Showing 42001 words to 45000 words out of 51041 words
Chapter 15 - HAMSHAƘIYA-UWA-_3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
kunna haske ya gauraye dakin ya shiga bandaki ya dauro alwalla bai san me ya sa zuciyar shi duk yaji babu dadi ba. Ya tafi kan dardumar Hajiya da ta ke yin sallar dare ya tada sallar raka a ta 'i nil fijir. Ya, na zaune yana tasbihi ya jiyo za a tada salla, ya mike ya nufi fita zuwa masallaci. Kamar ance ya kalli kan madubin Hajiya. Wayoyinta guda ukun duk suna kan madubi. Gabanshi ya fadi, yace wai Hajiya manta wayoyinta ta yi ko ya abin yake? Ya sa hannu ya dauka ya kunna duk suka kunnu, amma abin alajabi duk ba komai an goge komai, sannan kuma babu layikan a ciki. Kamar dai ba a taba amfani da su ba.
Jikin sa ya hau rawa ya aje su ya nufi masallaci jin ana sujjada. Suka idar ya fito da sauri sam baiji maganar da liman ke masa ba. Ya nufi dakin Hajiya ya kuma daukan wayoyin, me kuma haka ke nufi. Ya nufi dakin shi ya dauki waya ya kuma kiran duk layikan su Hajiya a kashe. Sannan ya nufi dakin Baby ko ita ma ta bar wayarta. Ya duba bai ga komai ba, ya fito ya nufi falo yana kiran wayar Maman Umar. Ta daga a firgice domin ta rasa abinda ya sa bata da kwanciyar hankali a ciki kwanakin nan. Ko sallama baiyi ya yace Maman Umar wayoyin Hajiya na gani duka ukun an share komai na ciki kuma babu layukan. Gabanta ya fadi, tace to me hakan ke nufi? Yace bani da wata basirar da zan gane haka. Tace Kaje ka duba ko zakaga sim din, in zanje kai yara makarantar sai in biyo.
Ya je yana duba kan gado. Yana daga bargo sai ga wasu takardu guda biyar. Ya kai hannu jikin shi yana bari ya dauki guda daya. Ya ga an rubuta Aisha. Ya kuma dakko wata ya duba yaga Maryam. Kanshi ya kulle, waye kuma masu sunan nan? Ya manta da batun sunan 'yan 'uwansa kenan. Sai da ya kuma dakko wadda aka rubuta Aliyuna. Sannan ya fuskanta.
Ya zauna a bakin gadon ya warware takardar cikin sauri da rawar jiki ya soma karantawa kamar haka....
Dana Aliyu nasan lokacin da zaka samu wannan takardar kasa ta jima da rufe idona, ko kuma numfashina ya jima da tsayawa. Ka yafe ni Aliyu na zabi in nesanta kaina daga gareku, ina auna yadda zakuji in kuka ga na mutu a gabanku, na tabbatar baza ku manta da wannan ranar ba. Ina son ka rike Baby da amana duk wata damuwarka ka sameta kubtattauna, na yaba da halayenta, itace matar da na sa ka saki mataye uku saboda sa ran zuwanta. Ina fata zakaci gaba da yin dukkan wani taimako domin dauka a taskar Allah. Na yafe maka dukkan wani laifi wanda ka yi min a cikin sani ko akasin haka. Ina son ka yafe min kuma ka ci gaba da yi mini addu'a domin ita na fi bukata. In kunga wayoyin na to ku saka su a gadon ku na goge komai na ciki na kuma zubar da layukan, duk wata mamba mai amfani na kwashe muku su a cikin wani karamin littafi yana durowa. Sauran bayani zaka samu a gurin matar ka. Sai mun hadu a darrussalam!!! Yasa hannu a wani jirwaye wanda ya tabbatar jirwayen hawayen Hajiya ne.
Ya mike da sauri yana fadin Innalillahi wa inna ilaihirraji un.!! Maganar nan ba gaskiya bane! ! Juma!!! Ya shiga kwala mata kira da karfi.
Da gudu Juma ta fito daga kicin ya kama hannuwan ta da karfi ya jijjiga ya ce, "Wai Hajiyata ce tabar wasiyyar mutuwa! Ina Wayata. Ya koma dakin Hajiya da gudu ya dakko wayar shi numfashin sa na fita da karfi. Ya danna lambar wayar Maman Umar. Tana dagawa sai kawai ya fa she da kuka. A razane ta ce Menene! Yace Hajiya ta! ta! sai ya saki wayar kawai ya zube gwiwoyinsa a kasa ba zai iya furta cewa Hajiya ta mutu ba. Juma wadda tafita da gudu tana kiran masu aikin gidan maza tana cewa su zo ba lafiya sun samu Shamaki yana kuka sosai ya durkushe a kasa.
