Showing 69001 words to 72000 words out of 155476 words

Chapter 24 - IDON NAIRA COMPLETE HAUSA NOVEL

MAMUGEE   

01 Jan 2026

390

insha Allah.


***Amal na Isa office din mommynta datake gudanar da harkokin businesses dinta apart from harkanta ta Daban da ake kira da karuwancin.

Ajiye jaridar tayi Kai tsaye gaban mommyn tana kallonta cikin Bata rai tace,

Mommy kina ganin alaqarki da wannan AQEEL ASAD din bazai kawo baci Rai da ninkin bacin sunaba akanki?

Mommy koma menene alaqarki dashi gabaki daya hakan Bai kwantamunba,
Shi kansa Bai kwantamunba,

Meyasa Zaki ringa tattala duk wani zancenza saikace shi din yafi sauran abokanan kasuwancinki,

Mommy idan akwai wani alaqar daba business ba a tsakaninku inason sani sbd Shi kansa dabiarsa akanki tayi hannun Riga kwata kwata da sauran kowace dabiar.

Mommy......

Katse Haj Zainab tayi cikin kulawa da kwantar Mata da hankali tace,

"Amal breath please,
Wannan rumours da bacin sunan ba yanzu aka fara ba,mun Saba,.ba komai bane,
Banajin komai akan hakan,
Damuwata dayace akaro nafarko akan irin wannan iskancin na Yan jarida shine sunan AQEEL ASAD dayake ciki,

Bantaba musantawa ko tankawa akan ire iren hakan sbd bana buqatan yiwa kowa bayanin halinda rayuwata take ciki Amma bazan iya Bari su Bata sunan AQEEL ba,

AQEEL ASAD shine Wanda raina zaiyi matukar baci idan suka lalata sunansa akan nawa sunan...

Mamakine ya sake shigar AMAL tana kallonta tace,

"Mommy?kinji abinda kike fada kuwa?
Mutuncinsa yafi naki ne?
Idanma sunansa ya baci shine ya kawo Kansa idan na tina,

Mommy please ki Dena fadan hakan kina sake sakamun zafinsa araina,
Tayaya shi din yasamu wannan mahummancin a gurinki?

Yanda ran Amal din yake a cakude yasa mommyn kokarin danne nata bacin ran akan lamarin Amma bawai Dan nata sunanba sai Dan mutuncin AQEEL dinta dakuma uwa uba babbar rigimar da hakan zata bullo sbd wanan jaridar zata tabbatarwa da duk inda uwarsa da kakarsa suke cewan itada AQEEL sun dawo rayuwar juna kenan,
Abinda Kuma ta guda din kenan sbd riqo da alqawarinta na cewan ta yanke duka wata alaqa dake tsakaninta dasu har abada Kuma tana Nan akan bakanta,

Idan Kuma suna Nan a yanda ta sansu to tabbas aduk inda suke zasu nemeta su sameta sbd isarda sakon zuciyarsu kaman Yanda suka Saba...
Hakan na na nufin Amal da siddi zasusan su din su wanene,.abinda Basu taba tambaya daga garetaba bakuma su damu da tambayarba Koda su din shegu ne Basu damuba tunda uwar data haifesu din tana taredasu kamar yayan sunna.

Shirunta tareda zurfi cikin tinani yasa Amal zuba Mata fararen idanuwanta tana kallonta cikin mamaki,

Amma koma menene batajin zata dauki cin fuska da sabon bacin suna ga mahaifiyarta sbd itace duniyarta gabaki daya.


*****Awar Haj Maryamah hudu a asibitin BP dinta ya dawo daidai saidai zuciyarta takasa Dena bugawa da sauri bp dinma tasan ba jimawa zaiyiba zai ringa hawane Yana sauka sbd ita kadai tasan yanda zuciyarta take bugawa tareda kasa Jan numfashin nutsuwa.

