Showing 48001 words to 51000 words out of 155476 words
umman kesa Rai a samun haihuwarsu..
Wani ciwo umman Cameroon tayi sosai Wanda yasa umman AQEEL ASAD din tafiya Cameroon kusa tsawon shekara biyu Bata dawoba Wanda ya bawa Bilkees damar adopting mufeeda itada AQEEL din acan qasar sbd mahaifiyarta data rasu a qasar batareda ansan danginta ba kasancewarta Yar Nigeria yasa aka bawa Aqeel din ita Kuma yasan mahaifiyar tata sosai tun kafin yayi aure lokacinda tayi auren ne Bai saniba bare Mijin data samu cikin dashi Dan Haka Bai musaba da Bilkees ta nace akan tanason babyn.
Ta karba babyn ne sbd kare matsayinta agun umma kada tasan Bata haihuwa shikuma ya amintarwa Bilkees karba babyn ne sbd tallafa rayuwar yarinyar kodan Allah yasa sakamakon hakan shima Allah ya basa wadda zai tallafi tasa 'yar uwar da Maminsa aduk inda suke duk da yasan tini Maryamah tayi girma yanzu.
Babban kuskuren dasukayi shine rashin sanar da umma ba Bilkees ce ta haifi mufeeda ba,
Shi yayi hakan ne sbd idan umman tasa daukota sukayi bazata taba barin su riqetaba sbd hakan kawai yayi shiru akan sune suka Haifa mufeeda Dan Haka a duniya bayan shi da Bilkees babu Wanda yasan basune asalin iyayen mufeeda ba har ita mufeedan wadda ta taso cikin gata da kulawa tareda daular arziki tana yanda takeso duk da kasancewar daddyn nata Mai zurfi a addininsa.
Ita kanta umma sosai take kaunar mufeeda kusan fiyeda komai Wanda hakan kesa Bilkees sake Jin Dadi tana sake sakewa a rayuwar aurenta data samu yanda takeso tako Ina wadatacciya rayuwar hutu da kwanciyar hankali sukeyi.
DR SHAYKH AQEEL ASAD lafiyayyen kyakkyawan matashi abokin manya ne dayakeda wayewarsa da ilimin Boko Dana addini masu zurfi dasuka kamasa,
Iliminsa na addini Sam Bai Hana wayayyar rayuwarsa ta matashin Alhajin Nera bayyanuwa a duk inda yake,
Rayuwarsa yakeyi cikin aji da nutsuwa da kwanciyar hankalin Wanda kudi da hutu suka Gama shiga tako Ina,
Shekaru da yawa shaawar dawowa kasarsa suka fita Ransa gabaki daya sai yanzu da mahaifiyarsa ta takura tanason dawowa gida yasa dole suka tattara suka dawo bayan shekaru masu tsayi da yayi acan tareda iyalin nasa,
Dawowarsu a Lagos zasu zauna sbd Manyan kamfaninsu da kusa duka huldodinsu da dukiyarsa suna Lagos din tun na mahaifinsa harma da nasa daya mallaka ya hade Dan Haka ya zabi zaman Nan din,
Babban qatoton gidansa da aka Gina Masa tun Bai dawo ba suka tare dake Victoria island,
Tareda ummansa suke zaune a gidan da nata bangaren na musamman.,
DR SHAYKH AQEEL ASAD yanada raayi da aqidar Boko sirke Acikin aqidunsa ta rashin raayi ko shaawar qarin Aure ko kula wata macen,
Dayar ta ishesa baya bugatan qari sbd rashin son damuwa ko tashin hankali Acikin rayuwarsa.
Dawowarsu duk duka baifi watanni ba aka saka mufeeda a university 100 level cikinma karatunta yayi sauri Dan batafi shekaru 17 ba,
Tarbiyar mufeeda gabaki daya ta ummenta ce Bilkees,
Komai kusan tare sukeyi kamar wasu Aminai shiyasa duk abinda Bilkees tayi raayinsu daya yake zuwa da mufeeda...
