Showing 51001 words to 54000 words out of 155476 words
anan basa hakan
Tana denawa din itama saitaji ta raba kanta da wahala sbd wani lokacin wahalarda Kai ne da sakawa Kai ciwon Rai faman ihu da wahalarwa ga masu aikin.
Karfe bakwai da rabi sukai dinner dinsu gabaki dayansu Kamar yanda suka Saba
Suna gamawa kowa ya nufi inda yake so
Wasu sukai dakunansu wasu Kuma palon sama suka nufa Dan acan suke fira iyasu familyn kawai baqi basa zuwar dasu palonsu na sama.
Amal dakinta tanufa sbd tanada abinda zatayi.
Uncle Lulu kuwa yayi magana dasu Barr Salahudeen sun basa tabbacin lamarin yazo da Dan tsauri Amma dai zuwa gobe zasu kashe zancen kwata kwata inshallah.
Sanarda IDON NERA yayi tace Gaskia Dole su kashe zancen zuwa gobe Dan har tafiya takeson Yi Amma wanna qarar zata tsaida ita ta Bata Mata lokaci.
#MAMUH#
#PURELOVE#MARRIAGE#
DS AQEEL ASAD#AMAL IDON NERA#
#SISTERS
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*π₯
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*π₯
Billyn Abdul
*IDON NERA*π₯
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*π₯
Safiya huguma
*KI KULANI*π₯
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
π³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*π₯*_Arewabooks@Mamuhgee_*
26
Washe gari tunda safe uncle ya fita zuwa Office dinsu inda zai tattauna dasu Barr Salahudeen akan maganar data fara qular dasu tun jiya Ana abu daya ankasa magana daya.
Isowar Barr Salahudeen da Salis babban Yaronsu makusancinsu shida Haj Zainab din yasashi kallonsu Yana kallon lokacin kusan karfe daya Amma sai lokacin suka samu barowa daga offishin Alkalin kotun..
Zama sukayi Barr Salahudeen na sauke numfashi me Dan zafi Yana zare farin glass din fuskarsa ya ajiye gefe Yana dawo da kallonsa kan uncle Lulu yace,
"Sir Lulu wallahi wanna karon matsala suke son bamu sbd Kamar ta inda qarar ta fito Suma sunada power sosai Kuma sunada qarfi a Bangaren amfani da musulincin...
Ajiye wayarsa uncle Lulu yayi Yana zare nasa glass din shima Yana kallon Salis da shima duk nasa ran yake a matuqar bace da koma wane Dan iskan ne keson kawo musu rainin hankali da wulaqanci a rayuwarsu dake tafiya daidai.
Maida kallonsa yayi kan Barr Salahudeen Yana kokarin danne bacin Ran dake cin Ransa yace,
"Barr Salahudeen kaman yanda kasaba kasan yanda zakayi wannan maganar ta 'bata,
Ta mutu,a rufeta gabaki daya kafin gobe ko sunan Zainab da IDON NERA kada akuma ambata kwata kwata a wannan kotun,
Ko nawa ne kaman yanda kasani Salis zai bada a tabbatarda zancen Nan Bai sake tashiba bare fita.
Sir Lulu insha Allah kafin goben zamu tsaya muga yanda zaayi.
Gyada musu Kai Kawai yai Yana Jingina da lafiyayyar kujerar dake office din nasa Dan ko magana bazai iyayiba sbd Ransa da yayi zafi,
Wannan hukumar musulinci ake magana wadda duk connections dasuke dasu bazasuyi aikiba agurin sbd kowa na shiga zaayi tir dashi sbd Cewa zaayi sun cin mutuncin addini da malamansa,
Su kansu sunada iko da damar da zasu kashe case komai girmansa cikin mintina kalilan Amma wannan ba damar wani nuna wani budadden iko ko girman dasuke dashi sbd tir da Mugayen diban albarkar da zaa bi zuriarsu dashi akan sunyiwa addini tsaurin Ido Dole a boye zasu bullowa lamarin suyi watsi da qarar kafin daga baya suyi lokacin Wanda yayi qarar Dan bazasu yafewa ko waneneba yakeson tarwatsasu a boye ba.
