Showing 18001 words to 21000 words out of 51041 words
Chapter 7 - HAMSHAƘIYA-UWA-_3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
zuba maka? Yace ina azumi fa kin sani. "
Nace Baka yi sahur yau ba, gaskiya bazaka yi dore ba, ka bari sai gobe tunda ka ga ai ba wai farilla bane. Yace "Baki tashe ni ba ne ai." Na harare shi, haka ma zaka ce? Ya yi murmushin mugunta, yace ashe fa gurin maulidi muka kwana. Hajiya ta kalle ni, ni kuma na kalle shi ya kauda kai. Azuciya ta nace karyar da ya yi kenan to wane maulidi kuma a salla.
Ya katse ni, "Dama ke ki ka takura inyi in gama amma yanzu zaki zo da zamiya. Na soma zubo masa kunu, sai na tuna da wayon da nake yi wa Jafar din mu in ya ki cin abinci a ramadan ya ce wai shi yana azumi. Sai in zuba masa kunu in ce ya sha baya karya azumi..
Na mika wa Shamaki kunu cikin tsokana na ce kasha wannan baya karya azumi. Ya karba ya kurba, nace Allah ya yafe maka. Ya ce "Ameen amma alhaki a kanki.
Ke ki ka sa na karya azumi. Ya dauki kosai daya da na zuba na tura masa. Ya gutsira yace na sani fa bakya son insha wahala ne ko? "Nace ta yaya zan so ka sha wahala, amma kai kana son insha ai tunda kai da kanka ne ka shayar... Ya nuna min Hajiya da ido, ya gane maganar jiya zanyi. Na rasa wani lokacin in muna tare da Shamaki gaba daya sai in manta da akwai wani a gurin.
Juma ta sake shigowa tana fadawa Hajiya cewa man shanu ya kare tace za a kawo shi yau kuwa domin miyar danyar kubewa nake son ci. Tace to sai an kawo naman rago shima ya kare.
Hajiya tace a yi ta kaza.
Na tuna da irin yadda Tsohuwa ta bani labarin yadda Hajiya Zeena ta ke yi wa Hajiya Gwamma abinci da kanta, sai naji ina shi'awar in aikata hakan. Na ce Hajiya ina son in roki wata alfarma don Allah. Ba Hajiya ba hatta Shamaki ya dakata dan ya ji me zance. Ita kuma Hajiya da alamu yadda na yi maganar cike da kwarin gwiwa shine ya sa ta dakata, ko da dai na lura Hajiya tana son jin magana ko tsegumi amma bata nuna cewa ta damu da hakan.
Ta ce ina jinki. Nace ina son ki yi min izini inna dafa miki duk abinda ki ke so. Ta dan yi kasake, sannan tace "
"Ai baki iya girki ba, amma zan baki dama ki fara koyon girki a gurin su Juma, in hannunki ya fada zuwa lokacin da ki ka cika shekara daya sai mu duba muga ko zaki iya din ko? Haka ya yi miki? "
Nace Na gode Hajiya, insha Allahu zan sa hankalina in koya. A zuciya ta nace in banci Jarabawa ba shikenan. Kukan Anisa ya dauki hankalinmu ta karaso da gudu Shamaki ya bude hannu amma sai ta fada Jikina tana fadin Mommy kinga Meema ko ta shanye min icecream kuma ba ni ce na bata ba."
Shamaki zai yi magana Hajiya ta daga mishi hannu alamun ya yi shiru ta gefen ido na lura da su.
Na rungume ta, nace, yi hakuri, na fara share mata hawaye. Nace. ba na fada miki Yaya meema zaki ce ba? Tace Yaya Meema ta shamin abuna. Nace zomuje daki zan baki wani amma ki ce kin yafe mata wancan din. Tace "e na yafe amma mommy za ki yi mata fada? " Na ce a a zan yi mata nasiha ne zakigani bazata kara ba.
