Showing 24001 words to 27000 words out of 51041 words
Chapter 9 - HAMSHAƘIYA-UWA-_3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
zan canza bana son fita kasuwa da babban riga musamman ta shadda.
Na amshi rigar da hular na nufi dakin shi. Ya shigo dai dai lokacin da nake saka hular a mazauninta. Ban ankaraba sai naji ya cakulkuli a gefen cikina na saki hukar nayi zillo nace wayyo, na fara dariya. Yace kwana biyu dai kin share ni, har wani shakkar taba ki nake yi." Nace ni din ka ke shakka babban bako, ni a suwa zakaji shakkata?
Ya zauna ya janyo ni ya zaunar da ni a cinyar sa. Yace Baby dan Allah kifahimce ni akan abinda zan fada miki yanzu. Na ce ina jinka, kaima ka san cewa zan fahimce ka. Yace "Wallahi an daura auren mu da Azima shekaran jiya Waccan. ' Yawun baki na ya kafe, kirjina ya buga, sai naji cinyarsa ta zame min kamar na zauna a kan kaya. Dan haka sai na zame na zauna a bakin gado. Ya zuba min ido, ni kuma na kasa magana domin bani da yawun da zan sarrafa. Kallon shi kawai nake yi.
Yace "Ban yi domin cin fuska ba, Hajiya ta yanke hukunci itama bisa wani dalilinta wanda bata fada min ba. Kuma ta bani sati daya in tare da Azima a wani gidan, ko da dai tace ta baki zabi ko? "
Har lokacin ban furta komai ba, na dai mike ina dan kai kawo a gaban gadon so nake indan samu makoshi na ya yi danshin da zan yi magana.
Na isa karamin fridge na dakin na bude na dauka ruwa na bude ina kwankwada kamar wadda ta kai azumi a cikin sahara. Sai da na shaye tas na aje robar, na kalle shi kamar zanyi magana, amma sai na fasa, na sa kai na nufi dakina domn bana son in masa kuka.
Ina son inyi tunani kafin in yi masa magana, sannan ina son in sauka daga giyar kishin da ya danne ni ya duramin ita babu zato ba tsammanin.
Na fuskaci kuka rahma ne duk lokacin da ma ace in yi shi don in samun salama a cikin duk wata damuwa da na samu kaina, amma yau kukan ya ki zuwa ko zuciyata zata rage radadin azaba. Na fada bandaki nayi alwala na fito duk da ba lokacin yin salla bane sai na zuba sujja ina kiran sunayen Allah. Kar ku ga laifina ina da mugun kishi, wanda ba ni nayi wa kaina halittar shi a zuciyata ba, Allah ne ya dasa min.
Na kwanta kan sallayar ina furta hasbunallahu wa ni'imal wakil. Sannu a hankali sai wani sanyi ya ke sauka a zuciyata.
Ina jin taku tafiyar shi da kamshin turaren shi, ban dago ba har ya yi zaman dirshan a gabana.
Yace "Baby. " Yanzu kam na shiraya yin magana da shi, na dago a hankali na kalle shi. Yace kiyi hakuri ni ma banso haka ba. " Sai lokacin wasu hawaye suka soma zirya a kumatuna. Cikin rawar murya nace tambaya daya zan yi maka, ina son ka daure ka fada min gaskiya. Dasauri yace "Insha Allahu. " Na ce nasha karantawa a littattafan hikaya kuma na yi imani haka ne, so daya ne tak ya ke, kuma mutum daya ake yi wa. Mu kuma a gurin ka Allah kadai ya san adadinmu sai kuma kai, ina son in san wakafi so ina nufin wannan son kwaya daya tak.
Ya mike da Sauri tare da fadin "point of correction! Baby,! ke da Azima zaki ce ba wai baki san adadi ba. Ina da wasu kenan ko ya ki ke nufi? "
Na tashi na koma baki gado na zauna.
