Showing 9001 words to 12000 words out of 51041 words

Chapter 4 - HAMSHAƘIYA-UWA-_3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

05 Jul 2024

6851

za a yi wa yara kitso." nace To ayi musu. Na je har lambu inda ake yi musu kitso na tambayi mai kitso ku?inta ta fa?a min nace in an gama Rahin ta zo ta amsa, na ?auki takarda na rubuta. Su kuma nace ta ba su cakuleti su daina rigima.

Haka nayi fama ina iya kacin ?o?arin ganin komai ya tafi daidai. Har kwanaki tara na gana duk ma'aikata da masu gadi jani albashin kowa kuma na biya su. Kuma ce ta sanar da ni cewa Hajiya tana ba su atamfar salla kala biyu maza shadda. A shagon Zeena na sa su Ahmad yaran shagon Shamaki suka kawo na biya su ku?in. Yaran kuwa a mota na zuba su muka je Zeena Supar market na za?a musu 'yan kanti masu kyau. Azima kuma tace Jallabiya take so, ta fa?i tsayi da kala muka zo mata da shi. Ni kam ban sai wa kaina komai ba,sai ku?in kitso ne a lissafina da kowa sunan shi na saka.
Sai kuma batun mama da kajin salla. "Shanu biyu ra?umi biyu kaji hamsin ake amfani da su." Inji Juma. Na zaro ido tare da fa?in wa zai je siyan wa?annan?
......
*HAMSHA?IYAR UWA????*


*NA*


*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*


_PAID BOOK_
_Ku?in karatu ?600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya ?ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_


*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*
*Page 40*
Allah cikin ikon sa a na sauran kwana hu?u salla sai ga Shamaki ya kira ni yace sun sauka a Abuja zasu hau jirgi zuwa Kano, nace shine jiya fa mun yi waya amma baka fa?a min ba. Yace "Bazata ce." Don haka na tashi na shiga shirin tarbar mai gida. Ranar kuwa mai ?unshi ta zo ta yi mana jan lalle, ita kuma mai kitso sai washe gari.

Nayi murna sosai da dawowar mijina, kasancewar Hajiya bata nan a gaban kowa na rungumi mijina ina murna. Shima ya ?an?ame ni sannan yace "To ga yaranki bari suma in ba su runguma." Ya ?auke su ?aya bayan ?aya, sannan ya mi?awa Rahin wata leda, yace a ba su chocolate kowa ya sha. Ko suna azumi?" Anisa tace bamayi Dady.Nace Kince min ki na yi fa Anisa Baby. Tace Mommy ai na karye shi fa. Muka sa dariya.

A ranar dai kam na tabbatar cewa na yi kewar shi na tsawo kwanakin,. ,amma shi ya fi kewata ya kasance kamar zai cinye ni.

Dawowar Shamaki ya taimake ni sosai domin sai dai naji an kawo shanu da ra?uma. Kaji kuwa haka aka yi ta rabon su, kamar in tambayar wa su Umma, amma sai nayi shiru tunda na san suna sane da su.
Juma ta same mi tace "Hajiya tana nemo wasu masu aikin su taya mu kamar uku sai kuma aikin cincin da duk kayan fulawa bamu ke yi ba Zeena ake kaiwa wanda suke cewa ko batiri ko me?." Nace ko dai Factory? Baba Juma tace "Yawwa haka." Muka yi 'yar dariya. Nace to zanyi masa magan. Sannan ina zani neman masu aiki ukun da ki ke magana? Tace "In kuma in samo su sai in samo, domin da akwai su."
Nace ki samo. Haka ta samo mata ta fa?i abinda za a ba su agaban su na sallama in an gama salla.

Ranar Idi na matsawa Shamaki don Allah zamu je sallar idi yace , "Ba wadda ta ta?a zuwa in tsoro kar Hajiya ta ga cewa an kawo wani abu daban." Nace amma wata ta ta?a cewa zataje Hajiya ta hana? Yace "A cikin su babu wadda ta ambaci zuwa Masallaci." Nace bana zaton Hajiya zata hana ibada. Yace Haka ne."
Haka dai ya kwashe ni da yara mukaje sallar Idi duk mun sha hijabai wa?an da na saya mana a kasuwa domin amfanin yau ?in.