Kafin minti talatin Gidan Hajiya ya cika da ahalinta, ba wanda ke iya rarrshin wani a cikin 'ya'yanta, kowa yana rike da takardar wasiyyar da ta bar musu. Maman Umar itace mai karfin halin bin hanyoyin da za su sami tabbacin halin da ake ciki.
Ni kuwa ina nan , banyi barci ba, inma ya dan sace ni, kadan sai na farka sai na kira sunanta, sai ta amsa. Karshe dai na tashi nayi alwalla zan tada salla sai naji muryar ta tana cewa lokacin salla ya yi ne? Nace a a ina son inyi salla in fadawa Allah ya baki lafiya da nisan kwana. Ta ya fito ni da hannu naje, tace zan sake neman alfarma. Nace To Tace "Dan Allah in Shamaki ya yi miki laifi dan Allah in zaki masa hukunci ki tausaya ki tuna da ni ki yi masa rangwanme. Hawaye suka sakko mata. Na ce Hajiya na fahimci kaunarki da Shamaki insha Allah zai baki sauki. Tace je kiyi salla ki roka min sassauci a gurin Allah. Na juya na tada salla zuwa yanzu bana iya kuka sai dai suyar zuciya. Na kasa ci ko ruwa na kurba sai inji daci.
Lokaci da na idar bacci ya dauketa domin ina jin numfashinta da karfi ya koma. Na ji dadi bacci ya dauke ta. Da safe likita ya shigo, muka gaisa ya tambayi jiki lokacin ya nufi gurinta, sai naga ya firgita, ya dakko jakar da ya zo da ita ya bude ya ciro wata allura ya hada ya yi mata. Ya daga wayar sa ya kira yana Indianci. Ba jimawa kuma sai naji motar Asibiti. Haka muka tafi asibitin ina jin zuciya ta kamar ta fado kasa. Likitoci suna ta kai kawo an hana ni shiga dakin amma ina kallo window. Cikin dare Hajiya rai ya yi halinsa. Ashe bacci da nake zaton ta yi ta shiga doguwar suma ne.
Likitan ya maida ni wannan gidan ya fada min za su adana gawar Hajiya sannan zai kira lambar da Hajiya ta bashi tace ya kira in ta cika a kira a sanar musu.
Cikin wannan jimamin aka kira Shamaki aka sanar da shi rasuwar Hajiya. Ta fiyar ba shiri ta tashi dan haka Shamaki da mazan yayin shi guda biyu suka tafi domin taho da gawar Hajiya.
Gidan likitan ya kai ni domin ba zan iya zama a wannan katon gidan ba, na kasa ci na kasa sha kuma na kasa kuka, ajiyar zuciya kawai nake yi iyalan likitan suna ta faman lallashina. Duk da banajin yarensu. Dole likitan ya daura min ruwa saboda na Ki cin komai. Shamaki kawai nake son gani.....
......
Bacci ya fara fizagata sai naji an dafa goshina, da sauri na bude ido. Shamaki ne, yana tsaye. Na tashi da sauri ina kallon shi kamar wadda na warke makanta duk ya fita a hajjacin shi. Zanyi kuka sai na tuna da muryar Hajiya kamar a lokaci tana fadin na baki amanar Shamaki.
Na bude baki zan yi masa magana, sai kuka ya kufce min. Ya zauna a bakin gadon bai iya furta komai ba. Na ce Shamaki mun rasa Hajiya. Ya daga kai, da kyar ya furta ta so muje. Munyi sallama da iyalan likita ya rakamu har mota. Ashe sunje sun kwaso kayanmu a wannan gida.
Lagos muka sauka, daga nan muka wuce Kano. Naga dauriyar Shamaki duk da ko magana baya iyawa sai dai da kai.
Dama anyo mata wanka tun acan na ba su duk wani abu data bada ayi mata amfani da shi kuma sunyi. Gidan ya yi cikar kwari dam da Jama'a haka muka iso Muna shigowa Falon Hajiya aka aje ta.
Na zauna ina kallon yadda yaranta suke zuwa suna yi mata addu'a, na kara tabbatar wa Duniya zancen banza ne, da kudi ko kauna ko dangata ko sanayya suna hana mutuwa da baza a fita da Hajiya daga wannan Hamshakin falon nata ba.
Haka suka gama yi mata addu'a aka fita da ita. 'Ya'yanta suna ji suna gani, Maman Nana har suma ta yi, Maman Iman ta tada aljanu amma haka aka tafi da ita.