Ya zo ya zauna shima, dole ne in latsa masa basira domin in fahimci wasu abubuwa. Nace Duk da na kasance karamar yarinya ba haka yana nufin bani da wayo ko basira ba, sannan duk da kasancewar iyayena talakawa ba haka shima yana nufin baza su binciki wa za su baiwa 'yarsu ba. Sa a daya akayi a lokacin sakamakon ya biyo ta hannu na, sai dai wutar sonka da ta ruru a zuciyata ta sa na boye sakamakon ko nice na canza gurin mummanan shima ya koma kyakykyawa. Ina tunanin wai ko zan iya zama silar canza warka, amma Sai gashi na kusa cinye rabin shekara ban iya wani katabus ba. Na lura Ya firgita, amma da yake namijin duniya ne, sai naga ya dake, yace "To me aka fada a kaina wancan lokacin? Kuma me ya baki tabbaci game da zargin har
kuma ki ka gaskata? "
Na yi murmushin takaici, ka san abinda nake nufi Shamaki, ina jin nauyinka har yanzu bazan so muna tattauna wannan maganar gatsal ba. Ka sani magace ta neman matan ka. Kuma na samu tabbaci ne daga cikin da ka yi wa Azima. Sannan auran ku da aka daura a shekaran jiya, ya samo asaline daga fitar da ku ka yi kai da ita kuka fake da zuwa gidan Maman Nana. Ya yi shiru ya sunkuyar da kai. Na ci gaba, har yanzu ina son ka, ina jin ka a zuciyata, ina son ka bani amsata kafin muci gaba da tattaunawa game da wannan matsalar.
Ya juyo ya kama hannuwana biyu, " Me ki ka sani game da ni? "
Na daga ido na kalle shi. Abubuwa da dama. "Fada min wani abu guda daya." Na juya masa baya Cikin bakin ciki nace, A tafiyar da ka yi zuwa kasar waje ka tafi da wata yarinya. Ya sa hannu ya juyo da ni, muka kalli juna cikin ido hawaye suka soma zubowa daga cikin gida nuna. Nace me ya sa haka Shamaki? Me yasa bazaka aure su ba.? Kai babban mutum ne, kai uba ne na yara mata, ka kare musu mutucin su mana. Ya dora yatsa a kan laben na, ki yi shiru ki taya ni da addu'a Kuma, zanyi iya kokari na inga cewa na daina. Sannan maganar Azima ita ce ta yi ta shige min tana kawo kanta dakina da sunan tambayar wani abu, zuciya bata da kashi Baby amma dai komai ya wuce Insha Allahu. " Na sauke ajiyar zuciya.
Sannan na rungume shi na ce don Allah in ka ga wata a waje ta birge ka to ka zo gida ina nan ina jiranka.
Sannan ga Azima, in kana da bukatar karin aure kar ka damu da ni.
Gam ya katse ni a jikinsa, yace na gode da ki ka
Fahimce ni, dan kuma nasan zaki rufa min asiri ko su Umma baza su ji ba. Nace karma damu.
A cikin satin aka yi gyaran gida ranar lahadi aka kaita, ba kowa sai wasu 'tan uwan su sai yayun Shamaki. Ni kuwa na fito falo gurin su aka gaggaisa ko a jiki na. Maman Iman tace wai meyasa ban yi kunshi ba. Nace mata na ga ba taro za ayi ba shine kawai ban damu kaina ba. Ta taba baki tare da fadin aifa. Wata matsala sai da ya zo wai in hada mishi kaya a karamin akwatin sa, na zuba masa harda jallabiyu da yakan sa da safe, komai da na san yana amfani da shi, na rako shi Hajiya suna zaune da wata kakar Azima. Ya yi musu sallama ya tafi.
Na dan zauna gurin su Jim kadan na tafi daki na na kwanta.
Bacci fa sai ya gagara zuciyata sai hasko min su take yi, gaskiya kishi bala'i ne. Yadda na ga rana haka na ga dare, ina yin salla na fito na shiga kicin Hajiya tana lazimi lokacin. Na gama na zo na gaida Hajiya, tace ya kadaici. " Nace haba ai ba wata damuwa ai yana tafiya kuma in zauna ni daya. Tace haka ne ayi ta hakuri dai. Na yi dan murmushi. Na yi ta zuba ido inga ya zo da safe shiru, ba ango sai wajen azahar sannan ya shigo lokacini ina hadawa Hajiya fura.
A ciki muka amsa masa gaisuwa daga ni har Hajiya. Ya zauna ta kalle shi, me ya hana ka fita kasuwa? Yace hadari ne aka yi dazu sai na kwanta Kuma bacci ya dauke ni. Na mike na nufi sasana, yau sai naji gaba daya haushin sa nake ji. Bansan ya suka kare da Hajiya ba, na garkame dakina. Ina jin kwankwasawar shi na share shi. Domin na zaci cewa zai zo da safe, ko dan Hajiya. Ya kira waya ta ina kallo, sai da ya yi kira biyar a jere sannan ya hakura ya tafi.