Koda ya dawo gida Bai fadawa Haj Zainab babu abinda aka samu akaiba akan zamcenba sbd kada ranta ya baci ta daga zancen duniya taji maqiyansu sufara musu dariya anfara fin qarfinsu.
Barr Salahudeen da Salis harma da wasu manyan lauyoyin guda biyu a ranar sun nuna duk wata basirarsu Dan kashe qarar akan wanna qarar rashin hujja ce Amma babu abinda ya girgiza malaman da alqalan sun tsaya akan sai Haj Zainab Idon Nera tazo kotu itada Lulu Idon Nera.
Zafi kan lauyoyin ya dauka Wanda yasa Dole suka sanar dasu Haj Zainab abinda ake ciki qarshe manyan hayoyin datake dasu tayi amfani Wanda ya sake tsanananta case din
Sadai sun samu yanda suke so zancen yafara sanyi.
Daya daga cikin alqalan dasu bilkees suke sakarwa wasu irin matsiyatan kudi suna qarya da sunan Mijinta DR SHAYKH AQEEL ASAD akan yasan duk abinda yake faruwa ne ya sanar dasu IDON NERA sunfara nasarar kashe zancen.
Cikin bacin Rai da baqin cikin wannan mummunan labarin yasa suka saka aka fidda zancen a Media take aka San da rikicin Idon Nera da kotun musulinci Ana Kuma jiran aga Suma malamai da alqalan musulinci idan tafi qarfinsu.
Fitar zancen a koina ya lalatawa su uncle Lulu komai Dan kuwa tini aka yada zancen a kafafen yada labaran media..
Su Amal sai alokacin sukasan me yake faruwa.
Ran Amal yayi mummunan baci matuqa musamman da kusan kowa neman abin yadawa akeyi akansu koyaushe tunda sun zamarwa mutane qayar maqoshi,wasu Kuma sonsu sukeyi suna matuqar burgesu.
Kamar yanda kowa ya Santa batada hakurin reni bare wulaqanci Dama babu Wanda ya Isa yayi Mata,
Mahaifiyarta itace rayuwarta babu Mai taba mahaifiyarta Tai shiru akan hakan,
Duk zagi da Mugayen sunayen da ake kiransu dashi musamman mummynsu bai taba damunta ba sbd tasan ba halayensu bane Kuma sunan Bai taba damun mommynba shiyasa suka taso da rashin damuwar duk abinda zaa fada akansu Amma Banda cin zarafi ko yunqurin tozartasu
Shi wannan wani abune da basa dauka, Dan kuwa suna amfani da iko da dukiya su koyarda duk Wanda yashiga huruminsu da niyar tozarci.
Kaf ahalin Haj Zainab itace wadda idan aka taba a ahalin kowa yake gaggawar kasa jurewa sai inda karfinsu ya qare.
Wannan cin mutuncin da aka bullo dashi Rana tsaka zaa musu ta tabbatarda daga matar SSG ya fito dan Haka zata nuna musu tafisu zama karuwar dasuke tinani.
Senator jarma mahaifin Anty Fareedah shima Kai tsaye yashiga cikin zancen da kamar familynsa ne su sbd 'yarsa dake cikinsu tana aure cikin kauna Mai tsanani da kwanciyar hankali da aminci.
Kusan shima Mijin Siddi yanata nasa kokarin gurin ganin an kashe zancen Amma tako Ina kamar anyiwa case din hayaqi.
Su Bilkees kuwa sai alokacin duniya tayi musu Dadi hankalinsu yakwanta suka tattara zancen dasukasan zuwa yanzu maganar auren yagama lalatuwa suka watsar zuciyoyinsu fes suda 'yayansu.
