Showing 6001 words to 9000 words out of 51041 words
Chapter 3 - HAMSHAƘIYA-UWA-_3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
da ana biyan su hidimar da suke mana an so ka fara zakka da makusantan ka,sannan ka kyutata musu shine kawai dalilina. Tace "Allah ya amsa." Nace Ameen.
Haka mutane suka yi ta zuwa kujera na saka na zauna duk wanda ya kira waya sai ince ya shigo ya fa?i suna da lambar waya,kafin ya ?auka kuma zaije ya yi wa Hajiya godiya a falo wannan shima tsari na ne.Direba kuwa ya kai na bashi na Liman da na Kawu, kuma bayan ya dawo na kirasu su suka tabbatar min da cewa an basu wannan ku?i. Na ce to su kira Hajiya su yi mata godiya.
Rabo dai bai tashi ba sai ranar Litinin muka gama, matar da tsohuwar nan ta turo tace min dan Allah tana son ganin matar Shamaki, sai na tuna ni nace ta neme ni. Na tambaye ta unguwar su tace min a Fage suke ta min kwatance na yi godiya muka yi sallama. Bayan ta kwashi kayan ta.
Bayan an gama komai kashi uku ya rage biyu masu ku?i ?aya mara ku?i na samu Hajiya na sanar mata cewa ga kashi uku ya rage kashi ?ari kuma kowa ya ?auka ga jerin sunayen su da lambobin su da kuma saka hannun su cewa sun amsa.
Na bata tsohon list ?in da ta bani da sabon da na yi da sauran ku?in dubu ?ari biyu. Tace "Iyayen ki fa kin ba su?" Nace ai ba sunan su a list. Tunda kuwa basu ai maganar ba su bata taso ba. Hajiya tace to wannan uku sai ki ba su shine dama na su. Na sake dur?usawa ina godiya,nace to sai a baiwa Ya'yan Abban mu ?aya shima Abban mu ?aya,?aya sai a baiwa dangin Umma su raba hakan ya yi?" Tace duk yadda kika yi dai dai ne ni bansan 'yan uwanku ba.
Na kira Umma ina murna na fa?a mata.nace Umma an gama rabo lafiya,ga naku ya za ayi rabon na fa?a mata niyya ta. Tace ba haka za a yi ba, shi Abbanku ya hi ?au ?aya,?ayan Abban zuhra ya ?auki kayan abinci ku?in kai Annan ku ya rabawa sauran ?anan sa, maza da mata kowa ya sheda ya shi albarka, sauran kayan abincin suma 'yan Kurna su sheda. Nace to zan aiko direba gobe duk yadda ku ka yi dai dai ne.
Ranar azumin farko a falon Hajiya muka sha ruwa duk gidan domin a nan muka bi salla dan haka kawai nace Juma ta barmin abinci na a nan,haka su Anisa sun kasance da mu duk da su ba azumin suka yi ba. Azima ana idar da salla ta koma ciki.
Abin ya birge ni banya da muka gama sallar asham na koma ?aki dan in yiwa su Umma sannu da shan ruwa.
Cikin satin Shamaki ya zama cikin yi musu shirin tafiya.
Ana jibi za su tafi Hajiya ta kira ni. Tace min nauyi ya hau kanki na kwanakin da zanyi kafin in dawo, duk wani abu da ake bukata ke zaki samar da shi a gidan nan. Ta ciro ATM kati ta bani,ga wannan katin duk wata hidima ta gidan nan a cikin wannan asusun ake yin sa, yau sha biyar ga watan bature zaki biya dukkan ma'aikatan gidannan ku?in su a ranar ashirin da biyar ga wata. Hidimar salla da abincin salla duk ke zaki samar, haka duk wanda ake ba goron salla zaki bashi, 'yan uwan Shamaki wadda duk bataje Ummara ba,nan zata yini da yaranta. Dan haka ki kula sosai ki mu'amalanci kowa da kyau bana son in dawo in samu wani ?orafi ko da na mutum ?aya ne. Nace To Hajiya insha Allahu zan yi bakin ?o?arina.
