Showing 78001 words to 81000 words out of 92699 words

Chapter 27 - MATAR SO BOOK 1

06 Sep 2025

862

da faɗa da nuna min kasawata, bansan ya akayi ya kyalesu suka koma bakin nimansu. Sam bana jin daɗi dan latsani da yake yanzun ya daina,

           A ɓangarenshi kuwa lokacin da ya karɓi wayar Fareeda nan yaga, abinda suke faɗa akaina na cewa..
"Wallahi wannan tauye hakkine akan mi zaku barshi ya auri yarinya karama ya lalata mata rayuwa, ai child abuse ne, gata yar karama ina zata iya ɗaukar laluranshi, kema ai..."
     Haka sukayita hiran duba chatt ɗin yayi sosai yaga yanda wasu suke kushe abin,( karku manta dama yana mata kallon jinjira)

            Da wannan tunanin yazo ya sameni har ɗaki yace.
"Ina takardun makarantarki."

         Mikewa nayi na bashi na jamb ɗin, ganin sassaucina fuskarshi nace.
"Daddy don Allah ina son nayiwa ɗalibaina magana suna zuwa gidan nan muna karatu asabar da laha...."
   Wani kallo yayi min wanda yasani haɗiye maganar da nake, tamke fuska yayi sannan yasaka kai yafita.
  Tun daga ranar ban kuma gane mishi ba. Sai dai su sani a gaba matanshi suyi ta min dariya gidan yasake watsinewa baka gane wacece mai girki. Da zaran yunwar bukatar mace ta kamoshu toh zai tunkari duk wacce tayi mishine.

          ******
"Kana nufin tunda ka dawo da ita babu abinda ya haɗaku." Inji Ahmad,
         Ya mutsa takardan hannunshi yayi cike da damuwa, yace.
"Ya zanyi mata? Ya kuke so nayi mata? Yarinya ce fa, har yanzun bata cika 18 ba, bazan iya ba wallahi."

"Toh ka sake musu yar mutane kans gasata, matanka suna gasata babu amfanin zaman haka tunda babu adalci a zamanku." Inji Aman yana tattara kayanshi,
"Haka zaku ce, bazaku bani shawara ba."

"Toh wani shegen ka ajiye zai baka shawara, kasan duk cikinmu kafimu shekaru mai nasara wani irin taurin kaine da kai haka, mace ma sai mun faɗa maka yanda zaka sarafata toh ka zauna mu ajiye matsalolin gabanmu mu kashe naka, banza nan d'an iska wallahi baka san darajar Aure ba, kasaketa Na nimawa Faisal tunda baka sonta shi nima aure yake nima mace ta gari."  Inji Ahmad,

        Mikewa yayi jikinshi har tsuma yake, ya tattaro kwalar rigar Ahmad tare da kai mishi duka, Aman kuwa ya kara tunzurashi yace.
"Wallahi sai kasaketa nima ina da ɗan uwana dake sonta, kasake musu yar mutane mugu azzalumi ma cuci, gidahumi kawai kuma daga yau zan zare hannun jarina a cikin kamfaninka."

              Cak ya tsaya cike da wani irin fargaba ya juya ga Aman, idanunshi na cika da kwalla bakinshi na rawa, ya nuna Aman da ya tsaya.

Aman Yace.
"Yess zan cire hannun jarina sai me kaima Ahmad kacire mu kyaleshi wanda bai san darajar Iyayenshi ba kasake musu Yar mutane, kuma zaka sha mamaki kana saketa yau za'a ɗaura Mata aure da Faisal, Wawa jaki kawai."

