Showing 72001 words to 75000 words out of 155476 words

Chapter 25 - IDON NAIRA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

01 Jan 2026

416

tareda kame kame.

Idan bamuje ba kina tunanin yanda ta riqa a rayuwar datakeyi zatazo ne Ida munkirata,

Da ita tazo takawo dauda tsaftataccen gidanku ba gwara mu mujeba idan munfito mayi istigfar mu goge daudar.

Wani yawun bakin ciki da 'daci Haj Maryamah ta sauke tanajin saitin zuciyarta na ciwo da radadin akaro na farko da Zainab tayi galaba akanta tasakata zuwa gabanta a ta sameta duk akan 'dan da natane ita ta haifi abinta da wani shegen ya haifar Mata ba.

Qarfe hudu na yamma da mintina suka fito cikin shigar alfarmar dasuka Saba da ita suka shiga 'daya daga cikin manyan motocin Haj Maryamah din driver ya jasa suka fito harabar gidan.

Bilkees Kuma qarfe hudu da rabi ta fito tareda mufeeda suka shiga motarta
yau itace zatai tuqin da kanta sbd a sirrance takeson aikatar da nata aikin...
Gidan IDON NERA ta nufa Kai tsaye.



*******Qarfe Biyar saura aka wangalewa motarsu Haj Maryamah babban gate din gidan IDON NERA sbd motar dakeda lambar motocin AQEEL ASAD Wanda zuwa lokacin securities sungama sanin yanada matsayi a gidan shiyasa suka budewa motar gate Kai tsaye.

Suna parking Mai aikin gidan Bilkisu data fito daga sashen Anty Fareedah ta tsaya ta gaishesu cikeda girmamawa saidai Babu Wanda ya iya amsata Kai tsaye Zainab suka baqaci gani.

Jagora Bilkisu din Tai musu saidai a daidai palon farko Haj Maryamah ta tsaya sbd numfashinta dake siqewa da duk taku daya datakeyi Acikin gidan...

Kasa cigaba da shiga tayi ta tsaya cak tana Jin bazata iyaba zuciyarta fashewa zatayi Dan Haka kai tsaye ta juya gwara Takoma gidanta AQEEL yazo ya zaba ko ita ko Zainab da 'yarta.

Juyawarta idanuwanta cikeda baqin ciki da zafi Mai tsanani yasa umma biyo bayanta tana kiranta itama zuciyarta na tafarfasa Dan kuwa Zainab taci amanarsu tako Ina ta cucesu data sanyasu zuwa Inda take ba shiri ba tinani Allah ya isansu wlh sunkai kofa kenan ta daga qafa zata fitar
Daddadar muryar Zainab ta sauka a kunnunwansu kamar saukan ganga.


"Su waye a gurin?"

Rintse jajayen idanuwanta dasuka sauya Haj Maryamah tayi sbd yankar zuciyarta da muryar tayi tareda kalmomin dasukai Kama dana kamar ankamasu.

Umma ma zancen ya daketa sosai Dan Haka ta juyo cikin mamaki,baqin ciki da takaicin zuwansu gidan mace kamarta.

Saukowa takeyi a staircase na palon tana sake zuba musu kyawawan idanuwanta Babu alamar ta sansu ko gane daga inda suka fito.

Umma jininta ne yafara Hawa ahankali ahankali Yana sama,

Yau take qara yarda da Zainab a rayuwarsu masifa ce babba Dan kuwa jininta take yafara hayewa sama daya ganin wannan macen ace itace Zainab....

Haj Maryamah data kusan hadiye zuciyarta juyowa tayi ahankali daidai qarasa saukowar zainab din tana kallonsu Kai tsaye fuska ba alamar sani.

Wani abune dayafi dutsi tauri ya Danni zuciyarta lokaci daya saidai bazata iya barin quncinta fita gaban zainab ba.

Kallon kallo sukewa juna cikin wani yanayi dayafi Kama da kowa ta cikinsa na ciki.

Ahankali haj Zainab din ta dauke Kai tana maida kallonta kan umma dake kokawa da kirjinta Amma tana daurewa sbd kada subawa Zainab din damar ganin tashin hankalinsu.

Bude baki tayi zatayi magana AMAL ta fito daga sama tareda fara saukowa stairs ahankali sanye cikin Riga Qarama Mara nauyi da tsayi tana waya hankalinta kwance.

