Showing 39001 words to 42000 words out of 51041 words

Chapter 14 - HAMSHAƘIYA-UWA-_3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

05 Jul 2024

6865

ya rage min ina son in nuna masa duk wata soyayya ta. Dole ta hakura ba domin ta so ba. Maman mubina. Ita kuma banda kokarin azurta kanta da danginta bata komai, duk lokacin da nayi mata gwaji akan wani abu kamar sadaka ko zakka ba ruwanta da dangin Shamaki kanta ta sani. Gashi bata san girma ko darajar kowa ba. Tana son ta yi mulki har da ni. Abinda yafi daga min hankali shine yadda ta ke tauye masa hakkin sa na kwanciya wanda hakan ne sanadin nitsawar. shi a neman mata.

Shima na sa ya rabu da ita. Kuma bai tambayi daliliba Na ci gaba da yi masa addu'a Cikin haka ya samo Maman Anisa yana sonta itama tana son shi amma sai tana kula tsofafin samarinta, har ta taba ziyartar gidan wani saurayinta wanda bani da sheda akan abinda ya faru, sannan tana waya da maza daban daban. Har zuwa yau batasan na sani ba, haka kuma Shamaki bai sanI ba domin ban fada mishi ba kar ya fara zargin ko ma 'yarsu ba tashi bace.

Ya jinjina kuma ya girgiza lokacin da na ce masa ya sake ta. Dan yana sonta, tsabar ladabi da biyayya har zuwa yau bai taba tambaya ta me ye dalilin sa shi ya saki matansa ba.

Abinda ya yi Imani shine bazan taba cutar da shiba. Gashi zan mutu bansan takamaiman gurin wa zan bar shi ba. Muryarta ta sarke hawaye suna kwaranya a kan kumatun ta, na sa hannu ina share mata hawayen, ga nawa suna kwaranya.

Na kama hannunta. Nace Hajiya ki barshi a hannun Allah ki barshi a hannu na. Ta saka hannunta ta damke nawa ta ci gaba da fadin Na yanke shawarar in bashi Azima wadda ta zama raino na ce, kuma sai ina kallon zatabi duk wani tsari nawa, sai Allah ya nuna min ban iya ba, wayo da dabarata, ba su isa su sani in samu biya bukata ta ba.

"Tun daga ranar da ya kawo min labarinki na fahimci yana matukar son ki, to ina ta tsoro kar a kuma ga lokaci yana ta kure min. Na saka ayi min bincike, naji dadin yadda aka kawo min sakamakon talauci ne kurum abinda suke ganin zai zama aibun ki, na nuna musu talauci ba aibu bane, dan haka ban dakatar da shi ba.
Ba dabi a ta bace in saka malamai wani aiki bayan saukar karatun kur, 'ani wanda ake yi mana duk litinin da Juma a, domin neman kariyar Allah da falalarsa, amma sai gashi na saka ayimin bincike a kanki, bayanin Malamin ya yi min dadi ko da ba gaskiya ya fada min ba. Matsalar daya ce bana son yafi sonki ina tsoro kar kiyi amfani da haka ki cutar min da shi, sai nasa aka hado wani sihiri wanda zaki so shi, da Allah ya ta shi nuna min ban isaba, sai gashi kunci dabinon tare ke dashi. In zaki tuna shine dabinon da na baki wanda kika ci a ranar farko da ki ka kawo ziyarar gaishe ni ke da kanwarki. Ki yafe min wannan cutarwar da na yi miki. Ta sauke a jiyar zuciya. Ta saka hannunta ta sake share min hawayen kan fuskata hannuwan ta sanyi kalau. Tace "Kafin kasa ta rufe idona, kuna zargina da son kaina game da 'ya'yana, ba haka bane ina kokari ne in nuna musu dukkan soyayyata a cikin kwanakin da suka rage min a duniya.
Zuwanki na yarda Allah ya amshi addu'a ta, ya kawo wa Shamaki wadda zai dora kai a kan cinyarta ya yi kuka ta lallashe shi. Kowata uku baki rufa ba ki ka cinye duk wata jarabawa tun kafin in miki ita. Abu daya ne kinyi karama da jan ragamar amma kamar yadda nace Allah ne zai taya ki.