Haka aka ci gaba da bikin salla, nace yaushe zamu gida? Yace in jira "yan uwanshi su zo. Sai uku ga salla suka zo, muka sha yini. Shine ya kawo min sabbin kudi 'yan ?ari biyu wai goron salla na shi kuma inzo in bashi nashi. Na zata wasa yake sai naga ya maida makullin ?akina ya mur?a, yana fa?in yau a ?akin nan nake shi'awarki, ga ?amshin ?akin ga ?amshin mai ?akin zan rufe ne saboda yaranki da zasu zo suna kiran Momy."Ni dai Nayi murnar ku?i ina ta godiya har sai da ya fara nuna rashin ya ?aci. Nace amma dai ka bari su tafi zuwa dare sai in baka goron sallar ka ?in. Yace har yau kin kasa gane cewa mu maza in shi'awar mu ta taso bata komawa ko?"Na fa?a jikinsa,a zuciya ta ina fa?in kar a kaita wajen matan banza. Bayan na fito sai na koma gurin su,Maman Nana tace "Wai ina ki ka shige bacci ki ka yi ne ki ka share mu ana hira." Maman Umar ta ce "kai! Ke kuwa kin cika bincike, agabanki Shamaki ya kira ta f." Sai ta ce "O haka na manta,sai suka sa dariya. Na yi ?an murmushi tare da fa?in kai Anty ba wani abu bane fa, sa?o ya bani. Maman Umar tace "E ai mun sani." Cikin kunya
Na ja Naman Iman gefe nace Anty Maman Iman dan Allah Hajiya tace duk abinda ake yi muku da salla in kuzo a yi muku,shine nake son ki fa?a min abinda ake muku? Tace ba a mana komai ai kin mana komai anci ansha anyi wasa da dariya ai shine abin da?in. Karki damu. Yara dai take bawa ?an goron salla na sabbin ku?i." Nace Nawa nawa? Tace duk yadda ya zama rabon su." Haka na ?auki ku?in na rabe musu dubu ishirin ?in,amma da niyyar zan ciri ku?ina a wancan account ?in tunda Nima ai zanje gida. Washe gari na tambaye shi yaushe zanje gida? Yace "inje, duk lokacin da na shirya. Na fara murna sai ya ce, "Amma kina ganin ya dace ki tafi Hajiya bata dawo ba? Kinga gidan nan a hannun ki yake,in Hajiya ta dawo baki nan fa?" Nace ai zata fa?a in zata dawo ko? Yace "Inji wa? Hajiya sai dai a ji kiranta tace aje a jirata a filin jirgi ?arfe kaza zata sauka. Ni ina zaton ma yau zata dawo." Nace to shike nan,na ha?ura zan jira.Yace Kama gefen kumatuna yace, "Daga cikin abinda ke ?arawa mace daraja a idon miji shine rashin gardama." Na ?ora tafin hannu akan nasa nace Insha Allahu zan ri?e wannan karatun. Ya sunbaci goshina kin haddace wannan Baby." Nace To ina godiya Malam.

Yana fita na tafi ?akin shi domin ci gaba da karatun littafin nan

Babi na gaba na shiga. Wanda ya ke magana akan Hajiya Zeena Amadu Shinkafi.

Hajiya Gwamma ta sa anje har Shinkafi ta jihar Zamfara an yo mata bincike akan Zeena. Tamkar dai shi Ali Baita
Itace 'ya ?aya tak da Ubangiji ya baiwa maihaifinta kuma ya bata ilimin zamani dana addini. Sai dai kullum yana cikin damuwar rashin samun ?a namiji wanda zai hutar da shi in ya kai matakin wasu shekaru. Zeena ta fuskanci damuwar da mahaifinta ke ciki don haka sai ta sawa zuciyar ta cewa zata share masa wannan kuka. Ta kuma nuna masa a zahiri ta karanci fanin kasuwanci. Dan haka data ?are taci gaba da jagorantar wani ?angare na kasuwanci sa.

Abinda ya ba ni mamaki shine daga daidai nan gurin sai aka sa wani abu mai kama da farin fenti aka goge rubutun aka ?ata shi har zuwa Babi na uku wanda yake magana akan cewa an ?aura Aure Zeena da Ali Baita kuma an kawo ta garin Kano. Me aka rufe a can? Na tambayi kaina baya na bu?e shafu kan na koma baya na duba,hakan dai suke ba ido na bane. Dole za a samu kwafi mai kyau a gidan nan koda babu a ko ina za a same shi a gurin Hajiya.

Na bu?e shafukan gaba duk dai bayani ne akan dukiyar da ya mallaka da tallafi da yake bayarwa sai hotunan karramawar da ya yi ta samu daga ?ungiyoyi da jam'i o'i sai hotunan su Shamaki da yayinsa an rubuta 'ya'yan Ali Baita. Na kasa ci gaba da karanta wannan littafin ina bukatar mai kyan. Na maida shi na aje.

