Showing 45001 words to 48000 words out of 51041 words
Chapter 16 - HAMSHAƘIYA-UWA-_3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
kwana talatin ya tsinci Video su yana yawo.
Dole ta tashi ta share masa wannan hawayen domin kuwa yanzu ita garkuwar shi....
.....
Gama wannan tunanin ke da wuya na tashi na kira Hassan yaron Kantin Shamaki da yake yanzu sun saba da ni, ina kira ina tambayar Shamaki ya ci abin ci kodai wani abu kamar dai yadda Hajiya kanyi, sannan Shamaki yana aiko su su kawo wani abun in ya siya kamar Zuma da dai sauran su.
Nace masa ina son ganinsa. Ya kuwa zo cikin sa`a , Shamaki ya fita. Muka zauna a falo. Nace Hassan dan Allah so nake ka kaini guri 'yan sanda zan shigar da ?ara ne. "Karan wa za ki kai kuma?" Ya tambaya cike da mamaki. Nace wata mata ce zata takura min. Yace "Anty matsayin ki a kasar nan ai kin girgimi ki je karamin ofishin 'yan sanda. Kina da kimar da zaki daga waya ki kira kwamishina ki fada masa bukatarki, yanzu dai ki fadawa maigida zai iya kiran kwamishina yana da wannan alfarmar."
Nace aiko labarin bana son yaji, yanzu dai ya ka ke ganin za a yi so nake ma ka tafi kafin ya shigo. Yace "In kuma kina son ¡äyan sandan farin kaya ina da wani aboki Dss ne zan baki lambarshi sai ki kira shi ki fada masa kece matar Aliyu Baita, kudi kawai za su yi aiki. Nace to ba matsala. Muka yi sallama ya tafi. Domin yanzu bani da wata damuwa akan kudi saboda ya bude min account dina kuma ya bude na harkokin gida kamar dai lokacin Hajiya. Washe gari Hassan ya turo min Number. Sai da Shamaki ya fita sannan na kira Nace masa nice matar Aliyu Ali Baita. Yace . " Ranki ya dade Hassan ya fada min zaki kira ni." Nace Yawwa wata ce take yi wa maigidana barazana zata saki wani Video na batanci a gurin sa, to ina son batare da ita da shi sun sani ba, ina dakatar da abin, Hassan yace in maka magana. Yace "Ranki ya dade maigida da kanshi kuma yabarta araye? Nace yanzu ma ba zata zan yi mishi domin shi yana nan yana lallashinta a karbi kudi to gara ku kuci kudi. Yace Angama Haiiya zan je in hadaki da oganmu yanzu."
Ya hadamu da shi nayi masa karin bayanin komai, nace masa abin da ya faru tun can baya ne yanzu baya tare da ita. Ita Kuma ga bukatar ta yanzu wai sai sun koma soyayya shi kuma yace ya ma daina gaba daya. Ogan yace "Ki turo min da Number dinta da kuma hoton ta. Take na tura masa duka saboda na ga hoton ta akan dp din ta na whatsapp na kira shi yace ya gani in jira zai neme ni.
Shamaki ya shigo dakina ya same ni muna Homework yace "Wai ina malamar Lesson din yaran nan ne ki ke ta fama da lesson?" Na ce ta bada uzri wai yau zata je wata gaisuwa shine nace ba matsala zan kula da su yau. Yace "Ya yi kyau. in an gama da su ki sameni a dakina."
Na barsu na nufi gurin shi dama akwai hanyar da ta hada ni da shi haka ma Azima ta cikin Falonmu. Na same shi yana kokarin kunna talbijin. Ya wai wayo yace " Au wai dama kina baye da ni ne? " Na ce to me zan jira in ban amsa kiran sanyin zuciyata ba. Ya yi Murmushi ya zauna, "Zonan" ya fada yana kallo na. Naje na zau a kan cinyarsa domin nasan nufinsa ke nan. Ya sulmiyo da ni ya dora hancinsa a kan nawa. "Mota zamuje ki zaba yanzu." Da sauri na zuba kwayar idanuna cikin nasa. Mota fa! Yace " To menene a cikin mota Allah na tuba. Na rungumeshi na sunbaci kirjin shi, zaka kai ni in zaba, to kuma wa zai koya min?
Yace "Samu ya fi iyawa Baby zan koya miki kafin sati kin kware. Sai muna fita dasafe a ranar asabar da lahadi. Na sake kankame shi cikin kauna.
