Showing 9001 words to 12000 words out of 92699 words
nasame ku lafiya, ya Alhaji da jikinshi dai."
"Alhamdulillah jikinshi yayi sauki, sai fatan afuwar niman afuwar Ubangiji, Ya matanka ? da mijina da kuma kishiyata?"
"Duk muna cikin koshin lafiya, basu san zamu zo ba shu yasa kika ganmu da huda da sun sani ai da, dasu za'ayo tafiyar."
Suna hira masu aikinta suna jera masa abin taɓawa,
"Aikuwa baka kyauta min, ba ga azumi ya kusa da fatan anan zasuyi sallah dan yace min doki zan saya mishi, har nabawa Barde kuɗin dokin za'a kawo mishi da kayan hawan dokin"
Ware idanu Mai Nasara yayi cike da mamaki yace.
"Mama Kilishi har biye mishi zaki, Sameer fa shekaranshi takwas ne ina shi ina doki."
Dariya tayi cikin dattako tace.
"Mai Nasara knn, Ai yaron da kaga yana da muradin abu matukar bai da fitina ka bashi, kuma ai bara yaga ɗanka yahau shine hankalinshi ya tashi faran shaddarshi sai da aka ɓata ta, sabida yaji haushi kuma, shima Uban wancan ɗanka ai sai da na musu tass, wai baisan Mijina nason doki ba ai,shine nace ya rike nashi ni zan saya mishi fara dan yace farin doki yake so."
Dariya sosai yayi yace.
"Mama kina taya ɓera ɓarna."
Jug ɗin kunun tsamiya ya tsiyaya a kofi sannan ya saka sugar mi y'ay'a a cikin kunun ya sauka kafet ya fara ci a nutsu, mikewa tayi tafita zuwa ɗakin Mahaifiyanshi ta idar da sallah tana sauraron kukan da huda take mata tare da korafin, abinda iyayenta sukewa Daddynta, daga bakin kofa ta tsaya bayan ta ɗaga labule huda tace.
"Hajiya Daddy baya farin ciki sai yazo nan, ni dama ki kirasu ki musu faɗa ko zasu daina mishi abinda suke yi."
Da sallama Mama kilishi ta shiga ɗago huda tayi, cikin nutsuwa tace.
"Jeki gurin Daddynki ki karya amma ki goge kukanki"
Share fuskarta tayi, cike da zolaya Mama kilishi tace.
"Yawwa Matar Marafa, da alamu bana nice zan baki kujeran Umrah dan banga Mijinki na sonki ba,"
Dariya Huda tayi sannan tace.
"Wai baki da labarin ya saya min Tap ne, har da computer xauna a gurin sai na aureshi zaki san da karfina na shigo."
"Hmmm! Jeki karya zamuyi gasar kyau a gidan nan zan nuna miki dani Alhaji yake."
Fita huda tayi tana dariya, zuwa falon Mama kilishi.
Zama Mama kilishi tayi a nutse, tare da sauke ajiyar zuciya, murmushi Mahaifiyar Mai Nasara tayi mata sannan tace.
"Kinji abinda kishiyarki take faɗa ko Rukayyah."
"Wallahi naji, abinda yake damuna ynx ko zai kara aurene?"
Inji Mama Kilishi,
Murmushi Mahaifiyarshi tayi sannan ta gyara zamanta tace.
"Kara auren bashi bane mafita, abunda zamu masa shine addu'a dan ni har yanzun banga alamar sauyi a tare da shi ba, sai yana tare da Yaranshi, kuma bana jin matarshi tana kusadamu dan nasha mafarki akan matar da zata.
Akan matar da zata zame mishi haske, kuma kinga yanayinshi yana da tsatsaran ra'ayi duk ya haɗan nunawa Sa'a taya zai fahimci kulawa bayan kowacce tana da abinda yasha kanta basu da lokacinshi, Hmm Allah ya kyauta."
"Amin" Mama tace,
Jikinta a sanyayye can tace.
"Ni ina tunanin kodan baya kusadamu ne, kinga yanda yake cin abinci kuwa, kaiii Allah ya kyauta."
"Hmmm! Eh toh dukda haka, amma Ya zaɓa mana abinda yafi alkhair."
Haka suka cigaba da tattaunawa har Mai Nasara ya shigo, mikewa Mama kilishi tayi tabasu guri zama yayi kusada Mahaifiyarshi, yace.
"Ina kwana Hajiya"
"Lafiya lau,"
Yanda yayi gaisuwar a takaice haka, itama ta amsa mishi sabida kunyar ɗan fari, bata iya sake jikinta dashi amma tana jin zafin abinda matanshi ke mishi har da Aneesa yar Kaninta,
Zaman shiru sukayi dukkansu har Huda tashigo ta buwaye su da hayaniya, mikewa yayi ya ɗauki wani key dake saman show glass ɗinta ya buɗe ɗakin dake cikin falon, kallonshi Huda tayi cike ds son surutu tace.