              "Eh nima zan cire hannun jarina ka zauna kai kaɗanka kamar mayye."
    Zuɓe gwiwarshi yayi a kasa tare da dafe kirjinshi dake mishi nauyi, tari ya shiga yi har da gudan jini da sauri sukayo kanshi tare rungumarshi Aman yace.
"Munyi haka ne dan ka fahimci halinda kake ciki, badan mu kaga maka lalura ba."
         "Abokaina ina sonta, Ina son MaryamSajida, ku daina cewa zaku haɗata da wani dan zan iya mutuwa, karku rabani da mata...."
   Kan Uba idanunshi kafewa yayi a tsorace suka saɓe shi sai motar Ahmad, asibitin Al-kalman suka kaishi. Take suka karbeshi cikin gaggawa aka shiga duba shi,

           Sun samu numfashinsa ya daidaita, har yayi barci.
                 Gurin likita suka je ya zare madubinshi yace.
"A gaskiya tension sun mishi yawa ga desire dake damunshi sosai ga jininshi da yayi mugun hawa don Allah ku daina sakashi a damuwa."

       Rubuta musu magani yayi da karin drip.
            Zama Ahmad yayi a gurin mai nasara Aman ya tafi sayo magani, daga nan kuma ya tawo gidanmu, ina ɗakina jikina duk yayi sanyi kamar mara lafiya naji sallamar Aman.
Hijab ɗina na sura nayo kasa. Tun a step muka gaisa ban karasa cikin falon ba, yace min.
"Ina yan uwanki suke?"
        "Basu nan sai Mamansu Huda. " na bashi ansa.
"Toh kice tazo muje mai gidan bai da lafiya yana asibiti."
       Bansan lokacin da nace.
"Muje mu ganshi,wayyo Allah mike damunshi? Muje naga jikinshi."

     Tausayina bashi yace.
"Ki mishi girki, zan tafi da Maman huda amma zan dawo ɗaukar abincin sai mu tafi tare."

        Kuka nasaka mishi na koma sama na faɗa mata kamar bazata tashi ba tasaka Gyaletanta babba tafito, kallonta nayi kamar zance wani abu sai nayi shiru kasa na sauko nazo narasa mi zan mishi.
        Komawa ɗakina nayi na kira Umma ina kuka nace.
"Ummana, Daddyn huda baida lafiya mi ake dafawa mara lafiya."
       Shiru tayi kafin tace.
"kiyi mishi kunun gyaɗa, sai faten wake da hanta ko da koda, kiyishi yayi ɗan kauri Allah ya bashi lafiya, toh miye na kuka ya isa kijw kiyi mishi yawwa ki haɗa da aleyawu."

      Zuwa nayi na fara aikin dole sai da natafi babban kitchen na ɗauko hanta, da alayahu nazo na karasa faten kunun na markaɗa gyaɗar a bledan nayi mishi na zuba a flast. Wanka nayi nasaka atamfa riga da zani sai hijab da nik'af ina jiranshi.

Ganin yaki zuwa kawai nakira Rahilah na faɗa mata ina kuka, kashe wayar tayi ta kirashi ta fada mishi can sai gashi ya ɗauko Rahilah muka tafi,

         Tsabar tashin hankali gani nake kamar nawa yake, muna shiga ɗakin har ya farka dama basket ɗin yana hannun Aman, da gudu na nufi gadon inda yake jingine da pillow na faɗa jikinshi tare da fashewa da kuka, rungume shi nayi ina kuka, ɗago kanshi yayi ya kalle Aman da Ahmad, murmushi suka mishi tare da gyaɗan kansu.

        Sanya hannunshi yayi ya kara rungume ni, fita sukayi har da balkisu suna fita na cire nik'af ɗina na fara kokarin sumbatarshi,  rike fuskana yayi yace.
"Nutsu don Allah karki min fyaɗe, ina gadon asibitine yanzun ki lalata musu komi." kwace fuskana nayi na shiga sumbatar bakinshi, da duk karfina.
                  Idanuna a lumshe, yana kallon yanda kwalla ke bin fuskana, saka hannunshi yayi yana goge min, sake bakinshi nayi na kwantar da kaina kirjinshi ina jin bugun zuciyarshi.
            Shafa kaina yayi cikin nutsuwa yace.
"Daga zuwa sai kuka, sai kiss toh don Allah zuwa an jima karki ce zakiyi disvirgin Daddyn kawarki fa."

