Showing 33001 words to 36000 words out of 51041 words
Chapter 12 - HAMSHAƘIYA-UWA-_3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
ya kasance bata hana ni ba, kila hakan yana nufin cewa bazata raba mu ba. " Nace kar ka saki jiki akan haka kuma sai ka tafi tace ka turo sakin ta waya. Yace "Wai ke baza ki taba fadi alkhari ba saboda Allah?" Nace to ai bana son in yaudari kai na ne, saboda ko zan tafi dai dama na dangana. Ya rungume ni insha Allahu muna tare har abada, sai naji dumin hawaye a kafatata. Nace dago dasauri, kuka kuma Shamaki? Na fada cikin mamaki. Yace Tunda shekara ta gabato sai ina samun kaina cikin yawan kuka da damuwa, wanda nasan cewa tsoron rabuwa da ke ne. Na sa hannu a fuskar shi ina shafo hawayen nima sai naji nawa sun soma sauka.
Ya tafi ya barni cikin jimami. Ranar da ya tafi da dare wayar cikin gida ta bugs misalin Karfe biyu na tashi na fita. Nasan cewa munyi sallama da Hajiya na kuma shafa mata man zafi.
Na fito
ba kowa a falon Hajiya na nufi dakinta, Tana zaune a tsakiyar gado, na shiga da sauri ina fadin Hajiya lafiya? Tace lafiya kalau zauna. " Na zauna jikina sai kyarma ya ke yi. duk na firgita. Ta kalle ni sosai tace "Me ya ke baki tsoro? " Nace Ba komai na yi tsammanin baki da lafiya ne. Tace lafiya ta kalau kwantar da hankali. Ta kara matsowa, kin kuwa san dalilin da yasa na bar mijinki ya yi tafiya? " Gabana ya yanke ya yi wata muguwar faduwa, nace a a. Tace "Saboda in har yana nan bazai taba barina in yi hukuncin da ya dace ba, saboda son da ku ke yi wa juna wanda ni kadai na san dalilin son. Ina fata kina aje da lissafin kayan azumi wanda ki ka raba, shine zaki gabatar min da lissafin."
Na tashi cikin fargaba naje na dakko takardar na dawo. Nace gata nan. Tace to kowanne zaki fada min dalilin da yasa ki ka bashi abinda ki ka bashi. " Na kalle ta cikin rashin fahimta, naji zuciya ta ta fara zuwa wuya, tana fadin wai gidan nan na Aljanna ne da nake ta fuskantar damuwa da wasu ka idoji? Wata zuciyar ta bani amsa da cewa ba gidan Aljanna bane amma na neman Aljanna ne. Dan haka sai lallashi zuciyata sannan nace ban gane abinda ku ke nufi ba Hajiya.
Tace misali ai kin ba kanina kayan abinci da kudi ko?" Nace E, Tace to fada min dalilin da yasa ki ka bashi. " Nace To gaskiyar magana ni dai na yi la'akari da kusanci, domin musulunci ya nuna mana muhimmanci fara taimako daga kusa kafin kaje nesa. Tace "su Juma fa? " Nace ai na fada muku kwanaki, suma kusancin ne sannan suna yi mana hidima duk da muna biyansu kyautatawa yana da dadi.
Sannan taimako ne. Na numfasa, don Allah Hajiya kar ku tambaye ni dalilin da yasa na baiwa sauran domin ban san su ba. Tace 'To ya akayi kika basu? " Nace nabi layin sunayen ne har zuwa adadin kudin daga nan na fara da wadan da ba kudi, su kuma daya zan iya fada miki wani abu akan su ba, saboda suma layin na bi, sai guda daya wadda itama ta fada min ne da kanta.
Tace "Wa kenan? Nace Wata tsohuwa makauniya. Ta zuba min ido da alamun mamaki a tare da ita, a hankali ta ce "Kinje Fage kenan? "
Gabana ya yanke ya fadi, ba shakka bazan yi wata karya ba, ko da banci jarabawa ba na san dai bazan zargi kai na da kar ya ba. Nace naje Fage Hajiya gurin tsohuwar nan.
Hajiya ta yi shiru tana kallon gefe daya, kamar tana tunanin wani abu. Can ta numfasa sannan tace, "Ban tsammaci cewa kema irin wannan hanyar zaki bi ba, amma dai zan yanke hukunci ne kawai daga abinda kika fada. Ta sakko daga kan gadon ta yi dan tattaki a hankali, ta kai kan wata kujera dake manne a jikin gadon ta zauna, sannan ta ce.
