Showing 93001 words to 96000 words out of 155476 words
tayi gabaki daya tareda maidawa kan hanya fuskarta ba sakewa ko kadan.
Gama wayarsa yayi ya ajiye ahankali tareda waiwayowa kadan ya kalli gefenta idanuwansa akan qaramin gyalenta dayake gefe daya kawai.
Jin idanuwansa na yawo ajikinta yasata kasa motsi tana Jin zafi na saukar Mata.,
Maida idanuwansa yayi kan farar fatar wuyanta dake bayyane.
Ahankali ya dauke idonsa akai ya bude Baki a natse yace,
Meye wannan din da Kika yafo??
Shiru tayi Masa batareda ta juyoba ko amsawa.
Sake maimaita tambayarsa yayi Nan ma takuma yimasa shiru.
Maida kallonsa kadan yai kan Ahmed Kai tsaye yace,
"Mu wuce gidan Karatu.
Juyowa tayi ahankali Jin abinda yafada taqi kallon fuskarsa dake sake sakar Mata zafi ahankali itama tace,
"Ku ajiye Ni Zan hau drp na qarasa.
Bakinta da yayi maganar ya kalla itama Jin baice komaiba yasata juyowa ta kalli fuskarsa idanuwansu suka hadu a fuske ta Dan janye nata Idon tana kokarin sake magan ya katseta da cewa,
"Meye wannan ajikinki nace??
Jikin nata ta kalla a sace taga gyalenta yake kalla dan Haka saita qi cewa komai.
Ahmed tuni ya kama hanyar gidan Karatu ganin baida niyar sake magana shima saita sake juyowa ta kallesa tana son magana Amma izzarta na hanata Dan Haka tai shiru tareda dauke kanta itama.
Babban gate din gidan Ahmed shige da motar bayan an wangale musu kofar gate din.
Danne zuciyarta tayi yaqi juyowa ta kallesa
Dan jiran takeyi ya fita motar Ahmed ya wuce da ita gida.
Ahmed na parking ya bude motar ya fice Dan Basu guri.
Fitar Ahmed yasata juyowa ta kalli gaban motar zatayi magana ya zuba Mata fararen idanuwansa takasa cewa komai cikin mamakin abinda ya tsaya jira a motar ta Dan kalli gefensa zatayi magana ya katseta ta hanyar bude motar ya fice ba tsammani taji ya bude ta gefenda take cikin kulawa.
Qin juyowa tayi ta kalli kofarma gabaki daya saita fiddo wayarta ta saka Kiran Ahmed Wanda daga shi har securities duka suka bace bat daga harabar gidan suka koma daga waje.
Wayar Ahmed na ringing ya daga ko magana baiyiba AQEEL ASAD ya saka hannuwansa masu tsayi ya karbe wayar daga hannunta cikin nutsuwa tareda sunkuyawa ya dauketa gabaki daya ya nufi ciki ita Yana kallon fuskarta dake bayyanarda fushi da bacin Rai me tsanani.
Bai ajiyeta koinaba sai tsakiyar master bedroom dinsa dake gidan
Yana ajiyeta ta fizge jikinta a zafafe ta nufi kofa ko Isa batayiba Yakuma dawo da ita ta baya
Duk yanda yake kaucewa haduwar jikinsa da nata saida suka hadu sosai ta bayanta ya matseta cikin jikinsa ahankali yana sauraron yanda take kokawar kwacewa.
Fuskarsa yakai wuyanta ya shaqi qamshi data tashi jikinta Mai sanyi na
Boadicea kafin yakai bakinsa kunnenta ahankali ya furta,
Menene wannan din Kika yafa??
Cak ta tsaya daga mutsu mutsun datakeyi sbd numfashin daya sakar Mata Mai zafi a kunne da wuyanta
Yasa zafi sauko Mata tako Ina..
Bai janye bakin nasa daga kunnentaba yasake cewa,
"Uhumm Ina jiranki??
Rintse Ido tayi ta bude qamshinsa da numfashinsa da jikinsa dayake zagaye da nata yasata Jin numfashinta Kamar Yana toshewa ahankali ta zare jikinta tareda matsawa gaba batareda ta bari ta juyoba.