Daga ita harsu Bilkees Babu Wanda yake cikakken hayyacinsa,

Ita Bilkees da mufeeda hoto ne kawai a kawo umma asibitin Dan kusan Bilkees din tafi kowa ficewa hayyacinta a tsaye kawai take Amma Sam Bata gane komai sai an maimaita Mata abinda aka fada din.,

Kallo daya Haj Maryamah tayiwa AQEEL ASAD din alokacinda ya shigo ta fahimci Babu wata magana dazai iya saurara akan Zainab,

Kamewar da yayiwa fuskarsa ce ta tabbatar Mata da abinda taketa qin yarda dinne dai ya tabbata wato Zainab dai tadawo rayuwarsa Kuma yana sane da abinda ya sakata cikin wanna halin kenan shiyasa yaqi Bata fuskar yin maganar....

Innalillahi wainna ilayhi rajiun,

Wace sabuwar masifar ce wannan,

A bayan ma da Zainab takeda tsarki Bata barta da 'danta ba Dan haka babu ta yanda zata bari 'danta ya sake ko kallon inda qazantarsu takeba bare ya kwaso najasarsu,

Bazata taba yarda wannan karon 'danta Mai tsarki tsarkakakke ya kusanci inda sukeba,

Kome zatai zatayi Amma wlh Zainab bazata dawo rayuwar 'dantaba itada 'yarta,
Wannan karon kome na dukiyarta zata watsar akan 'danta ya tsaya gurinta bazai sake kallon zainab bama bare wata 'yarta wadda itama take baqin cikin fadar sunanta da aka sakawa 'yar gashinan ta qare a rayuwa irinta uwarta,

Sake kallon AQEEL din tayi idanuwanta da zuciyarta na sake daukan zafi da ciwo,

A natse cikin kamewa yagama tabbatarda Babu wata matsala zasu iya tafiya da umman gida.

Bilkees data gap da faduwa sbd tiririn da zuciyarta take ciki itada mufeeda,

Bata tafi gidaba itama saida aka duba bp dinta daya kusan haura 200 daqyar akai Mata controlling dinsa tayo gida a gigice saidai cikin rashin saa tana isowa akace AQEEL din yabi jirgin dare ya wuce Abuja.

Cikin tashin hankali ta kalli umma wadda itace ta matsa Masa akan ya tafi din taji sauki sbd tanada buqatan barinsa a garin na kwana biyu Dan tabbatarda abinda tasani,

Zainab tazama masifar rayuwarsu itada ummanta da 'danta,

Tayaya zata fuskanci wannan tashin hankalin dayake dawowa musu???

Bilkees data kasa gane kan umman ta qaraso gabanta hankali baa kwanceba tana jiran Jin ta bakin umman tukuna tasan ta inda zata fara da lamarin.

"Idon Nera" duk sunan ya fado a ransu sai anrasa tsakanin zuciyar haj Maryamah data Balkees wacce tafi girgiza dashiga mummunan yanayi,

Tashin hankali da rikicewar Balkees a zahirin bayyane yake ga duk Wanda ya ganta yasan tayi kololuwar fita hayyaci da tsananin kishi da tashin hankali akan lamarin tun lokacinda idonta ya kyallo jaridar,

Ga AQEEL ASAD din yaqi tanka kalma ko daya akan lamarin bare a bude zancen komai Susan matsayarsa saima kaman harda bayason zancen yasashi tafiya a Daren,

Idan AQEEL ASAD baiyi niyar magana akan abu ba Sam ko fuskar a tayarda zancen baya bayarwa Amma wannan ma yafi kowanne yanayinΒ  qin bada damar saima wata irin tsananin rashin bada Dama ko fuskar da zatai tashin hankali da aibata Idon nera,

Haj Maryamah kuwa sake juya zancen takeyi a ce Zainab idon Nera, qanwar mahaifiyarsa wadda itace yakewa kallon uwa sbd itace tasan wahala da dawainiya dashi tun Yana cikin mahaifiyarsa take dawainiya da wahala dasu harya fito duniya ta renesa tamkar itace ta haifesa haryayi girman dasuka rabu,

Itace macen da a duniyarsa mahaifiyarsa data haifesace kawai tafita haqqi akansa Amma shaquwa da kaunar zahirima tafi girma a tsakaninsa da ita,
ta sadaukar da rayuwarta da kuruciyarta gabaki daya gurin kulawa dashi,

babban abin firgicin shine 'yarta daya a duniya itace wadda yakejin kamar yayi failing malaminsa akan rashinta,

Ko a cikin mafarki ne kunya,baqin ciki, takaici da qyamar fadan tasan Zainab ma zatayi bare a zahiri,

Duka wannan bayanin idan duniya taji mutuncin AQEEL dintane zai zube,
Tayaya zata Bari asan alaqarsa da Zainab Idon Nera,
Bazata yardaba.

