Showing 36001 words to 39000 words out of 51041 words

Chapter 13 - HAMSHAƘIYA-UWA-_3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

05 Jul 2024

6860

ce na am! Hajiya cikin mamaki da fargaba nayi maganar, tace "Zan baki amanar Aliyuna. Na ma manta waye Aliyu. Nace waye kuma Aliyu? Tace "Shamaki nake nufi. Na zaro ido, tace na baki amanar 'ya'yan Shamaki."
Nace me yasa zaki bani amanar su banyan muna nan tare da ke su kuma suna gida? Tace "Zan baki dama ki min tambaya amma sai mun isa can zaki tambayi duk abinda ki ke so. Cikin tsanaki. Ta sake rike hannu na Na baki amanar Azima kar kiyi amfani da son da Shamaki yake miki ki cutar da ita ki yi mata adalaci kar ki bar kishi ya yi tasiri a zaman ku.

Na baki amanar zumunci Shamaki da ''yan uwanshi, duk yadda za ayi kar ki bari zumuncin su ya samu tangarda! Na baki amanar dangina da dangin Shamaki."

Jikina ya hau bari na soma tunanin ko jirgin ne zai fadi. Nace Hajiya in jirgi ya fadi ai har ni ne baza mu rayu ba. Tayi murmushi, sannan tace ba jirgine zai fadi ba, ina son ki kwantar da hankali ki amshi duk wannan amanar da nake baki, domin zaki iya. Dan Allah kar duk wani me aiki ko wani wanda muke dangantaka da shi ya ce, wayyo yau ina ma Hajiya tana nan. " Nace to Hajiya duk da kince kar in tambaye ki, a can zaki zauna in munje?
Tace za kiji komai. Ta sakar min hannu. Na zura mata ido ina tunanin abinda Hajiya take magana kamar me wasiyya kuma gata dai lafiyar ta lau. Ko kuma dai in mun koma ne zata koma gefe ta sakar min komai? Na sauke ajiyar Allah ya sa ma haka ne zai fi sauki aka ace Duniyar ta ke maganar bari.
Haka dai muka isa Kasar wata mota ta zo ta dauke mu da kayanmu zuwa wani katafaren gida. Mun samu wasu hadimai kamar dai irin wadannan da muke gani a fina finan India. Sune suka amshi kayanmu zuwa wani daki da ke sama. Muka shiga dakin kato ne sosai gadon da kujerun duk a ciki suke. Muka yi salloli sannan muka kwanta duk da cewa garin ma yariga ya waye. Na farka naga Hajiya zaune kan kujera tana shan shayi suna tattaunawa da wani mutum Baindiye wanda nake zaton likita ne, saboda rigar likitoci dake jikin shi. Nabi mamakin yadda mutumin ke yin magana da Hausa duk da cewar Hausar bata goge ba.
.....
Yace "Hajiya ciwo ya zo matakin karshe kamar yadda muka fada miki a wancan lokacin.

Abinda Gwajin mu ya nuna shine kin shiga matakin karshe na ciwon Allah zai iya ganin dama ya barki. Sannan a ka ida bai kamata muna fada miki halin da kike ciki ba, yaranki sune ya kamata su sani ke kuma a boye miki amma kin ce a a. Banda kina da karfin hali da yanzu kin mutu saboda fargaba. " Tace Dr ni musulma ce tun daga lokacin da ku ka fada min ciwona zuwa matakin da nake kai yanzu ban taba jin cewa bazan mutu ba. Kuma fasa yin bautar Allah ba, kuma nasan cewa dole zan mutu watarana ko babu wannan ciwon. Ina da dalilaina da bana son yara na su samu labarin wannan ciwo tsawon shekaru biyar da kuka ce zan iya kaiwa na rayu, da su cikin farin ciki, in da sun sani ni da su zamu rayu cikin damuwa da tashin hankali. Nakasan ce ina boye musu, kuma ina neman mafita ba wadda zata hana mai aukuwa ta auku ba, ina neman mafita ne kawai wadda zata zama madadi a gare su. Nasan babu madadin mahaifiya tabbas, amma ana samu mai share hawaye.

Cikin jimami yake ce mata "Kin samu? " Tace Ina fatan cewa na samu. Ka ga waccan ta nuno inda nake da yatsa tare da waiwayo ta kalli Inda nake kwance, sai muka hada ido fuskarta sharkaf da hawaye ina yin wata irin ajiyar zuciya mai hade da kunshe kuka irin na tashin hankali. Da sauri Hajiya ta mike ta nufo ni.