      Dariya nayi tare da kai mishi duka nace.
"Daddy Maza ma ana disvirgin ɗinsu ne? Wannan abin da ban dariya yake."
                 Ina jin hannun shi ciki rigana na ɗago kaina nace.
"Wai don Allah mike damunka, dan naga kamar ba ciwo kake ba, tunda ga hannunka da basajin magana sun fara aikace aikacen sirri."

          Cire hannunshi yayi yace.
"Yar kwaila kawai ciwon kirjine, amma da sauki  bani abinci sannan hannuna da ake ganin laifinsu, daga zuwarki kika shiga lalata min baki banyi magana ba kuma ban damu ba shine hannuna suka rama min, sai ace nayi ɓarna toh zanci abinci kafin nayi tunanin cin mai abinci."

Kamar sokuwa na kalleshi sannan nace.
"Toh abincin ma bai isheka ba sai kaci mai abinci taya knn."
Kunshe dariyarshi yayi sannan yace.
"Mai dear bani abinci ko."

Zuba mishi abinci nayi ya fara ci, yana murmushi, can yace.
"Kin kora min mutane fa, har da matata."
Tura bakina nayi cikin niman rigima nace.
"Nifa sai ka faɗa min taya zaka cinyeni, kuma ni ban koresu ba."

Nik'af nasaka nafito zuwa waje kamar munafuka, wayam na gani komawa ciki nayi na wurga nik'af ɗin nace.
"Sun tafi fa."..

    "Toh dama tsayawa zasuyi daga zuwa sunga zakiyi fyaɗe su gudu ba dan basu son ayi bincike ya faɗa kansu."

Cire hijab ɗina nayi na shiga buga kafana akasa nayi kanshi ina buga hannunshi, cikin sakalci nace.
"Daddy amma alluran magana suka maka ko"

"Eh toh har da alluran cinye masu tambaya duk suka min."

Komawa gefe nayi ina mamakin shi yana gamawa na taimaka mishi yayi alola ya gabatar da azhar da la'asar.

      Yana idar da addu'a yace.
"Rufe kofar kizo nan."

               Mikewa nayi naje na rufe kofar buɗa min hannunshi yayi na shige jikinshi ajiyae zuciya na sauke,  sosai na makele shi muna hira a haka har na soma fahimtae yanayinshi ya sauya sosai, ta hanyar birkita min lissafi. Dakyar na shawo kanshi ya kyale ni sai da na fashe da kuka tukun ya kyaleni.
Shiru yayi yana nazarin abubuwa da yawa, musaman yanda yake min kallon baby maganarsu Fareeda ce ta sake dawo mishi ya shiga kare min kallo, kafin ya kai bakinshi kunena yace.
"Maryam zaki iya..."

Sai kuma yayi shiru yana kallona ganin naki buɗe idanuna yasashi fara min cakulkuli aikuwa na fara dariya har ina niman faɗuwa a gadon kallona yayi yace.
"Na kiraki baki amsa min ba."
D'aga mishi gira ɗaya nayi sannan nace.
"Zama da ma ɗaukin kanwa...."
"Tohfa yaushe Zabarmawa suka iya hausa haka ban sani ba?" Injishi.
"Daddy kenan shafa kaji."
Jin inda hannunshi zai koma yasani mikewa da sauri dan naji ana buga kofar gyara hijab ɗina nayi ina dariya nace.
"In ba tsoron ba kataso mana."
Lumshe idanunshi yayi yana jin wani nishaɗi na ratsa shi yace.
"In ba tsoron ba ki tsaya mana."

"Kutt." nace bayan na murguɗa mishi bakina, nace.
"Lallai ma, kalan ka zubar min da aji na ina yar 17yrs saura two month na cika 18yrs kuma sai ka shirya min birth."

Haka kawai jikina ya bani tumakan shine suka ɗibo jikinsu ina buɗewa kuwa suna min kurrr da ido basu hanya nayi Fareeda ta bangaje ni. Duk akan idanunshi bai ce komi. Komawa gefe nayi ina kallonsu sai iyayi suke nan suna jajjanta mishi, idanunshi na kaina.