"Daddy!!"
Juyowa yayi agajiye da hayaniyarta tace.
"Kardai barci zakayi ni kuma ina son zuwa gurin Marafa."
Lumshe idanunshi yayi yana jinjinawa wanda zai auri Huda, dakyar yace.
"Don Allah princess jeki drvn yakai ki, na gaji sosai."
Mikewa tayi ta ɗauki side bag ɗinta tace.
"Ok Bye, hajiya mi zan sayo miki?"
"Ke tafi can magananiya."
Inji Hajiya knn, fita tayi tana dariya, har wajen gidan,
Shigewa ɗakin yayi ya kwanta, taɓe baki Hajiyarshi tayi cike da mamaki wato hali zanen dutse, halinshi ba iyakan mutane tsiraru yakewa ba, har da Yaranshi toh ai dole yasamu matsala da matanshi suma dake shashashune basu san yanda zasu bi dashi ba.
Haka ta ɓata lokaci tana nazarin halayar ɗanta da matanshi tana niman ta ina mafitar take.
***
A nutse muka ka dawo gida, dukda tulin gajiyar dake bibiyarmu dan dakafa muka shafo, daga makarantarmu, wai ma da zamu tafi a napep dawowa kuma asayidarmu, ga rana da ake tsulawa ajiyar zuciya na sauke lokacin da muka shiga harabar gidanmu, ganin motar Aunty Shukra da na Aunty Hamdiyya.
Da gudu khalifa ya fito ganinmu yasa shi komawa da sauri tsabar k'iwuya, Dariya Rahila tasaka tace.
"Baby Khalifa, ko kuntuna maganarmu na daren jiya..."
Kafin ta kai aya na shige a guje Rahima itama ta rufa min, dariya take lokacin da taga mun zaune muna sunne kai, tace.
"Annamimai, wallahi tunda kuka nuna min kuna jin kunya sai na cire muka kafin mu bar gidan nan"
Kasa kasa take maganarta wanda iya mune zamu jita, mikewa nayi na shige ɗakin Maman Amarya shewa tasaka, har da buga cinyarta, da sallama a bakina na shiga ɗakin Aunty Shema'u, da sauran Yaran gidanmu mata, har da Aunty Gausiya, zuɓewa nayi a jikin Aunty Hamdiyya ina dariya, waya take muryanta kasa kasa, idan baka ga wayar ba sai ka rantse ba waya take ba, kurawa bakinta ido nayi yanda take motsawa.
"De Aunty Hamdiyyarmu knn, kanwar sharuhkhan yayar Amisha sharma, irin wanga luv ɗin Aradu ko uwar gulmar da ta zuba miki ido bata san mikike cewa ba, Allah zan zo gidanki ɗaukar class."
Katse wayar tayi ta wawuro wani laida ta wurgawa Rahilah, dariya Auntys ɗinmu suka saka basu ɗaya ba, har da Mama da take gadonta,
"Rahima ɗauki kayan can ki kaiwa Ummarku, ni sun isheni"
Mikewa Rahimah tayi ta shiga ɗaukar kayan fruit ɗin da aka kawo can idanun Rahilah ya faɗa kan Ayaba, ɗauka tayi ta gutsura, daga jikim uwar haɗa ido mukayi da ita aikuwa ta kashe min ido da sauri na ɗauke kaina, daga gareta dan na lura iskanci take ji a ranta.
Kallonmu Aunty Shema'u tayi tace.
"Mama wai yaran nan basu da tsayayyune, ko jiya sai da Hayatu mukayi magana dashi, wai ana ta binshi akan ana niman izini akan su saura kwanaki su gama, scndry amma har ynx babu samaruka,"
Dariya Mama tayi cikin jin daɗi, tace.
"Yan ukuna har ynx Allah bai kawo musu mazaje ba, sai dai ina da Yakinin mazajensu suna hanya, toh da kike maganarki shema'u yaran nawa suke, sha bakwai ne fa da watanin biyar, kuma ai koke a sha tara malam ya aurar dake, sai jariraina ne za'a saka musu ido,"
Da dariya Rahilah tabar ɗakin zuwa ɗakinmu na yan mata, tasamu na cire kayana ina jiran rahimah tafito wanka, sai gata rike da ayabar tana min bayani tace.
"Kinsan lokacin da aka sani a zubar gado fans ina jin ana banana banana, Yaseen sai nazata nacine, asheeeee"
Mikewa nayi nabar ɗakin babu shiri, dariya tasake har da rike cikinta, Rahimah da ta gama wanka ta kasa fitowa tsabar, mun gaji da iskancinta.
