Showing 30001 words to 33000 words out of 51041 words

Chapter 11 - HAMSHAƘIYA-UWA-_3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

05 Jul 2024

6852

namiji. Zuwa yanzu zan iya kirge miki matan da ni na taba cewa ina son su da kaina.

Dan haka ki daina yimin tambayar da bata shafe ki ba. Nace Allah ya baka hakuri, amma zan baka shawara ka bi a sannu, sannan in har da gaske kana daukar Maman Anisa to ka bawa Hajiya hakuri ku maido auren ku. Na fadi haka ne don in latsa inji gaske ne. Sai naga ya zura min ido, "Ina ki ke jin maganganu haka? " Nace Kana mamaki ko? Ka daina mamaki domin cikin mafarki na ina iyaganin duk wani abu da ake boye min. Na daure fuska tamkar gaske. Ya zura min ido kila yana mamaki ko Kuma bai kama ba. Amma dan abar maganar sai yace "Zan fadawa Hajiya gobe a kai ki a yimiki International passport ban sani ba ko Hajiya zata ce a tafi da ke aikin hajji. Na lura baya son maganar nima sai na barta, nace Allah ya sa ina da rabon zuwa amma Hajiya bata ayyana ni a cikin 'yan wannan shekarar ba.

Wani abin mamaki washegari sai Hajiya ke ce min Shamaki ya bada kujeru goma kamar yadda ya saba a rabawa dangi ina son ki duba ki lissafo min mutum takwas ni da Shamaki mu ne cikon goman." Nace Hajiya don Allah ki taimaka domin ni ba kowa na sani a cikn dangin ku ba.
Tace "Mijinki ya bada su, dan haka duk yadda ki ka yi ba mai cewa don me kuma ke ma ai kina da dangi ga iyaye.

Nace Hajiya in muna raye kuma ina gidan nan shekara me zuwa lokacin na kara sanin abubuwa sai in yi wannan aikin amma yanzu ki yafe min ba jayayya zanyi da ke ba. Na fada cikin zanyi jiki da sanyin murya.

Hajiya tace "Shike nan, ashe Maman Mubina ta fiki kokari tunda har ta iya rabawa tsaf a dangi ta, kuma sukaje lafiya suka dawo lafiya. " Nace Ba damuwa wata shekarar sai in yi idan Allah ya sa hakan za a yi.

Haka dai suka shirya tafiya aikin Hajji ciki harda Azima. Ban damu ba domin Hajiya ta ce a tafi da Azima na ayyana cewa domin hankalin dan ta ya kwanta ne cewa tana kusa da su, bazata janyo masa wani ba kamar yadda ya ke fada. Shi da Hajiya kuwa dama duk shekara bata wuce su. Kafin tafiyar su nan ma aka sake wata diramar, an kawo ragunan layya, Hajiya ta ta sani wai in raba raguna, har sai da na kusa kuka ina fada mata bazan iya ba, musamman da na tambaye ta ko wadan da aka baiwa sadakar Azumi za a baiwa tace "A a. Daga baya sai ta ce in zabi na gidan mu. " Nace su kowanne aka ba su, tace lallai saina zaba. Ban ko kalli layin manyan ba na nuna wani dan tsaka tsaki nace to akai musu wannan.

Budar bakinta sai cewa ta yi. "Au ke bazaki zaba ki darje ki zabi narkeke ba irin yadda Maman Meema ta yi ko ki dauki biyu kamar yadda maman Anisa ta yi kuma duk sunci lafiya, iyayen ki
nefa?" Na yi Dan murmushi na kara yadda duk wani motsi mai karfi na gidan Hajiya jarabawa ce. Nace Wannan din ma Allah ya amfana.

Ranar da zasu tafi karfe biyun rana ce zasu wuce, dan bai fita kasuwa ba. Muna kwance a dakinsa ya hanani sakat ina masa mitar me yasa yake yawan damuna. Yace "Baby kullum addu a ta in ganki da ciki ina tsoro kar ki shekara ba ciki Hajiya ta ce kun fadi jarabawa. " Nace dama a cikin gwajin nata harda ciki? Yace "Bansani ba, amma dai ni na zaci haka. Nace duk da bansani ba, amma bana zaton Hajiya zata shiga hurumin Allah domin shine yake da ikon bayarwa kuma bai Bayard ba. Yace "Haka ne, ga shi Azima tana da ciki, Hajiya ta so a barta nace ta yi hakuri mu tasa ta kar ta kama yawonta kafin mudawo. A nan na gane dalilin tafiya da Azima kamar dai yadda na zarge. Wanda da farko har na zarge su da son zuciyar su a farko. Yace zan roko miki Allah ya baki ciki da zarar mundawo." Nace masu albarka zaka rokofa amma, yace "Insha Allahu masu albarka za a samu, na shawo Zam Zam da Laban na ciyo dabinon mai daraja na yo addu'o'i ke kinsan zamu samu 'Dan albarka ko? Nace haka ne. To haka dai suka tafi aka barmin gida amma Juma nan ta dawo saboda aiki harma sai da ta karo mana wasu matan.