Kwanan baqin ciki da zullumin tunani sukai aranar wadda sukaga safiya daqyar.


****
Haj Maryam kusan tafi Balkees shiga qunci da damuwa tareda baqin cikin bayyanuwar wannan Al'amarin sbd kaman 'dacin zuciyarta tun na quruciya ne yake Shirin dawowa idan bata datse wannan alqar tasuba da wuri,

Idanma 'yar Zainab dince IDON NERA duk baqin cikin daya ne sbd girman Zainab a zuciyan aqeel ganin takeyi ya wuce nata itada ta haifesa saidai batajin har abada zata iya karban Zainab da itace qurjin zuciyarta,

Aqeel tsarkakakke ne itakuma yanzu najaza ce abar qyama daga ita har 'yarta....
Babu ya yanda AQEEL zai iya ko kallon Zainab din bare dawo da matsayinta na uwa a zuciyarsa matuqar itace IDON NERA din
Koda 'yarta ce IDON NERA AQEEL saiya qyamacesu..

Qarin abin kunya da baqin cikin da zubewar mutunci da darajarsu zai fara ne daga lokacinda duniya tasan ita din yayar Idon nera dince,
Jininsu daya,
Mutum daya ya haifesu..

Haka zalika girman MUHAMMAD AQEEL ASADULLAH a duniya zai rangwanta a idon mutane idan sukaji Karuwar da kowa yasani IDON NERA qanwar mahaifiyarsa ce,
Jininsa ce,
Marikiqiyarsa ce wadda yake Kira da uwa.

Babban tashin hankali da tsoronta yace zaiyi yunqurin dawo da Zainab rayuwarsu wadda AMAL IDON NERA itakuma itace babbar tashin hankali da masifar datake girgiza bilkees da duniyarta gabaki daya sbd daga lokacinda tasamu damar ganin hotunan IDON NERAs din a Media kiris ya hanata samun shanyewar rabin jiki badan mufeeda tayi gaggawar taimaka mataba.


Abinda ya sumar da Balkees shine bayan gama qarewa hotunan haj IDON NERA kallo shine Ido biyu da hoton AMAL Idon Nera wadda duniya ta shedar da mutuwar so datakewa mahaifiyarta haj Zainab Idon Nera.

Ganin Amal yasa bilkees daga kwanciyar hankalin gidan gabaki daya akan lamarin sbd son sanin asalin meke faruwa...

Haka zalika batajin ko gida jaridar daya wallafa wannan jaridar zata qyalesu mataki zata dauka tako Ina sbd ko wannan qazamtaccen zancen Adena yadawa bare wani abin ya biyo baya,

Dan Koda zata rasa komai da kowa a duniyarta bazata taba yarda asake hada sunan tsarkakken sunan mijintaba da sunan IDON NERA Koda uwar Koda 'yar.
##MAMUH#

ZAFAFA BIYAR 2023

*RUMBUN K'AYA*πŸ”₯

*DAUDAR GORA*πŸ”₯

*IDON NERA*πŸ”₯

*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯

*KI KULANI*πŸ”₯

*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊

*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*

*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*

*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️

*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*

*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*

*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!**_Arewabooke@Mamuhgee_*
34
Wayar umma Haj Maryamah ta Kira
Saida takusa katsewa umman ta dauka,

Wani irin kukan da Bata taba fashewa dashiba ta fashewa umman dashi zuciyarta na tafarfasar da kunci da bacin Rai harma da baqin ciki.,

Zaune umma ta tashi daga kwacen datake akan doguwar kujerar dakinta ta hutawa hankalinta na tashi Dan Bata taba jin kukan Maryamah dinta ba tun bayan rasuwar Mijinta na farko,
Ko mijita na biyun daya rasu batai wani kukaba saidai hawaye Amma yau din lamari ya girmama,

Maryamah??
Lafiya?
Waye ya rasu?
Ina AQEEL lafiyansa kalau kuwa?
Ya matarsa da 'yarsa Suma lfy dai??
Meyene ya faru gayamun kafin hawan jinina yayi sama.