Zuwan su Rahimah nace mishi.
"Daddy zan bisu zuwa gida."

Basar dani yayi suka cigaba da hira da matanshi, tare dasu Ahmad ni da Rahimah muka fito waje dama yana amsa musu yana ganin mun fita, ya gintse hiran ta hanyar lumshe idanunshi tare da harɗe hannunshi a kirji dole duk sukayi shiru Ahmad da yasan kwanan zance, dariya yayi sannan mike.
"Toh mukan zamu tafi, amma ina ga kaman da maryam zamu tafi a sauk..."

Wani irin kallon banza yayiwa Ahmad, wanda yasashi gintse maganar da yake.

Dariya yayi ya fita, har yakai bakin kofa mai nasara yace.
"Dan Uban mutum ya tafi min da mata sai na nuna mishi karshen iskanci."

"Allah Angon jinjira toh ka daɗe baka yi iskancin ba, kuma tafiya da ita zanyi."

Lumshe idanunshi yayi yaki magana, har ahmad ya gama dariyar shu'umancinsa ya fita daga Fareeda har Aneesah sun cika fam, sai lokacin ya tuna dasu sake nanike fuska yayi irin kar wata tayi min magana,(Kaiiii Jama'a Yunus na buga Game a gidanshi.)

Shiru sukayi suna kallon Ikon Allah, ganin har yanzun ban dawo bane, yasa shi mikewa ya zauna sosai dama a kishingiɗe yake, ya kuma zubawa kofar ido, can ya ɗaga agogon dake ɗaure a hannunshi, ya kalla ya maida yayi haka yafi a kirga can sai gani na shigo, ajiyar zuciya ya sauke tare da galla min harara ya tsume fuska.

Niman guri nayi na tsaya sabida irin kallon tuhumar da yake min.
Aneesah ce tayi karambani cewa.
"Ai na kika tsaya? Wato dan yana kwance shine bari ki fara yawon tazub..."
D'ago kaina nayi cike da mamaki ina kallonshi, amma ko yace kala asalima kauda kanshi yayi kamar bai ji abinda tace ba.

Murmushi nayi cikin nutsu nace.
"Eh toh da kuma haka, abinka da tashin balaga, na saba da tsohon zuma shine nake tunanin ko idan na fita zan sami sabon jini wanda zai min full tan....."

"Maryam!!!!!!" ya daka min tsawa, kallo ɗaya nayi mishi kwalla suka cika min ido sunkuyar da kaina nayi, ya juya ga Aneesah cikin masifa da kishi yace.
"Wani ɗan iskane yace ki mata magana ina ruwanki da ita, akanki take ko niman gidan zama ku tashi kubar min asibitin ke kuma ki zauna kifaɗa min inda kika jiyo wannan maganar."

Fuuuuu sukayi waje, suna fita na fashe da kuka, sosai sabida cin mutuncina da akayi kuma bai wani ɗauki wani mataki ba, zamewa nayi na kifa kaina da gwiwa na na cigaba da kuka, na cika mishi kune.

"Mi kike nufi, da kika ci kin je niman sabon jini ne, eyye zaki bani amsa ko sai na nuna miki yanda tsohon jini yake."
D'ago kaina nayi naganshi a tsaye a kaina, mikewa nayi na tattara kayan abincina da pose ɗina na saka kai zan fita a ɗakin ya finciko ni, ranshi nakara ɓaci cikin sababi yace.
"Mi yasa kika renani ne? Mi na rageki dashi da har ban sami kimar aure ba, maryam da na zuba miki ido baya nufin bansan mi nakeyi ba komi nake ina da hujja da matakin da zan taka."

"Really! Toh cika ni na koma gida, na gaji wallahi su tumakin matanka baka iya tsaresu da faɗa zsai ni da zaran nayi laifi sai faɗa sai duka ko fincika dan ka ga Mahaifiyata tana tsawata min shi yas...."