Qarasowa yayi ya Kama hannunta ya dawo da ita kan lafiyayyar sofan sake dakin nasa ya zauna tareda kokarin zaunar da ita Amma ta kafe taqi zaunawar...
Tashi yayi tsaye gabanta kirjinsa na gap da gugar nata ta daga qafa zatayi baya yakai hannunsa ya yangota ahankali ta fado jikinsa ya riqeta da kyau ba tareda ya matsetaba Kamar Wanda bayason takura qashinta.
Haduwarsu hakan yasa numfashinta sake toshewa taqi yarda ta dago Dan batason kallon fuskarsa.
Idanuwansa ya zuba mata Yana Jin gyalen nata data fita dashi Yana yankar zuciyarsa Amma taurin kanta da kafiyarta ya hanata bude Baki tayi magana.
Wuyanta yake kalla zuwa fuskarta dataki kallonsa.
Hannunsa yakai ahankali zai taba gyalen nata tayi saurin dagowa suka hada ido.
Bazata iya jure kallonsa ba Dan Haka ta motsa zata qwace jikinta kirjinsu Yakuma Mannuwa Dana juna..
Ahankali ya janyeta daga jikin nasa da Kansa yana dauke kallonsa daga kanta.
Yana sakinta ta bude kofar bedroom din ta fice fuskarta na bayyanarda bacin Rai da fushi Amma zuciyarta bugawa takeyi da qarfi sbd tsoro da mamakin abinda ya faru din.
Mota ta nufa Kai tsaye ta Shiga ta zauna sai alokacin tasamu numfashinta yafara warwarewa.
Saida tayi mintina hudu a motar kafin ya fito a kame cikin nutsuwa kwarjininsa na qara bayyana Kamar bashine yayi abinda yayi aciki dinba.
Motar yanufa Kai tsaye yashiga daga ita harshi Babu Wanda ya kalli juna saidai qamshinsa datake ji maqale jikinta shima akwai nata qamshin daya mannewa kayansa.
Ahmed yakira a waya da sauri ya taho yashiga motar ya tada suka fice.
Kai tsaye gidan IDON NERA suka nufa akai Amal din kafin ya wuce gidansa Dan dawowarsa kenan daga airport yakira Ahmed din yazo ya daukesa malam Rabiu Kuma ya wuce Kai Al-Amin da gida.
****Haj Maryamah da umma suna Isa gidan IDON NERA Kai tsaye securities suka qi bude musu gate Saida suka sanar da Haj Zainab wadda tayi shiru da mamakin Jin su waye din.
Numfashi ta sauke kafin tace abari su shigo din
Daman tasan zaayi hakan
Sunma Dade Basu zo ba Dan Bata dauka zasuyi shiru har tsawon lokacinba.
Parking sukayi a harabar gidan
Bilkees ce ta tuqo su Kuma bada mufeeda sukazo ba yau din.
Itama haj Zainab tana kashe wayarta daga gate din ta miqe ta sauko kasa Dan Jin meya kawosu gidan Dan idanma akan auren AQEEL ne kofa zata nuna musu su can suyi dashi
Babu Wanda zai kasheta lokacinta baiyiba tana zaune lafiya cikin iyalinta.
Harta sauko Basu qaraso cikiba Dan Haka ta nufi kofa zata taresu tin acan harabar suyi acan saigashi sun shigo Bilkees ce agaba tana yiwa koina gidan kallon qazanta da qyama.
Haj Maryamah da umma ne a baya
wannan karon fuskokinsu Babu alamar sauki da gaske sukeson akawo karshen komai.
Batayi wahalar cewa su zaunaba da tasan ba zaman zsuyib ba Kai tsaye tace,
Lafiya dai inace ba???
Itama Haj Maryamah Bata tsaya batawa kanta lokaciba sbd ta gaji Kai tsaye tace,
"Kin shayar da AQEEL nononki nakeson ji daga bakinki.......
Wani kallo Haj Zainab ta dago tabi Haj Maryamah din dashi cikeda matsanancin mamakin dayafi na koyaushe,
Bata taba tunanin tsanar dasuke Mata takaisu ga rasa ilimin addinin dasuke dashiba.