Kasa magana Haj Maryamah tayi sabd takasa riqe kukanta akan Zainab datake riqewa shekaru,
Yau tasamu abinda yake makoshinta akanta ya fashe shiyasa kukan yakasa tsayuwa.

Kukane takeyi dayake fitowa can qasan zuciyarta da ranta,

Umma daga zaunen qarasa miqewa tsaye tayi tana sake ambatar sunan maryamah din hankalinta na tashi.

Saida tasamu ta danne zuciyarta ta cusawa kanta dauriya da taurin Rai kafin ta share hawatenta da tissue ta sauke ajiyar zuciya ahankali tukuna ta bude baki tareda Dan gyara muryanta datayi nauyi takoma daidai
ranta na quna tace,

"Umma Zainab tadawo rayuwar AQEEL,
AQEEL yaga Zainab da 'yarta,
Zasu Bata suna da mutuncinsa a Idon duniya,
Zainab magajiyan k.....umma Ni bama Zan iya fadan qazantaccen sunan da bakina Mai tsafta ba..

Umma AQEEL zai koma gurinta ya sake juyamun baya,

Me nayiwa Zainab data zabi shiga tsakaninsa da rabani da 'dana daya danake dashi a duniya??

Umma wannan karon wlh bazan iya daukaba......

Zama umma tayi a hankali tana shiga nata mamaki da tashin hankalin itama sbd abune da Bata taba kawo tunanin shine zaa fada ba wato dawowar Zainab rayuwarsu,

Tun tana qaramar karuwarta sun samu sun yakiceta sun rabu da ita rayuwarsu ta huta sai yanzu zata dawo rayuwar 'dansu tana shahararriyar karuwa,
Me take nufi da hakan?

Rayuwar ta bare Mata ne kokuwa?

Cin mutuncinsu da barnar suna zatai musu kome?

Baqin ciki da damuwa zata dawo musu dashi bayan sun samu nutsuwa da salama tareda dangana ya shiga AQEEL ASAD baya rashinta shine yanzu tunda ya zama babban mutum Mai fada aji zata bullo Dan tozartasu da kawo musu sabuwar masifa...

Wani 'daci ta hadiye a makoshinta bayan Haj Maryamah ta zayyana Mata komai na bayyanar Zainab harma da yarta..

IDON NERA??" itama ta mamaita sunan a bakinta tana Jin ranta na tsananta soyuwa da bacin Rai da tashin hankali...

Tashin hankali dasuke gujewa na tsayuwar AQEEL akan zance daya ne idan ya tsaya ya tsaya kenan baya magana biyu,

Idan har yace ya yarda da zainab da rayuwar karuwancinta Babu me sauya Masa hakan,

Kafin ya yarda da hakan sukuma bazasu taba yarda tadawo rayuwar tasaba tinda ba ita Maryamah ta haifawa 'dan ba..

Cikin damuwa da takaici umma tace,

"Maryamah ba kuka Zaki tsaya kiyiba tufkar zakiyiwa hanci tun lamarin Bai fita hannuba,
Karki tsaya sanyar Dama zaasan ita din jininki ce Dan kuwa Babu wani sauran mutunci da girman da zakuyi a Idon mutane idan akaji kinma Santa bare Kun hada uba daya tunda ita nata sunan qaurarre ne,

Karki jira komai ki nema inda take Ina hanya zuwa gobe inshallah Zan biyo jirgi
Kafin AQEEL din yadawo daga tafiyarsa zamu tabbatarda tabar rayuwarsa wannan karon har abada tunda ba fin karfinmu taiba,

Maza ki Dena yiwa kowa kuka,.
AQEEL Dan ki Babu Wanda ya haifar Miki shi,
Kece Kika haifesa kece kikeda iko da Isa akansa fiyeda kowa,

Tasan hakan tunda itama tanada 'yayan ta Haifa da Yar halak data banza dan Haka tasan me ake nufi da 'da yanzu.