Can tayi shahadar kuɗa ta fito, suna haɗa ido ta ɗaga mata gira, dake ita rahimah tana da sauri kuka take ta fashe da kuka tace.
"Wallahi sai na kai karanki."
Fuuuuu tafita, kiciɓis suka yi da Umma cikin shashekar kuka tace.
"Umma kinga Rahilah ko! Ta addambemu wallahi ku mata addu'a ko Allah zai aiko mata shirya."
Duk Yayunmu suka fito, sai kallonsu ake ita rahilah dariya yaci karfinta, ke Rahimah kuka, sai da Umma ta daka musu tsawa sannan tace.
"Bana son shiririta wucce ku bani guri."
Sunsun suka wucce, suna shiga ɗaki, aunty shukra tana bin bayansu, a bakin kofar ta tsaya tana jin dariyar Rahilah tace.
"Mi yasa baki ce ina kiran Banana bane, Allah da gske yaren novel ne, ki ji sunce joy stic.."
"Rahilahhhhhh" a firgice ta yarda ayabar, tura kofar Aunty shukra tayi tana mata wani irin kallo daga sama zuwa kasa.
"Kinsan abinda kike kira kuwa, gaban ɗa namiji a ina kika taɓa, gani yau zanci kaniyar." take jikinsu ya ɗauki rawa, tace.
"Don Allah Aunty kiyi hkr wallahi ban san wani abu akanshi ba, na rantse miki da Allah nima a online nake ji a novel Aunty ki rufa min asiri kiyarda dani bansan kome ba."
Buɗe kofa tayi ta kwala min kira da sauri na fito, na shiga ɗakin, nan ta shiga mana tambaya da bin didiginmu har da kwanakin da muke Period ɗinmu, kaii karshe cewa tayi sai ta duba kasarmu zata yarda dake Nurse a nan kaduna a wani prvt hospital take aiki kuma ba laifi babba ce, a gurin aikinta kuka nake cike da tashin hankali nace.
"Aunty Yau na fara bin month don Allah ki yarda damu bamu san kome ba "
Ganin yanda muka gigice yasa jikinta sanyi faɗa tayi mana sosai sannan ta karɓi wayar ta goge Whatsp ɗin ciki da face book, tace.
"Idan nasake kamaku kuna irin wannan maganar a kunen malam wallahi."
Cikin rarrashi tayi mana nasiha sosai wanda ya shiga jikinmu, tace.
"Wayarku sabida karatu da wasu uzuri aka saya muku bawai dan ku lalace ba, idan da a gidan mazajenku kuke wallahi bazan taɓa damuwa da ku ba, don Allah ku rufa mana asiri mu aurar daku, lafiya aikuna jin yanda ake sukar iyayenmu akan gausiya don Allah ku zame mana jakadu na kwarai."
Bamu iya kome ba, sai gyaɗa kai kaman kadangaru a jikin bango,(lolx kun tuna inna wuro kuwa)
Fita tayi tabarmu a ɗakin bayan ta bimu da addu'a shiriya,...
*****
"Hello Adda Nafi'a bazan sami zuwa wunin gidansu Sailuba ba, sabida Ahmad ya dawo, amma ki karɓa min nawa."
Daga can ɓangare aka " kutt yanzun zama zakiyi dan yana gari dalla kifito shi yarone da zaki bashi nono, a gidan common ma dear ki zo."
"Taɓ akan haka kina jinshi yana ikirarin kara aure sai na fito, bikin wasu na lalata nawa kicewa sailuba tayi hakuri, da baya gari zan zo amma ynx yana gari, nasan mi yake shirya min, tunda Yan uwanshi basa zuwa ko sunzo koransu nake da masifana kawai ki bata hakuri."
"Wai nikam yaushe kika koma haka, ne wato namiji yafi, bikin besty frnd ɗinki "
"Ai bashi yafita ba, kishiyar da yake ikirarin zai min tafita muni a idanuna kinga sai an jima dan ɗazun yagama f**ck ɗina son ranshi boons ɗina har ynx ciwo na suke min, yanzun zansan yanda zan shawo kan kayana clear."
Tana kai aya ta datse kiran, cike da takaici ta mike zuwa ban ɗaki wanka tayi sosai, har ynx tana jin zogin kirjinta sunce towel ɗin tayi cikin nutsuwa taga yanda bakin nipples ɗinta sukayi jajjur, dake fara ce, tsaki tayi tace.
"Banza mayye kawai, ko Jannart bata cinye min bakin nono haka ba."
Shiryawa tayi cikin riga da skirt na lace, purple tayi kyau ba laifi kitchen ta shiga tayi musu tuwo miyar wake, wanda yaji kifi da nama, a leda ta ɗaure tuwon ta kawo table ta ajiye sannan ta koma ɗaki tasake wanka sosai, ta canza kaya, tafito.