Maman Umar ta shigo da sallama Falon shiru. Ta nufi ciki, Juma ce take hada miya yayin da Tabawa ke firar doya. Tace "Juma kina ciki?" Juma tace Sannu da zuwa Maman Umar yanzu ki ke tace? "Wallahi nice, ina Mamanmu take ban ganta a cikin ba. " Juma ta bi Maman Umar da kallo, domin bata taba jin ta kira Hajiya da Maman su ba. Maman Umar ta yi yar dariya tace "Juma mamaki ki ke ji ne?" Juma ta ce Ato ai dole inji mamaki na ga wata sabuwar Shagwaba. Ta kawaikwayi muryar Maman Umar wai Mamanmu.

Maman Umar ta yi dariya tace kin san Allah ina zaune naji kawai ina son ganin Hajiya na kira wayar ta sai naji bata shiga, shine na ca bari dai inzo." Juma ta saka dariya tace wannan karon Hajiya ta yi wa kowa bazata, nifa kawai kira na tayi tace tanason za su yi tafiya da matar Shamaki Uwargidan. Tace mudawo nan gidan har Azima, a kula da gida da kuma yara. Nace ina za suje tace kasar waje. Cikin tsananin mamaki Maman Umar ta ce, Hajiya ce kuma yau tayi tafiya ba tare da saninmu ba?"

Juma tace ina zaton Uban dakina shine kadai zai iya sanin tafiyar nan. Maman Umar tace to ina taje kuma wai harda matar Shamaki? " Juma tace ni dai bansan kasar ba, ta dai cemin kasar waje.

Maman Umar ta danno lambar Baby tana fadin ba lallai a samu Baby a waya ba saboda layinta in ba anyi masa aiki ba to fa ba zai yi amfani tana wata kasar ba.

Layin kuwa bai shiga ba. Ta kira layin Maman Nana wadda tasan ko Hajiya ta boye ma wani wata magana sai ta fadawa mata. Suka gaisa, tace "Wai kuwa Maman Nana Hajiya ta fada miki zata yi tafiya? Maman Nana tace a a gaskiya bata fada min ba, ina taje? Ban sani ba, ji nayi ina son ganinta na zo sai kuma wai ashe sun fita waje da matar Shamaki. "Wace kasa?" Maman Nana ta tambaya cikin mamaki. Maman Umar tace bansani ba nima, ga wayoyin ta duk basa shiga. Maman Nana ta yi shiru, can tace "Tofa! To kuma Shamaki ai ya sani ko? " Maman Nana ta ce Shamaki yana da masaniya ki kira lambarsa ta Dubai ko ta Chaina Nima zan kira.

Har Maman Umar ta tafi bata samu layin Shamaki ba, kuma duk su Maman Afra da Maman Iman babu wadda bata kira ba amma basu san komai game da tafiyar Hajiya ba. Gashi wayar Shamaki ta kasa samuwa.

Maman Umar ta kira su gaba daya zuwa gidan ta, tace itafa tana ji a jikinta akwai wani abu, tana zargin Shamaki ya gudune domin kar Hajiya ta sa shi ya saki Baby. " Maman Iman tace ni kuma na kula Hajiya tana son Baby, kila dai ta fita da ita ne a dubata ko zata samu haihuwa domin kusan so biyu tana yi min magana akan rashin haihuwar Baby.? "

Maman Nana tace "Hakan ma zai iya yiwuwa. " . Maman Afra tace in har batun Haihuwa ne nasan Hajiya
India zata nufa a duba mata lafiyar Baby, dan haka sai mu bincika mu gani ko can ta tafi idan canne sai mu daina daga hankalinmu.
Take Maman Umar ta kira wani a office din masu yin bizar wanda tasan shine Hajiya ke yin Hulda da shi. Ta tambaye shi ko bizar wace kasa ya yi wa Hajiya? Yace ta India ce, maman Umar ta tambaye shi tsawo lokacin da bizar zata dauka. Yace "sati biyu ne ta yi masa godiya suka yi sallama.

Daga nan suka ce bari su jira har su dawo, sai dai cikin su kowa na mamakin abinda yasa Hajiya ta ki tayi musu sallama. Domin koda Hajiya take boye musu wani abu na sirrin gidan ta, bata taba boye musu cewa zata yi tafiya. Tana yin sallama da su koda a wayane kuma ta nemi gafarar su ta kuma ce ta yafe musu, tun suna jin babu dadi game da sallamar ta ta harma suka saba bama sa jin komai game da hakan.