Ganinsu yasata kashe wayarta tana kallon mommynta da itama ita din ta waiwayo tana kallo sbd bazaso Susan waye Amal dinba Dan suna sani AQEEL zai iya sani
Shikuma idan yasani zai iya karbanta Wanda tana Tina alqawarinta akan shine ikonta tunda shine amanarta tashiga hannunsa tun Bata fito duniya ba daga mahaifinta.
##MAMUH#
#HOTLOVE#AQEEL ASAD#



*_ZAFAFA BIYAR_*

*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano

*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul

*IDON NERA*🔥
Mamuhgee

*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma

*KI KULANI*🔥
Miss xoxo

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN

0022419171
Maryam sani
Access bank

Shedarka ta 09033181070

MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥*_Arewabook@Mamuhgee_*
35
Umma dake Jan numfashi ta qurawa Amal idanuwa tana sake shiga tashin hankali idan har wannan itace MARYAMAH sun shiga uku,
Ta tabbata kenan da karuwancin sukai amfani suke kokarin dawo da AQEEL hannunsu,

Innalillahi,sun shiga uku da wannan masifa..

Haj Maryamah kallo daya tayiwa AMAL da sitirar jikinta ta dauke Kai sbd koina gidan cin jikinta da zuciyarta yakeyi kamar wuta na balbala a jikinta da zuciyarta takeji.

Ita kanta Amal ba wani kallon sosai takeyi musu ba saidai ganin irin kallon da umman keyi Mata da Kuma qazantaccen kallon da haj Maryamah Tai Mata ta dauke Ido yasata Dan matse fuska ta qaraso batareda ta sake kallon ko inda sukeba Dan bayan zafi,fushi da tashin hankali Babu abinda yake bayyana a fuskokinsu.

Da muryarta Mai nutsuwa Kai tsaye tace,

"Mommy what's going on here??
Wainnan baqin fa?
Basuyi Kama da mutanen dakike kawowa gida ba,
Komai lafiya kuw.....

Kafin Haj Zainab da kwata kwata Bata so fitowar Amal ba tayi magana cikin wani irin zafi daya Gama cinye zuciyar haj Maryamah da umma akan maganar Zainab ta farko akansu da wadda yarta tazo tana fada yanzu,...Wai basuyi Kama da mutanen datake kawowa gidaba,
.....Su waye agurin..?¿

Umma ta katse Amal din cikin zafi da baqin cikin zuwansu nan tace,

"Mu ba irin baqin dake zuwa ne nanba sbd Dama ba gurin zuwanmu bane,
Ki wuce da uwarki zamuyi magana.

Gurin Zainab ta maida kallonta cikin zafin maganarsu dake cin zuciyoyinsu tace,

"Tarbiyar da Kika zabarwa kanki da yarki kenan, rayuwar da Babu tsafta da tsoron Allah aciki,
Wannan yanzu duka rayuwarki ce kece kikai raayi kikabi
Mu yanzu tamu rayuwar muke magana anan wadda kike kokarin shigowa..

Kallon bakin umman Haj Zainab keyi sbd Kamar Bata gane maganganunta Dan suna sauri cikin fada da fushi.

Ahankali Zainab din ta sake kallonsu cikin nutsuwa tace,

"Haj Ina wuninku?
Barka da zuwa
Ku qarasa zama......

Cikin wani irin zafin Rena musu hankali datakeyi Haj Maryamah ta kalleta tareda matsawa gabanta idanuwanta jajir daukeda wani quncin bacin Rai tace,

"Zainab ba Idon Nera Kika zamaba ko karuwar duka duniya Kika zama kisani har gobe mune a gabanki,

Nice a sama dake,
Sbd Ni kike anan tsaye sbd alfarmata....

"Tabbas sbd ke nake tsaye anan sbd kece Kika haifi Zainab Adamu,
Saidai wadda take tsaye anan din da kike magana Idon Nera ce wadda batada alaqa ko daya da zainab Adamu bare wainda ta dauka jininta a dah,
Idon Nera batasan abinda kike magana akaiba ki Fadi abinda kikazo nema a gurin Idon Nera shugabar karuwai......