Naje na sako Jallabiya da mayafinta nace wa su Meema Dady zai sai min mota yanzu zamuje.Suka kwashi murna nace da Juma bari mu dawo.
pShi na baiwa zabi ya darzarmin mai kyau fara kal kirar Yaris sabuwar zubi. Muka dawo gida yara sai murna duk yawan motocin gidan amma sai fadi suke Mommy zaki kaimu makaranta gobe? Nace Sai na koya.
Muna zaune da Shamaki kira ya shigo waya ta. Na tashi da sauri na fita zuwa tsakar gida. Yace Ranki ya dade zaku iya zuwa yanzu mun kama wannan matar. Nace Inane Office din? Ya yi min kwatance' nace zamu zo yanzu. Na koma na shiga na same shi, ya bini da kallo ya ga na yi abinda ban saba ba nafita waje na daga waya. Nace taso muje. Yace "Yace ina kuma da wannan daren?" Nace Yanzu zamu dawo. Ya taso yana fadin Baby bazan yi miki musu bane amma bana son fita yanzu. Na kama hannunshi yi hakuri. Kai zaka jamu bazamu fita da direba ba. Saida muka hau titi nace Office din Dss zamuje. "Mu yi me?" Ya da sauri, nace taimako? Yayi shiru har muka isa,. Shugaban yana ta kallona yana mamaki wai dashi muka yi waya,ya sa rai zaiga wata babbar mace. Nace ni ce Shamaki tunda suka gaisa sai naga ya kame guri daya,da alama bai son wannan tattaunawar da muke yi da dansandan farin kayan ko ince kishi ne ya sa shi daure fuska.
Dansandan yace Hajiya kinsan a ina aka kama matar nan? Nace a a Yace a Kaduna tunda muka sa layinta a trak muka gano tana Abuja yaranmu sun kama hanya sai kuma muka ganta a Kaduna. A Hotel aka kamata sun sha ita da saurayin ta sun bugu. wayar muka fara karba yanzu kuma sai abinda megida yace za a yi, ya dubi Shamaki yace Ranka ya dade. Shamaki wanda ya kasa gane me muke nufi ya ce "Kunsani a duhu."
Dansanda ya daga waya yace ku kawo wannan "yar iskar. Shamaki ya mike tsaye da sauri yana kallon ta. Ya nuna ta da yatsa yace Sakna. Wata zuciya ta zo wa Shamaki wuya ya daga hannu ya falla mata mari sannan ya kalle ni ida nunsa suka kawo hawaye. Na girgiza kai, nace wannan ba wata damuwa. Na kalli Dansandan nace ina wayarta? Ya miko min wayar tare da fadin ta cire cord din wayar. Na ba Shamaki nace ka yi yadda ka ke so. Yace a bata ta l goge Video da hannun ta. Nan take ta goge Sannan Shamaki yace ku bata layinta ne kawai shima in kunga dama amma ku rike wayar domin ni ne na saye ta. Sannan kar ta bar nan sai ta tabbatar muku cewa tafita harka ta. Ogan Cikin son tsorata ta yace ai kasar nan zata bari ba ta ce ita ba 'yar Najeriya bace wai 'yar Nijar ce. Na karya ta ke yi domin 'yan Nijar sun san karamci da mutunci ta dai fadi daga inda ta fito. Yace koma dai daga ina take ko dai ta koma can, ko kuma mu kashe banza mu ba karnukanmu namanta su cinye.
Shamaki yace na gode
sannan ka tura lambar asusunka zan baka sako kai da yaranka. Dansanda ya yi godiya sannan yace ka kara rike madam sosai domin a sanin da nayi wa halin mata a wannan lokacin da wahala matar ka ta ga wannan abin ta yi shiru sai ta yada ka a gurin kawayenta da 'yan gidan su, sannan ta ce ka sake ta. Shamaki yace Na gode zan kula sosai. Ya rako mu har mota.
Mun fara tafiya ba wanda yace kala, sai ya tsaida mota a gefen titi ya Juyo ya kalle ni. Baby naji kunya yau nayi..... Nasa hannu na rufe masa baki,sannan nace tawuce wannan maganar fatana ka kara kiyayewa kuma idan ka ga wata mace wadda ranka ke sonta ka zo ka fada min zaka aureta akwai gurbin mata biyu a gidanka. Yace haba Baby Allah ya bani ke me zanyi da wasu matan kinsan Allah ko Azima darajar Hajiya ne amma wani lokacin ko kallon ta bana son yi." Na ce amma na jima da hanaka fadin haka taci gaba da cin albarkacin Hajiya Ka dinga sakar mata fuska. Yace jiya da kika sani gaba dole na kwanta da ita sai naga duk ta bani tausayi kinga yadda ta ke yin rawar jiki kuwa? Nace ka gani sai ka dauki alhakinta. Yace shikenan duk na bari zan yi yadda ki kace. Na kama hancin shi nace to mijin tace muje gida....