Zama tayi a falo ta kunna kayan kallo, wayarta da yake kashe tun jiya ta kunna a can tashiga niman inda zai ɗauke mata kewa.
Mbc bollywood ta saka, tana kaiwa suna fara hoob Ghaad, nan tasamu ya ɗauke hankalinta, data wayarta ta buɗe a hankali sakon Whatsp ya fara shigo mata kafin ta fara ganin na IG, Whatsp ta buɗe ta cikaro da hidimar bakin da suke yanda ake shagali, kwalla ne ya fara bin fuskarta,
A hankali ta fashe da kuka dan har jin kafarta tayi yana mintsininta, Ig ta buɗe anan ta ɗaura hannunta akanta ta fashe da wani irin kuka zaka rantse sakon mutuwa ta gani a'a tsabar shagali ya wucceta ne, take bakin ciki fushine ya cika zuciyarta yau ita ko Ahmad.
****
Kallon Rahilah mukayi sannan muka fashe da dariya cikin zolaya nace.
"Don Allah yaren novel nike son ki min."
Kwanciya tayi, daga ita sai zanin kirji tayi rigingine juya kanta tayi tana murmushi tace.
"Kuyi lokacinkune, zan kamaku bebs"
Zama nayi akan stool ɗinmu ina duba chemstry, dariya mukayi tashi tayi ta zauna, tana kallonmu tace.
"Wai shin dariya nake baku ko?"
Girgiza mata kai mu kayi nace.
"A'a baki bamu dariya, kawsi muna mamakin duk rashin kunyarki da bakinki daga ance za'a faɗawa Umma da Malam duk kin gigice sai kuka kike kina yarfe hannunki, hahahah."
Dariya Rahimah tayi cike da tsokana haka muka hanata sakat, sai da ta dawo mana da halinta dan ba tare da mun ankara ba ta zare xaninta tace.
"Zafi nake ji."
Da gudu muka fita daga ɗakin, gyara zaman zani ta tayi, ta shiga ban ɗaki wanka tayi ta fito sannan ta saka, doguwar riga tafito, tsakar gida ta karɓi busar shinkafan da Umma take nima ajiye buƙ ɗin nayi, na karɓi aikin yin miya, munayi muna hira.
"Maryam Sajidah kin kaiwa Hajiya Falmata hand out ɗin nan kuwa."
A raxane na ɗago kai nayi cike da tsoro dan Umma yanzun zata balbaleka, sake robar da ake ajiye garin kuɓewa nayi, na fito daga ɗakin girkin a tsorace ina yarfe hannuna nace.
"Wallah.."
"Wallahi kin manta ko? Toh ai yayi miki kyau sai ku tashi ki ɗauko ɗari biyu ku kai mata, dan yau zatayi amfani dashi sokuwa kawao kuma ki kwashe min garin kuɓewana kafin na raɗeki........
\(-ㅂ-)/ ♥ ♥ ♥
```Ita Rayuwa saukine da ita ɗauketa yanda ka ganta```
[8/25, 2:59 PM] Real Mai Dambu: 🌹🌹🍀
*MATAR SO*
🌷🌷🌻
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER'S ASSO*
(HWA)
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....
Dedicater To Hafsat Abubakar💋
_Idan kinsan baki saya karki karanta sabida na kuɗine, idan kika samu an sato toh karki faɗa min maganar banza dan zan iya miki Allah ya isa, duk wacce ta fitar min Na barta da Allah_
*BOOK ONE👈*
*Page.5*
Jikina na rawa na kwashe garin kuɓewar sama sama, na mayar cikin robar na rufe kallona umma tayi cike da mamaki yanda Allah ya ɗaura min tsoron jaraba, gashi na iya laifi amma cikina cike ya da tsoro, bani ɗaya ba harsu Rahilah haka muke da tsoron kata'i.
Da sauri nabar kitchen ɗin zuwa ɗakinmu, na ɗauko sakonta na fito kallonsu Rahilah nayi cikin nutsuwa nace.
"Jiranku nake kar lokaci ya kure."
"Amma dai kya jira na gama sai mutafi ko?" tace min,
Ina zaune ina jiranta har ta wanke shinkafar tuwon, ta jika Rahima tana gurin Mama dan ba zata bimu ba,
Da sauri muka fito ni ina sanye da Nikk'af ita kuma taki sakawa, muna tafiya muna hira har muka fito daga unguwarmu, abin hawa muka tara muka faɗa mishi sunan unguwar da zai kaimu, ba tare da wani gardama ba ya kwashemu zuwa unguwar,
A kofar gidan aka saukemu, unguwar sabon gurine dan kamar manyan mutane ne, suka sayi filayen, tura get ɗin mukayi da sallama, mai gadin gidan ne ya mike gaisheshi mukayi, sannan nace.
"Malam hajiya tana gida kuwa?"
"Eh tana ciki,"