Cikin tsawa Mai qarfi umma ta tsaya gaban zainab tace,

"Idan me Kika zama Maryamah yayar......

Manyan idanuwanta dasuka fara sauyawa ta watsawa umman Kai tsaye tana danne fushinta tace,

"Itace zatayi magana sbd itace nasan na taba hada jini da ita,
Abayan kin fada Kuma na riqe cewa bakuda alaqa dani,

Meya faru yanzu???
Alaqar ta dawo ne?
Kun sanni?
Wadda kuke tinani Bata Nan
Ta mutu,
Wannan IDON NERA ce duk inda zaku tambaya ku tambaya babu Zainab Adamu,baiwa 'yar aiki Kuma Mai renon gidan marigayi Asadullah...

Hannuwan umma dake wata irin rawa ta daga a zafafe zata kaiwa zainab din Mari akaiwa hannun kyakkyawan riqo.

AMAL ce wadda ranta yagama baci batareda tagama fahimtar meyake faruwaba a tsakanin nasu
Amma dai abu daya tada sani koma mahaifiyar mommyntace wannan bazata daketaba a gabanta.

Daga zainab har haj Maryamah da umman hannun Amal dake riqe Dana umma suke kallo kowannensu zuciyarta na qarasa shiga firgici da tashin hankali,

Jikin umma rawa yadauka sbd masifar Zainab basuyi tunanin ma takai hakanba,

Bakin umma na rawa tace,

"Zainab Kinga abinda haihuwar titi take tattare dashi ko???
Kin haifi Yar aure Kika hauro Kika haifi yar tit......

Hannun Amal dake riqe Dana umman ta karba tareda kallon umma hakurinta na qarasa qarewa tace,

"Da wadda na Haifa da aure da wadda na Haifa Babu aure duka 'yayana ne,
Basuda bambamci agurina tunda nice na haifesu Kuma tarbiyarsu da rashin tarbiyarsu duka matsalatace data shafi iya wainda nasani kokuma nakeda alaqa dasu...

Kallon Haj Maryamah da idanuwanta ke gap da zubarda hawayen datakejin kamar ta mutu a take ta huta da baqin ciki hada jininta da zainab,

Zan Kama 'yata Mara tarbiya masu tarbiyar zasu iya komawa inda suka taho..

Katseta Haj Maryamah tayi da cewa,

"Har abada bazan yafewa kainaba na sako qafata a gidan qazamar rayuwarki,
Akan 'dana nazo Wanda idan har kin yanke alaqar da gaske to inason daga yanzu ko sunan AQEEL ASAD kada ki sake fada har mutuwarki Zainab kamar yanda Kika gogewa 'yarki sunan MARYAMAH Kika maida Mata wani sunan to inason yau ki goge Dana daga rayuwarki,

Idan har kinsan keba zainab Adamu bace baiwata,Yar renona, keda qazantarki ki fita daga rayuwar AQEEL ASAD.....

"AQEEL ASAD Dama yanada mahaifiya??
Yanada uwa yayi kamar ta mutu batada duniya batada amfani??...Amal ce ta katse Haj Maryamah da maganar tana kallonta da Dan mamakin dayafi yiwa umma Kama dana wulaqantawa..

Kallonta sukeyi umma da Haj Maryamah Banda haj zainab data rintse idonta sbd batason Amal tashiga wannan fadan da tun batazo duniyaba ita kanta yake,
Fadane na mahaifiyarta data Dade da mutuwa yadawo kanta bazataso yazo kan yartaba,

Idan ban mantaba AQEEL ASAD shine Wanda yake kwana a gate din gidan Nan sbd son ganin Mommy,
Daman yanasa mafada?
Yanada dangi?
Harma da uwar data haifesa??
Unbelievable na dauka shima 'dan titin ne kamarmu sbd alokacinda yake kwana Babu alamar yanada uwa harma da.....umma takalla tace,

"Waye wannan?
Kece wa??

Koma ku din su waye agurinsa kokuma a rayuwar mommy tace batada alaqar yanzu,
Zaku iya tafiya??
Zaku gane hanya??

Dan daga muryarta da Bata rawa ko sauyawar sautin Dan bacin Rai Tai ta daga murya hankali kwance tace,

"Bilkisu zo ki nunawa baqi kofa sun manta inda suka shigo da alama.