....
Sannu a hankali rayuwa ta canza girma ya hau kaina da kananan shekaru. Ina kokori sosai ganin cewa na kula da kowa yadda ya kamata. Bangaren su Maman Umar ina mu 'a mala da su kamar 'yan uwana na jini kuma sai dai munfi shiri da Maman Iman. Duk da cewa wani lokacin suna dan nuna min wai na mallake musu kani, sai dai na barshi a wasa suke sai dai inyi dariya ince dan Amana ne shi ko dana mallake shi bazan cutar da shiba.
Ko zaman minti biyar ka yi da mu ni da Shamaki sai ka fahimci akwai kauna mai yawa kuma mai karfi tsakanin mu. Ance zomu zauna zo mu saba amma muna kiyaye wa domin ban tuna wani rikici da muka yi ba a tsakaninmu. Sannan ga fahimtar juna.
Bayan hannu na ya fada da tukin mota wata asabar nace yau zan kwashi yarana muje ziyarar dangi. Yace "Ina ne? Nace gidanmu mana. Yace "Karfe nawa za atafi a kuma dawo karfe nawa? " Nace haba Gaye kai dakana kasuwa ma. Yace ni bana son a kai magariba ne Baby wallahi in na dawo bakyanan wani irin kunci nake ji a zuciya ta. " Nace to insha Allahu ana yin la asar zamu dawo. Nace tun jiya nake jin marmarin tuwon Ummanmu. Yace "Allah ya bada sa'a in kuma ba tuwon suka yi ba fa?"
Nace dama izni nake jira in kira Jamlla in ce amin tuwona sukuma yaran nan zan tafi musu da abinci kasan basa kaunar tuwo kuma bana son in saka Umma girki kashi biyu. Kafin ya yi magana Azima ta yi sallama ta shigo da yake muna zaune a falonsa ne.
Ta zauna sannan ta gaishe damu. Muka amsa tayi shiru alamun zatayi magana da shi. Zan tashi ya kamo kunnena yace ina zakije?" Nace zamuje mu yi shiri ne. Yace "Ban sallame ki ba,ki jira." Na kalli Azima wadda ba hakan ta so ba. Nace Ina Safna yau ba a kawo taba. " Tace tana bacci. Nace ta zo ta rakamu cikin gari.
Na fada da tsokana. Azima tace "Cikin gari zaku ke nan yau?" Na ce I. Tace "A gaishe su. Ta kalli Shamaki tace "Yaya Dama zantuna maka maganar wayar ne ina son ina kiran su Maman mu muna gaisawa don Allah." Yace in siyo waya ki ci gaba da Tiktok kenan. nace miki sai dai mai botira kin ce ke bakya son mai botura ba sai ki sha zamanki ba. Na zuba mishi ido ina kallon shi, Ya ki kallona domin ya san na fada mishi ya sai mata wayar tunda ya zo ya fada min yadda suka yi. Ta ta mike zata tafi. Nace Azima wace iri ki ke so? Ta ce Ipone ita na saba rikewa. Ya yi karaf yace "Wallai baza a sai Ipone ba." Na ce ka yi hakuri ka sai mata duk wadda ka ga dama amma banda mai botura.
Ya rike min hanci dakarfi tare da fadin "Ya zanyi tunda kin ce ayi. Na saki yar kara nace Azima knga Yayanki zai ciran hanci ko? Tace "Ummm sai anjima sai kun dawo ku gaishe su." Nace za su ji. Tana fita nace yanzu kai dama baka sai mata wayar ba. Yace to Allah ya baki hakuri yau zan siyo. Yanzu muje ciki dan Allah ki dan yi min tausa ko da minti goma ne. Nace Amma dai iya tausa zanyi maka dai domin na san hali yanzu sai ka canza labarin. Yace banyi alkawarin iyatausa ba sai abinda hali yayi.Na kira wayar cikin gida na fadawa Rahin cewa ta shirya min yaran nan zamu fita. Na dube shi Nace to goyani muje in yi maka. Ya duka na haye bayansa ina dariya, yana fadin sai in goya irinki goma.