Ilai kuwa a ranar sai ga kiran Hajiyan Shamaki a waya, yace min a sanar da direba yaje filin jirgi ya jira Hajiya suna Lagos.

Nace to na fita da kaina na fa?a masa.
Na kira wayar Juma kwanan ta biyu taje gida. Nace Hajiya na hanya ta dawo domin ita ce tasan wanne irin girke girken da za a yi domin tarbar Hajiya.

Cikin rawar jiki sai ga Juma ta dawo,tace don Allah in Hajiya ta dawo karki in ce mata taje cikin gari saboda zata yi fa?a, tace min kar inje tunda bata nan. " Nace ba komai karki damu bazata sani ba..Ni dai burina ki shirya mata abinci wanda ki ka san tafi so zata yi marmari. Ni kuma zan shiga ?akinta da kaina in gyarra mata shi, amma ina son ki Kunno turaren da ya fi yi mata da?i ki bi?e gidan da shi lungu da sa?o.

Cikin mamaki tace 'Yannan ke ta daban ce sauran in Hajiya taje wani guri zata dawo sun dinga takaici kenan wai takura zata dawo. "
Nace Ni kam ina farin ciki da dawowar Hajiya wallahi Baba Juma ina son Hajiya har cikin zuciya ta, kin san dalili? Tace "A'a. Nace ta haifa min Shamaki wanda nake masa wani irin so mara misaltawa. Kullum ina mata addu'a Allah ya sa ta gama da duniya lafiya tare da mu gaba ?aya. Juma ta saki baki tana kallo na, nace yaya dai Baba Juma? tace, 'yannan ashe Kema kikan ta?a rashin kunya ashe. Na yi dariya wuce na nufi ?akin Hajiya. Ta biyo ni har ?akin tace "To zan baki wata shawara, komai nata ki barshi a inda yake karni canza masa guri." Nace Juma zan gyara ?akin nan kamar yadda zan gyara ?akin mahaifiya ta ne zan iya canza komai zuwa inda ya dace. Tace To shikenan. Na canza zanin gado da labulaye. Na wanke ban?aki na share na goge komai na kuma canza mata shirin wasu abubuwan. Na duba durowoyin ta ina neman kwafin littafin nan ban samu ba, zan fita sai na kula da wata durowar ta ?arfe ina ganin irinta a finafinai. Wandda ake bu?e ta da lambobin. Nace tabbas ya na cikin nan,in kuwa haka ne to abin yafi ?arfina.

Nafita nace Juma ta saka turare a cikin ?akin.

Shamaki dama ya tashi da azumin sitta shawwal sakamakon matsa masa da nayi akan ya fara kawai, kuma fa nayi haka ne saboda na duba wayar shi naga al?awuran haduwa da wata da suka yi da zarar anyi salla da kwanaki ka?an. Na yi ta mamaki,nace anyi ibada kuma daga yin salla za a bi ibadar da zunubi.

Yace "Wai me yasa na damu ya yi azumi ana cikin bikin salla. " Nace saboda ka saba da azumin kafin cikin ka ya bu?e kayi kayan ka in yaja Lokaci ?ila ya yi masa wuya.

Yace Gaskiyar ki kam domin bara haka ce ta faru, ina ta furta zanyi amma ban samu na yi ba." Ni na tashe shi ya ?auka.
Hajiya ta iso gida lafiya muka tare ta da murna da farin ciki Ni da yaran. Ta ji da?in yadda ta samu gidan muka bita har cikin ?aki, ta yi turus ta dubi Juma mai ri?e da jakar Hajiya. Tace "Wanene da wannan aikin ko maman Umar ta zo ne?" Juma ta kalle ni, tace 'A'a ?iyar ki ce dai ta yi gyaran. Hajiya ta kalle ni, sannan ta zauna baki gado. Muka fita domin ta kimtsa. Ina falo ta fito ta yi wanka ta shirya tsaf cikin doguwar riga. Sai lokacin na bu?e mata kujerar zaman ta wadda na saka wani farin kyalle na rufe, ko masu shara sai dai su kakka?e su share su mayar su rufe. Ta zauna tace Alhamdulillahi Allah mun gode maka, ya Allah ka amshi ibadarmu.

Muka ce ameen. Sai da ta yi salla sannan Juma ta soma gabatar mata da abinci. Na zauna ina zuba mata. Tace Juma sannu da ?o?arin wannan hidima. Juma tace matar Shamaki za a yi wa godiya ita ce ta bada umarni a yi komai.