*************
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

Makarantar Lafiya dake garin Kazaure (Kazaure school of health technology) tana farincikin sanardaku cewa ta Kawo wani sabon tsarin karatu a saukake na part-time Degree da Diploma a wasu kwasakwasai domin ma'aikata masuson karin karatu da 'yan Kasuwa wanda basu da isasshen lokaci.

Kwasakwasan kamar haka:

DIPLOMA

1.Dental surgery Technician

2.Medical X-ray Technician

3.Health Information Technician

4.National Diploma in Biomedical Engineering

5.Public Health Technician

6. Community Health Extension Worker (Re-trainee)

7.Junior community Health Extension Worker (JCHEW)

DEGREE

1. Health Information Management

2.Public Health

3.English Language

4.Public Administration

5.Business Administration

6. Economics

7. Accounting

8.Computer Science

9.Mass Communication

10.Agricultural Economics

Domin karin bayani a tuntubi wannan Lambobin:08035298851, 07066542055 ko Azo haraban makaranta dake No 3 Emir's Palace road off Kano-Daura road Kazaure a jihar Jigawan Nijeriya.


***********
Bilkees da mafeeda dasuke tsaye kofar shigowa Basu qarasoba tun lokacinda umman taso Marin Idon Nera..

Rawa kafafunta keyi zufa na tsiyayowa ta cikinsu kamar Mai fitsari...

Mufeeda ma da idan ta fahimci abinda umminta ta fahimta shine IDON NERA itace wadda AQEEL yake cikin qunci dominta shekaru masu tsayin nan,
Umma tace musu ta mutu shine sanadin dayake wannan halin....

Innalillahi wainna ilayhi rajiun" suke maimaitawa a tare,
Waye MARYAMAH daya sake sakawa mufeeda sunan suke kiranta da mufeedan sbd sunada tabbacin ba ummarsa yayiwa takwararba sbd Kai tsaye aranarda ya saka Mata sunan yace,

"LITTLE DINA NA MAIDA"

Zainab dince little?
Sauya suna tayi daga MARYAMAH zuwa Zainab ne?
Shin Idon Nera din itace dai da gaske Maminsa da akace ta rasun kokuwa dai Basu Gama fahimta bane...

Wani haqayin masifa da tashin hankaline takejin Yana fitowa ta kunnuwanta da bakinta harma da hancinta,

Wutace takeci a zuciyoyinsu sunsai sbd tiririn dake tashi a jikinsu dake wata irin rawa.

A zafafe mufeeda Bata ganin ko gabanta ta yunqura zataje ta shaqe Amal Dan kuwa idan har uwarta Idon Nera ce wadda aka saka Mata sunanta sbd ita wlh saita fasa Mata Baki Dan kuwa anci amanarta...

Idanuwanta a rufe suke bataji Bata gani sbd baqin ciki Mai tsanani na yanda zaace daddynta ya hada zuria da wainnan din...

Bilkees ce ta riqota da qarfi tajawota suka fito batareda angansuba..

Janta takeyi da qarfi itama bataji Bata ganin sbd itama gabaki daya neman Aron hauka takeyi Dan kuwa su umma sunci amanarta da 'yarta dasuka ce musu Maminsa ta rasu

Ta shaida quncinsa da zurfin kaunarsa ga Maminsa MARYAMAH tsawon shekaru,
Sunan Maryamah shine qurjin zuciyarta Amma sanin ta mace shiyesa ta danne kurjin ta gogesa Ashe tana raye,

Meye nufinsu umman da Haj Maryamah?
Sunsan wacece Idon Nera din shine suka barta tana hauka hawan jini dana zuciya su kasheta tana bulayin neman qwato Mijinta daga hannun karuwai,

Rufeta sukayi sukazo neman sulhu????
Idan sulhun yakai AQEEL dinta ga shigowa rayuwar wainnan karuwan abanza,
Idan yadawo da kaunar Maminsa cikin Ransa Yaya zatayi??
Uwarshi ma Dan taga Babu kusanci da shaquwa tsakaninsu ne yasa Bata damuba Amma wannan a tsawon shekarun Dama Bata Raye ta sheda irin zurfinta a zuciyarsa bare yanzu tana raye,

Kenan Babu ruwansu da ita ta kansu sukeyi shine aka boye Mata aka taho bada itaba bayan itama tanada right na Azo da ita tunda itace matarsa tafi iko akansa akan wannan lamarin,

Mota ta bude a zafafe ta jefa Mufeeda dake Jin kamar ta kurma ihu kowa yazo.