Siddi data biyo mommyn tana bayanta ta fito bayanta itama cikeda mamaki tace,
"Nono kuma?
Kunsa me kuke fada kuwa?
Shayarda Shi na nufin aurensu ya haramta kenan fa??.....
Katseta Haj Maryamah tayi cikin fushi Mai tsanani da bacin Rai tace,
"Ki ringa tsayar da Yayanki inda Ina magana sbd tarbiyarsu daban take data yayan da muka sani,
Dake nake magana
Amsa Kuma nakeso idan ba hakanba kotu ce zatayimun maganin duk wani mummunan aikinki akan Dana tun Yana qanqaninsa.......
Cikin fushin dayafi na Haj Maryamah din Zainab ta katseta da cewa,
"Indai wannan shine halin yayan da kike magana akai to abarmin yayana ayanda suke din haka sbd jahilci da kaucewa Allah kawai nake hangowa a wannan rayuwar da kike fada..
Katseta itama umma tayi da cewa,
"Amsa aka tambaya ba rayuwar 'yayanki ba Zainab Idon Nera,
Kin shayar da AQEEL nononki ne Kuma sbd son abun duniya Kika Bari ya auri 'yarki da sukasha nono daya
Dan Haka auren ya haramta Babu Wani sauran Bata lokaci a warwaresa kawai.......
"Meyake faruwa Anan?" Sukaji anfada daga bayansu
Dukkaninsu suka juyo gabaki dayansu suna kallonsa.
Ganinsa tareda Amal wadda itama kallo daya tayi musu a ranta dayake baci da baqin cikin ganinsu tace,
"Meyasa duk haukan tsoffin Nan ya motsa anan suke zuwa su sauketa??ยฟ
Bilkees da ganin AQEEL ASAD dinta da Amal din tare yasata sakin Baki zuciyarta na tsalle bakinta na neman bushewa sbd saninsu baya gari tsawon kwanakin to da ita yatafi kokuma Daman baiyi tafiyar bane Yana Nan ya tare???..
Cabdijam" suka fada dukkaninsu atare su ukun
Da Haj Maryamah da umma da Bilkees wadda tafara Jin zafi na shigota ta ko Ina.
Da mamakin ganinsu a gidan shima yasake maimaita tambayarsa fuskarsa akan mahaifiyarsa wadda take kallonsa cikin fushi.
A natse kamewarsa na tsananta ya sake kallonsu kafin ya kalli Mami wadda tagama girgiza da haukarsu ta wannan karon yace,
"Meyake faruwa Anan??....
Zuciyar Bilkees data gama konewa da baqin ciki da takaici babu shakka ko tauna zancen sbd gwara yaji yasan aurensa ya haramta da Amal
Tasan ba lallai sunsha nononba tunanin su umman ne kawai Amma gwara ace sunsha din auren ya watse kowa ya huta...
Kai tsaye tace,
"Maminka ta shayar dakai kana yaro Dan Haka aurenka da......
Wani irin kallon daya juya yayi matane yasa kalmomin bakinta watsewa suna gagara haduwa sbd duk abinda takeyi duk haukarka kallonsa daban ne..
Haj Maryamah dataga Bilkees din ta rude saita qarasa zancen da cewa,
"Aurenka ya haramta anan saika sakar Mata 'yarta....
Ita kanta Amal wani matsanancin mamaki tashiga Jin zancen gabanta yayi wani irin faduwa ta juya ahankali ta kalli mommynta wadda shima ita ya zubawa fararen idanuwansa dasuka sauya take yana jiran maganarta wadda kalma daya zata bude Baki tayi ya fahimci gaskiyar zancen.
Duk inda zafi da ciwon zancen yakai yayiwa Haj Zainab din ciwa mai tsananin gaske,
Me suke nufi?
A wancan lokacin tana budurwa me suke nufi da Tasha wani abin ta shayar dashi??