Shamaki wanda shima ya kashe wayoyin shi domin kar Hajiya ta kira shi ta ce ya turo mata sakin Baby tun da yaje Dubai ya kasa tafiya China domin rayuwar bata yi masa dadi, tsawon wane lokacin zai dauka yana gujewa Mahaifiyar shi, yasan yana son Baby amma ko kusa bazai hada sonta da na Hajiya ba. Yanzu gashi tun da ya zo tunanin ya gujewa Hajiyar ke damun shi. Baby sai dai kewa da tunani rabuwarsu ke samun shi. Ranar da ya cika kwana biyar a kasar, ya yanke shawara cewa ya kunna waya ya san zuwa yanzu Hajiya ta kira shi sau babu adadi. Sai dai har aka yi kwana biyu Hajiya bata kira shi ba. Tabbas Hajiya tayi fushi da shine domin da yanzu ta kira shi. Yace bari ya kira ta. Wayoyin Hajiya basa shiga. Ya kira wayar Baby ita ma bata shiga. Dan haka ya soma shiri tafiya gida domin ya gyara kuskure da ya bata.

Sakna wata yarinya ce 'yar Niger wadda suke soyayya da Shamaki, yana sonta sosai amma fa bada batun aure ba, yana ji da ita a matan da ya ke nema. Duk lokacin da zai fita zuwa wata kasa, to da ita yake fita, Ko wannan tafiyar ma da ita suke tare, sai dai tana ta yi masa korafin cewa wannan zuwan bata san meyasa ba, kamar ya fara gajiya da ita, domin tun da suka zo, babu wata shakatawa da suka fita kamar yadda suka saba, sannan bashi da labari sai na Baby da Hajiya har ta gaji da jinsa. Gashi yanzu yana maganar zasu koma.

Shamaki yana hada kaya tana tambayarsa cikin rashin jin dadi, "Wai Sweetheart mun fasa zuwa kasar China din ne? "E " ya amsa kawai ba tare da ya kalle ta ba.

Tace "Gaskiya nifa bazan tafi yau ko gobe da ka ke magana ba. Ya aje jakar da ya gama hadawa sannan ya zauna tare da daukar wayar sa yana kara danna kiran Hajiya da Baby. Kamar kullum dai layuka a rufe. Sakna ta maimaita cewa ita fa ba yau zata tafi ba. Yace kina iya zamanki mana, bani da matsala akan haka. Tace zaka biya min kudin Hotel din kenan da abinda zan ci abinci da wanda zan kashe? " Yace akan wane dalili kenan zan yi hakan? Tace akan dalilin cewar kaine ka kawo ni." Yace ni dana kawo ki maidaki kawai zan iya yi amma ba wai in dauki nauyinki ki zauna kici gaba da karuwanci a nan ba. Ta fusata, nice karuwa? Ya dago a fusace to fada min sunanki matar aure? Ta lumshe ido cikin ta kaici sannan tace na gode ba laifinka bane. Shamaki ya yi tsaki ya tashi ya fice daga dakin.