Shiga motar tayi a zafafe ta bugawa securities wani mugun horn daya sakasu bude Mata gate da sauri suna mamakin motocin gidan AQEEL ASAD yau dasuke zarya a gidan.

Da mugun speed ta hau titi tana cewa,

"Mutuwar kanso Zanwa kowa
Dame hawan jini dana zuciya kowama nasa ya tashi me mutuwa yayi me rabon cigaba da yaqin ya wuce.

Wayarta ta daga Kai tsaye ta saka Kiran Hafiz Wanda yake aikin duk wani Abu data sakasa,
Yana daga wayar muryarta a hargitse tace,

"Hafiz kaje babban police station ka daukomin motar Yan Sanda suzo gidan IDON NERA kame zasuyi Ana can Ana dambe da fashe fashen Kaya..

Mufeeda kuwa Yan jarida ta boye number ta Kira itama ta turasu gidan tana cewa,

"Su umman zanga yanda zaayi sulhun yanzu idan kota Ina mutuncinsu da sunansu ya bayyana a gidan IDON NERA tareda sanin alaqarsu da ita da basason asani.

Hafiz ne ya Kira yabata tabbacin an isarda sakonta kowane time police zasu Isa gidan.

Burki taci a zafafe tareda yin ribas tayi kwana ya juya Dan kuwa yau so take a gaban idonta sunan kowa ya baci ayi barnar da zaayi zumunci da alaqar taqarasa yankewa kowa ya koma rayuwar data fi masa IDON NERA tayi nesa da Mijinta babu ruwanta da ita din Maminsa ce
Karuwa tasanta
Kuma ahakan zataci gaba kallonta.



*****Amal kallon mommynta tayi wadda idanuwanta suka sauya da qunci da baqin cikin dake kwance cikin ranta na shekaru,

Riqo hannunta tayi tana matsawa jikinta tace,

"Mommy Allah ya Dade da kawar da baqin ciki rayuwarki tareda duk wani qunci,
Karki damu da tsayawa sakawa kanki damuwar wahalan wasu,
Kece Haj Zainab Idon Nera bakya buqatan daukan reni ko wulaqancin kowa..
Koma su din su waye a rayuwarki na tabbatarda basuda mahummanci tunda Kika rufe shafinsu arayuwarki.......

Wannan da kike magana cikin rashin girmamawa sbd rashin tarbiyarki da rayuwar da kuka taso ita din yayar uwarkice uba daya,
Jini daya ne yake yawo ajikinsu
Saidai ita Bata Mai tsafta Bai gurbata da kowane jinin qazantaba..

Ita din jinin mommyna ce naji
Kefa waye ce?
Jininta ce?

Cikin nutsuwa Haj zainab ta katse Amal din da cewa,

"Amal ya isa, shekarunta sun wuce amsa duka maganganinki,
Kije ciki
Sungama tafiya zasuyi ai tunda sun Gama.

"Zainab kin nuna tsintacciyar mage Bata mage,
Kin nuna har abada halak daban take da Haram,
Yau nice Kika tsaya gabana kikaci mutuncina da 'yarki,
Kin nuna Mana babancin tarbiyar titi zuriar titi wadda takeda dogon Nisan banbanci da tamu rayuwar Dan Haka ki saka aranki ki ajiye
AQEEL har abada rayuwarsa ta wuce qanqantar rabar inda wannan rayuwar taki takeba,

Me kikeso?
Me Maryamah tayi Miki Bayan alkhairi da Zaki saka Mata da wannan muguwar sakayyar?
Meyasa Kika zabi rabata da 'danta?
Baga taki 'yar ba anbarki da itaba a gabanki idanma Mara tsarkin ce idanma Mai tsarkin ce.

Zuciyar haj Maryamah data kasa daukan komai ce ta fara dauke wuta tana neman kasa bugawa...