Tashin magariba za su yi ranar Shamaki bai fita kasuwa ba, na gama shirya masa komai na tafiya. Yace "Na so ace tare zamu tafi Baby." Nace Allah bai kawo lokacina a yanzu ba, in kaje ka saka ni cikin addu'o'in ka, Allah ya amince inje wata shekarar. Yace haba Baby ai ya amince insha Allahu. Ni addu'a zanyi ina dawo wa in samu in baki cikin Zeena 'yar mitsila." Nace wai kuwa in tambaye ka mana. Yace "Ina jin ki." Nace meyasa duk yaran sunansu ?aya ko Hajiya ce ke za?a musu? Ya kama kunne na ya ri?e da ?arfi har sai da na yi ?an ?ara yace, bansan ko so nawa zan baki wannan amsar ba, amma in na kama kunanki zaki fi ri?ewa, ni na za?a musu wannan sunan in zan haifi yara mata guda ?ari duk sunan su Zeena in kuma maza ne duk sunan su Aliyu." Na ?wace kunne na da?yar, nace na haddace amma fa ka handame da yawa. Kenan bani da damar saka sunan Umma da Abbanmu? Yace baki da hurumin haka, wannan hurumin su Jafar ne." Yin hakan laifi ne? Na jefa masa tambaya cikin harar wasa. Yace Babba ma kuwa amma fa a gurin Shamaki." Nace To Allah ya bamu masu albarka." Yace kinji batu.
Haka dai suka tafi har ina kuka ranar lokacin da zasu wuce. Hajiya tace, "Ba kuka zaki yi masa ba, addu'a zaki yi masa dan ga su Anisa nan bye bye suke yi masa ." Nace Hajiya kewa ce harda ta ku nake yi. Tace "Au to muna godiya. Ashe abin harda mu."
Na dai koma cikin gida bayan sun suka wuce. Ni sabo ne da ni,ko ina naje in zan tafi sai na yi kuka.
Na shiga ?aki na zauna nace ni Baby wai gidan nan a hannu na yake sai yadda na yi da shi. Gashi babu wani cikakken bayani na sosai da Hajiya ta yi min bada ku?in albashin ma'aikata. To kayan sallar ya zan samar da su,? Na mi?e. bari dai in kira Umma inji shawara sannan in samu Ba Juma in kalla?a ta.
Lokacin da zan kwanta na kira Juma na fa?a mata cewa ayi duk yadda aka saba,a bawa kowa abincin asbahi in ba wani abu a yimin magana.
Tace "To Hajiya." Na kalle ta da sauri nace Kul Hajiya ?aya ce a gidan nan bana son in kuma ji...
......
Da safe na kira Umma na ke fa?a mata hali da ake ciki game da gida da aka bar min, tace to ki yi komai tsakanin ki ga Allah sannan wannan katin na ku?i kar ki kuskura ki ta?a ko ficika, duk abinda zakiyi ki ke rubuta an ciri kaza an sai kaza, ko naira hamsin ce ki tabbatar kin rubuta da kwanan wata da komai, domin in ta dawo zata bu?aci kiyi mata bayani, sai kawai ki ?ako ki karanta. Sannan duk wani mai aikin gidan ki ke?e da su ?aya bayan ?aya ki yi masu tambayoyi game da albashin su da kuma abinda ake masu a salla. Yaran nan nashi ki yi musu kayan salla da duk wanda ake yi wa." Nace to Umma sai dai abinda ke damuna wata magana da Juma tamin kwanan baya,tace wai Hajiya zata tambaye ni wanene Shamaki wai kuma in har ban sani ba,na fa?i gwajin ta, to ni da ba Allah musu su gare ni ba,yaya za'a yi in san wani sirri na su na ?oye. Sai dai akwai wata mata a cikin wa?anda ake bawa sadaka da tace sunyi wa kakar Shamaki aiki wato uwar Alhaji Ali Baita, sai naji ina son inda tarihin asalin su,shine na tambayi kwatance sai kuma Juma ta yi min wannan maganar. Umma tace "Iko sai Allah, ni lamarin na ku kamar almara, to ai kuma akwai wata shekara da wani marubuci ya rubuta tarihin Alhaji Ali Baita har aka yi taron lancin na littafin a gidajan Radio aka yi ta sanar wa,me zai hana ki nemi littafin ki karanta,ba za a rasa shi a wannan gidan na ku ba." Amma ki bincika maganar kafin ki nemi littafin amma ba shakka na ji wannan da kunnen na.