Hajiya ta juya ta kalli likitan tace zaka iya lafiya, sannan maganin da nake sha ya kare, yana taimaka min gurin rage radadin da jikina ke yi. Dr yace Hajiya kiyi hakuri maganin ba zai ci gaba da amfani a jikin ki ba, mana ana ko kinsha nazai yi amfani ba saboda matakin da kika shiga. Amma akwai abu daya, zan zo da wani magani zamu sa shi a ruwa sai mu jona miki, anyi gwajin maganin a jikin wani balarabe kuma ya samu sassauci. Hajiya ta daga kai kawai. Sai lokacin na lura da wata rama da baki wanda Hajiya ta yi. Tafiyar da take yi a hankali nake kallon kasaita ce ashe karfin haline. Tana zama kusa da ni sai na fashe da kukan da nake kunshewa. Na dora kaina a kafadarta ina fadin Hajiya da gaske ne wai baki da lafiya? Ni fa banyar da ba, suna karya ne, Allah shine kadai yasan ranar mutuwar ki kawai ki tashi mu koma gida. Insha Allahu bazaki mutu yanzu ba. Na sauka na soma hada kayan mu ina fadin ki daina sauraron su. Na sauke akwatuna ina kuka ga hawaye ga majina. Hajiya tana ta kallona cikin yanayin da bazan iya fassarawa ba. Na zo na kama hannunta tashi Hajiya mu tafi gidanmu. Hajiya ta janyo ni tare da fadin zo nan Rabi'atu. Ta zaunar da ni kusa da ita, ta kama gefen mayafinta ta share min hawaye, tace yi hakuri ki yi shiru za muyi magana ne
Na dora kaina a kafadar Hajiya ina ajiyar zuciya tana shafa bayana tana fada min cewa "Kiyi hakuri muyi magana, na zo da ke nan ne domin mu tattuna abinda ya kamata, ina son ki sani ba karya likitocin nan suke yi ba, ilmin ne Allah ya basu, ciwona na Cancer ya bayana ne tun a ranar da na haifi Shamaki. Babu wanda ya sani daga ni sai mahaifinsa, Kafin rasuwar mahaifinsa ya tada hankalinsa sosai saboda likitocin su fada mass cewa canser a bakin mahaifata yake, za a iya yanke ta, sai muka amince aka yi aiki aka yanke kamar na samu lafiya lokacin Shamaki yana guje gujenshi ya fara wayo sai ciwo ya dawo. Lokacin da likita ya fadawa mahaifin Shamaki cewa Cancer nan ce ashe ta yadu a wasu sassan jikina hankalisa ya tashi kuma ya gama likitan ya fada min, ya dage gurin nema min magana. Na gargajiya daba bature. Na samu sauki ba tare da nasan meke damunka ba. Har zuwa lokacin da Allah ya yi wa mai gidanta rasuwa bani da masaniyar ciwona. Soyayyar Mahaifinsa na tara ta a kansa, munyi wata irin shakuwa wadda ta sa har 'tan uwansa suke min mita akan nafi sonshi. Gado daya muke kwana har sai da yakai matakin balaga sannan na yakice shi. Dakyar ya fita waje karatu lokacin da ya kai matakin Jami'a, bai zauna ba sai da na bar komai naje muka kama gida na zauna da shi tsawon wata uku.....
.....
, Hajiya ta ci gaba da fadin. "Bayan ya gama karatu 'yan uwanshi duk sun kama dakunan su, nice nake kula da kasuwancin dukiyar Shamaki da kuma tawa. Allah cikin ikonsa ya gama karatunsa yazo ya kama kasuwaci. Iyaka biyayya Shamaki yana min, addu'a ta kullum a gareshi ita ce, ta samun mace mai hankali wadda zata kula da rayuwar shi bayan mutuwa ta.
Shekaru biyar da suka gabata ciwona ya sake tashi ya tsananta lokacin ne
aka fita da ni aka kawo ni nan kasar. Likitan ya gano cewa Cancer ta riga ta cini, Kafin ya yi magana da su Shamaki nace masa nasan ina da ciwon Cancer ina rokonsa don girman Allah kar ya fadawa duk wani ahalina zasu rayu a bikin damuwa kafin in mutu, ko menene ina son muna magana da shi cikin sirri. Yace min nan da shekaru biyar zan iya mutuwa na yi tsawon rai in shekara biyar zuwa watan uku kamar dai irin wannan watan.

Ina matukar kaunar yarana ina tausayin su, ina soyayyarsu irin wadda Allah ya dora min kamar yadda ya dorawa ko wace uwa akan yaranta. Na kan shiga daki inyi kuka sosai domin nasan mutuwace take tinkaroni kuma zata rabani da su, dan haka sai na damu da lamarin Shamaki, wanda zai tattara dukkan soyayyarsa ga matarsa gashi bai iya kai matsalarshi ga wani abokin shi bare 'yan'uwan shi komai nice abokiyar shawarar shi. Ko zai iya samu wadda zata tallafe shi ta yi hakuri da shi a duk yadda ta same shi? Farko ni ce na bashi dama ya memo wadda yake so, suka hadu da Maman Meema a bikin abokin shi Shamsu. Na samu kaso shidda a cikin goma lokacin dana sa a gabatar da bincike akan yarinyar, na hakura ya aureta aka soma zama, amma sai na yi kokarin gwada halayenta ta hanyar gwaji. Sai na gano cewa ba itace matar da ta dace da shi ba, bata da rufin asiri ko kada, ga son kanta kuma bata shiri da 'yan uwansa, bugu da kari ga ta sai ta dauki wayar sa ta yi transfer na kudi masu yawa daga bankinsa zuwa nata, kuma tace ba ita bace. Dan haka na sa shi ya bata takardarta ya kuma bata ba tare da ya nemi jin daliliba. Kasancewar bamu da ishasshen lokaci saboda kwanakin mutuwata kara kusantowa ya ke yi. Sai na saka Kawata Hajiya Zaliha ta memo masa mata, ta so ta bashi 'yarta, amma sai na nuna mata ta hakura bana son yara su shiga tsakanin zununcinmu, na fada mata haka ne domin bazan iya kara akan Shamaki ba. Dan lokacin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login