Karfe Tara na safe Amal ya fito daga gidansu cikin motarta Ford fiesta fara Ranta har lokacin quna yakeyi sosai akan haukar matar Hayat ta isheta gwara ta nuna Mata su waye IDON NERA.
Kai tsaye Office dinsa ta nufa sbd yanata Kira Bata dauka batajin zata kirasa da Haka ta nufa office dinsa Kai tsaye.
Tana Isa babban building din tayi parking ta fito motarta Kai tsaye ta nufi reception Bata tsayaba ta nufi office dinsa Kai tsaye dayake receptionist din ta San itace Sabuwar Amaryar Sir din nasu sai Bata tsayar da itaba saima sannu da zuwa datake Mata Amma ko ta kanta Amal din batayiba ta wuce.
Tana Isa kofar office dinsa secretary dinsa ya taso da sauri Yana Mata sannu da zuwa bakinsa a washe Amma ganin yanayin fuskarta yasashi Dan takaitawa da cewa "Welcome Ms AMAL" kawai.
Zaune yake Yana waya cikin black suits dasukai Masa kyau sosai
Wani mahummin conference meeting zasuyi da turawa shida Amininsa akan wani kasuwancin hadin gwiwar dasuke dasu shiyasa yayi shigar suites din.
Shigowarta yasashi katse Kiran cikeda mamakin ganinta da Kuma sanyin jikin ganinta bayan tsawon kwanaki data qi barinsa ganinta.
Dayake yau batada school futan safe ne zuwa gurinsa kawai Dan Haka blue pencil jeans me ajikinta da farar free Balenciaga sweater data bayyanarda wayewarta da rashin ruwanta a lamarin kowa sai nata.
Kanta silk Versace scarf ne wayarta daga wayarta sai key din motarta a hannunta sai qamshinta Mai sanyi da kashe jiki tareda Kama guri ahankali.
Tasowa yayi cikeda kaunarta data Gama Masa illa Yana kallonta Yana cewa,
"AMAL da kinkirani kinsan cewa zanzo.....
Rufe fararen idanuwanta Tai tareda budewa Kai tsaye tana kallonsa ta bude baki tace,
"Kasan me abinda matarka takeyi kuwa?
Kasan meyasa tun farko naqi yarda da auren masu mata??
Sbd irin wannan rashin hankalin da hayaniyar ne,
Meyasa matarka zata ringa shiga alamuran family na??
Hayat kafi kowa sanin bazan aurekaba matarka namun wanna haukan tun ban shigaba wlh na shiga tamun makamancin haka saina saka anrufeta asibitin mahaukata har tsufa ko kai bazaka fiddotaba,..
Meye hakan?
Meye matsalarta damu?
Sbd zaa aura Mijinta??
To tun wuri ka janye maganar auren tunda bazaka iya controlling dinta da haukantaba.....
Zafi Kansa ya dauka sbd idan ran Amal din ya baci Dama Bata saurarawa
Gashi ya kasa fahimtar kokuma yarda da Nafee nada saka hannu a lamarin tunda ta saduda ta hakura da rungumi qaddara Amma Kuma bazai nuna qin yardarsaba kada Amal din ta sake Hawa tun Bata furta kalmar fasa auren ba tazo ta furta..
Shirunsa yasa Amal kallonsa cikin tsananin bacin Rai da mamaki tace,
"Like seriously HayatΒΏΒΏ
Dama mezata tsammata agurin me Mata sbd matansu sungama maidasu wawaye and useless.
Juyawa tayi ranta a matuqar bace da har tayi gangancin yarda zata auri Hayat din tun farko bayan Daman batada raayin auren masu Matan.
Cikin sauri da damuwa yayi saurin zagayowa ya tareta Kansa na sake daukan zafi gashi meeting dinsa ya kusa Baqonsa ma yakusa isowa ga rigimar Amal din Kuma wadda bazaitaba son bacin ranta ba.
"Amal koma menene na Miki alqawarin Zan duba komai da kyau Ni kaina bazan taba barin duk Wanda ya tabaki ko familynki ba....