Ashe qiyayyar bamai rahama bace,
Wani Abu Mai ciwo da zafi ta hadiye sbd ta fahimci haqiqa sbd kawai su haramta aurensa da Amal a warware auren suka bullo da hakan Amma ta tabbatarda sunsan Bata shayar dashiba.
Idan Akan AQEEL ne suke Mata wanna qiyayyar to tagaji da lallabasu
Duk me mutuwa ya mutu Mai Rabin wahala Kuma saiya shirya...
AQEEL dake kallonta Yana jiran amsarta ta kalla kafin ta maida kallonta kansu umman da duk suka zuba Mata ido suna jiran tayi zuciya tace eh hakan ne sbd auren ya qare duk su huta,
Abinda zata fada sunsan shine AQEEL zai yarda dashi Dan Haka gabaki daya palon idanuwan kowa na kanta hankali tashe suke jira abinda zata fada Wanda yake duka zuciyar duk Wanda yake gurin musamman Amal data kasa motsawa daga inda take.
##MAMUH#
#HOT LOVE/AQEEL ASAD
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*๐ฅ
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*๐ฅ
Billyn Abdul
*IDON NERA*๐ฅ
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*๐ฅ
Safiya huguma
*KI KULANI*๐ฅ
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
๐ณ๐ช๐ณ๐ช๐ณ๐ช๐ณ๐ช๐ณ๐ช๐ณ๐ช๐ณ๐ช
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*๐ฅ*_Arewabooks@Mamuhgee_*
47
AQEEL ta kawai ta iya kalla cikin kaunarsa da Babu Wanda ya Isa ya cire Mata hakan duk mugun sharri ko qazantar dasu umman zaku bullo Mata dashi,
Maida kallonta tayi kan Haj Maryamah ta zuba Mata su tana kallon cikin idonta ta bude Baki tace,
"AQEEL bantaba shayar dakaiba,
Bantaba tunanin shayar da kaiba Koda Ina shayarwa awancan lokacin wallahi tallahi bazan taba shayar dakaiba sbd mafarkin irin wannan ranar da zaka iya zama jinana.
Dawo da kallonta tayi Kansa tace,
"Aurenka da Amal halastaccen Aure ne Babu ta inda kuka Sha nono daya duk Wanda ya fada ya fadane sbd son Rai da alamun samun matsalar qwaqwalwa dasuke bayyana ataredashi,
Auren Amal yariga ya dauru duk Wanda yakeda matsala da hakan zai iya faduwa ya mutu sbd a yanzu Kam Babu Wanda ya Isa ya sheganta auren Nan,
Kamar yanda kukeson rabuwar auren Haka nakeso Amma daga yau wallahi koshi Bai Isa ya saki wannan aurenba idan har na Isa inada iko dashi kaman yanda kuke fada zamu gani,
Wanda ya shirya ganin 'yayan AQEEL da 'yar karuwa saiya riqe lafiyarsa Wanda Bai shiryaba shirye nake da zuwa zaman makokinsa..
A zafafe umma ta bude Baki zatayi magana ya daga Mata hannu bacin Ransa da baya bayyana ko kadan
Yau din ya bayyana
Ran nasa a bace Amma cikin nutsuwa yace,
"Me zakice Bayan duka wainna abubuwan da kike jagoranta anayi wainda hankali da mutunci baya dauka.,
Kan mahaifiyarsa ya maida kallonsa itama shi take kallo cikin bacin rai da baqin cikin Yana musu fada gaban Zainab da 'yarta.
"Meye Haka kukeyi umma?
Meya amfanin ilimin da baa aiki dashi?
Kunce kune masu ilimin da mutuncin anan to me kukeyi umma?
Umma idan tsufa ya juyar Mata da hankali ke umma lafiyanki kalau Meye duka amfanin wannan??.....
Waye yafara kawo zancen shayarwar Nan??
Shiru sukayi kowa na jiran amsar da zaa fada,
Cikin zafi Yakuma cewa,
"Waye ya kawo maganar??
Umman Cameroon da bazata yarda yaji sune suka fara feso zancenba sbd zasu qarasa rasashine
Kuma Daman tana qule da lamarin Bilkees Dan Haka Kai tsaye tana matse fuska da baqin ciki tace,
"Matarka gatanan itace tace kafada Mata......