Na yi wa Umma godiya sannan na fita domin in tabbatar da komai na tafiya daidai. Kasancewar azumi ne kowa na bacci kuma yaran dama an basu hutu dan haka na ?akko makullin ?akin Mijina na nufi can na tabbatar in har an buga littafin nan to dashi a gidan, in kuma tabbas akwai shi a gidan to ?akin Shamaki yana ?aya daga cikin ?akunan da ya kamata a ganshi.
Ban wani wahala ba na ganshi a cikin wasu littattafai a durowar gefen gadonsa.
WANENE ALHAJI ALI BAITA?
Wannan shine sunan da ke manne a bangon littafin. Na kalli sunan marubucin Aminu Sani Takai.
Na rufe durowar na dawo bakin gado na zauna na bu?a shafin farko an rubuta Babi
na ?aya.
Na fara karanta wa kamar haka..
Alhaji Baita wanda Asalin sunan shi Aliyu ?an asalin ?asar Sudan ne ya shigo Nigeria a lokacin yana matashi ?an ?asa da shekara ashirin,ya zauna a gidan wani malami inda yake karatun ?ur'ani,daga nan sai wani attajiri mai suna Alhaji Sani Aliyu ?an kasuwar kwari ma?ocin Malam ya ?auke shi a matsayin yaron shago bayan Malamin ya nemi alfarmar hakan saboda shi Aliyu ya fa?awa Malam cewa ya na sha'awar kasuwanci.
Alhaji Sani shine ya sawa Aliyu suna Baita saboda irin sunan mahaifin shi ne ba zai iya fa?in sunan sa ba.
Biyayya da gaskiya da amana ita ta sa Alhaji ya maida Baita babban yaron shi wanda ya san dukkan sirrikan shi kasancewar shi duk 'yayan shi mutuwa suke yi sai guda ?aya tak Amina suna kiranta da Gwamma . Saboda ya ?ara ?arfafa zumunci sai ya wanke 'yar shi Gwamma ya bai wa Baita auren ta ya ci gaba da gudanar masa da kasuwanci har tsawon shekaru goma sannan ya fitar da shi ya yi masa sallama wato ya yi masa nasa Katin.
Cikin ikon Allah sai kuma Allah ya sa masa albarka kafin shekaru biyar sunan Baita ke yawo a sassan Najeriya da ma?wafta. Sai dai Allah bai bashi haihuwa ba, ya yi ta neman aure yana yi amma ba wadda ta haihu sai a shekarar su ta sha takwas da aure sai Gwamma ta samu ciki, ta haifi yaro na miji wanda ya ci sunan Aliyu ana kiranshi Ali. Haka ya taso a cikin gata. Allah ya yi wa Alhaji Sani rasuwa mahaifin Gwamma inda ta samu gado mai yawa da ?adarori da ku?i tsaba sai ta bi ta sa sunan ?an ta Ali a matsayin mamallaki dukiyar ta. Shima Ali ya taso da cikin son kasuwanci shima tun kafin ya kai wani mata har sunan Ali ya doke na mahaifinsa Baita sunan Ali Baita ake ji domin shi ya yi karatun zamani.