Ummana suna gidan su da su Umman Amina, Abba da Abban Zuhra duk da su aka yi jan iza sun dawo daga makabarta su ka kirani muna gaisawa suna min ta aziyya aka ce ga Shamaki can anyi Asibiti da shi ya ki tasowa daga gaban kabarin Hajiya, da aka kamoshi sai ya zube a sume. Da sauri na ce wane Asibitin aka kai shi, sai aka ce wai inyi hakuri maza suje. Nace a a ni sai naje. Maman Umar ta dauke ni a mota muka tafi.
Yana kwance a gadon tamkar mai bacci, nace Maman Umar ya farfadone? Tace "E bacci yake yi. Nace zan jira ya farka, tace inzo muje akwai su Baban Umar a nan din in ya farka sai a dawo da ni.". Nace kuyi hakuri ba taurin kai zan muku ba kubarni na soma kuka ina fadin Hajiya ta bani amanar shi, ta maimaita min har a kalamanta na karshe tsakanina da ita. Dole suka barni suka tafi.
Kamar awa daya, sai ya yi mika da salati ya farka sai kuma ya mike zaune da sauri yana kallona, ya kalli dakin,yace "Baby da gaske ne Hajiya ta rasu? " Na ce Shamaki muyi hakuri Hajiya ta yi kyakykyawan karshe kuma ta tafi tana sa muku albarka. Ba ta bukatar komai sai addu'armu. Ka kwantar da hankali muna yi mata kyakykyawa zato. Yace nifa Baby abinda ya bani mamaki Hajiya lafiya lau take sai dan zazzabi dama ba ke ta kai ba kamar dai yadda muka zata. Nace haka muke kallo. Ashe Hajiya tana dauke da ciwon Cancer tsawon lokaci. Ta fada min cewa tun a lokacin haihuwar ka, kuma ta fada min shekaru biyar baya likitoci suka gano cewa bazata wuce wannan lokacin ba.
Ya soma girgiza kai hawaye suna zuba, yace "Amma me yasa Hajiya zata boye min wannan maganar. " Nace na gamsu da dalilin Hajiya, tacev in ta rasa muku baza ku rayu cikin farin ciki ba, zaku rayu a cikin damuwa da fargaba da lissafi. Ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Allah sarki Hajiyata, shike nan mun rabu, Allah ka sakata a dausayin rahama. Baby ina ganin fa na gama farinciki a Duniya,. " Ya sake fashewa da kuka.
To a haka likita ya same mu. Shamaki yace zamu tafi tunda shi ba wai maganin damuwarshi zai samu a wannan Asibitin ba. Likita ya kada ya raya, aka Shamaki ya kwana a kara duba shi, amma Shamaki ya ki. Gashi ba mota da zamu tafi, ba wanda ya zo da waya cikinmu. Sai likitan ne ya kaimu gida
. Haka aka ci gaba da zaman makoki, na tausayawa, Azima, ga tsohon ciki ga tashin hankalin rashin Hajiya. Aka yi addu'ar uku aka watse, kullum Shamaki a kabarin Hajiya ya ke yini kamar mahaukaci sai an Kamo shi an sako a mota. Abinci kuwa sai na matsawa Shamaki yake iya kurbar dan shayi ko 'yar fura. Yace shifa ba zai iya ci gaba da zama a wannan gidan ba matsawar dai ba Hajiya a cikin shi.
Duk da na sa an dauke kujerar Hajiyar ankai dakinta. A daddafe aka yi bakwai ya sa aka yi feti a wani gidan sa dake Rafin Danana yace can zamu koma. Duk ya birkice kasuwa ma baya fita. Wai in ya dawo wa zai taya shi lissafi nace masa ni ce.
Yace "To ya nake gani game da Azima in zata zauna da mu. Nace kar muyi gaban kanmu ka kira Maman Umar ta kira duk sauran yayinka mu zauna a kira Azima aji ra'ayinta. Yace shikenan tunda Hajiya tace komai inyi shawara dake mu tattauna ai duk yadda ki ka ce haka zanyi.
Aka kira su muka zauna gaba dayanmu aka kirata. Jikinta ya yi sanyi tace tafi son mu zauna tare. Kowa ya ji dadin haka. Maman Iman tace Allah sarki Hajiya ta, yanzu shikenan haka gidan zai ci gaba da zama tarihin gidan ya shafe! "
Shamaki yace "Za a samu ko a dangi a ba wasu aro su zauna matsawar ina gidan nan har in mutu zan rayu a cikin tashin hankali. Aka sa ranar tarewarmu sati biyu da rasuwar Hajiya. Jamila da Zuhra sunzo mana aranar tarewar.