Na mike muje na bata Icecream ta tafi na dawo in tambayi Hajiya ko yaushe zan fara koyon. Tace "Ni da bani ce wadda zan koya miki ba, ai saidai ki tambayi Juma din ta fada miki ko? " Nace to Sai ga Meema da Mubina da gudu suma gurina suka zo Mommy mufa Icecream? Nace yawwa Yaya meema akn wane dalili ne ki ka amshi abin Anisa ki ka shanye shi? Tace Mommy tayi abazanci ne fa ta jiye kuma kin fadavmana cewa ba kyau." Muka sa dariya har Shamak, nace almunbazaranci aka ce, Duk da haka ba sha mata zaki yi ba, a matsayin ki na Yaya zaki sa mata a cikin fridge ne. Bana ce ke zaki na kula da su ba?Ta daga kai alamun E. Na ce in kuma bazaki na kula da su ba, to zan bawa Mubina ta zama Yaya. Ta kama kunneta "Na daina Mommy har yanzu ni ce Yaya ko? "
Nace ke ce mana, amma in kuwa kin kara kuma zan ba Mubina. Muje in ba ku. Muka tafi.
......
A cikin satin na soma koyon girki, tunda Allah ya bani damar shiga kicin sai nayi amfani da wannan damar na ke yi Caearching da waya ta ina nemo kalolin girki na zamani, saidai Hajiya bata bukatar su, kuma ni ina son in koya, na fara tunanin yadda zanyi, sai na kuma zuwa na nema iznin Hajiya, nace ina son in ke dafawa su Anisa abincin zuwa makaranta maimakon Indomie kullum. Tace in fada mata dalilina kawai wannan ba shine ainihin dalilin da nake son yiwa yaran abin tafiya makaranta ba, nace ina shi'awar inga ina hadawa yaran abin kari ne. Tace "Bata Hana ba, amma in fada mata ya zanyi da Babansu? " Nace ai lokacin yana nan kafin Juma ta gama komai na karin kummalon gidan zan sallame su.
Tace "Bana son a shigar min rayuwar da na saboda jika. " Nace zan kiyaye haka. Tace in gwada so daya a gani. Ranar na saka a zuciya ta zanyi. Daga sallar asuba na shige kicin. Dama tun dare na tanadi kayan girki na, soyayyar taliya mai kaza na fara yi musu Allah ya taimake ni nayi yadda naga an koyar kamshi ya cika gidan Shamaki ya tambayi Juma cewa yau kuma me ake dafa mana ne? Tace Mommy yara ce ta shiga kicin da kanta yau, tace yaran ta sun gaji da Indomie da planten yace "kice za su ci dadi. " Juma tace ga shi nan dai yana ta kamashi a range mana. Na hada musu lemon Apple da kwakwa da madara. Na zuba musu a cikin jarkokin su na makaranta wanda ake sa musu shayi. Tare da
Juma muka kammala, na shige da sauri na yi wanka sannan nazo na samu suna jiran abin kari, na zuba musu lokacin yaran suka fito suka gaida Hajiya da Daddy sannan suka gaida ni. Anisa ta sunbaci kumatuna Mommy bye, nace bye kada ku manta da addu'ar fita gida, suka ce tom. haka suka tafi ina binsu da kallo cikin kauna.
Haka kuma da Shamaki ya tashi ya nufi
Cikin domin shirin tafiya Kasuwa haka nan kuma na tashi fatana Allah ya sa kar ya zo min da bukata tun da ya zamar masa jiki.Ni kuma na gaji tulus farko yi na yi kamar bazan je dakin ba. Hajiya tace "Kina son dai ya makara fita ne ke? " Haka na tashi na nufi ciki.
Yana shirin shiga wanka na yi sallama, yace yawwa zo ki min wanka yau duk na gaji. Sai da na shiga don in masa wanka, ashe wai yau kuma a bandaki ya ke son biyan bukata da ni. Haka na yarda. Ina mamaki yadda Shamaki ke min. Ko haka kowane namiji ya ke yi wa matarsa shine bansani ba.
Sai da ya tafi na dawo na karya na kwanta, aikuwa sai azahar na farka.
Azima ta shigo kicin muna yin girkin dare, ta kalli Juma ta ce. "Ina son a yi min jolof na kuskus. Juma tace, sai mun karasa tukunna. Ta bata rai yanzu nake so. Na dago na dube ta kamar zanyi magana sai kuma na fasa. Juma tace yanzu sai Allah wannan 'ya me zan sauke in bai dahu ba in dora naki? Tace ko ma meye a sauke ina jin yunwa gaskiya." Nace Haba Azima kicI ga tuwo can angama, ko ga sauran abincin rana in kina so, amma ayi miki sabon abinci bayan ana aiki da gurin sai ki jira. Ta kalle ni a fusace tace, "Amma dai kin jira na saka sunanki ko? " Raina ya baci domin bana yin rashin kunya kuma bana son me yinta ko kada. Nace bazata dafa miki ba, in kin matsu ki dora da kanki. Ta dube ni ke a wa kuma!? " Na yi mata banza, Juma tace Kiyi shiru 'yarnan ki rabu da ita a dafa mata. Nace wallahi baza ki dafa mata ba, ko mun gama zangani ni da ita..