Make min baki yayi da yatsar hannunshi, yana tsare ni da manyan idanunshin nan masu matukar, kaife da aikan sako.

Tsalla mishi kuka nayi tare da tsalle, ina yarfe hannuna sosai kamar wacce aka yanka na fasa mishi kuka, jin damshi a bakin na taɓa aikuwa nayi tozali da jini, zaro ido nayi na kara fashewa da kuka nace.
"Sai na faɗawa Hajiyata ka fasa min baki, wayyo bakina wayyo ciwona wayyo jinina zai k'are."
Tissue ya ɗauko ya goge min bakina, yanzun baya jin haushin abinda nake sai ma dariya nake bashi, gani dai da girma amma sakarcin da nake mishi ko yar goma sai haka,

Mai dani bakin gadon yayi na zauna yana goge min bakina.

Ban daina kwalla ba, har ya gaji yace.
"Keee baki gajiya da kwalla ne, kiyi a hankali dan ba lallai ki rayu da wannan idanun naki masu kama da na maciji ba."

Turo bakina nayi bayan na murguɗa mishi, nace.
"Toh ina ruwanka dani, kaga idan na auri wani shi zai nima min magani har na wark..."

Sake ɗane min bakin yayi, nayi kwalkwal da idanu dama hawayen fake ne, rike bakin nayi ina niman kukan amma sunki zuwa, dariya yayi ya dangware min goshi yace.
"Munafuka wato kukan ma, nimanshi kike dole Anya Maryam kina tsoron Allah kuwa."

Hararanshi nayi na cigaba da niman kukan kwallar taki zuwa haka na hakura na zuba tagumi, zama yayi a bakin gadon ya kwantar da kaina akan kafaɗarshi yace.
"Naga Jamb ɗinki amma naga kin cika zaria ne, shine nayi tunanin nima miki medicine ki karanci ɓangaren mata da yara, wata rana zaki yi alfahari da haka."

D'ago kaina nayi cikin nutsuwa nace.
"Nikam bana son medicine, kawai kabarni na cigaba da koyarwata a gidan asabar da lahadi ce fa, sau biyu a sati Kuma kaga akwai lada me gwab'i"

" Ban ki miki ba, maryama kawai ganin Rayuwar aure yana bukatar gogewa ta ilimin boko da Addini..."

" Inji ka ba, amma ai wayewar Addini itace wayewa kuma rayuwar gidanka ba rayuwar addini a cikinta asalin kazamar rayuwa ake, kayi hakuri fa gaskiya zan faɗa maka duk matanka sun ɗabbaka boko fiye da Addini, ka ga shigar da kowacce keyi kamar ba matan aure ba, akwai wasu sinadarai dake cikin jikin Y'a mace wanda lullube jikin mace yake kara musu garkuwa, amma matanka sun rasashi ta hanyar buɗe jikinsu Daddy ka fahimci wani abu matsalar gidanka ba daga ko ina bane kaine kayu creating ɗinshi amma kayi hakuri duk ranar da ka shirya muyi magana akan haka zamu duba matsalarka da na matanka."

Ina gamawa na shige ban ɗaki nayi alola, nafito nayi sallah magrib.

Shima alola yayi yazo ya gabatar da sallar, sosai maganata yake damunshi.
Wayata na duba naga har lokacin babu wanda yayi tunanin kawo abincin dare, Umma na kira nace mata babu abincin dare tun narana da na kawo. Faɗa tayi min akan mi yasa ban koma gida nayi girkin ba, sai na jira wani ya kawo min bayan nima na iya.

Ina zaune akan kafet sai gasu tare da Malam gurin tara na dare, nan Umma ta ajiye mana basket ɗin muka gaisa sannan sukayi mishi ya jiki, sun taɓa hira sannan suka tafi.

Zaba mishi tuwon semo miyar egusi, sosai ya ci har da kari, yana gamawa nima na zauna zanci yace.
"Kawo nabaki Yar babyn Umma."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login