Shima dai gida babbane kowacce da gefenta shima da nasa, a nawa gefen na fidda dakin su Meema da Rahin mai kula da su. Su Tabawa da Juma dakinsu yana kusa da babban kicin. Haka muka dawo wata sabuwar rayuwa mara kan gado, abubuwa duk sun dagule mana sun canza.
Munfi karfin wata biyu ko yatsana Shamaki bai kama ba da sunan auratayya zamu kwanta guri daya muna manne da juna kila kafin muyi bacci sai mun yi maganar Hajiya munsha kuka, ko yaushe maganar shi bata wuce ta Hajiya. Gashi kullum yana hanyar makabarta. Sai da fa Maman Umar ta amso mishi tofi a gurin malamai wandan da suke yi mana saukar kur'ani so biyu a sati.
Sannan aka dan samu ya dangana. Azima ta wayi gari da ciwon nakuda, Shamaki ya kaimu Asibiti, ta sauka lafiya dama tun a hoto ya nuna mace za a haifa. Ita ma dai Zeena ce, amma aka sa mata Safna. Shamaki yace babu taron suna domin shi dai farin cikin shi ya tafi, yanzu kawai yana rayuwa ne kafin tashi mutuwar ta zo. Haka dai ina lallabashi har ya fara fita kasuwa a hankali ya fara warwarewa,
wata safiyar lahadi an tashi da ruwan sama gari ya dauki sanyi ya kara kankame ni muna baccin safe, a kunne ya rada min cewa Baby ina jin kamar shi 'awata ta dawo. Nace to ko zamu gwada mu gani. Yace gaskiya dai. To ranar kwanan Hajiya dari ba uku da rasuwa wata uku da kwana bakwai sannan Shamaki ya iya saduwa. Tun daga ranar kuma sai komai ya soma canzawa. Ina matukar kokarin ganin naji da kowa a cikin dangin nan. Shawara komai Shamaki dani yake yi. Haka nan lissafin dayake ina dan sauraren da Hajiya ina dan fahimta kuma ina taimaka masa a yanzu.
Yara kuwa duk yadda na tsara zan kula da yarana in Allah ya bani haka nake kula da su, Meema ina mu amalantar Azima daidai da yadda nake ganin nayi mata adalci ba nai mata kallon kishiya.haka nan bana bari Shamaki yana hantarar ta kamar da. Ina fada mishi itama amana ce a gurina.
''Yan uwanshi kuwa komai ina shawara da su wanda ya shafi su sani, abinda kuma ba hurumin su ba, ni da Shamaki zamu kashe shi mu rufe.
Bana bukatar sai an fada min Shamaki ya daina neman mata, domin mutuwar Hajiya ta saka Shamaki a tashin hankali ya kuma hankalta, macen sunna ma sai da ya manta yadda zai kusance ta bare ta banza.
Sai dai sannu a hankali sai naga ya shiga wani yanayi na damuwa, sannan yakan kebe yana waya in ya ganni sai ya maza ya kashe, wani lokacin sai inga ya zuba tagumi. Na tambaye shi in da wata damuwa ya fada min amma yace shi dai babu komai. Araina nece Dan Adam yana da mantuwa bari dai in sake caje wayar bawan Allah nan na gano ko ya koma ruwa ne.
Sakna naga an rubuta a lambar da suka yi chat, nabi chat din na karanta.
Sanka ta fara da yi masa ta a ziyyar Mahifiyarsa, sanna ta ce masa "Dama jira nayi ka dawo cikin hankalinka daga mayen mutuwar mahaifiyar ka. Zan turo maka wani Video ka daure ka kalla in yaso sai ka nemeni in kana da magana.
Sai kuwa ga Video Na bude. Na girgiza sosai har na saki wayar Allah ya sa a kan gado nake zaune bata kai ?asa ba. Jiki na bari yake na sake dauka ina kallon yadda Shamaki yake haihuwar Uwarsa ga fuskarshi da komai yana saduwa da yarinyar. Na aje masa wayar dama ya fita motsa jiki ne,na koma daki ina tunanin wane mataki ya kamata in dauka domin fidda shi a wannan damuwar. Tunda na duba shi rokonta ya ke yi tare da fada mata cewa ta fadi duk abinda take so zai bata ta goge wannan Video kar matarsa da a halinsa su gani. Ita kuma tace "Ai ba matar ka ba,Duniya ma sai ta gani,dan bayan naturawa matarka sai kuma in tura a Internet.
Sannan tace ita shi take buka?a su ci gaba da soyayya. Shikuma ya fada mata cewa ya dai yin duk wani abu na sabo domin shi ba zai yi abinda za a tada Hajiya ace ta kalli abinda tabari a baya ba.
To ta bashi kwana talatin kodai ya yarda su ci gaba da Soyayya ko kuma nan da