Ta fice fuuu Juma tace yanzu zataje ta zanawa Hajiya. Nace taje mana waye bawanta? Tace ai matsalar Hajiya tana da kwatanta gaskiya amma tana da son nata, amma dai yanzu bari muga yadda abin zai zama.
Shiru bata dawo ba har muka gama wai Juma bari ta dafa ta kai mata, nace bazaki dafa ba.
Na zaci Hajiya zata min magana amma shiru har zuwa washe gari da na tambayi Juma ko Hajiya ta yi mata magana tace ai na yi mamaki Hajiya bata yi maganar ba. Amma da ace da ne fada zatayi sosai tace dan haka ta dauki masu aiki su kula mata da gida, kuma kowa a bashi abinda yake so yadda muma bata taba yi mana Shamaki da abinda muke so ba.
Nace ni dama haushina take ji Azima bansan me nayi mataba. Tace ga abinda ki ka yi mata nan kin auri wan da take mutuwar so, yarinya karama kar kiga irin yadda ta ke kicifi a kan sa. Nace ai gashi nan zata aure shi ni menene nawa. Juma tace auren ma ai ba wata daraja zata yi ba, tunda ta zubda kai, a waje sai dai ina mamakin yadda Hajiya ta yi gaggawar saka rana duk da cewa yarinyar ta yi ciki, kuma ya ce ba shi bane amma ta kuma ce shi zai aure ta. Son kai irin na Hajiya ina mamaki sai dai da yake duka nata ne. "
Nace Allah ya kyauta amma ai dole ta yi abinda zata rufawa 'yar dan uwanta asiri.
Juma tace haka ne, amma abin da mamaki. Nace to ke kina tunanin ko shine ya yi mata? Tace 'A'a ni bance ba. Ina zan sani 'yannan karki daure ni, Hajiya ta ji na fadi haka ai sai tasa an rataye ni. " Nace Juma ai dan Adam bashi da garanti kuma zuciya bata da kashi. Tace Hamm haka ne, Allah dai ya shirya uwar wannan yarinyar ta biyun bana rike sunanta. " nace Mubina tace, "ai bata cika magana ba, amma ta kamashi da wata yarinya amma Hajiya ta shafawa idon ta toka tace anyi wa danta sharri." Nace abin dai sai addu'a. Tace shike nan kin gama magana.
Bisa ga dukkan alamu Juma suna zargin shine wanda ya yi cikin kamar yadda nake zargi. Amma zan yi kokarin bincikar haka.
Wata asabar ta karshen mako, ya fita motsa jiki da safe, lokacin da na fita gaida Hajiya baya gurin, na zauna na gaishe ta, ta amsa, zan tashi tace ina da magana da ke, gaba ya fadi, na koma da sauri na zauna. Tace "Da anyi babbar salla da sati daya za a daura auren Azima da Shamaki. Na hadiye yawu da kyar, tace gaba, "zai aje ta a daya daga cikin gidajensa dake unguwar nan ko kuma wata unguwar dake kusa da wannan, amma kije ki yi shawara in ke ce ki ke son ki zauna a can to na baki kwana biyu ki yi tunani ki zo ki fada min . " Na ce ba sai na yi wani tunani ba, duk yadda ya yanke ai shine mai gida.
Hajiya
Tace "Kije dai ki yi tunani karki yanke shawara cikin fushi, yau saura kwana arba'in a yi biki, bana son danasani ne a rayuwa, kuma bana son yin abu ba hujja shiyasa na baki dama, kiyi tunani kuma ki yi shawara a inda ki ke da yarda da aminci. Bana son jayayya ba halinki bane kije sai na jiki.