Sake danne zafin zuciyarta Haj Maryamah tayi tana cewa,

"Umma ko Baki fadaba walh bazan taba barin 'dana ya kusanci rayuwar Zainab data haramtacciyar zuriarta ba kome zaayi bazan yardaba Koda hakan na nufin AQEEL din zai zabi daya ko Ni ko zainab din.

Zuciyoyinsu Babu Dadi Sam sai bacin rai da tashin hankali suka Gama wayar da Shirin isowar umman a gobe wadda takejin kamar tayiwa Zainab tsinuwar da zata bita tabi duniya ta bace daga rayuwar 'yarta da jikanta har abada,
Hada jini da Zainab ko masifa da balai.


*********
Haj Zainab da AMAL harma da Uncle Lulu dake jiran zuwan AQEEL ASAD a ranarda jaridar ta bullo Bai samu yazoba saidai yayiwa Mamin tasa waya akan tafiya ta kamasa ta gaggawa saiya dawo zaizo.

Juyar da Kai AMAL tayi cikin Dan takaicin sakon nasa sbd taso yazo din Mommy ta Kai karshen alaqarta dashi,
Har cikin ranta Bata kaunar kusancinsa da mahaifiyarta,
Babu alamar alkhairi a tarensa da mommynta tunda hakan ya fara bullowa,

Duk wani Abu dayake taba Mata mommynta tsanarsa takeyi da gaske shiyasa aurenta da SSG har abada bazai taba faruwaba Koda ta rasa Mijin.

Bedroom dinta Takoma ta zare kayan jikinta ta shige toilet.

Wanka tayo tareda alwala ta fito lafiyayyan farar fatarta na daukan Ido.

Sama sama ta shafa body cream da turaruka marasa karfi
Fuskarta bata shafa komaiba Bayan Mai kadan ta miqe ta nufi kayanta ta saka Malaysian Riga da skirt marasa nauyi rigarma as usual batada hannu sai Dan qarami siriri.

Abaya ta saka tayi sallar magrib tana idarwa ta Dan Yi waya da Siddi da sai alokacin tasan meyake faruwa ta Kira mommyn tana cewa zata dawo zuwa next week.

Harta fito cin abinci waya takeyi da siddin wadda taji kamar ta dawo a ranar Amma Dole zata Bari zuwa next week idan Mijinta yayi tafiya zata dawowarta.

Baya sun Gama cin abinci Bata tsaya fira ba ta shigewarta sbd kanta yau ciwon Yar hargitsin data Shiga yakeyi akan lamarin.

Baya shigewarta Haj Zainab ta kalli uncle Lulu cikin tabbacin abinda zai iya faruwa tace,

"Matuqar zancen Nan ya Isa kunnen dangin AQEEL ASAD inada tabbacin bayyanarsu gareni saidai Kuma bazasu taba iya sako kafarsu muhallinaba sbd tabbatarda qyamarsu gareni.

Qayataccen murmurshi yasake Yana cewa,

"Ta duk inda zasu bayyana dabararsu ce,
Abu dayane anan
Shine bazasu taba bayyana sirrin Siddi Yar da Kika Haifa a bariki bace.

Qaramin numfashi ta sauke ahankali tana ajiye wayar dake hannunta tace,

"Siddina ce kawai damuwata,
Itace Bazanso su tona wani sirrin dazaisa tasan ita waceceba shiyasa nace tabari sai zuwa next week idan Mijinta yayi tafiya ta dawo Dan inada tabbacin zuciyarsu bazata dannesu sukai har wannan lokacin ba Basu bayyana ba sai idan basa Raye a duniyar ne to.

Sun Jima suna tattauna zancen harkokinsu kafin suka shige.