Wannan ya sa Hajiya Gwamma ta fara tunanin matar da ya kamata Ali ya aure ta saboda mutane sai kyautar 'ya'yansu suke bashi yana cewa baya so.haka kuma Hajiya Gwamma tana bincike a hankali, sannan ta baza malamai suna mata addu'a Allah ya ha?a shi da mata tagari. Ganin yanda idon matan birni ya tsayu aka Ali Baita kuma ya gane dan ku?insa ne sai ya koma in yaga Yarinyar da yake so sai yaje gidansu da shiga irin ta talakawa, amma sai yarinyar ta wula?anta shi, washegari kuma sai ya yi shiga ciki ?asaita yaje a Ali Baitan sa, sai ka ga yarinya ita da iyayen ta sun hau rawar jiki. Shi kuma sai ya zo ya fa?awa Hajiya cewa ya fasa, anyi haka ba bu adadi dan haka ya ha?ura. Wannan ya sa ya ja lokaci bai yi aure ba abin yana damun Hajiya Gwamma har ta hakura kan cewa zuwa yanzu duk wadda ya samo ita ce alkhairi.
A Shekarar 1950 yaje wani taro na 'yan kasuwa na ?asa wanda aka gudanar a jihar Lagos da yaje ya ha?u da wata 'yar kasuwa da ta zo daga jihar Zamfara. Ali Baita ya kamu da son wannan mata bayan sun tattauna hira akan kasuwanci kuma ya fahimci tana da basira da kuma nasibi a harkar kasuwanci sai kawai ya yi mata ta yin soyayya kuma ta amince ya dawo ya fa?a wa mahaifiyar shi Hajiya Gwamma, ta yi murna amma tace sai ta saka anyi mata binciken wacece Zeena Amadu Shinkafi.
Na ?ago kai tare da sauke ajiyar zuciya. Babi na ?aya ya ?are na mi?e naje na ja durowar na maida littafin na nufi ?aki na. Na hau gado na kwanta lamo. Kafin in ci gaba da karatun ina bu?atar in yi nazarin abinda na karanta domin in rike shi kuma in haddace..Yanzu dai naji tushen Shamaki tun daga Kakansa labarin ya fa?o kan mahaifinsa wanda shine dama ake bada tarihinsa ko ince aka rubuta littafin domin minsa. Zai zama dole akwai iya inda labarin zai ?are ba bu cikakken bayani akan Shamaki. Sai dai zanbi labarin a hankali har zuwa inda ya ?are sanna in nemo sauran labarin in ?ora.
Na tashi na fito zuwa kicin na samu su Juma suna ta goge goge. Nace Juma ta min bayanin abinda ake bu?ata na bu?a baki, sannan yara a tabbatar an ba su abinci da wuri tunda basa yin azumi. Ta ce "Dama yanzu nake fa?awa Laure ta ?ora musu Indomie zanje gunki in tambayi abinda za ayi,sai kuma in fa?a miki abinda ake bu?ata. Nace babu damuwa ki sanar da ni yanzu. Kuma tace yau ranar kunun tsamiya ne da ?osai sai farar shinkafa da kayan ciki, sai lemon zo?o sannan akwai fura da kilishi." Nace to duka akwai su ko sai an nemo? Tace Nono ne za ayi waya a kawo. Nace to ina lambar? Tace bani da ita, sai dai ki kira Hajiya ta baki. Nace to na fita na koma falo na duba in da Hajiya ke zama akwai wani ?an littafi da na fahimci tana rubuta lambobi. Na ?auke shi ina dubawa, ?auke ya ke da suna da kuma lambobin waya. Tabbas zan gani tunda ga sunayen masu kaji da nama. Bo?ejo mai nono, take na kira lambar wani namiji ya ?auka muka gaisa yace gidan Alhaji Baita ko? Nace e yace to zan fa?a mata za a kawo ne? Nace E .