"Hayat please kaje kaji da kanka Kuma,.Ni na Gama da Nan Kuma..
Kofa ta nufa ranta a bace kafin takai hannu kan kofa aka turo kofar ahankali cikin nutsuwa tareda shigowa Kai tsaye sbd baiyi tunanin akwai mutane a kofarba.
Kirjinsa da nata ne ya kusan haduwa batareda kowannensu yasan da zuwa kowannensu din ba.....
A lokacin daya kowannensu ya ja baya musamman shi din da har qamshin jikinta ya shiga hancinsa Sosai sbd kusan dasukai Sosai.
Qamshin tsadadden Turaren VICTORIOUS CARBON na Boadicea da Bata taba jinsa agun kowaba yasata dagowa zata kalli Wanda yake daukeda wannan coolest qamshin Mai nutsuwa.....
AQEEL ASAD da baya buqatan ganin ko waye tunda ya shaqi qamshinta ya fahimci mace ce,
Tana dagowa ya tabata ya wuce ciki office din sanye cikin Royal blue Slim fit D&G suit qamshinsa na gauraya office din Kai tsaye sofa ya Isa ya zauna sai alokacin ya dago manyan idanuwansa masu kyau da kwarjini Mai nutsuwa ya kalli Hayat Wanda shigowar AQEEL ASAD ta sanyasa kasa bin Amal wadda itama Bata waiwayoba ta fice ranta a bace.
Wani numfashi Mai zafi SSG din ya sauke tareda dawowa ya zauna Yana kasa kallon AQEEL ASAD wanda yasan bazai ce Masa komaiba akan ganin mace a office dinsa duk da babu ta inda Amal tayi Kama da maaikatansu bare yayi tunanin maaikaciyarsu ce duk da yasan ko Kallonta AQEEL ASAD baiyiba barema ya damu da sanin wacece.
Zaiyi maganar gyara zancen ganin mace da AQEEL ASAD din yayi Dan kare Kansa,
AQEEL ASAD din ya katsesa da dagowa ya kallesa a natse cikin sanyin kalami da kamewarsa yace,
"Muje time yayi.
Miqewa yayi tareda wucewa gaba Dan Dama conference meeting dinne kawai ya kawosa office din Hayat din da safen.
Inda zasuyi conference meeting acikin maaikatansu SSG din suka nufa Kai tsaye sbd suna gamawa AQEEL zai bar maaikatan yanada gurin zuwa Mai mahummanci da aka gayyacesa akan wani case na manyan Bata garin da aka Kama Ana tuhuma da yada barna Wanda akeson shigarsa cikin lamarin sbd qarfin dayake dashi a kotun musulinci dayake taimakwa sosai da dukiyarsa Mai yawa.
Sai qarfe goma Sha daya harda rabi suka kammala Dan Haka Kai tsaye yabar gurin,..
Yaso komawa gida Kansa ya 'dan sake yakuma sauya kayan jikinsa saidai lokacinda ya bada na zuwansa ganinsu yayi Dan Haka yace drivernsa ya wuce dashi can din Kai tsaye tunda yasan suna can sun taru manyan malaman Ana jiran isowarsa.
Yana Isa babban ofishin yaqi da barna a musulinci Wanda yake cikeda offices na manya malamai da manya alqalai na musulinci da manyan lauyoyin musulinci,
Babban guri Mai tsaro da dokoki tareda tsayawa addini da musulincin da musulmai harma da human rights duk sunada aciki.
Yana daya daga cikin manyan masu bada gudunmawa Mai girman tsoka agurin tafiyar da komai,
Bawani babba bane a shekaru sosai Dan kusan da yawan alkalan da malaman sun girmesa Amma Kuma Ana respecting dinsa sosai sbd tsayawa dakuma dukiyar dayake bawa agency din sosai ga kuma iliminsa a addinin da saninsa daya qara Masa girma da suna sosai agurin mutane bayan sunan dayake dashi a harkar business dinsa da aikinsa da uwa uba dukiya wadda ke qarawa mutane suna.