Sai da na tabbatar ya tafi sanna na fito. Haka na yi ta masa har kwana uku muna wasan buya. Ranar ya ritsani a kicin muna girkin dare, yacc wa Baba Juma da Tabawa su dan fita. Ya dube ni, "Saboda ke na dawo daga kasuwa yau da wuri. " Na dubw shi kamar wani abu bai faru ba. Nace lafiya zaka dawo saboda ni? Ya zaki fada min memene abinda na yi miki wanda ya sa kake guduna? Nacc ban gane gudu ba. Yace Kinga nifa bazaki yi min wannan azabtar war ba. In wani laifi na yi miki don Allah ki fada min in baki hakuri. " Na yi 'yar dariya . Nace baka min komai ba. Juma ta shigo tana fadin gafaradan ku dai, naji girki na yana kauri.
????????
?Na kalli Juma wadda ta je tana kashe gas ta dan tsaya ko zata tsinci wata Magyar a raina nace kai Juma akwai ta da son jin zance. Yace Juma kin kashe gas din? " Tace na kashe Dannan Ta fice ba don ranta ya so ba. Ya dube ni. "Yi magana ina jinki." Nace Dan Allah ka tafi sabgogin ka, ni ba wani laifi da ka min, haka kuma banga abinda na yi maka ba. Yace
"Ke da Hajiya duk kun canza min ko kinsan wani abu game da haka ki kara min haske? "
Wani sabon haushin sa ya kamani, wato shi bai san ma ya yi wa Hajiya laifi ba, tunda ya yi auran nan bance sun yi zaman minti talatin da shiba wanda na san hakan yana cin ran Hajiyar. Kuma babu tabbacin cewa yana zuwa kasuwar a kan lokaci. Na tabbata Hajiya tana cike da datasanin auren nan. "Ki min magana kin yi shiru. " Ya katse min tunani
Nace kaje ka tambaye ta mana ba mahaifiyar ka ba ce? Dan Allah ka rabu da ni, bana son ka sa raina ya kai ga baci. Na kai karshen maganar cikin daure fuska da fusata. Yace "Wata magana zamu yi ki zo muje daki. " Nayi masa wani irin kallo, Nace a yi ta anan koma wace magana ce. Ya dan yi shiru ya zura min ido, ya ce 'Sai ina ganin kamar ba ke ba, wai munata gaddamar magana zamu yi akan kwana nawa ya kamata in ke yi muku, sai mu yi shawara. " Na yi murmushin takaici, sannan nace yau kuma za ayi shawara da ni, tun da na zo gidanan waya taba jin koda ra'ayi na akan komai ma, da Hajiya ka ke shawara hatta akan abinda ya shafe ni, sai yau ne kuma za ayi shawara da ni saboda za a kwana da ni? Menene a cikin kwanan ne, ka kwana da ni ne fa kawai. Na yi 'yar dariyar takaici, dan Allah kaje in domin kwana ne Shamaki na bar mata kai, kuje ku yi ta kwana. Zaka iya tafiya yanzu ko dai ni in bar maka kicin di?
Ya kasa magana na san yana mamaki na wai kuwa ni ce nake yi masa magana haka. Ganin ba zai fita ba, sai na fice fuu na nufi dakina ko gurin da Hajiya ta ke ban kalla ba.
Ko minti biyar ban yi ba, sai wayar cikin gida ta yi kara, na daga Hajiya tace inzo falonta. Nace a zuciyata yanzu zabga son kai. Suna zaune ita da shi, a nasan yanzu zata goye masa baya.
Na zauna tare da fadin gani. Tace "Me ki ka fada masa game da kwana da ya zo ku yi magana a kai? " Nace ya je ya kwana can na hakura. Hajiya ta yi dan murmushi, wannan hakkin ki ne in kin sarayar musu ba zance komai ba, amma ba zai taba yiwuwa ya zauna a can gidan ba, zai zo nan duk kwana biyu ya je can kwana biyu. " Nace Ai na fada masa dama ni bansan ya ake yi ba da yace wai zamuyi shawara nace yasan da ku ake yin shawara kune kula san abinda y kamata ayi, shine ya zo gurina. Hajiya ta ce ni dai na gama magana." Nace to amma Hajiya yanzu dai ai sati daya zai yi tukunna ko,? Tunda dai budurwa ce. Suka kalli juna da Hajiya ni kuma na kauda kai ina murmushi nasan dai sunsan magana na yi nima. Hajiya ta ce "Haka ne." Nace Hajiya zan iya tafiya? Ta daga kai. Na wuce a raina nace na dai aje muku magana.