?warya ?aya aka kawo nace nawa take bayar wa? Suka ce dubu ishirin nace to ina lambar akawut ?in su, sukace Hajiya na dashi a rubuce. Nace to ba damuwa. Sai lokacin na tuna ai ba amshi lambobin sirrin ba.
Na sake ?akko ?an littafi tabbas ga account ?in su. Lambobin shirin sune matsala yanzu koda na saka direba ya kai ni banki ai babu su, sannan wani ?alubalen ban ta?a zuwa banki ba tunda uwata ta haife ni.
Na shiga kai mari ina kai gauro, ina ganin dai Hajiya tana sane bata bani number ba. Na sake zuwa ?aki na kira Umma na fa?a mata. Tace " Ki samu nutsuwa Baby duk lambobin sirri suna zama na musamman ne, haka kuma zasu kasance ?ayan biyu, kodai wasu daga cikin lambar waya ko kuma ya kasance ranar haihuwa. Zai iya kasance wa ranar haihuwar ?a ko miji, wani abu dai da ba'a manta shi. Nace to, sai dai ya zanyi in gwada.
Nace wa Juma ta fa?awa direba zamu fita zuwa banki. Har na hau mota sai na tuna da Azima na sauka da sauri na cewa direba ina zuwa. Na je na shiga ?akinta. Tana zaune tana kallo. Ta bini da kallo nace Azima zo muje banki mana. Tace Hajiya ta ce kar in sake in fita zuwa wani guri. Na zauna bakin gadon nace kin ta?a zuwa ciro ku?i da Hajiya?
Ta dube ni. Ta sake mai da kanta ga kallon TV kamar ita ce Hajiyar sannan tace, ki duba jikin katin zaki gani. Na kalli katin da kyau banga wani rubutu ba, na mi?a mata nuna min. Ta amsa ta kalla tace wannan ba katin da na sani bane, kije ku duba gurin da take zama, ko kuma ki kira ta mana. Na fita na koma na duba bangani ba. Na kira Shamaki a Video call, ya ?auka suna Madina yace min "Yi ha?uri Baby ina ta son in kira ki in na samu nutsuwa. To ya gidan ya kowa da kowa?" Nace duk muna lafiya . Kaga dama zan tambayi Hajiya ne bata bani lambobin sirri na katin ba, kuna tare ne? gashi masu nono sun kawo za ayi musu Transfer. Yace "Gaskiya ban sani ba,amma tana yawan amfani da 1950 ki gwada ki gani. Sai dai kuma kada ki ce mata ni na baki,domin tsawon shekara ?aya ne bazan shiga wata magana da ke tsakanin ke da Hajiya ba, ?a'idar shi ne in an cika shekara zata bani umarni." Nace Umarnin saki na ko? yace "Bana fatan haka. Ke dai kiyi ta ?o?ari duk da bansan me take dubawa ba ina yi miki kyakkyawan zato. Nace direba zai kai ni banki zan tura ku?i in ciro wasu in aje a gida saboda bu?atar gaggawa. Yace "To amma dai ki sani Hajiya ce zata kar?i alert. Nace Karka damu. Yace ki kula da Azima in tana bukatar wani abu ki mata. Nace ." To. Sannan ban ta?a zuwa banki ba yaya za ayi in gane yadda zanyi amfani da katin? Yace ki samu ma'aikacin gurin gurin guda ?aya sai ya nuna miki, kar ki yarda da kowa fa." Nace to.
Cikin sa a da naje banki ashe ita ce lambar da na fa?awa ma'aikacin. Ya nuna min yadda zan tura ku?i da yadda zan cire da kuma yadda zan duba ragowar ku?in.
Da ya tafin na shiga gurin duba ragowar ku?in ban gane ko nawa bane sai tarin ziro. Na ciri dubu ?ari na koma mota.
Washe gari Rahin ta same ni tace