Isowarsa gurin yasa jamaa da Dama suka iso Ana Masa barka da zuwa..
Wani irin kwarjini da cika idone dashi Wanda yasa da yawa ake sauke Masa Kai koda an girmesa,
Yanada kamewa da haiba datake qara Masa girma a gurin mutane Dan haka ake yawan neman shaawara ko zaunawa dashi idan suna neman maganin matsalar data addabi bangaren aikin nasu,
Duk wani taro babba na addini dazai buqaci manyan mutane Yana daya daga cikin wainda baa iya Dena gayyata ta musamman wannan yasa da yawa suke kiranda da DR SHAYKH AQEEL ASAD sbd Basu ciresa cikin manyan malamai masu daraja da aka saniba gashi matashin daya fara zama dattijo abokin Manya,ga kudi ga ilimin Boko Dana addini ga kamewa da wayewar rayuwa Mai aji da tsafta.
##MAMUH
#AQEEL ASAD/IDON NERA
#PURELOVE/HOTLOVE
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*π₯
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*π₯
Billyn Abdul
*IDON NERA*π₯
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*π₯
Safiya huguma
*KI KULANI*π₯
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
π³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*π₯*_Arewabooks@Mamuhgee_*
27
Kai tsaye cikin babban palon alfarma na tarbon manyan Baki aka nufa dashi Yana tafiyarsa cikeda nutsuwa da Dan kokarin sake fuskarsa dabai cika sakewaba.
Cikin girmamawa da mutuntawa sosai ya gaisa da Alkalai kusan uku da manyan malamai kusan bakwai sai Lawyoyinsu biyu.
Cikin nutsuwa aka fara karanto halaye da babbar shaharar da IDON NERA sukai a barna,
Shiru yayi kyakkyawar fuskarsa na Dan sauyawa da irin munanan abubuwan da aka fada wainnan IDON NERA din na aikatawa,
"Ita asalin IDON NERA din aurarrakinta iya wainda aka kiyasta aka sani aure goma Sha daya,
Sauran aurarrakin nata da baasan dasuba awainda tayi ne kafin daukakarta sai Wanda taje har qasashe biyu tayi ta dawo Wanda hade lissafinsu abin ba dadin fada,
Duka wannan auren babu Wanda tayi da zuciya daya,.
Da manufofi takeyinsu Kuma ta kashe auren ta fito Kai tsaye babu shakka ko tsoron Allah,
'yayanta biyu duka babu mai tarbiya gashi Suma ta dorasa akan wannan muguwar tarbiyar ta auren masu kudin suna fitowa domin yada barna,
Yayanta dasuke uwa daya uba daya 'dan daudu ne na musamman dayake tareda manya Yana yada tasa barnar shima,
Babban gidan barna na karuwai dake garin Nan nasu ne ikonta ne,itace uwar karuwai da Yan daudu,
Tako Ina yada barna sukeyi,
Akwai babbar qungiyar manyan karuwai dasuka zama manyan Mata sun mallaki gidaje da dukiyoyin kansu suna sake lalata tarbiyar alumma da wasu dabiu da halayensu,
Ita IDON NERA ta tsaya musu tako wane bangare na hukuma,
Tanada manya connections,
Tanada manyan mutane,manyan Yan siyasa masu mukamai maana manya qasa,
Tanada manya tako Ina dasuke tsayawa aduk lamuranta..
Tana amfani da 'yayanta Mata guda biyu gurin mallaka da juya manya yanda takeso, maana yayanta sune mukullin barnar datake aikatawa manya da yawa suna tsaya Mata sbd kwadayi da shaawar auren yayan nata,
Dayar tahau hanyar uwar na aure aure,
Dayar Kuma a yanzu itace take yanda takeso da manyan mutane,
Sun tarwatsa aurarrakin mutane da Dana da nasu son ran da ganin iko
Qarshe dai kullum sake samun qaruwar karuwai da yan daudu akeyi na yayan musulmai da dama da yawa duk a qarqashin iko da sunanta...