SSG Hayat Aminin AQEEL ASAD ne tun a UK suke tare harsuka Gama karatu suka dawo Nigeria suna tare sosai sai daga baya da AQEEL ASAD din yabar kasar suka rabu Amma still suna tare sbd iyalansu da daman sun san juna sun shaqu da juna matuqa sun zama kamar family daya,
Duk fushin da Nafee keyi ta tafiyarta da yayanta subar qasar akan AMAL IDON NERA da Mijinta gidan AQEEL ASAD take tafiya gurin Aminyarta Yar uwarta Bilkees su taru suyita jajanta lamarin, shiyasa Bilkees da mufeeda Suma sukaiwa IDON NERA muguwar tsana tun Basu sansu ba sbd ayanda suke tsananin kauna da so da kishin AQEEL ASAD dinsu akace wata zata shigo ta lalata rayuwar farin ciki da kwanciyar hankalinsu basusan ya zasuyi iya daukan lamarin ba.
***Ayanzu ma da maganar auren ya tabbata na AMAL Idon Nera da SSG din Basu Dena tsinewa zuriar Idon Nera din ba Dan Haka kusan kullum babu ranar da basa adduar Allah ya kawo abinda zai Hana auren su huta.
***Yauma suna tareda Nafee din wadda tafara figewa kamar ba matar a dah take rayuwa cikin hutu da kwanciyar hankaliba.
Nafee dai zuwa lokacin ta fara hakura ta sare sbd SSG dai ya nuna zai iya rabuwa da ita akan hakan Dan Haka takejin tayi sanyi zata hakura.
Cikin zafin zuciya da takaici Bilkees tace,
"Nafee Ni inaga tunda matar Nan kowa yasan karuwai ne bayan barna babu abinda suke yadawa a duniya
Mezai Hana mu shigarda qarar barnarsu ga kotun musulinci kokuma ga shugaban Yan hisbah gabaki daya,
Kinga fa ba Dan Allah zasu auresaba shigowa kawai zasuyi su tarwatsa zamanki da Mijinki da Yayanki su qara gaba,
Wallahi karki yarda duk haukar da SSG zaiyi ki Dage ki qwacesa daga tarkon wainnan mutanen da babu Allah a ransu.
Inaga kawai mu sanarwa da hukumar hisba babba abinda suke aikatawa
Wannan barna ce da cin mutuncin auren sunna,
Su ringa auran maza suna fitowa sbd kwadayi suna Tara kudin Haram...zamu sanar kawai a kamasu ayi musu hukuncin abinda sukeyi daidai yanda shariaa ta tanada...Ni so nakema idan an Kama uwar ai Kinga komai zai lalace ba maganar aure
Mijinki ya tsira sai aqara gaba
Allah yasa su samu Wanda ya fisa kudi da komaima saisu karkata zuwa can mu huta da zancen wannan masifar Mai suna IDON NERA...
Amin Amin ya Allah yasa su samu Wanda yafi nawa Mijin su qaratacan na samu aurena ya dawo daidai.
A ranar Bilkees takira babban Dan hannun damar DR SHAYKH ta sanar Masa qarar datakeson ya shigar akan a San irin barnar dasu Idon Nera din sukeyi.
Baya komai bada sanin Dr SHAYKH din Dan Haka ta fasa Dole qarshe Dan uwan Nafee din ne yakai zancen hisbah wadda Daman Suma sun San da IDON NERA takuma zamar musu kamar qayar makoshi,.
Dukkanin laifin da suke tihumarta dashi saita fita bayan ga barna Nan da yawa da ake aikawata da sunanta....