"Jikina ya yi sanyi domin na gama yanke shawara cewa ke ce matar gidan nan, amma sai gashi kuma kin kama hanyar neman jin sirrin da da kin yi hakuri da na fada miki shi daga bakina kuma sahihin labari. Amma zan yi miki uzrin na sauraronki sannan in auna, zan kuma baki makin ki cikin adalci.
Kafin inji abinda ya kai ki gidan tsohuwa da kuma abinda ki ka jiyo da sauran abubuwan da suka biyo baya ina son ki taya ni kallon wannan. "
Ta kunna TV da Remote din hannun ta. Cikin sauri na maida kai na ga kallon TV.
Ba kamar fimba da za a nuna can da can ko sunaye, Hotona ne ya bayyana. Gani lokacin da ake shigo da ni, babu magana hoton ne kawai, ga lokacin da za a kaini daki na, sai kuma ga ni ina neman dakin Shamaki, Sai kuma aga Juma ta nufi dakina da kayan abinci. Sai kuma lafon Shamaki, duk ga shinan lokatan da muka zauna ko muka ci abinci ko wasu dai 'yan wasanni ba masu yawa ba. Haka kuma ga lokacin da Azima ta shigo falon kuma ga lokacin da ta shiga dakin Shamaki. Zuciya ta dauki zafin takaici kamar a lokacin abin yake faruwa. Har na tambayi kai na ina ina a wannan lokacini.
Sannan ga lokacin data fito.
Haka dai muka yi ta kallo, akwai gurare da na yi ta fargabar kar a gani gurin duba wayar Shamaki amma sai da wani guri daya ya fito da na dauka a falon. Sai anan Hajiya ta yi magana idanunta suna kan TV din, tace 'Wannan ba wayar Shamaki bace? " Nima ba tare da na dauke kai ba, nace ita ce. Me kika yi a ciki? Nace duba masa sakwanni na yi. Sai lokacin ta waigo ta kalleni, kina zarginsa ne a lokacin? " Nace kwarai kuwa. Tace me yasa ki ke zargin sa? " Nace akwai wani guri da aka wuce, inda zan shiga dakin na dawo baya har nayi karo da fulawa ya zo yana kirana ban dawo ba, shine dalilin da yasa na binciki wayar sa.
Ta tsada TV din,
Me ya faru a lokacin? " Nace samu yana waya da wata mace wadda ta turo masa hotuna na sassan jikinta, yana yabawa da hotunan, yana fadin wasu kalamai da suke nuna jin dadin kasancewar su da ita. Na juyo da sauri domin bana son ya ganni bare yaji kunya tunda ya san na yarda da shi kuma in wani ya fada min cewa Mijina yana neman mata bazan yarda ba. Kuma sai Allah ya kaddara na ji da kunne na. Garin in gudu karya ganni sai fulawa ta fado shine ya biyoni. Hajiya ta sauke ajiyar zuciya. Tace "sai me ya faru daga nan? " Nace kawai naje nayi kuka ne a daki ban fada masa abinda ya faru ba har zuwa yau? "Me yasa baki fada masa ba? "Hajiya ta katse ni da tambaya. Kila ya musa, domin ban kamashi ido da ido ba, ko ya fusata ya dauki matakin da bai dace ba a cikin borin kunya. Na san cewa ta hanyar tattaunawa ne kadai ake iya warfare matsala.
Shine na fara bincikar wayar sa domin in samu tabbbain abinda naji. Anan na gano yadda suka shirya da wata yarinya zasu hadu a wani Hotal a ranar wata lahadi. Hajiya tace "To na fahimci cewa lahadin da ki ka yi karyar ciwo ce domin kar ya fita." Na jima ina tunanin dalilin wannan karyar. Na.