Tare muka fito dashi wai shima muje ya gaida su Umma sannan mu aje shi a kasuwa nace dawo wa fab? Yace zan kira Malam Bala. Har mukaje layin mu ba wani gyara da ya yi min atuki. Muna fakin yace "Kin san Allah Baby zaman su Umma a lugun nan ya ishe ni,da zasu yarda sai a sai musu wani gidan koda awata unguwar ne." Nace za su yarda mana kuma kaga wannan gidan na nuna masa wani gida, a bakin titi. Nace masa maigidan ya rasu kwanaki an saka gidan a kasuwa za a saida saidai bansani ba ko an siyar domin Abba naji wani abokin shi ya taya ba a sallama ba,nazo gida lokacin naji suna maganar. Yace ai bashi da girma. Nace kuma ba laifi dan ya yi biyun na su Umman. Yacc "Inda wannan za su sai da (ya nuna na kusa da gidan.)ai da sai a hada ayi musu harda karamin masallaci Allah ya kai ladan a Hajiyarmu. Nace wallahi kuwa, amma bari zan tambaya. Muka shiga layin muna dan gaisawa da wadanda muka sani har muka shiga gida. Jamila ta shimfida tabarma yazauna sukagaisa da Umma ya tambayi Abba tace ya fita. Su Jafar suka gaida shi. Ya mike yace to shi kam zai wuce kasuwa kar in manta duk yadda akayi sai in fada masa. Nace ka manta ne ni zan kai ka yace to ko dai in amshi makullin . Nace ba girman ka bane. Ni zan kaika, Kuma ina son in zaga in nuna wa "yan uwa motata. Nace da Jamila ga sunan ki kai su gidan kitso kafin in kai Dadyn su kasuwa. Tace "To".
Muka fita muka hau mota. Muna tafe muna hira. Nace sai na bishi naga office din sa. Yace "Bana son a kalle min ke. Nace ai ba a sanni ba. Muka taka zuwa gurin Kantin na su yana ta gaisawa da mutane har muka shiga ciki. Nayi murmushi na tuna lokacin da muka zo siyayya da bikinmu. Su Hassan da Dahiru suka taso suka gaishe mu,sannan muka nufi sama inda office dinsa ya ke. Ofishin kato ga kujeru ga bandaki, ga Dininig ga talbijin ga Firji. Nace in tambaye ka wani abu baza kaji haushi ba? Yace "Tambayi." Nace ka taba amfani da wata mace a nan? Yace Haba Baby ai duk abinda mutum zai yi a rayuwa ya tsare kimar shi a gurin sana'ar shi da kuma unguwar da yake, saboda su za su fara bada shedar sa in ya mutu. Ko na Azima wata kaddara ce ko ishara Allah ya nuna mana. Ya zuro hannayen shi a kuguna yace kuma fadin haka da kika yi har kinsa naji ina shi a war yi a nan din." Na ce haba dai Yalabai da zu fa a gida daga tausa ka zarce a ringa daga kafa mana yau ma dai girkin Azima ne.Yace ai sai dare, kuma kinsan irin wannan abin da kwakwalwa ta amsa abinda tunani ya bata sai ya taso ba maganar anyi dazu bane. Mu maza muna samun karin lafiya. Haka dai yaje ya rufe kofa Hassan ya kira yawar Ofishin wai yana da baki, yace su jira akwai wata bakuwar a ciki. Abin mamaki Shamaki ya kusance ni a ofishinsa cikin wani irin doki kamar ranar ya fara gani na. Sai da muka nutsu nashiga na yi wanka tsaf harda ruwan zafi a bandakin. Nace abin mamaki yanda naga kayi kamar ba dazu a gida sai da ka samu natsuwa muka fito ba.Yace "Yace Baby akwai abinda mata basa ganewa. Wato kinsan ita shi'awa da ki ka ganta wata abace da bata da madakata, sannan ba komai ke motsa ta ba, haka karamin abu kan iya motsata.Mu maza muna son abubuwa irin wani abu da ba a saba yi ba. Misali kamar wannan, in ba dama irin haka ta samu ba ai bazaka dakko matar ka daga gida ka yi auratayya da ita a Office ba. Watarana a mota wata rana kaje da matar ka Hotel kamar yadda na taba yi kina ta yi min shirme." Mukasa dariya. Nace Na gane yanzu kawai duk inda ka ke so a shirye na ke. Yace na gode da wannan damar da ki ka bani, domin ina son ire iren haka. Wannan shine yake sa mazan da dama neman mata, saboda suna son irin wannan kalolin amma mata basa ganewa wata sai tace mijinta dan iskane, ko tace yara ita ta girma.
Nace Allah ya kare mana ku da daga sharrin matan waje da duk musulmi yace "Amine."
Nace muje