Hajiya ta ?aga kai ba tare da ta dube ni ba.
Shamaki ya shigo, cikin murna yana yi wa Hajiya sannu da zuwa. Ya zauna suka gaisa. Ta gama cin abinci na soma matsa mata ?afa, tace a ?akko maganin nan domin ?afafun sunyi tsami.
Na je na ?akko lokacin da na dawo na samu Azima ta na zaune a gaban Hajiya. Hajiyar tana cewa Azima. "Kina nufin baki ji ba duk wannan hayaniyar kusan awa biyu da suka wuce? Tace "Wallahi ni dai banji ba." Hajiya tace shike nan. Na zauna na ci gaba da matsa mata ?afa.

Washe gari na tashi cikin shirin zuwa gida.
Naje gaida Hajiya tace "Ga akwatuna nan an kawo na tsaraba, na kwana biyu banyi tsaraba ba in naje Ummara ko aikin Hajji.
Nace sannu da ?o?ari. Tace "Yanzu sai ki bu?e ki raba." Nace Hajiya zan iya kuwa? Bata amsa ba dan haka sai na bu?e akwatunnan na dinga ?aga wa ina kallo zannuwan gado, dardumai, kayan yara da dai sauransu. Na cire wa su Anisa riguna yaran su Maman Umar kowa ?anta ?aya ya samu. Dogayen riguna Jallabiyu. Na cire wa Azima guda biyu su Juma hijabai. Shamaki wata Jallabiya bulu ta yi kyau na ce wannan dai tamuce, masu gadi dama nasan adadin su tun a biyan albashi, na cire musu dardumai da carbi. Nace Hajiya gashi na cire na wa?an da na sani. Na lissafa mata, tace "Bari in zana miki sauran tana ta fi?i ina cirewa aka gama. Tace ina nawa. Nace ai ko ban ?auka ba babu komai. Ta ce shike nan tunda baki so cirewa Ummar ki. Na ciri Hijabi irin na su Juma. Abbanmu kuma carbi da dardumai. Tace shike nan aba kowa na shi a kai mata sauran stor.
Hajiya tace in bari sai ?arfe goma sannan in tafi. Tace me zanje dashi ina cincin da nama ko haka zanje hannu rabbana? Nace ai gida ne ko ban kai komai ba babu wata matsala. Tace "To da aka fitar da zakkar fidda kai an kai masu?" Nace gaskiya bansani ba dai domin shi ya raba. Ta ?auki waya ta kira shi, yana waje Shamsu ya yi sallama da shi. Tace "Ankai zakkar fidda kai gidan su matar ka?" Yace baki fa?a min cewa za a kai ba. Na bayar ne a guraren da aka saba kaiwa.
Tace "Ya Salam! Ban ji da?in wannan lamarin ba sam. To yanzu me zata kai gidan su? Yace duk abinda ki ka ce .

Hajiya ta kashe waya sannan ta dube ni. Kira Juma. Na kirata. Tace Juma A samu manyan ledoji a zubo dambun kajin nan,sai kuma na naman shanu, wata ledar a zubo cincin,aka kawo gabanmu, tace Juma ki sa rabe ya fitar da lemo kat an goma ya saka a mota akai wa?annan ledojin." Ta duba ni, kije ?aki na kija wannan durowar da kika gama bince su ki ?akko sabbin 'yan ?ari biyu ki ri?e saboda ta?awa yara. Nace "To. Amma jikina ya yi sanyi da jin kalma durowar da ki ka bincika. Na ?akko na fito. Tace in gaishe su,sannan kuma Shamaki zai zo ya ?akko ni daga nan sai ya gaishe su,,ko hakan bai yi ba?" Nace ya yi na gode sosai.
?????????
Gida ya kaure da murnar zuwana. Direba ya na ta shigo da kayan lemo na saka yaran ma?otanmu su taya shi ?akkowa. ma?ota harda le?e ance Baby ta zo.
Wani abu da ya ?aure min kai shine yadda naga buhunan shinkafa guda biyu a ?ofar ?akin Umma. Nace wannan fa? Tace "Wadda mijinki ya kawo mana ce ta salla buhu biyar muka rabawa dangi da ma?ota guda biyu, Abban su Zuhra kuwa muka bashi rabin buhu, rabin ce muke dafawa, sai sauran biyun sune kin gansu nan." Nace Kuma ni sam bai fa?a min ba, Hajiya ma bana zaton ta sani. Domin ta tambaye shi ko ya kawo muku zakkar fidda kai, yace a a. Umma tace "Ikon Allah wato su dai mutanen kirki haka suke, to kaji goman ma bai fa?a miki ba kenan?" Na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login