Juyawa tayi ta nufi kofa tana cewa,

"Umma bazan iya qara ko second dayaba anan
Bazan iya shaqar numfashin gidan Nan ba
Zanje nayi da Wanda nakeda iko akansa idan nice na haifesa to zai zaba tsakanin ni da Idon Nera da qazantarta.
##MAMUH#*_Arewabooks@Mamuhgee_*
36
Kofa ta nufa Kai tsaye idanuwanta basa gani sosai sbd zuciyarta kowanne lokaci bugawa zata iya yi,

Ita kanta umma zuciyarta bugawan take neman Yi tana kokarin dannewa,
Hawan jininta kuwa tanaji yarigada ya hau Amma bazasu iya bayyanarda rauni ko tashin hankalinsu agaban Zainab ba da 'yarta,

Dukkaninsu Babu Mai gani suka tinkari kofa suka fice Babu Mai sassauci a zuci...

Haj Maryamah ce agaba umman na bayanta qafa ba qwari,

Motarsu suke kokarin nufa kawai ba tsammani aka fara daukansu hotuna Ana jeho musu tambayoyin dasuka kusan sumar da Haj Maryamah datayi mutuwar tsaye cikin mummunan tashin hankalin da Bata taba shigaba,

Umma tsabar firgici rudewa Tai tana neman faduwa cikin tashin hankali.

Innalillahi wainna ilayhi rajiun
Innalillahi wainna ilayhi rajiun
Meye Haka?
Me Zainab take nufi da hakan?
Tozarci mafi Muni ne tasa ayi musu¿

Innalillahi wainna ilayhi rajiun"
Kasa magana Haj Maryamah Tai sbd numfashinta dake kokarin daukewa tana kokarin kamosa Amma lamarin yafi qarfin abinda zuciyarta zata dauka,..

Isowar Bilkees ne tareda motar Yan Sanda yasa kallo komawa kansu Ana sake daukan hotunan da rahoto
Yau dai ga Yan Sanda mota guda a gidan IDON NERA
Hakama ga familyn AQEEL ASAD a gidan,uwarsa da matarsa da 'yarsa,
Kenan dai ga gaske akwai alaqa a tsakaninsa da IDON NERA...

Isowar Lulu a guje da mota yasa Yan sandan dakatawa daga waje suna jiran isowarsa Dan kuwa basu dauka gidan IDON NERA dinne da gaskeba sukazo.

Babu Bata lokaci kallonsu kawai yayi yacewa Barr Salahudeen yaji da matsalar,

Ciki yayi da sauri Yana mamakin abinda yake faruwa..

Bilkees kuwa haukace take cewa Yan sandan su shiga su Kama Idon Nera sbd itada yarta sun Zaga iyaye Mijinta tareda cin zarafinsu...


Umma Bata taba jin ta tsani hada zuria da Mai sunama Bilkees ba bare wannan datake gabanta ayanzu,

Allah ya tsinewa wannan Bilkees da Allah yayota mahaukaciya,

Wannan 'ya anyi mahaukaciyar asararra,

Wayace takira Yan Sanda da jarida,
Su tayiwa mummunan tonan asiri da tozatawa ba Idon Nera ba,

Yau tayi musu abindama yafi Wanda akayo musu daga ciki batareda kowa yasaniba,

Yau balkees taja musu abin kunyar dasukai ta gujewa shekara da shekaru na boye alaqarsu da Zainab Idon Nera da basa kaunar Koda Wasa wani yasan alaqarsu da ita.

Haj Maryamah kasa dago Kai tayi Saidai taji muryar AQEEL ASAD akanta Yana Kiran sunanta ahankali cikin kulawa da damuwa Mai tsanani....

Daga hakan ta Dena Jin komai sai numfashinta dake gizga Yana neman daukewa take ta yanke jiki ta Fadi...

Bilkees da batasan ta Ina AQEEL ASAD ya sauka ya bullo ba sai ganinsa sukayi a gabansu sumewa takusan Yi tsabar firgita da tashin hankali Sabo,

Mufeeda hannu ta Dora akai tana neman kurma ihu Amma takasa,

Umma dataga 'yarta a jikin AQEEL Rai hannun Allah itama sarewa kafafunta ke neman Yi Saida uncle Lulu ya riqota aka sakasu mota da gudu akai asibiti dasu.

Securities ne suka Kori Yan media daga gurin wainda suka kwasa wasunsu suka bi asibitin da aka nufa da cika rahoton nasu tunda ga Mai gayyar Nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login