Na bigi cikin Juma dan in samu labari. Nace Juma tunda naji ki shiru na san cewa ana zaune lafiya dama shiyasa nace kije dai a gani. Tace "Injiwa ya fada miki so biyu dai ina hada kaya Zan tafi sai tazo tana bani hakuri domin tasan in na tafi zataci gidansu gu Hajiya da shi uban dakina. shine ya sa take dan shakka ta, dan duk radda ya kaini karkiga yadda ya ja mata kunne a gabana, har sai da ta bani tausai."

Nace To ai haka yafi, kuma tunda tana sanshi ya na santa ai baza kiji suna husuma ba, tunda shi tashin hankali ko ba da kai ake yi ba kinsan bashi da dadi. Na fada tare da baza kunne inji me zata ce. Tace "To wani lokacin su yi tsiya wani lokacin kuma su yi dadi, amma fa akwai radda ya yi mata dukan tsiya,. Na zaro ido tare da maimaita fadin duka! Juma tace Nima dai nayi mamaki, domin ban taba gani ya daki mace ba duk matansa na baya." Nace kuma ke baki je ceto ba? Tace Ai bari nai sai da ya lallasa ta sannan naje ceto, ina fadin wannan ba dabi'ar ka bace uban dakina. Yafice yana fadin ki sake min bincike a waya. Ita kuma zan je in bata hakuri sai ta huce a kaina wai infice bata son gulma. Shine nace, a a kinga "yarnan bani ce na kar zomon ba kuma ratayar ma ni ba a bani ba. Na tafi ina dariya.

Nace duka dai Juma Shamaki ne da dukan mace? Tace "Af sai dai kar a kuma. Waya fa ta bincike masa, kin taba ganin mace mai binciken wayar miji ta zauna lafiya? A zuciyata Nace Ai ko bai dake ta ba da ya barta iya ciwon zuciyar abinda zata gani ya ishe ta. A fili nace ummm ai shike nan amma dai magana ta gaskiya wannan bai kai abin duka ba shima. Juma tace Ni kuwa har Allah ya kara nayi mata saboda rainin da ta yi min. "

Haka dai akayi salla ta wuce mahajjata suka shiga dawowa. Ni a sallar banje gida ba, amma su Jamila da wasu 'yan unguwarmu sun zo.
Ranar da zasu dawo munsha aiki, ni sai lokacin na yi gayun sallana, wato kitso da kunshi, sannan nayi dinki. Na yi kyau cikin leshi. Shamaki bai ji nauyin Hajiya da Azima ba ya rungume ni. Yace "Na yi kewar ki Baby. " Nima nace na yi kewar ka Babban bako. Sannan na rungume Hajiya.
Sunci sun sha sannan aka kama hirarraki. Azima tace Juma ta zo su tafi Juma tace sai dare zata zo. Hajiya ta ce min "Mijinki ya shiga ciki amma kina nan. Nace yau ai gidan Azima zai tafi domin ranar da zaku tafi ai yana nan. Hajiya tace "To ai da Azimar aka tafi suna tare ai. Na tashi na shiga dakin yana kwance kan gado yana chatin motsin taba kofata da sallamar tawa sai suka dan tsorata shi alamun rashin gaskiya suka bayyana a fuskarshi.
Ya aje wayar ya tashi zaune, Baby me yasa ki ka ki zuwa kinsan abinda ya shigo da ni. Nace ce ni tsoro ya hani zuwa na yi mafarki na dauki wayar ka ina bincike sai ka kamani shine kamin duka. Ya zaro ido, "Ai bazaki taba daukar min waya bama bare ta kaimu ga haka. "

