Showing 96001 words to 99000 words out of 155476 words

Chapter 33 - IDON NAIRA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

01 Jan 2026

419

ba Amma dai Babu dare Babu safiyar da basa miqa adduarsu ga ubangiji Akan kada Amal din ta tare a gidan 'dan su.

Shi kansa AQEEL ASAD din gabaki daya ya daukewa kowannensu wuta Babu me ganin sauki a fuskarsa musamman Bilkees daya tattarata ya ajiye gefe daya
A gidan mufeeda ce kawai ke ganin fuskarsa
itama sbd laifin Bai shafeta bane.

Su umma tun suna daukan lamarin da sauki harsun fara girgiza da fushin nasa Dan kuwa bayan gaisuwa dayake shigowa ya musu basa ganinsa gabaki daya baya wani zama a gida.


Ta bangaren su Haj Zainab dinma sunsan an tabasa sbd Suma ya dauke kafa a waya yake kiranta yaji lafiyansu,

Ahmed kullum Yana zuwa yakai Amal school ya dawo da ita kokuma duk inda zataje daga school din,

Yana sane da duk inda take zuwa sbd Ahmed na fada Masa Kuma itama tasan Ahmed din Dole zai fada Masa tana zuwa duk inda taga Dama Amma Bata damuba ta watsar da zancensa

Shima shiru yayi Mata Yana sane sbd fahimtar Mata kusan dukansu hankalinsu baya aiki duka,


**Hankalinta yakwanta takoma rayuwarta hankalinta kwance sbd rashin zuwansa yasa ta manta da duka wata damuwa da aurensa Dan haka yanda take rayuwarta yanzu sai tafi samun nutsuwa.

Haj Zainab kuwa rashin zuwan nasa yasa tafara shiga Yar damuwa sbd gashi tafiyarsu tazo Amma har lokacin Bata samu tayi maganar dashiba,
Tasan aqidunsa zai iya Hana Tafiyar da Amal Amma Kuma gaskia ita tanason zuwa da ita din Dan gaskia yanayinta itama Yana Bata tsoro duk wata
Ta Dade tana wahala tinda tafara period duk wata Haka take fama da wannan wahalar.

Daurewa tayi ranar da daddare ta Kira wayarsa alokacin shima yanada tafiya ne washe gari.

Cikin nutsuwa ya daga wayar Yana zaune palonsa Yana kallon labarai hankali kwance.

Gaisawa sukayi tana sake tambayarsa lafiyarsa.

Am fine Alhmdllh" yace yana sauraronta.

Ahankali ta Koro Masa bayanin ciwon Amal din da tafiyar tasu tana dorawa da rokon yabar Amal sbd tana Shan wahala sosai.

Shiru yayi tsawon sakanni bayan yagama jinta batareda yace komaiba.

Numfashi Mai sanyi ya sauke daga baya kafin yabude Baki anatse yace,

"Mami kuje kufara ganin likatan akan Siddi ita daga baya sai a kaita din.
##MAMUH#



*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*πŸ”₯
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*πŸ”₯
Billyn Abdul

*IDON NERA*πŸ”₯
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯
Safiya huguma

*KI KULANI*πŸ”₯
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*πŸ”₯*_Arewabook@Mamuhgee_*
48
Shiru itama Haj Zainab tayi Jin abinda ya fada din jikinta na sanyi
To Amma ba damuwa zataga yanda zatai idan sunje Koda ta wayane likitan suyi magana da Amal din Koda akwai abinda zai iya cewa akan matsalar.

Sallama sukayi itama tana sake Dan shiga sanyin jiki sbd har lokacin tasan Yana cikin quncin abinda yafaru dinne,

Shikadai yasan halinda suka kusa sakasa da zancensu na rashin tinani,
Sun girgiza fiyeda yanda Shi kansa yake tinani Dan Haka ya zabi bawa Kansa da zuciyarsa hutu Akan dukkaninsu kowa da kowa sai gashi hakan na azabtar da kowaccensu Banda Amal da hakan yayi Mata daidai yanda takeso wato fitarsa arayuwarta.