Amma wannan karon lamarin ya ishesu sbd ko jiya ankama mota biyu ta kusan Yan Mata marasa tarbiya da qazamar rayuwa karshe da sunanta sukai qarya suka kubuta sbd akwai Wanda acikinsu yasan asalin halayyar Haj Zainab din Kuma Yana bada shedar gaske akanta sosai babba ne acikinsu.
Bayanin dasu bilkees suka bayar akanta yayi muninda wannan karon babu wani sauki ko shirun da zaayi akanta Dole suna buqatan zama da ita.
Lamarin ya ishesu Kuma wannan karon zasu dauka mataki akanta idan har dabiarta ce aure aure tana fitowa itada yayanta sbd kawai Tara arziki da Kuma koyarda barna ga alumma.
Motar hisba aka Aika har babban gidan Haj Zainab IDON NERA Wanda hakan ya kawo wani irin tashin hankali da mamaki tareda zantukan koina...
Ahakan sbd su Bilkees su tozarta ahalin sai suka sake saka Kara a gun police akan Amal tayiwa Nafee bara zana akan Mijinta..
Wannan masifar ta saka zancen yaduwa Kamar gobarar daji Wanda da yawa wasu ke fatan ayi maganin Idon Nera kokuma a tozartasu tunda sunfi karfin hukuma.
Shi case din Amal a police ko zuwa batayi ba cikin mintina kalilan aka kashesa tareda watsi da qarar tasu Bilkees Wanda hakan ya tinzira Bilkees suka fito fili suka fada waye mazajen nasu.
Hisbah sun kasa samun zama da Haj Zainab sbd duk dalilan da aka kawo na Kamata ko ganin laifinta sun watse karshe take ta saka babbar qara akan matar SSG din sbd ko tana Wasa da komai Bata Wasa da yarta...babu Wanda zai taba yarta ta qyale.
##MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*π₯
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*π₯
Billyn Abdul
*IDON NERA*π₯
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*π₯
Safiya huguma
*KI KULANI*π₯
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
π³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*π₯*_Arewabooks@Mamuhgee_*
25
Lokacinda SSG ya samu cikakken bayanin abinda ya faru harma da matakin da Haj Zainab ke Shirin dauka akan matarsa da matar Aminin nasa Wanda yama fisa mutunci a idanuwan mutane sbd kamewarsa da Kuma Arzikin dayafisa uwa uba Yana cikin manya malaman addini sosai wainda duniya kewa kallon zallan mutunci da girmamawa..
Cikin bacin Rai da damuwa ya sallami Jameel daya isar Masa da sakon,
Sake kallon wayarsa yayi a karo na babu adadi Yana tunanin yanda zai tinkari Haj Zainab da ban hakurin janye matakin datake da niyar dauka din sbd mutuncinsu su duka Bai Kamata zasu hada zuria ba duniya tajisu tun yanzu suna daukan matakai akan junaba...
Ta wani bangaren kuwa shakkar tinkararta da maganar yakeyi sbd antaba 'yarta ne Kuma kowa yasan 'yayanta sune rayuwarta Bata Wasa da lamarinsu ko daya.
Dafe goshinsa yai Yana sauke numfashi Mai dumi bacin Ransa akan halayensu Nafeen Yana qara sosa Ransa.
Wane irin kishi ne wannan se sakasu yin abinda zai kawo fitinar da baasan ya zata qare ba.
Ya debo shekaru Yana bibiyar AMAL Idon Nera yasamu ta aminta da aurensa gashi sune neman lalata Masa auren tun kafin ayi.
Cikin bacin Rai da damuwa ya soke duka schedules dinsa na ranar ya fito da yamma kai tsaye the IDON NERA's ya nufa wato gidansu kenan da ake Kira da hakan.
Daga haj Zainab har uncle Lulu babu Wanda ya sama a gida mutuniyar tasa Kuma Daman a abanza ma tayi aji barema an tabata gata Bata daukan reni Kona Wasa bare irin wannan.
Siddi kawai yasamu damar gani ta sanar Masa babu kowa sai masu aiki Amal Kuma tace Bata buqatan ganinsa..