Anyita rigingimun daukan mataki akan wannan barnar tata datake yawa Amma babu wani nasara sakamakon koyaushe juyar da dalilan akeyi a kashe to wannan karon lamarin ya dauki zafi sbd motar karuwai biyu da aka Kama masu qananun shekaru dasuka tabbatarda a qarqashinta suke,
A bangare daya Kuma yarta AMAL IDON NERA tana yunqurin lalata aurarrakki da dama gurin amfani da kyanta gurin raba maza da matayensu na sunna da 'yaya da ubaninsu..
Karshe dai anyi magana da lauyoyinta da manya da suka Shiga zancen mafita ake nema akan lamarin nata Dan Haka aka yanke shawarar janye shariar zaa zauna da ita ayi sulhu tareda magance yawan barnar datake yadawa.
Wannan shine taqaitaccen bayani Dan kadan akan Haj Zainab IDON NERA..qarasa zancen lauyan musulincin yayi Yana dagowa ya kalliΒ AQEEL ASAD Wanda ya Dan Yi qasa da Kansa Yana rintse fararen idanuwansa sbd sunan da aka ambaci wannan matar dashi Wanda agurinsa sune ne mafi girma da tsarki da kauna a rayuwarsa gabaki dayanta...
Yayi baqin ciki da 'dacin Jin wannan sunan Ita wanna matar takedashi..
Bude idanuwan nasa yayi ahankali tareda Dan jinjin Kai Kawai ahankali sbd harga Allah basan ma me akeson yaceba akan lamarin Dan lamarin wannan IDON NERA din yayi Muni da girmama sosai,
Da alama babu ilimin addini kwata kwata a tsakanin familyn IDON NERAn sbd komai lalacewarta Bai Kamata ta lalata rayuwar 'yayanta sbd su din Amanace Allah yabata Dan 'yaya Amana ne ga iyaye..
Koma menene Lamarin yayi munin da bazai iya shigaba Amma dai yabada goyan bayan a dauki matakin gyara da kawar da barnar sbd alummar gaba da Basu taso ba kada barnar tayi yawa.
Tattaunawa sauran alkalan da malamai sukayi aka bawa lauyoyi damar su sanar da lauyoyinta Kiransu gareta a gobe...
AQEEL ASAD yabada uzurin bazai samu zuwaba gaskia so duk yanda sukai yayi Allah yasa hakan shine sanadin shiriyarta da zuriarta.
Fitowa yayi ya shiga motar drivernsa yaja suka bar gurin.
Wani sanyayyan numfashi Mai sanyi ya sake Yana Dan kokarin yakice tinanika akan masu irin wannan rayuwar barnar da sabon ubangiji,
Shi ya rasa wani bangarene Mai mahummanci a rayuwarsa Amma gabaki daya rayuwarsa tayi duhu baya cikin walwala da farin cikin daya Kamata sbd kullum da Abin yake kwana yake tashi tsawon shekaru Amma yakasa sabawa da rayuwa babusu Babu masaniyar halinda sike ciki,
Ganin yakeyi Allah bazai barsaba idan har wadda tayi dawainiyarsa fiyeda tasa uwar,.
ta sadaukar da rayuwartaba ta basa kaunarta da dukkanin rayuwarta,
Taci kashinsa,
Tasha fitsarinsa da guminta,
Amma karshe tana can tana garari a duniya batareda yasan wane Hali ko rayuwar take cikiba alhalin shi Yanada arziki da wadatar da zuriarsa zasuyi rayuwar hutu da wadata har jikokinsa Kila,
Meye amfanin Arzkin idan har wadda ya dage ya zamo wani abin dominta Bata tareda shiΒ hakama Alqawarin daya dauka mata ya tashi a iska,
Menene makomar alqawarinsa akan MARYAMAH wadda ayanzu yasan ta girma batareda tasan Shiba...
ahakan Yaya yake jinsa bare masu aikata laifi