Lokacinda mommyn ta fada musu AQEEL Bai bar tafiyar da Amal ba shiru Amal din tayi batareda tace komaiba zuciyarta na nauyi duk da Daman tasan hakan zata iya faruwa Amma Kuma idan har yayi ne Dan ta rokesa da kanta to ta hakura da tafiyar itama.

Siddi datake mamaki da Jinjina lamarin da ita Bata Saba gani a rayuwar nata aurenba ta kalli Amal dataqi cewa komai kan maganar tace,

"Amal Zaki iya da AQEEL ASAD dinnan kuwa?
Kiga yanda fa yake magana Kai tsaye baya shakka ko tsayawa Dan inda inda,
Gaskia Amal ki kwantar da Kai Kawai ki rokesa yabarki sbd kina buqatan tafiyar Nan fa.

Girgiza Kai Amal tayi tana cigaba da duba wayarta tace,

"Nafasa tafiyar inada abubuwan Yi a school.

Haj Zainab dake jinsu kasa cewa komai tayi sbd damuwar rashin zuwa da Amal din dakuma taurin kanta dazai Hana ta rokesa yabarta duk da tasan koda Amal din ta roka tunda yace aa to bazai canjaba.

Dukkanin Shirin tafiyarsu angama
Su duka gidan zasuyi tafiyar harda uncle Lulu da Anty Fareedah hadda Fahat
Daga ita saisu Bilkisu zaa Bari,

Baqin ciki da bacin Rai ne a cikin zuciyarta Mai tsanani akan rashin tafiyar Amma tadanne ta barshi aranta Dan kadama tabawa zancensa mahummancinda zaayi tunanin ta nemesa.

Tanaji tana gani suka wuce Kuma ko a Daren ranar da zasu wuce din yazo gidan da daddare taqi fitowa Haka shima Bai tambayetaba bare ya nemeta, Maminsa ya bawa kudi masu yawan gaske da zasu buqata komai acan harsu dawo sbd dawowarsa rayuwarsu zuwa yanzu hatta abincin gidan yanzu shine yake kawo komai batareda ya tsaya tambayaba Haka ake kawo abinci duk wata a jera a gidan.

Ranar dasuka wuce a school ta wuni sai yamma sosai ta dawo,

Wanka tai ta fito taci abinci kadan ta koma bedroom dinta Bata sake fitowa ba sai washe gari.

Ranar batajin fita koina Dan Haka very late ta tashi ko wanka batayi ba brushi kawai tayi tafito sanyeda riqa da wandon bacci masu santsi gajeru sai slippers da wayarta a hannunta tana kokarin Kiran su mommyn taji isarsu.

Saukowa tayi palon qasa tacewa Bilkisu takawo Mata abincinta sama.

Juyowa tayi zata koma daidai shigowarsa palon sanye cikin black hoodie fendi Riga da wando masu fadi dasuka fidda hasken fatarsa sosai,

Da alama shima yau din ba fitarda zaiyi sbd kayan dake jikinsa suna nuni daga morning jugging yake.

Ba zato tagansa Dan Haka idanuwanta suka Shiga cikin nasa
Cikin basarwa ta dauke nata Idon tareda nufar hanyar saman zata wuce yakira sunanta kai tsaye fuskarsa a kame.

Daka tawa tayi batareda tasan tayi hakan ba.

Takowa yayi ya qaraso zaiyi magana saiga Bilkisu tafito daga kitchen daukeda breakfast din nata tana ganinsa tayi daurin dakatawa tareda gaidasa cikin girmamawa ta juya kitchen da abincin.

Fasa maganarsa yayi Ana ya Kama hannun Amal din Kai tsaye yajata zuwa sama suna Shiga tsakiyar palon ya saketa tareda kallonta zaiyi magana saiya fasa yayi mata kallo daya ya dauke Kai yace,

"Jeki ki sako wani kayan.