Na ce Kenan zaka iya dukana in abin ace an daukar maka wayar? Yace Baby waya sirrin mai ita ce, kar ki fara bin al aurar wani, ko Allah baya son kana bin diddigin neman sanin sirrin wani bawansa da ke boye wanda shi bai bayyana ba." Nace haka ne. Ya kama hannu na, Baby ina son ki, ina son mu haihu da ke Baby, na yi ta rokon Allah ya baki ciki duk shekara." Na kwace hannuna ya zaka min wannan addu'ar in Allah ya amsa fa? Yace haka nake fata sai inyi murna, ya amsa addu'a ta." Nace ni kuma in tashan wahalar goyo da ciki? Yace zan taya ki, kuma ga su Mubina za su taya mu. Sai mu karo masu raino mu hada da Rahin. " Na kai mishi dukan wasa tare da fadin dubu nawa zan haifa ne har da lissafin 'yan raino babu adadi? Yace zo in baki amsa. Ranar sai da Shamaki ya shafe min duk wani kokwanto da ke zuciya ta, ta sake amincewa da shi, harma na yarda cewa ni daya ce a zuciyar sa.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, na dan ja baya da duba masa waya sai jifa jifa. Abinda na lura shine bazan iya raba Shamaki da neman mata ba. Kuma tunda yana boye min in tafi a haka.
Dan haka na duka fadawa Allah.
Kwanci tashi har shekara ta gabato, saura sati uku in cika shekara, na zama cikin tunani da yawan addu'a Allah ya zaba min abinda yafi alkhari, sannan na sanar da Umma dan ta tayani da addu'a kuma dan kar suga na dawo gida kwatsam. Shi kanshi Shamaki ya fahimci cewa ina cikin damuwa 'yar kibar da na fara duk na jeme, hakan ya jefa shi cikin damuwa wanda har sai da ya tsarani don jin ba a si. Na fada masa. Yace "Baby Allah ya jarabce ni da son ki, na tabbata in har na kuskura na sake ki Hajiya ce zatafi kowa yin da ta sani, wanda hakan shine zai kawo taje da kanta ta nemo ki. Ya numfasa sannan yace ina son kimin alkwari, ko da Hajiya ta sa na sake ki, karki kula kowa na san zata kawo kanta in taga zan mutu."

Na girgiza kai tare da fadin Aiko sai dai ka mutu, domin ni bazan taba dawo makaba matsawar ka sake ni, sai dai in sonka ya zama ajalina. Na daga yatsana dan manuni, na ce na rantse da girman Ubangijin daya busa min numfashi in har ka sake ni har.... Sai sai naji ya toshe min baki, yana fadin "Bazan sake ki ba Babyna. Karki rantse, ni mijinki ne na har abada, zan san ya zanyi in fahimtar da Hajiya cewa ke din mace ce mai wahalar samu. "

Haka dai muka yita gardama, wannan lamarin ya hana Shamaki sakat shima ya rage bacci ya shiga addu'a Allah ya sa Hajiya ta hakura.

Cikin kwankin Hajiya ta zama cikin yawan damuwa tare da ganawa da lauyoyin su har na fara tunani duk cikin aikin hada sakamako na ne.
Azima ciki yana ta girma har ya fito, amma daga Hajiya har Shamaki banga suna wani marari akan cikin ba.