Wani mummunan tashin hankalin ba zata ne ya bugi Bilkees a rikice ta juyo gurin umman tana cewa,
"Laila ha illallahu,
Qalu innalillahi
Me wannan tsohuwar kike fada???
Wallahi qarya takemun......
Wani Abu Mai nauyi ya hadiye a kirjinsa kafin ya zubawa Bilkees fararen idanuwansa dasuka sauya gabaki daya lokaci daya,
Kasa qarasa zancenta tayi sbd tsabar rudewa da tashin hankali Mai tsananin gaske tana tsinewa umma da mugun tsufanta.
Baicewa Bilkees din komaiba ya juya ya kalli mahaifiyarsa yace,
Kingani daga umman har wannan din basuda cikakken hankali???
Meyasa Kika zabi biyewa...
Kuka Mai ciwo da qarfi umman Cameroon ta fashe dashi tana cewa,
"To daga qarshe dai gashinan AQEEL ya zageni yaci mutuncina,
Zainab burinki da buqatarki ta biya,
Allah ya Isa tsakanina dake da zuriarki,
Kin cuci halaccin da mukai Miki muka taimakeki alokacinda bakida kowa,
Allah ya Isa da wannan......
Cikin zafi da boye fushinsa ya dakatar da ita tareda Kama hannun mahaifiyarsa ya juya da ita.
Bilkees cikin tsananin mutuwa da tsoro ta biyo bayansa zatayi magana ya daka Mata wata irin tsawar datasata dakatawa tana kallonsa cikin firgici da tsoro.
Wucew yayi ya fice da mahaifiyarsa yabarsu umma na kuka sosai
Bilkees na hawayen tashin hankali.
Da gudu Bilkees tabi bayansa qafafunta na rawa saidai kafin ta Isa yabar gidan a motarsa da Haj Maryamah.
Motar da suka zo da itace ta nufa da sauri ta shiga hannuwanta da duka qafafunta na wata irin rawa tana kokarin Shiga umma ta fito ta nufo motar saidai kafin ta bude Bilkees cikin ficewar hayyaci tace,
"Aurena kikason kashewa umma
Me nayi Miki?
Kokuwa Nima angama Dani kamar yanda aka Gama da Zainab dinne?
Wallahi umma aurena ya mutu da AQEEL saina tabbatarda Bai rabu da Amal dinba sbd ku tabbata zuria daya dasu din da bakwa so.
Nude motarta tayi ta fada tareda ja da gudu tabar umman a tsaye tana sake shiga tashin hankali da mamakin wannan shegiyar Diya Bilkees..
Cikin fushi tace,
Wlh ko Bai sakekiba akan wannan saina saka ya koreki daga gidan
Wannan gwara ma karuwan da ke.
Barinta Bilkees tayi gidan ta tafiyarta
Rasa inda ta nufa tayi Dole ta nufi gate tana share hawayen baqin ciki da takaicin hada zuria da Bilkees din itama.
Uncle Lulu ne yadawo zai shigo gate yaga fitowarta tana share hawaye Kamar zai wuce sai Kuma dai ya tsaya yace ta shigo motar.
Batada zabi tinda ko waya babu ahannunta Dole tashiga tana matse fuska babu Wanda yayi magana acikinsu.
Juyawa yayi yakaita har gate din gidan AQEEL ASAD din tana fita Bai tsaya komaiba ya juya Kamar yanda itama Bata tsaya cewa komai dinba tayi ciki jininta na tafarfasa akan Bilkees.
Koda ta shigo palon Haj Maryamah ranta a bace tana hawayen abinda Bilkees Tai Mata sai ta taddasu dukkaninsu a tsaye cirko cirko Fuskar AQEEL Jin tayi ja kasacenwarsa fari sai bacin Rai da fushinsa yasa Fuskar yin jajir batareda yace komaiba.
Kallon Bilkees data baro umma sukeyi shida Haj Maryamah data rasa Abu fada akan Bilkees dinma.
Shigowar umma ta fashe da kuka tana cewa,
Yau zata kwashe kayanta tabar gidan gwara Takoma Cameroon dinta tunda tozarcin da Bilkees tayi Mata ya wuce tinani.