Sai alokacin ta dago itama ta kallesa batareda tayi abinda yace dinba sbd zafinsa datakeji akan rashin tafiyarta gashi kowane lokaci period dinta zai iya zuwa azabarta na hanya tasani.

Ganin taqo motsawa daga inda take yasashi zuba Mata idanuwansa cikin mamaki yasake maimaita abinda ya fada din.

Kujera ta nufa da niyar zaunawa akawo Mata abincinta
Bata qarasa zamaba akai ya riqota gabaki dayanta ya nufi bedroom dinta da ita.

Qwacewa take kokarin Yi daidai lokacinda ya bude dakin nata ya sakata aciki tareda rufe kofar ya tsayar da ita gabansa Yana kallon yanayin kayan nata,

A kirjinta da Babu bra ya tsayar da idanuwansa sbd Kai tsaye shima ya fahimci Babu bra a tareda ita.

Motsawa tai zata janye jikinta daga nasa ya matseta jikin kofar suna fuskantar juna,

Faduwa gabanta yayi Jin kirjinsa daya dafe nata kirjin jikin kofar dashi.

Lokaci daya suka dago suka kalli juna tana kokarin boye tsoronta da faduwar gabanta dake bayyanuwa.

Qamshinsa ya sauya numfashinta dake fita da sauri kirjinta na harbawa ahankali batasan lokacinda takai tafin hannuwanta zata tufesa daga jikintaba cikin rashin sani hannuwan nata suka sauka a fatar cikinsa da rigarsa ta Dan janye sbd hannuwansa dake sama gurin Mata runfa.

Sanyi da taushin hannuwanta suka sanyashi rintse idanuwansa tareda zura hannunsa daya ya sake matsewa da ita Yana bude idanuwansa akan fuskarta datai saurin janye hannunta..

Qamshin jikinta ya shiga hancinsa ya sake bude idanuwansa akanta Yana kallon yanda take kokarin turesa daga jikinta.

Fuskarsa ya goga Mata a cikin wuyanta ahankali
Take jikinta ya dauki rawa ta rintse Ido cikin sauri batasan lokacinda ta bude bakiba tace,

"Me kakeyi???

Bakinta da yayi maganar ya dago ya kalla kafin yakai bakinsa kan kunnenta ahankali yace,

"Kina magana Ashe??

Na dauka kurma nake aure.

Turesa tayi da karfi sbd takaicin maganarsa da wani irin shock da dumin numfashin maganarsa ta sakar Mata a kunnen.

Tana turesa da sauri ta qarasa toilet tashige tareda fincike kayan jikinta tana wurgi dasu sbd qamshinsa dasuka Kama ba Bata lokaci.

Bai kalli kofar toilet dinba shima ya fice dakin yabar gidan gabaki daya Yana Dan saita Kansa kamar Babu abinda ya faru.

Wanka tayo tafito ta shirya cikin doguwar Riga ta fito taci abinci ta Kira Ahmed duk da batayi niyar fitaba taji tanason fitar kawai.

Ahmed na zuwa suka fita zuwa makaranta Dama tanada lecture daya kawai dai batayi niyar zuwa bane sbd Bai cika zuwaba lecturer din.

Bata baro school dinba sai yamma bayan sun biya ta siyo maganinta sbd ciwon mararta daya fara zuwa kadan kadan
Daman tasani lokacin yayi.

Koda ta dawo gida a sanyaye tadawo sbd jikin nata Dan Haka ko abinci bataciba wanka kawai tayi ya Dan sha magani ta kwanta tana Jin ciwon na fara qaruwa kadan kadan.

Tea Mara shuga Bilkisu ta dafo Mata takawo Mata daqyar ta iya Shan kadan ta ajiye Takoma ta kwanta.

Da daddare ma sake dafo mata tea din Bilkisu tayi takawo shima kadan Tasha cikin azaba ta jiye takoma ta kwanta.

Ahankali ahankali yafara yawa tanata Dan daurewa har tasamu gari ya waye suka Kira Dr saidai Bata gari.