Bai tsaya ba Dan yasan bazata fito dinba tunda tafada gashi Bata daukan wayarsa,
Uncle Lulu da haj Zainab ma duka basa daukan waya da alama suna guri Mai mahummanci.
Daukan dumi Kansa yayi sbd Allah ne kawai zai Hana auren Nan samun matsala,
Nafee sun lalata Masa komai,
Wani irin bacin Rai mai tsanani yake ji
Abin mamaki Kuma Yana Isa gidan yatadda Nafee tadawo..
A karo na farko da Nafee taga mummunan bacin Ransa da Bata saniba,
Ita kanta Bilkees Saida ta tsorata da kalmarsa ta karshe dayace matuqar aurensa da Amal ya lalace akan wannan abin dasukai abakin igiyar aurenta 'daya Kuma wlh saiyayi wani auren Koba Amal ba tunda yayi niya.
Bilkees a duniya babu kalma mafi Muni da tsoro gareta kamar kalmar kishiya da saki sbd duk inda sunan kishiya ya tabba to saki na kusa idan ba Allah ya rufa asiriba,
Kukan da Nafee keyi Sosai yasa balkees sake shiga damuwa da mamaki mai tsanani,
"Yanzu sai Hayat ya iya sakinki akan wannan yarinyar??
Wlh tallahi ba dauka lamarin Nan yakai hakabama,.
Rabuwa fa yake nufin yayi dake idan Bai samu wannan din ba,
Duk 'yaya da shekarun da kukai Bai dubaba yake iya furta Miki wannan kalmar akan karuwaΒΏ
Menene wannan yarinyar take dashi da Hayat ya haukace Haka kamar Wanda Bai taba sanin maceba ciki da Bai sai wani rawar jiki da mutuwar zuciya yake akan wannan..
Nafee Bata iya cewa komaiba bayan kukan datakeyi na qunci da tsoro,
Allah yagani tanason Mijinta sosai,
Kuma zuwa wannan lokacin ta fahimci idan namiji yaso aure idonsa ya rufe a auren kaikuma kace baka yardaba karshe naka auren ne zaiyi rawa.,
Da daddare ta samesa Dan suyi magana Amma har lokacin Ransa a matuqar bace yake Bai saukaba..
Abinda takasa ganewa shine ba iya fashin auren yakejiba matakin dasu Idon Nera din zasu dauka na saka qarar ko wani Abu akanta akan abinda tayi din.
***Amal kuwa gabaki daya kashe wayarta tayi sbd ko sunan Hayat din Bata buqatan gani,
Idan Dama baifi qarfin matarsaba Baya iya controlling dinta Kuma ita yayi Mata alkawarin babu inda zasu hadu bare matsala ta biyo baya gashi sunje itada mahaukaciyar kawarta suna son saka Mata ciwon kai tun Bata auresaba.
Sidda ma takaicinta da mamakinta duka yaqare akan yanda matar Hayat din tasamu guts na aikata wanna rainin hankalin da rashin hankali.
Ita dai Amal ta tattara Hayat din da lamarinsa ta watsar tukuna sai idan taji zata iya saurararsa tukuna tasake bi takan maganar neman auren nasa.
***Kwana biyu Nafee ta dauka fushinsa da bacin Ransa Mai wucewa ne Amma sai abin ya shallake tinaninta sbd tafiya ma yayi kusan sati daya kafin ya dawo Kuma still babu wani sauyi a yanayinsa.
Tayi kukan,tayi adduar tayi fushin itama Amma duka babu sauki bare sauyi Dan Haka ta tattara makaman yaqinta tafara zubarwa sbd mafita dai Bata samuba sunyi sunyi Amma babu alamar samun mafitar Dan Haka tafara saduda akan lamarin Dan batason rabuwa da Mijinta,
Shikuwa daqyar yasamu ya kwantar da Kai gurin Haj Zainab da uncle Lulu aka janye zancen sukai hakuri saidai baisan ya makomar zancen aurensa yakeba da AMAL amma tunda Haj Zainab da uncle Lulu sun sauko yasan komai yawuce sauran gimbiyar yasamu ta sauko tayi hakuri.