Mubina ta wayi gari tana irin wannan suman wanda yara ke ayi a yananyin karshen damina. Aka kwatar ta a Asibiti ni ce a gurinta. Randa muka kwana biyu tana kwance ta tada kai da cinyata tana cin ayaba. Sai ga wata mata ta turo kofa ta shigo da sallama. Na amsa tare da yi mata sannu da zuwa, na nuna mata kujera, ta zauna muka gaisa. Tace baki sanni ba ko? " Kafin in amsa sai naji Mubina ta dago da sauri tace, Anty. Matar ta janyo kujerar ta matso gaban gadon tace Mubina ya jiki? " Take na gane mahaifiyar ta ce, Na daga ta na zaunar suna kallon juna. Ta kamata ta rungume tsam sai hawaye a idon Uwar, nace Allah sarki, ki yi hakuri ai jikin nata da sauki. Tace 'Yar uwa ya mai jikin nace da sauki. Tace kece matar Shamaki? " nace e. Tace "Kin shekara a gidan Shamaki? " Nace A a, saura kwanaki. Tace "Kin haihu? " Nace ban haihu ba. Tace ki godewa Allah domin da kin haihu sai kin fi fuskantar tashin hankali da damuwa.
Mutuwa ita kadai ke iya raba da da mahaifi sai kuwa gidan Alhaji Baita. Da ana kawo su hutu yanzu kuma an daina gaba daya. Jiya na yi wani mugun mafarki game da Mubina. Na kira Shamaki da farko bai fada min ba, sai na soma kuka ina fada masa cewar ina son ganin yarinyata, nayi wani mafarki a game da ita, in har na rasata zan bi ba a sin haka. Shine ya fada min wai kuna nan bata da lafiya. " Nace sai hakuri, domin bawa baya tserewa kaddarar sa. Ni kam tuni na yi imani cewa zan bar gidan na saka raina cewa ta ina cika shekara. Tace "Haka zai zo miki da dan sauki, ni dama ba wata soyayya muka yi da shi ba, amma ya iya kalamai ga iya wanka, sannan mutum yana ganin daula, kinsan dole ya rikice rana daya a diro a ce ka fice. " Nace Dama ba wata tambaya da aka ce Hajiya na yi duk karya ce? Tace zata tambaye ki game da wasu abubuwa musamman na rabon zakka da kujerun hajji, kamar ni dama da tace in raba uwa da ubana sune farko sai kannasu, san nan na sirka danginta biyu. To ko banza dai sun meta hazo. Sai kuma ta tambaye ki waye Shamaki. Ni cemata nayi danta ne mana. Saine tace in fice mata. Amma rabani da 'yarnan yafi komai ciwo a gurina. Nace dole zata nemeki bare "ya mace in ta samu gidan mijinta lokacin da zata ke zuwa ina za su sani. Tace "Amma kafin hakan ai an wahala da sauran lokaci. Nace kiyi ta mata addu'a muma ko bana gidan zan kasance mai musu addu'a domin ina so su yarannan dukansu. Tace Na gode ke ma Allah ta baki ko ba a nan ba, ya kula mana da su baki daya. " Nace Ameen muna ta hira tana bani wasu 'yan bayanai, kuma na yi mata alkawarin zan binciko dalilin da yasa aka daina daina kai yaran hutu. Da kyar ta iya tafiya sai da wanda ya kawota ya shigo ya lallasheta. Haka ta barmu cikin jimami.
.....
*HAMSHA?IYAR UWA????*


*NA*


*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*


*????????????Masoya masu jiran littafin HAMSHAKIYAR UWA Complete Document,a yanzun haka ya kammala akwai document din HAMSHAKIYAR UWA Complete game bukata zai iya tura kudi kai tsaye ta wannan account number ?600????*
*0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn*
*Phone 08140004302*


Shamaki ya shigo dakin Asibitin da dare, ya same mu muna hira da Mubina tana bani labarin Antynta yace wacece Antinta. " Nace wai Maman ta, yace to mu hada kaya mutafi an sallame mu". Nace to. Mubina ashe tana rike da maganar sai cewa ta yi, Mommy ba kince zaki tunawa Daddy a kaini gidan Anty ba. " Shamaki yace "Wacece kuma Anty? Nace Mamanta, mana meyasa yanzu aka daina kai su hutu ne? Yace "Uwar Meema ta ja musu, tana fadawa yarinyar abubuwan da basu kamata ba, kuma tana yi mata tambayoyi yarinyar ta zo tana min tambaya a gaban Hajiya Wai Maman ta tace Hajiya tana yi musu wasa ko sai fada. Sannan wai in an basu kudi tana boyewa in za a kawo ta sai ta saka a kayanta ta kaiwa maman. Shine Hajiya tace baza a kara kai su ba." Nace gaskiya bata kyauta ba gashi ta sa an shiga hakkin saura, domin su baruwan su, amma ba zai yiwu a kai su sukadai ba. Dakatarwar dai shine abinda ya dace a yanzu ha na har abada ba. .

Muka isa gida Hajiya tana kwance a gurin da take salla, ban taba ganin ta kwanta a gurin ba, na isa na zauna kusa da its nace Hajiya lafiya kuwa naga kin kwanta. Ta tashi zaune fuskar ta ta fada. Nace bakya jin dadi ko? Tace bana jin dadi amma da sauki. Shamaki ya iso shima ya tsugunna, yace Hajiya tun jiya nace baki da lafiya kin ce a a. Ta yi dan murmushi zazzabi ne kuma na samu sauki, karfine kawai bani da shi. Muka yi mata sannu, ya zauna ni kuma na shiga ciki dan in watsa ruwa.

Satin da Zan cika shekara Shamaki ya sanar da ni cewa zai tafi China daga can zashi Dubai. Kuma gaba daya tafiyar sati biyu zai yi. Nace to in ka tafi gashi saura kwana shida in cika shekara to kuma in banci jarabawa ba, yaya za ayi baka nan? Yace "Yadda za ayi ke nan ta yi hakuri domin haka na kirkiri wannan tafiyar sai dai na yi mamaki da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login