Sake Shan magani tayi tayi wanka da qyar tana fitowa takasa shiryawa ta kwanta a qasan dakin nata tana juye juye tareda kuka sosai sbd tsananin azaban ciwon da Marar keyi Mata.

Sanye cikin navy blue plain luxury yadi yashigo palon dayayi tsit Babu kowa,
Ahmed ya sanar Masa da Bata fitaba tana gidan Dan Haka Kai tsaye ya wuce saman Yana shigowa Bilkisu na fitowa daga dakinta daukeda tray din abincinda Amal din takasaci..

Tana ganinsa tayi qasa da Kai cikin damuwa da tsoron rashin abinyi da Amal din.

Yanayinta yasashi kallon kofar dakin Amal din inda ya jiyo kukanta na fitowa ahankali.

Kofar bedroom din ya nufa Bilkisu Kuma tayi saurin yin qasa.

Kwance take a kasa daga ita sai towel din wankanta fuskarta tayi jajir tana dafe da cikinta.

Mamaki yasashi qarasowa Yana kallonta.

Yanayinta yasashi daukanta gabaki daya ya Dora akan gado Yana tayata dafe towel dinta da bazaiso ya kunce ba shima Dan bazai iya gani ba.

Kuka takeyi sosai ahankali tana dafe cikinta..

Wayarsa ya fidda ya Kira Maminsa da Bai Dade da Gama waya da itaba.,

Tana dauka ya tamyeta yanayin na Amal.

Damuwa tashiga ta Masa bayanin hakan takeyi daman Akira Dr kawai.

Kashe wayar yayi Yana kallon agogon hannunsa sbd tafiyar da zaiyi Nan da awanni uku shima.

Yanayinta ya kalla yaji zuciyarsa na nauyi da yanayin nata,

Al'amin yakira yace aturo Masa likita mace yanzu a Idon Nera Rs.

Yana kashe wayar ya kalli fuskarta datayi ja ya dagota ahankali tareda shigar da ita jikinsa ya rungume hannu daya Yana dafe Mata towel dinta da hannun daya.

Kasa kwace kanta tayi itama sbd bada lafiya bare qarfin Dan Haka ta samu ta Dan dafe towel dinta shima ya tayata dafewar.

Cikin qaguwa yaketa duba agogonsa akan zuwan likatan Amma har lokacin shiru.

Zafi Kansa ke neman dauka da rashin zuwan likatan dakuma jikin nata ga tafiyarsa dolece Amma bazai iya tafiya yabarta a gidanba ita kadai.

Al-Amin yasake Kira Yana dauka yace,

"Kasake siyan ticket daya da sunanta.

"Ok sir.

Yana kashe wayar ya janyeta jikinsa ahankali tareda miqewa tsaye ya fito ya turo Bilkisu ta shiryata kawai.

Time yake Kallo din bayan seconds sbd hankalinsa daya rabu biyu.

Doguwar jallabiya Bilkisu ta sako Mata da tunanin asibiti zaa tafi da Amal din.

Ana Gama shiryata handbag dinta kawai aka daukar mata ya daukota da Kansa suka fito Bilkisu na sauke Kai qasa.

Su malam Rabiu ma hango fitowarsa da ita a jikinsa sauke kan sukayi Saida ya shiga motar.

Yana Shiga malam Rabiu yashigo yatada Kai tsaye airport suka wuce inda al'amin ke jiransu.

Suna Isa acan taga wani likitan gaggawa yayi Mata allurai take bacci ya dauketa ajikinsa batareda tasaniba har suka daga zuwa portharcourt.

Har suka Isa bacci takeyi sosai
Saida suka Isa ta farka a hankali jikinta Babu qwari sai alokacin tasan tareda wa take.

Tashi tayi daga jikinsa tana Dan Bata fuska saidai bazata iya maganaba.

Ganin akwai mutane manya a inda suke din yasata yin shiru har suka fito jirgin suna Shiga mota tace a maidata gida.