Ce yawwa haka ne, sai kuma ciwon duba wayar ya kamani wanda kullum na duba sai na ci karo da sabon bakin ciki wanda sai dai in shiga daki insha kuka na. Hajiya ta dube ni, ta girgiza kai, sannan tace "Wane matakin ki ka dau ka". Nace fatan shiriya nake ta yi masa a gurin Allah, kuma dai har zuwa lokacin da ya yi wa Azima ciki ina cike da tashin hankali game da zaman mu. Zubur Hajiya ta mike tsaye, ta tsura min ido, "Da wane lokacin ya yi wa Azima ciki.? "A raina nace kaji wani raining wayo. Sai nace. Ban san da wane lokaci bane amma doke zai zama a cikin lokutan da take zuwa dakin shi ne ko suke fita, bana zaton cewa ko su zasu iya sanin lokacin. Hajiya tace "Ke nan kinsan tana zuwa to kina matar shi ke kina ina? Nace Hajiya bansan tsawon lokacin da suka dauka suna yin abin su ba. Kilama kafin in zo ne, haka kuma ai suna fita Hotel kamar dai yadda ki ka datse yin hakan ta hanyar daura musu auren gaggawa. Hajiya ta zauna a bakin gado, sannan ta kure ni da kallo. "Wane kokari ki ke yi zuwa yanzu domin ganin ya bar duk wadannan dabi u.? " Na ce zuwa yanzu ya san na san komai, ban yi rigima da shi akan haka ba, kuma na fahimci Allah ne kawai zai rabashi da haka, saboda haka shi nake fadawa, ina saran zai shirya shi lokaci daya. Sannan ina kokari fita hakkin shi yadda ba zai zama cikin bukata ba sai dai wani abu na sharrin shaidan.
Hajiya ta kada kai cikin gamsuwa. Sannan tace, bazaki nemo wani taimako ba ga masana domin hana shi aikata duk irin wannan biye biyen? " Nace Hajiya Allah shine mafi girman mai bada taimako nasan zai yi haka, sannan bazan tauye shiba in yana da bukatar sake aure fa tunda na karanta a wani group cewa maganin hana maza su nemi mata wani sihiri ne sai dai su tsaya ga ke kadai in sunje gurin wata baza su iya yin komai da ira ba. Hajiya ta ce je ki hau gadonki ki kwanta zamu dora gobe,. Saura kwana uku jara bawarki. Kin yi kokari sauran tun a text suka fadi,. Na kalle ta, ba wannan ce Jarabawar ba? Tayi murmushi Ai kin san kafin Jarabawa ana yi Text ko? Ban iya amsawa ba har sai da na kai kofar fita na waiwayo nace sai da safe. A daki ina kwance in tunani in har wannan text ne to ya jarabawar zata kasance?
*????????????Masoya masu jiran littafin HAMSHAKIYAR UWA Complete Document,a yanzun haka ya kammala akwai document din HAMSHAKIYAR UWA Complete game bukata zai iya tura kudi kai tsaye ta wannan account number ?600????*
*0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn*
*Phone 08140004302*
.....
Da safe bayan na yi salla na koma bacci saboda zaman cikin dare da muka yi da Hajiya Bacci mai nauyi ne ya sani na makara. Kwankwasa kofar da Juma ke yi shine ya farkar da ni, ashe wayar cikin gida ta jima tana ruri amma ban ji ba saboda bacci.
Na tashi da sauri na bude kofar Juma ce nace lafiya Juma na ganki da sassafe? Tace ni da matter gidan muka taho, Hajiya ta kira mu. " Nace har na zaci ko haihuwar ce. " ta ce a a, lafiya baki fito ba? Nace lafiya lau. Tace Hajiya tana neman ki, na shiga ban daki na yi fitsari sannan na fita. Hajiya bata falo na shiga dakin ta. Tana zaune akan kujera ta nuna min wani akwatin ga kayan ta a kusa da akwatin tace, " Shirya min kayan nan a cikin jakarnan. Yawanci dogayen riguna ne marasa nauyi, sai wani farin yadii wanda lokacin da na dago shi sai da gabana ya fadi, duk da cewa bansan likkafani sosai ba, ba shakka shine wannan. Sai wasu turaruka da kuma ganyan magarya. Na gama tsaf. Tace "Kin karya? Nace 'a 'a, tace kije ki karya sai ki zo. Nace Hajiya bana jin yunwa. Haka nan naji duk firgici ya kamani. Tace to inje in shirya kayana kamar kala biyar a karamin akwatina in zo. Na shiga uku, Hajiya kodai gida zata maidani ne! Ko yaya abin ya ke? Na tambayi kaina, amma bani da amsa.