Tun a farkon shekarar nan jikina ya motsa likitana muka yi waya, ya turo min likitocinsu na nan suka dubani, ya sanar da ni cewa ba shakka in har ina da wani abu da zan gabatar in gabatar kafin watannin farko na sabuwar shekarar nan da muka shiga. Abinda Azima da Shamaki suka aikata na dauke shi a matsayin fada Allah ya ke min, in gane wayona da dabarata baza su kaini ba. Ciwona ya tashi saboda damuwar da suka jefani a ciki, wanda tun daga ranar jikina ya motsa gaba daya. Maganin da nake amfani da shi ya daina min aiki.

Likitana yace in taho amma in tabbatar cewa na yi duk wata wasiyya kafin in taho domin ba lallai in koma da raiba.

Muka fashe da kuka a tare sannan ta dora kanta a cinyata, munyi kuka mai tsuma zuciya tsawon minti biyu, sannan ta dago tana lallashi. Kiyi hakuri Rabi'atu, ki dauki girman da Allah ya baki. Cikin dashasshiyar murya da makyarkyata nace bazan iyaba Hajiya abubuwan suna da yawa. Tace zaki iya kinyi na gani, har abinda ya shafi kasuwar Shamaki zaki shigo ciki domin taimaka masa. Na rubuta na aje masa a cikin wasiyyar da na rubuta musu kowa da tasa. Abinda ya shafi sadaka ko zakka kinyi na gani, sannan za a samu karin wasu duk Allah zai haska miki tunda shi ya kawo ki.

Ranar da na kiraki cikin dare jikina ya matsa na zaci ranar zan mutu gashi ina son in tabbatar ko kinsan waye Shamaki. Duk abinda Juma ta ke fada miki da tattunawar da ki ke yi da ita nice na tsara domin in kara tabbatar da wacece ke, haka kuma tura Juma gidan Azima shima nayi ne domin in gano ko za su baki wata matsala bayan bana nan.

Dan haka ki rike Juma sosai tana da Amana zata taimaka miki. Na hanaki zuwa aikin Hajji da Ummara domin in auna hakurinki, na tafi da kishiyar ki domin in jaraba kishinki sai na samu Allah ya miki baiwa ta hakuri kawaici da kuma tsaida zuciya daya tare da dayanta Allah. Ba bukatar sai na fada miki tsakanin Shamaki da "yan"uwansa, domin kin binciko duk ina da bayanin yadda kuka fara, ni ce nasa Juma ta fada miki cewa zan tambaye ki waye Shamaki saboda ina son ki saka hankali ki gano waye shi din. Ni ce na aje littafin da kika karanta. Kuma ina sane da zuwanki gurin tsohuwa a Face. Ta nuna akwatin ta, dakko min waccan akwatin. " Na mike jiki babu karfi na tafi dakko akwatin Hajiya wadda na jasu zuwa hanyar fita danzun nan.

A kasan muka bude dan tashin hankali ya sa bani da karfin da zan iya daga ta in dora saman gado.

Muka zauna kasa muka sa akwatin a tsakiya. Ta ciro littafin tarihin Alhaji Ali Baita. Tace ga mai kyan duk da kinji komai, amma komai yana cikin nan. wancan wanda kika karanta wanda aka yi kuskure ne aka kawo na duba, shine aka rufe gurin kar wani ya karanta.
Ta ciro wata folda ta miko min wannan ki adana masa su, duk wata sheda ta dukiyar Shamaki tana cikin nan. Lauyoyinsa amintattune mutanan Lagos, sune suka je na gabatar musu da ke a matsayin matar Shamaki wadda zata saka ido akan dukiyarsa."

Na zabura, bazan iya ba, banajin yaren turanci bansan Hajiya ta dafa kafadata, ki kwantar da hankalinki, sannu zaki gane komai, abin duk mai sauki ne, kuma su sunajin Hausa. Taci gaba. Zuwa yanzu dai Allah ya sa zan mutu cikin natsuwar cewa zan bar Shamaki a gurin ki. Kar ki manta kuma karki shagala, amana ce. Kin riga kinsan waye Shamaki ma ana, kinsan dabi'unsa masu kyau da marasa kyau, kinsan halayen shi, kin san me yafi so da kuma abinda baya so, kinsan me zai iya da kuma abinda ba zai iya ba. To dan haka kin san ya zaki zauna da shi. Ta dube ni cikin ido, haka ne?" Na daga kai, alamun eh. Tace kinsan Shamaki Allah ya baki hakurin jure duk wasu matsalolin da zaki fuskata.