Bai kulataba yacewa Al-Amin su tafi kawai Ana jiransa bayason Bata time.

Kai tsaye gurinda zaiyi meeting dinsa Al-Amin yafara ajiyesa da driver kafin ita ya wuce da ita masaukinsu kafin AQEEL ASAD din yazo daga baya.
##MAMUH#
#HOTLOVE#ROMANCE#
#AMAL IDON NERA.



*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*πŸ”₯
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*πŸ”₯
Billyn Abdul

*IDON NERA*πŸ”₯
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯
Safiya huguma

*KI KULANI*πŸ”₯
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*πŸ”₯*_Arewabooks@Mamuhgee_*
49
Already anyi reserving lafiyayyan daki da sunan AQEEL ASAD din tun jiya a Echelon heights Dan Haka suna isa Id card dinta da akai amfanin dashi airport dashi Al-Amin yayi amfani aka isar da ita dakin dakin AQEEL ASAD din dake sama gabaki daya.

Sosai take cikin wani irin Hali dakuka period dinta dayake zuba sosai shiyasa ta Isa dakin Kai tsaye tareda Al-Amin da maaikatan gurin dake janye da qaramar luggage din AQEEL wadda take tunanin kayanta aciki Dan Haka suna Isa dakin aka bude Mata tareda shigar qaramar luggage din Al-Amin yayi Mata fatan hutawa lafiya yajuya.

Toilet ta qarasa kan tsaye tana takawa ahankali sbd duk motsinta azabar mararta datake Kamar a qulle takeji.

Babban toilet din dayake a tsare tashiga tafara zare kayan jikinta,

Tana gamawa ta shiga ruwan zafi wainda ke Dan sanyaya Mata wani lokacin.

Tana Shiga ta rufe idanuwanta hawaye na gangarowa daga cikin idanuwan jikinta na Dan rawa sbd azaba.

Ta Jima aciki kafin tayi wanka da suka products na kayan wankan dayake amfani dasu sune aka jere a toilet din sbd Al-Amin yayi order na komai da AQEEL ASAD yake amfani dasu an jera a dakin tun daga kan su toothpaste dayake amfani dashi da sabbin brushes na sonicare dasu shampoos da shaving kit,

daqyar a durqushe ta Gama wankan ta dauro qatuwar towel din dasuke jere ta fito a daddafe tana fitowa ta silale qasa tana tsananta hawayenta,

Mommynta take nema sbd wanna shine karo na farko data shiga Hali na ciwonta Amma babu mommy Babu ko siddi ko Anty Fareedah atareda ita,
Koyaushe idan Hakan ya taho suna tareda ita suna kulawa da ita tareda yawon asibiti da ita,
Yau Babu kowa atareda ita ga azaba tanaji kaman ranta zai barta.

Kuka takeyi sosai batareda tasan tanayiba
Gashi Daman bawani zuba takeyi sosaiba azabar ce takeda yawa kawai.

Kukanta Yana sake tsanantane tareda ciwon nata,
Rawa jikinta yakeyi sosai tafara Wani irin numfashi da juye juye....


Acan cikin rashin Bata lokacinsa ya gana sama sama dasu yana Dan kallon time a agogon hannunsa.

Baifi awa daya da rabi ba yagama ya fito Kai tsaye ya shiga motarda aka tanadar Masa Dan hidimar garin tareda Al-Amin suka bar gurin.

Tun kafin su Isa yasa aka Kira Masa likitan dazata duba Masa ita Dan haka Koda suka Isa likitar na Echelon din Dan Haka suka wuce Kai tsaye dakin.

Shine yafara amfani da card na dakin ya bude yashiga,

Kwance take a qasa tana numfashi daqyar dukkanin jikinta na kakkarwa Kamar zata shide.

Kai tsaye yayo kanta ya tallafota gabaki daya jikinsa Yana kallon fuskarta datayi ja cikin damuwa yakira sunanta ahankali Yana nufar makeken gadon dake dakin ya shimfidar da ita ya ja duvet ya rufe Mata jikinta ya budewa likitar kofa ta shigo Kai tsaye inda take suka nufa ya tsaya Yana kallon fuskarta dake hawayen Bata hayyacinta idanuwanta arufe.