Haka dai ya cika sati a gidan amarya. Ranar da zai da wo gidan
Tun safe da naje gaida Hajiya tace min yau mijinki zai kwana a nan, "Me ki ke shiryawa? " Nace bana shirya komai. Tace kina ganin kuma hakan dabara ce a gurin ki? Na sunkuyar da kai, na san nufin ta in zubar da duk wani haushina in rugumi danta kar in bata masa rai. Ta katse ni. "Kar ki taya fushin kishi kin san dai namiji shi kamar yaro yake, inda ake lasa masa zuma can ya ke zuwa yawo." Nace bana fushi da shi. Tace to kamata ya yi kije yau ki yi kunshi ki gyara kanki duk da cewa na lura sosai bakya zama da rashin tsabta. "
Nace to zanje. Ina zuba mata abin karin ya shigo. Na gaida shi kafin na tashi, duk da kokarin da nake yi na kar in kalle shi sai da ya yi yadda ya yi muka hada ido. Na daure fusaka sannan na mike na nufi dakina. Da gudu na karasa na kullo kofa na sai zai biyoni. Ya gaji da kwankwashen shi ya tafi. Sai da na tabbatar ya bar gidan sannan na fito da shiri tafiya unguwar su Maman Iman dama na mata waya.
A gidan aka samin lallen muna ta labari. Tace min Baby wai kuwa ni kullum ina son in tambaye ki amma ina jin tsoro kar Hajiya ta san na tambayi wani abu game da cikin gidanta, kinsan bata son maganar gidanta na fita waje harmu sai iya abinda ta ke son mu sani muke iya sani. " Nace To Anty dan munyi magana tsakanin mu wa zai fada mata.? Tace
"Bansani ba, amma na lura kin karbu a gurin Hajiya duk da bata da korafi da yanzu ko so daya ne munji ta yi maganar ki ko da yaya ne. In kika fahimci Hajiya zakiga saukin kanta sosai, Soyayyar Hajiya daban ce ba lallai kiyi saurin fuskanta ba,. Wanda Hajiya ta ke so yana da wahala ya gane ta na son shi lokaci guda. Son mutum daya ne bata iya boye shi ko a gaban waye, son Shamaki shike sa Hajiya ta yi ba dai dai ba, kullum cikin uzri take masa. Kunsan Allah mun sha yin tunani akan wace mace ce zata iya zama da Shamaki saboda irin yadda Hajiya ta ke matukar son shi da boye laifin shi, shi kanshi ya na son Hajiya fiye da kowa a rayuwar shi kafin ya yi aure lokacin Hajiya take gudanar da harkokin kasuwanci, shi lokacin yana dan makaranta da ya taso daga makaranta office din ta zai wuce, lokacin da aka kai shi China karatu ya dawo kusan so uku, sai da Hajiya ta aje komai ta je can ta yi wata uku tare da shi kafin ya zauna. Dan haka duk matarshi sai ta yi hakuri ta kauda kai. "
Nace na lura da haka, amma ko hakan yana da alaka da rabuwar sa da matansa? Maman Iman ta ce duk da Hajiya bata bari a san dalilin ke inaga ko shi kanshi Shamaki ba zai ce miki ga cikakken dalilin sa na rabuwa da matansa ba. Hajiya ce ke sa ya sake su, amma tana da wani dalili da ita ce ta bar wa kanta sani. " Nace shiyasa kullum a fargaba na ke, in Shamaki ya sake ni Anty na shiga uku, son sa nake har bana iya boyewa a gaban kowa, kuma ga shi yana min abinda ya kamata in nuna masa jin haushina amma bana iya wa. Maman Iman ta yi dariya. Tace "Shimaki yana son ki fa, na sani in Hajiya tace ya sake ki zai iya, amma za a sha fama. Sai dai kuma kamar bana zaton Hajiya zata ce din duk da ita kadai ta san dalilin ta." Nace ina ta fadawa Allah ya zaba min abinda ya fi zama alkhari a rayuwa ta. "Kin gama magana, ni ma abinda ya sa na kawo wannan maganar saboda