Ta ce ciro likkafani da ganyen magarya ki saka a waccan durowar domin kar ya yi nisa. Ta ciro wani makullin karami ta bani, tace "Wannan ki saka a jakarki, makullin wannan durowar ce ta daki na, akwai gwalagwalan da nake amfani da su wanda yanzu zai zama gadon yarana, bana son makullin ya fada hannu da ba daya daga cikinsu ba, amana ce ki ba Maman Umar. Ta saka hannu ta ciro dan kunen kunnenta ta ce ki saka wannan a kunnen ki ta ciro zobe daga karamin yatsanta ta ce saka wannan shima, duk lokacin da ki ka kalla sai ki tuna cewa nice na baki, kuma ki yi min addu'a.

Wani irin kunci naji zuciya da idanuna suka kafe da hawayen sai radadin yaji. Nace Hajiya to wai yaushe suka ce miki abin zai faru? Ta lumshe ido cikin fargaba wadda nake gani a idanunta. Tace "Su kansu baza su iya sani ba, bare ni. " Nace ni nafi zargin cewa ba gaskiya bane kuma in Allah ya yarda ba zai faruba, ga ki lafiyar ki lau. Hajiya tace "Ba
ki san abinda nake ji ba da kuma wanda nake gani a mafarki na. Ina tabbatar miki abin zai faru, ki tayani addu'a in hadu da Allah lafiya. In amsa tambayin kabari. " Na sake rike kai. Mutuwa fa, kuma kasan cewa zaka mutu har ma da wa'adi, gaskiya Hajiya jaruma ce wadda ta cancanci a bada labarinta. Na dago kai nace kuma nace Hajiya me yasa ki ka zo dani domin inga wannan tashin hankali?

Tace saboda kar ki shagala da Duniya, kuma hakan zai baki dama ki rike amanar da na bar miki.

Ta ciro turaruka guda biyu, ki aje su kusa da ke za a yi amfani dasu gurin wanka gawata da kuma likkafanina.


Shamaki ya kira direban su Malam Bala lokacin da zasu taso daga filin jirgin Abuja. Sakna wadda take fushi tun da suka taso ta dauki jakarta tana yi masa kallon sama da kasa "Zan iya tafiya yanzu ko?" Domin nan ba Dubai bane ina da masu daukar nauyin na.

Shamaki ya kalleta. "Ko a can ban rike ki ba kece baki ga damar zama ba, Sakna zan fi son haka kije abinki.

Haka ka fada ko, zaka nemeni babu shiri. Ta wuce. Ko kallo bai bita da ba, ya maida kanshi ga abinda ke damunshi, har a Abuja ya kasa samu su Hajiya. Ya danna kiran Maman Umar ta shiga, a ringing na biyu ta daga. Ina ka shige ne mun nemeka mun gaji? Yace farko dai "Hajiya fa wayoyinta basa shiga. " Tace Hajiya suna India suda Baby, muna sa ran ta kaita ne a duba ko akwai matsala ne game da rashin rashin haihuwar ta...
.....
Shamaki ya ji wani dadi ya rufe shi, yace "Alhamdulillah! Ba shakka Hajiya ta gamsu da Baby, Maman Umar Hajiya zata yi min bazata ne. Allah na gode, "

Maman Umar ko dai in bisu ne? " Cikin dariya ta ce dan autan Hajiya, to in kace zaka bisu kwana nawa ne kafin ka samu visa? Kilama har sun dawo. Yace akwai yadda zanyi sai dai ina son in bar Hajiya ta ida muradinta." Fari ciki fal zuciyarsa ya sauka a filin jirgi tun yana mota ya fara waya yana neman visa ta India gaskiya gara ya bi su shima ya yi musu bazata. Domin ya kasa fasssra yanayin da yake ciki.

Yana shiga falon Hajiya sai ya ji gabanshi ya yanke ya fadi, falon ya yi masa duhu domin ga mazaunin Hajiya amma bata nan. Juma ta fito tana yi masa sannu da zuwa, ya amsa sannan yace "Baba Juma gidan wayam. " Juma tace har ka tuna min da Uwar dakina takance Baba Juma. Yace ashe sun tafi India. " Juma tace ah dama Hindiyar ne kasar waje? Shamaki yace "E canne kasar waje mana.,, " Tace Allah ya dawo da su lafiya. Yace "Ameen. " Ya nufi dakinsa kewar Baby ya ke yi a kalla ko muryarta ya ji, amma wannan bazata da Hajiya ke son yi masa tana azabtar da shi, ba Hajiya ba Baby, gaskiya dai ba Mutum. Ya furta yana cire kaya. Ya fito falonsa ya zauna yana ta kiran yayunsa yana fadin Hajiya zata yi mishi ba zata, suma suna tsokanar cewa ya gudu domin kar ya rabu da Baby.