Nafee kuwa nuna Masa tayi ta sauko gabaki daya ta hakura da auren nasa da AMAL Amma ta bayan fage itada Bilkees din Basu saki komai dukaba sunata fafutikan yanda zasu samu auren daya fara lalacewa ya qarasa lalacewa afasa gabaki daya.
Dukkanin mafita da hanyar neman lalata auren sun rasa face daya wadda kusan itace suka gwada farko saidai wannan karon babbar Kara zasu saka malaman addini su saka IDON NERA's a kotun musulinci Dan harga Allah barnar dasuke yadawa da koyarwa tayi yawa ga alumma,
Babban gidan karuwan da IDON NERA takedashi a garin yafi wasu makarantin girma nesa ba kusa ba.
Bilkees ce ta bada wannan shawarar Dan harga Allah cikin tsakiyar ranta takejin tsanar duka ahalin IDON NERA shiyasa har lokacin ko hotonsu babu Wanda ta kalla Dan ma kada ta zuciyarta tasake 'daci da kyansu da ake zuzutawa Wanda ya zama na banza tunda ya qare a rayuwar banza da wofi.
****Ajiye wayar hannunta tayi bayan tagama sauraron duka bayanin Barr Salahudeen,
Kallonta uncle Lulu keyi Yana jiran Jin abinda zata fada.
Numfashi ta sauke ahankali tana qarasa ajiye wayarta gefenta ranta na Dan neman baci tace,
"Qara ce aka Kuma sakani Kuma Wai malaman musulinci a kotun musulinci...
Bansan wannan karon waye zai Kuma yin wannan yunqurin ba,
So nawa Wai akeson ganin bayana da ahalina?
Kusan komai na irin wannan rigingimun sun kwanta Amma Kuma yanzu ko wane me tsaurin Ido da zafin kan ne ya sake Kai sunana???
Uncle Lulu mayar da bayansa yayi ya Jingina da kujerar dayake Kai Yana Dan hade fuska yace,
"Ko waye wannan banajin yasan illar abinda ya aikata,
Me suke nema da wannan familyn ne dako yaushe ake Mana barazana da kotun musulinci.,
Yanzu me su Barr Salahudeen din sukace???
Wani numfashin son watsar da zancen kada ya dameta ta sake kafin tace,
"Zasuyi abinda zasuyi Amma bazani kotun ba idanma malaman sun tsananta ne zanje muyi magana Amma baa kotun ba,,shine abinda Barr yafada.
Amal ce tashigo palon sanyeda Riga da skirt na cotton lace Mara nauyi da ado sosai,
Ba dankwalin kayan a kanta sai qaramin gyalen data daura iya kanta da qaramar bvlgari handbag a hannunta sai key na motarta..
Siddi siddi ce a bayanta suka qaraso tsakiyar palon tareda zama Amal na cewa,
"Uncle barka da yamma.
Mommy Yaya dai Naga fuskanki a yamutse??
Siddi datake maqale kusada mommyn batama lura ba ta dago ta kalleta cikin kulawa tace,
"Mommy All ok right????
Numfashi haj Zainab din ta sauke tana kallon Amal kafin ta kalli Siddi tace,
"Yes baby,
Kan Amal datake kallonta har lokacin ta maida kallonta sbd Ko kadan Amal Bata Wasa da damuwar mummyn Koda mummyn tace babu komai Amal Bata yarda idan taga alamar damuwa ko tunani atareda ita tana ganewa Dan haka take nuna tata damuwar har sai mummyn ta cire komai duk da basuda wata damuwar sai irin wadda baa rasaba data danganci sanaoi da huldodinsu mummy dashi uncle Lulu din.