****Bilkees kuwa daqyar taga safiya ta waye ta daga wayarta tafara da Kiran Nafee tayi Mata tatas akan Bata nemetaba Bayan tanada tabbacin tagani Kuma taji abinda yake faruwa IDON NERA na neman dawowa kan Mijinta.

Fuskewa tareda marairaicewa Nafee tayi tace bata saniba sbd itama SSG yaqi sauraronta
Neman hanyar gyaran aurenta takeyi.

Bilkees data Gama quluwa tako Ina cewa tayi,

"To gwara ki Dage da neman mafita kuwa Dan wlh Ina Nan koro IDON NERA tadawo asalin inda tafara sbd Babu gurinta a rayuwar Mijina.

Kashe wayar Tai ta wurgar zuciyarta na tafasa,

Umma taqi cemata komai haryanxu akan zancen,
AQEEL ASAD dinma yaqi lokacinta bare tayi Masa zancen,

Mufeeda ma tana cikin baqin ciki da kuncin lamarin bare su taru suyita tsinewa dangin kaf ahalin IDON NERA ta uwa ta uba,

Koma dai menene ita tinda Babu gurin Wanda zataji cikakken bayanin abinda yake faruwa zata tinkari inda ya Kamata taji Dan bazata zauna ta haukaceba sbd gap take da bugawa idan ba bayanin komai tajiba.

Zatai maganin matsalarta tareda takawa matsalar kyakkyawan burki kafinma tayi tunanin shigowa gonarta.


Da yamma umma ta iso driver yaje airport ya daukota tareda Fatima jikar yayanta sbd manyanci sosai yasa Dole yanzu tafiya Saida Dan rakiya.

Koda suka iso Babu Mai walwala ko farin ciki a gidan musamman Bilkees wadda tashin hankali dake cinta a fili yake bayyane,

Haj Maryamah ta danne nata sbd basa son kowa ya fahimci ko abu dayane dazai iya nuna alamar alaqarsu da Zainab ciki kuwa harda Bilkees wadda itama kanta bazasu yarda tasan matsayin Idon Nera agunsuba.

Tunda umma tazo ko abincin kirki kasa sakawa cikinta tayi
Ita Haj Maryamah kuwa Daman tun jiyan duk wani qunci da baqin ciki yagama cike Mata ciki
Daurewa kawai sukeyi sbd Hana kowa fahimtar abinda suke fama dashi.

Shi kansa AQEEL Babu Wanda ya sanar Masa da zuwan umman Dan kuwa Yana Jin zuwanta zai fahimci meyake Shirin faruwa Dan Haka basuda masaniyar yaushema zai dawo kowannensu yaqi yin waya dashi Dan isarda kudirinsu batareda yasaniba dagasu har Bilkees da 'yarta.



*****Washe gari karfe goma na safiya Al-Amin yagama korowa umman bayanin komai akan Idon Nera da offices dinsu da gidansu harma lokacinda take gida da lokacinda office zaa sameta.

Kallonsa Haj Maryamah tayi tace ya tafi Kuma karya sanarda AQEEL ASAD bayanin Idon Nera dasuka saka ya Nemo musu.

Yana fita haj Maryamah tace,

"Bazan taba saka kafata inda Zainab takeba sbd zuwa gabanta shine mafi qanqantar da zanyi a rayuwa,

Kafafuba bazasu taba taka haramtaccen gurinta ba......

Wani numfashi umma ta sauke tana kallon haj Maryamah din da zafin dayake cikin ranta tace,

"Kinada wani zabi ne Bayan takawa kije gabanta ki Kai karshen matsalar rayuwarki?

Rashin zuwan naki kina saneda masifa da baqin cikin dazai kawo daga baya alokacinda ta sake mallake Miki 'dan,

Bakida wani zabi Maryamah baya zuwa Inda take din sbd shine kawai mafita batareda AQEEL din ya dawo yamasan meya faruba,

Zuwanki Dole ne sbd mugama magance damuwar nakoma basaima AQEEL din ya sameniba yayi zargin wani abun tunda munkoma mune mukejin shakkarsa duk akan Zainab,

Wlh malam ya auro Mana irin masifa gashinan an haife Mana anbarmu da kuka da baqin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login