wani magani da Abbanmu ya siyo mata lokacin da ta yi wannan haihuwar na hawan mini ne ana sha da zuma taji dadin sa ko ta aiki Jamila ta kawo mana. Nace bari dai in fara tambayarta domin nasan su basu cika bawa maganin gargajiya muhimmanci.
Na fadawa Hajiya tace a kawo mata.
Kwanan Hajiya biyu tana jinya ta murmure ta samu sauki.
Duk bansan an daura auren Azima da Shamaki ba. Sai a rana ta uku. Wadda ta kama juma'a. Shamaki yaje daurin auren wani abokinsu daga can ya dawo gida, nace ai na yi tsammanin
Kasuwa zaka wuce, yace kayan jikina