Na yi yadda tace. Na dawo nace Hajiya na shirya. tace in kira Juma na kirata, tace in fita suka gama magana tukunna. Na fita Juma ta fito. Nace. Wai Juma ya na ganki a nan? Tace za kuyi tafiya ke da Hajiya. Ni da Azima ne muka dawo nan na fada miki tun dazu. " Mamaki ya kamani amma sai na yi shiru. Na koma dakin Hajiya. Tana rubuta wata takarda ta gama. Sannan ta amsa wayar da aka kira ta ana fada mata ce karfe daya jirginmu zai tashi, tace kije za a kai ki a yi miki passport yanzu ai kina da Karin zabe ko? Nace sai na dan kasa, tace duk daya kije dashi in kin dawo ki ci abinci kiyi wanka ni kuma zan dan saka kalle a kafa da hannu kafin lokacin. Ki kira Ummarki ki fada mata zamuje India baifi muyi kwana bakwai ba. Nace to. Muka fita da direba zuwa Immigration office, wanda mukaje gurinshi ya ce, maimakon Hajiya ta turo aje ayi miki har guda. Nace ba damuwa ai duk daya ne. ko a wa daya banyi ba na dawo da ID card dina na fita kasashen duniya, wanda ni ban ma san wai dai anyi shi sannan za a fita wata kasa ba.
Na ci abinci sama sama, ina ta yin tufka da warwara, domin bansani ba ko jarabawar acan za a yi ta . Na shirya tsaf sannan na kira Umma na fada mata zamuyi tafiya zuwa kasar India da Hajiya. Ta yi addu'a Allah ya sa mu je lafiya mu dawo lafiya.
Na samu Juma a kicin nace wai ni abinda ya daure min kai, naga Hajiya ta saka likkafani da gayan magarya a jar tafiyar ta. Juma tayi dariya, tace to ai ita Hajiya ko Zamfara zataje sai ta tafi da wannan guzirin nata, tun muna tunanin in ta tafi bazata dawo ba har muka saba muka dai. Na sauke Ajiyar zuciya nace har na tada hankali na wallahi. Tace "Dan tafiya bata taba hada ku lokaci daya bane.
Na sake shiga gurin Hajiy sai yanzu ta fara saka lalle Tace ani naki ya yi sauri,. " Nace haka ne, na amshi lalle ina saka mata. Tace inyi mata sukuf gaba daya, nace tsohuwa ta fada kwanta da na miki irin lallben da ki ke yi. Tace "Kayya zamu bata lokaci kinsan jirgi baya jiran kowa. " Nace to shikenan,
Tace amma baki sanar da mijinki cewa zamu yi tafiya ba ko?"
Nace ai baki ce in fada masa ba ne shiyasa. Tace Yawwa ina jin dadin yadda baki da gaggawa da rawar kai. bana son ya sani har sai mun dawo." Nace kuma ba laifi inna tafi babu izninsa ko? Hajiya ta dube ni,. "Har yanzu baki yarda cewa kai da kaya duk mallakar wuya bane kenan? " Nace na yarda mana.
Karfe daya saura mukayi salla, Hajiya ta sa aka kira kowa kamar yadda ta yi lokacin da za su tafi aikin Hajji. Ta shafa kan kowa tace na yafe muku kuma ku yafe ni. Duk aka yafi juna nima nace a yayyafe. Daireba ya jamu zuwa filin firgi. Mun samu wasu mutane guda biyu wadanda nake zato ko lauyoyin ta ne, amma ba wadanda na sani bane masu zuwa gida, ko kuma sune ban gane su bane oho.
Tare da su muka hau jirgi zuwa
Legas daga can muka rabu da su bayan sun yi wata ganawa ta musamma da Hajiya na misali minti talatin zuwa. dare aka kwashe mu zuwa India. Duk a tsorace nake domin ban taba hawa Jirgi ba, daga Kano ma da zamu ta so sai da na kama hannunuwan Hajiya na kankame, ji nayi kamar hanjin cikina ne zai koma kirji. Salati kuwa da na kama sai da Hajiya ta girgiza min kai tana fadin ki samu nutsuwa addu'a a hankali ake yinta. To da zai tashi daga legos kuma sai naji kamar zanyi amai kafin daga bisani na daina ji sai kuma fargaba da tsoron Allah. A zuciyata nace ganin damar Allah ne faya sa jirgin nan ya fadi da mu, gaskiya Ubangiji yana son bayinsa. Na shiga istigfari ga shi na shigo duniya bada iznin mijina ba. Koda yake mahaifiyar sa ce ta gayyace ni. Naji an kama hannuna a hankali na daga ido na kalli Hajiya wadda ta tsura min ido, tace Rabi 'atu tsoro ki ke ji ne? Nayi dan murmushi nace Tsoron Allah ne ya yake ratsa zuciya ta. Tace kar ki damu haka duk wanda bai saba hawa jirgi ba ya ke fuskanta. Ki kwantar da hankali. Ta sake sauke ajiyar zuciya, sannan tace, "Zan dora miki wani nauyi wanda Allah shine ka dai wanda zai taya miki. " Na