Bilkees datakejin Kamar mutuwa ta samu umman a lokacin tayi kowa ya huta kasa magana tayi daga ita har Haj Maryamah sbd fushin da bacin ran AQEEL wani Abu ne da Basu taba ganiba irin hakan,
Fushi ne sosai a ransa dayake kokarin controlling sbd kaucewa hukunci cikin fushi.
Dakatar da umma yai batareda ya iya magana itama ganin yanayinsa yasata yin shirun suna sauraronsa kamar shine uban nasu,
A zahiri Basu taba ganin bacin Ransa Haka ba shiyasa suka shiga shakkarsa Musamman Bilkees datasan ta taqare kila ko darajar mufeeda tasani bazata ciba tunda basune suka haifetaba bare taci darajar haihuwa.
Haj Maryamah da umma ya kalla cikin nutsuwa da kakkaifan sautinsa dake nuni da magana daya yace,
Maganar aurena da alaqata da Mami daga yanzu na zare kowa aciki,
Daga ranarda wani yasake shiga maganar Zan yanke alaqata dashi ko wanene bayan mahaifiyata,
Itace ta haifeni itace takeda iko Dani Amma ko ita nata ikon baikai na Allah ba,
Allah ne yayi Amal matatace Babu Wani Wanda ya Isa ya aibata ko yanke auren idan ba Allah daya nufa ba,
Dan Haka duk Wanda yasake yiwa lamarin Kai tsaye ko waye daga ranar na yankesa daga cikin ahalina.
Gurin Bilkees ya juyo yayi Mata wani irin kallo dayake bayyanarda ficewarta a ransa kwata kwata Amma zai sake Bata wata damar sbd kaucewa aiki cikin fushi.
Wannan maganar na kasheta anan
Ko mufeeda kartaji abinda yafaru ayau din,
Idan wannan maganar ta fita ta bangarenki ki shiryawa kanki hukuncin da Baki taba tsammaninsaba.
Ummansa ya kalla wadda tai zuru tana kallonsa cikin mamakin Wai zai yanke alaqa dasu aka auren 'yar Zainab...
"Gidan Mami ma na sokewa kowa zuwansa daga yau din idan kunyi hakurin abinda kukeson fada 'yarta na zuwa idan tazo saiku ringa fada Mata tana isar muku da sakon.
Juyawa yayi ya fice yabarsu sake da bakuna cikin tsananin sanyin jiki da mamaki da tashin hankali,
Ya harda baqar magana AQEEL yake fada musu akan zuwa gidan Zainab,
Yau sune AQEEL yake gindayawa sharudda da iyaka duk akan wannan auren na zuriar Zainab.
Bilkees da zuciyarta ta dauki wani masifaffen nauyi akan abinda AQEEL yau yafada mata,
Kamar fa barazana ce yayi Mata akan aurenta?
Wainnan tsofin nasa tasan tunda suna tsoron rasashi zasu iya yin shiru din dayace akan auren
Shikenan ita ancuceta ake nufi anmata kishiya da wadda tasan matsayinta a ransa daban ne.
Wallahi bazata yardaba
Ai sai duniya tasan da zancen maganar Shan nono daya dinnan
Basai ansan itace tayi zancenba tukuna zai iya daukan matakinยฟ
Mamin tasa ko su Amal din zata maqalawa fidda zancen suje can suyita zuba balai daganan auren ya lalace kowa ya huta.
A fusace ta miqe ta fice itama tabar su haj Maryamah cikin rasa abinyi da abin fada.
Tana Isa sashensu ta tadda mufeeda tadawo school itama Dan Haka sukai cikin daki suka rufe ta fadawa mufeedan komai wadda itama tayi naam dasu fidda zancen idan yaso ayita aibata auren Harma asamu masu shiga cikin maganar a Bata auren gabaki daya.
Da wannan shawarar sukai tsit abinsu suna dubarun yanda lamarin nasu zai kasance.
Haj Maryamah da umma kuwa Suma Dole tsit din sukayi Basu sake kowane yunqurin