Temperature dinta Dr tafara dubawa kafin taji pulse nata
Ta tambayesa Yana Dan tunanin abinda yake damun nata badan ya tabbatar da shi dinneba a Dan natse yace,

Inaga monthly pains ne na ummm,
Period I think..

Dawo da kallonta kan Amal din tayi cikeda mamaki tana miqewa tsaye ta bude jakarta datazo da ita ta fidda allurar pain reliever tayi Mata tana cewa,

"Amma sir Bai Kamata ace tana samun pains Haka sosai ba da wahala tunda tanada aure,
Mostly masu fama da wannan matsalar duk wata da sunyi aure kokuma sukai having first sex dinzu zuwa 3rd ko 5th Haka Marar na sakewa ciwon zai fara denawa ahankali shikenan,
Wasuma idan Basu denaba suna haihuwar fari kokuma samun miscarriage suna denawa.

Komawa yayi kan couch ya zauna tareda Dora kafa daya kan daya Yana sauraronta idanuwansa akan matarsa dake kwance kamar Babu Rai ajikinta.

Drip tasaka aka kawo daga asibitinta aka daurawa Amal din sbd qarfinta data rasa gabaki daya Dan tayi matuqar azabtuwa
Bakuma ta Dena azabtuwan ba.

Ana daura Mata drip din bacci Mai qarfi ya dauketa a jikinsa kwance ya rungumeta da hannunsa daya cikin kulawa sbd lokacinda suke kokarin neman jijiyarta da zaa saka cannula sai cakudata sukeyi duk da lallabawa sukeyi Amma ganin yakeyi kamar suna yamutsa da yawa Dan Haka ya taso ahankali ya zauna tareda janyota jikinsa ya kwantar ya miqa musu hannun nata da Kansa suka sake lallabawa aka saka Mata ka daura drip din.

Magani dasu tarin always dr din takawo da kanta Bayan ta tafi tadawo takuma nuna Masa yada zai cire Mata idan ruwan ya qare ta fice Al-Amin yabita yayi settling bills da payment dinta Dan babbar likita ce sosai.

Lokaci Mai tsayi ta dauka tana bacci har ruwan yaqare ya zare Mata ya gyara Mata kwanciya tareda rufeta dakyau yayi sallah tareda kashe wayoyinsa bayan yakira ummansa sai mufeeda.

Bata farka ba sai bayan sallar magrib shima ciwon ne yadan sake tada ita,

Idanuwanta ta bude ahankali Basu suka a koina ba sai akan kyakkwar fuskarsa datayi haske Yana zaune kan sofa cikin black Riga da wandon Calvin Klein dasuka fiddo sauran kuruciyarsa da asalin kyansa da nutsuwarsa Yana amsa waya ahankali cikin turanci.

Maida idanuwanta tayi ahankali ta rufe tana gangaro da hawayen kewar su mommynta.

Yana wayar idanuwansa suka sauka kan fuskarta da hawaye ke gangarowa ya fahimci ta farka..
A natse yayi sallama da Wanda yake wayar dashi ya kashe tareda ajiyewa gefensa ya miqe tsaye tareda nufar gadon ahankali ya tsaya akanta yasake kallon fuskarta yaga yanda hawayen ke gangarowa ya zare hannuwansa daga aljihunsa ya zauna bakin gadon ahankali tareda Kai hannu a wuyanta ya shafa yaji zafin jikinta yafara dawowa.

Hannuwansa ya zura cikin duvet din ya cirota daga cikin rufar gabaki daya tareda tada ita zaune Saida bazata iya zamanba ta zame zata kwanta ya tarota jikinsa Yana kallonta
Tayi fayau hasken fatarta yafito sosai
Jikinta ya saki Bata iya ko wani dogon motsi.

Tanaji tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login