Na ce to na tashi na nufi daki jiki ba karfi. Nafada kan gado na saki kuka, bansan ina son Shamaki har haka ba. Hajiya bata san zafin kishi ba tunda ba ayi mata kishiya ba. Shiyasa take fada min maganar auren mijina kamar yadda zata fada min abin arziki. Na dau lokaci ina yi sannan na lallashi kai na, na nufi dakinsa don inga ko ya dawo. Ya kashe wayoyin sa ya zube su a kan gado. na kunna wadda nake bincike na shiga ina bi, har yanzu dai yana nan akan halinshi akwai wadda na lura sun dinke da alamu yana matukar son ta kuma ya nuna ya matsu su hadu. Na dakko wayata na dauki lambarta. Na saka wayata na kashe masa na koma daki. Ina ta shawara in kira ta ne ko kuwa in goge, me yasa nafi kishin wadannan matan wajen akan Azima wadda zai aura.
Nasan yana fada min kalamai, amma meyasa baya fada min irin wadanna. Me yasa ina masa duk yadda yake so koda ni bana so amma hakan bai hana shi bin matan baza ba.
Na kira Umma muka gaisa na fada mata cewa maganar auren Shamaki ce saura kwana arba'in yau. Sai naji zuciya ta ta karye, na soma kuka. Umma Cikin sigar lallashi tace menene abin kuka, ki share hawaye mu yi magana. Nace Umma wadda aka yi wa kishiya kawai zata iya gane me nake ji a halin yanzu. Umma tace, "Ni dan ba a yi min ba shine yasa bazan fahimci radadin da ki ke ji ba? " Cikin kuka nace Umma kirjina kamar zai fado, ni sai inji ma kamar ince masa ya sawwake min, ina cikin damuwa Umma. Tace "Amma ban taba jin ance wata ta fadi ta muru dan kawai anmata kishiya ba. Dan haka kema bazata gagare ki ba, abu ne ma kowa ya zauna da halinsa. Shi mijin naki ya canza miki ne? Nace A'a bai canza ba. Shi ko maganar so daya ya min, Hajiya ce tana fada min kamar mai fadin alkhari ko a mijinta. "Umma tace alkhari ne mana insha Allahu. Ke dai ki kwantar da hankalin ki kar ki nuna cewa abin ya dame ki ko da wasa. Ki zuba ido akwai Allah Karki yarda ko da kalmar magana ki cutar da wani, ki sa zuciya daya tsakanin ki da kowa, kuma gara a ce kai aka cuta da ace ka cuci wani. Nace insha Allahu. Yanzun ma Hajiya ce tace wai wani gidan za a kai Azimar amma in ina son ni a kaini can to inyi shawara ni ina ganin gara in bar gidan nan domin Hajiya ni ba wai ina son ganinta bane tunda ta min wannan maganar.
Umma tace ko kusa karki matsa ko ina. Hajiya tana bukatar ki kusa da. Ki nutsu ki fahimci maganar, Zai aje amarya a wani gida, amma in kuma na so sai ke ki koma can. Ina fatana kin gane cewa can din ba naki bane. Nace shikenan zan zabi nan din. Tace yawwa Allah ya miki albarka ya baku zamavlafita dukanku. Na cw ameen. Na dan samu sauki da Umma ta taushe ni. Idanu sun min jawur fuska ta kumbura. Na koma kan lambar yarinyar nan. Na yanke shawarar in kira ta. Na kira tayi ringing ta katse a na biyu sai aka daga, bance komai ba na yi shiru sai naji ance "Waye ne.? " Gaba ya fadi kunsan muryar wa naji??
Muryar Azima naji wadda na yi sauri na kashe jiki na ya kama rawa yanzu Shamaki saboda Allah ya yi wa kansa adalci kenan? Na yi shiru ko zan iya tuna kalaman da suka yi musaya na batsa. Na mike na nufi dakin dan in sake dubawa, muka ci karo da shi a corridor din dakin. Muka kalli juna. Yaune na fara jin wani abu na tsanarsa a zuciya ta na kauda kaina sannan na juyo Yace "Baby/" Na tsaya can ya tako zuwa gurin ya kama kafada ta ya juyo da ni, ya dago fuska ta "Kukan me ki ke yi? "
Nace ni banyi kuka ba. yace "kar ki yi min karya ga nan fuskar ki a kumbure." Na ce bacci na tashi. Ya ja hannu Na muka nufi dakin shi. Bakin gado ya zaunar da ni wai in fada masa me aka yi min. Na kafe akan ba komai har ya fara fusata, yace shine nan tashi kije tunda kin kafe. " Na mike na nufi dakina, dama ni zantukan shi sun dame ni. Na kwanta ina mai bankin cikin auren Shamaki da na yi. Yanzu banda ta'addanci me zai sa