Cikin basar da yanayinta dake nuna ciwon kan da ake neman saka Mata da sabon lamarin daya bullo da batasonma su Amal su sani Dan dukkaninsu zafi zasu dauka.
Tana kyakkyawan murmushi Mai Fadi akan fuskarta tace,
"Sweetie babu komai kaman yanda nafada Miki ki Dena kallona Haka Mana.
Dariya siddi tayi tana kallon fararen idanuwan Amal din akan mummy tace,
"Mummy Nan gaba Amal ce zata ringa Miki juyamu duka.
Wani kallo Amal din tayiwa siddi zatayi magana uncle Lulu ya katseta dacewa,
"Karki biyeta sweetie idan na nutsu zuwa gobe idan kin dawo makaranta zanyi magana dake.
Ok Uncle" Amal din tace cikin muryarta me tattarreda rashin rawar Kai ko hayaniya.
Kallon Haj Zainab tayi yace,
Zanyi magana dasu Salahudeen anjima da kaina
Zan sanar dake duk yanda muka Kai qarshen zancen.
Miqewa yayi ya fice daga palon zuwa bagarensa dan yasamu magana dasu Barr cikin nutsuwa tunda acan basa son su Amal su San da zancen zasu kashesa batareda kowama daga familyn ya saniba tunda Daman an Saba ba yauba suke kashe case bataredama ko sunansu an Kuma maimaitawa a idan aka fadesaba.
Tashi Amal tayi ta nufe bedroom dinta Kai tsaye bayan ta cewa Bilkisu ta dafa Mata Noodle daya da carrot kawai sai dafaffen kwai.
Tana shiga bedroom din Jakarta da key na mota dake hannunta ta ajiye gaban mirror ta zare kayanta ta nufi toilet tana zare band dake daure da manyan kalban kanta masu tsayi.
Wanka tayo ta fito da bathrobe ash ta nufi gaban mirror ta shirya sharp sharp sbd sallar dake Kanta ta laasar da bataiba sbd fitowarsu lectures kenan ta dawo gida.
Skirt da hijab na sallah ta saka tayi sallah tana idarwa Bata tashiba akai magrib ta miqe tayi tana idarwa tayi adduointa ta miqe tareda zare kayan ta maida closet ta janyo wata doguwar Riga Mata hannu ta saka ta nufi comfortable resting kujeran dake dakin nata ta zauna ta janyo wayarta daketa haske alamar Kira.
Hayat ne me kiran,
Qaramin numfashi ta furzar tareda maida wayar ta ajiye tana miqewa ta fice dakin.
Kitchen ta nufa Dan duba idan an dafa mata abinda tace din sbd batason abinci Mai zafi Sam shiyasa tace a dafa din kafin ta fito ya rage zafi.
Tana shiga ta tadda an dafa Mata din Dan Haka anan kitchen ta zauna kan dan qaramin dining din ciki tanaci tana Dan fira sama sama dasu Bilkisun Dan Dama kusan gidan itace tafi sakewa dasu bayan mummy wadda ta dauki duka masu aikinta kamar 'yayanta ko qannenta tunda a qarqashinta suke.
Siddi ce Sam Bata wani sake musu Amma Kuma bata wulaqantasu,
Uncle Lulu kuwa babi abindama yake hadasa da masu aiki idan ba masu gadi da securities dinsuba na gidan Suma Kuma baya wani zama bare yasan yanda zaiyi treating nasu unfairly barema suna aikinsu yanda ya Kamata Dan Haka Yana musu ma yakeyi duk lokacinda yasamu damar tsayawa dasu din.
Fareedah ce take Dan wulaqanta masu aikin gidan sbd ta taso gidansu basusan darajar masu aikinba Amma Kuma ahankali ta tattara ta Dena itama ta Dena kyararsu sbd