Juma ta shigo ta same shi. Uban daki me za a dafa maka ne? Yace "Baku dafa komai ba? "Tace mun dafa taliya kai kuma ba layinka bace sosai. Yace inda a kwai kayan ciki ko wani dai farfesun a dumamamin shi. Tace akwai na kaza. Yace to shima zai iya yi. Har ta juya sai yace mata, wai Ina Azima ne? Tace tana ciki bari a kira ta.

Har ya manta da cewa za a kirata, sai gata ta shigo, ya bita da kallo, duk ta kumbura, Ta yi masa samnu da zuwa ta zauna. Yace kin koma Asibitin kuwa? " Tace Ni banje ko Ina ba, ta turo baki, bayan duk kun tafi ba mai kula da ni Hajiya ma ta dauki wannan matar sun barmi. Shamaki ya bata rai, in basu barki ba ina zasu da ke?" Ko kuwa wani zai tsaya gadinki ne, sannan kuma baki motsa jiki sam kamar yadda likita ya fada. Ta bata rai kamar zata fa she da kuka, tana fadin shi likitan da zaice haka dan ba a jikin shi cikin yake ba, Ina zan iya wani motsa jiki! Shamaki yace to naji yanzu dai tashi kije bana son ki kai ga hasalani karki bata min farin cikina." Ta taba baki sannan ta tashi ta wuce.

Haka dai Shamaki yaji gidan babu dadi sam. Fatanshi yasamu visa da wuri ya bisu.


A dai dai wannan lokacin Hajiya ta kalli Baby bayan likitan ya gama daura mata ruwa tare da zuba magungunan a ciki, yace zata samu bacci kar a tashe ta. Baby tace to. Ta zauna kan kujera wadda ke daf da gadon ta shimfida tafin hannunta cikin na Hajiya, tace Hajiyata Allah ya baki lafiya. Ta bude ido ta kalle ni, ta cije lebenta da alamu wani guri yana mata ciwo. Nace Hajiya me yake miki ciwo? Ta bude ido, ta kalle ni, ko ina ma ciwo yake min. Nace sannu insha Allah zaki samu sauki. Can tace Amanar me na baki? Nace Amanar duk wani wanda ke karkashin ki insha Allah amanata ne Hajiya. Ta bude ido, sunyi jajir. Tace ina jin Bacci ne amma na kasa hamma tun jiya, kila har hammata ta kare." Nace zaki yi insha Allah. Ta lumshe ido, ki ci abinci fa Rabi'a ki sa a kawo miki abinci kinji?"

Nace to. Amma ina wani cin abinci ni ko yunwar ma banaji. Ta bude ido ta rufe tana dan cije lebe sannan ta na motsi da baki kamar salati ta ke yi, can kuma bacci ya kwashe ta. Likita ya shigo ya ce kar inyi wani motsi mai karfi domin ta samu bacci mai kyau. Na fada masa tace ta kasa yin hamma, yace kar ki damu komai zai yi dai dai.
Na idar da salla ina zaune ina addu'a sai naji motsinta.
Da saurin na tashi na tafi gurinta. Ta bude ido tace zanyi salla. Nace to zata iya zuwa bandaki? Tace bari ta gwada. Mukaje na rike ta domin jikin ba karfi. Gani nake kamar ma su ne suka dora mata ciwon domin lafiya muka zo. Na zaunar da ita tayi fitsari na yi mata tsarki na yi mata alwalla na maida ta kan gado ta kasa zama, tace duk ji take yi ta gaji. Dan haka a kwance ta yi sallar. Haka dai har bacci ya kuma daukarta.

Shamaki ya kasa bacci ya mike ya shiga falon Hajiya yaje yana shafa kujerar zamanta. Har yanzu kamshin turarenta kujerar ke yi, ya zauna kasa ya dora kansa a saman kujerar yana fadin ina kaunara ki Hajiya Allah ya dawo min da ke lafiya. Can kuma ya tashi har ya nufi dakinsa sai kuma ya fasa ya nufi nata dakin, da duhu fitilar dakin a kashe. Bai kunna ba ya nufi gadon ya laluba ya kwanta.

Cikin bacci yake mafarkin ana biki a gidan gida ya yi cikar kwari ba masaka tsinke ga Hajiya ta caba ado cikin kaya na alfarma amma kuma shi da ''yan uwansa duk suna cikin damuwa.

Ya farka ya ji ana kiran sallar farko ya tashi ya lalubi makunna ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login