Showing 27001 words to 30000 words out of 92699 words
bata da iyaka, Rahilah rayuwace wacce bata da farko balle karshe, yakine a gabanki mara makami, amma idan kika so zaki ya sayan makamanki ki shiga dasu, sabida baki san mi zaki tarda a inda zaki jeba, dan tafiya ce mai cike da tsire gashi dajine mai cike da kayoyi,
A tafiyarki da zakiyi akwai bukatar guziri, wanda zaki nemi hakuri,juriya, biyayya, ladabi, amana, gaskiya, Iya magana, girki, tsafta, uzuri, da yafiya,fahimtar juna..... Idan kika duba kalamar yakin dake gabanki wancar bayanin yake bukata, haka idan kika duba kalamar daji me cike da kayoyi wancan jawabi yake bukata, Rahilah bansan waye Aman ba, amma ke zaki fini saninshi sai kinyi hakuri da halayarshi dan ba kabir bane ko Yayanku Hayat, ba kuma malam bane da zaki ce kinsan halinshi kece zaki san meyake bukata, miye baya bukata wani abinci yafi so, wani irin rayuwar aure yake so dake, shi yana da hakuri ko ma faɗacine, Rahilah, Rahimah, Maryam,ina faɗa muku ne, dan ya amfaneku badan raɗin kowa ba, ni baxan muku, show glass na kayan mata ba, dan bazai baku namiji a hanunku ba, idan kuka maida alamarinku ga Allah shine yake rike da zuciyar mijinku, kuma shine yake tallafe da al'amuranku, bazance rayuwar aure nada daɗi ba, amma nasan wuyarshi sabida ɗaɗinshi kalilane, kuyita addu'a da azkar ku yawaita sallar dare, idan ya barku ku rike axumin nafilla, iyayenshi da danginshi su zama sune, asama da iyayenki karki fifita iyayenki sama da nashi, haka zai kara miki daraja da kima a idanunshi, sai gaɓɓa na musaman, shine jikinki za'a wayi gari ya mallaki duk wani abu naki, a cikin yanayinda koda kiranshi kikayu ko rokonshi, kaiii duk abinda zakiyi kiyi bazai taɓa jinki ba, sabida kudirinshi da hakkin kasancewa dake zai bijiro masa,Maryam, Rahilah, Rahimah wannan ranar idan yazo ku kira kowa dan su taimakeku bazasu iya taimaka muku ba, sabida nauyi ne da ya rataya akanki ki sauke kuma zaki sauke shi, da zaran haka ya faru toh kin fita sahun yara kinshiga kwaryam Manyan, duk abinda muka sani kunsani, koda wasa karki bari mijinki ya gano kazantarki ko wani nakasu a jikinki, zan baku misali akanmu kun taɓa ganin Malam yace wani abu mara kyau akanmu,"
Girgiza kai mukayi, cikin kuka, tace.
"Yawwa sabida, mun yarda da kanmu karku bari mazajenku su gano illarku, a fagen girki da tsafta nasan renonane ku, a fagen hakuri da juriya renon Mamanku ce, sai iya magana wanda nasan wannan renon malam ne, kuma Alhamdulillah ta kowani fuska bamu da aufi akanku, sai da Rahilah kina da kishiya, kuma nasanta nasan halinta bazan ce miki komi akanta ba, ke dakanki zaki gano halinta karki rena mishi mata, naso da sai kon gama karatunki amma Mahaifanshi sun nuna bukatarki zaki karasa a gidan don Allah ki rufa mana asiri ki bawa mara ɗa kunya, ki tayamu ganin lafiyar Amarya ya inganta tunda gausiya ta dawo kullum sai Amarya ta shaki Inhelarta, sannan ki ajiye kunyarki washi garin ranar da kika zama Mace dan daga nan zaki mori aurenki, iya abinda zan faɗa miki kenan kuma Wallahi naji labarin yarinya tace kasuwar ganye ko wata banzar mata ta kawo mata maganin matq ta saya na rantse da Allah sai na mata shegen duka, idan kina son maganin mata, kiya shema'u magana balle hajiya falmata bazata barki haka ba, naji daɗi da kika sameta a surikarki, Rahimah kema an nan za'a zo niman aurenki, saura Uwar masu gida yarana sun mata wayo."
Tana gama mana nasiha da huɗubar da yasamu cusa kai a cikin cinyoyinmu, tafita kuka Rahilah tayishi ba iyaka, musaman da aka zo ɗaukarta za'a mata wanka da lalle mai haɗi da miski, tana fitowa akasata a gaba sai da tashanye zumar nan, tana kuka tana kome,
Abin tausayi, sai muka zama kamar wasu kala aure zai rabamu da Rahilah, kukanmu yaki karewa, sai da Umma tazo ta balbalemu da masifa sannan mukayi shiru, karshe sai ga Rahilah tana janmu da hira da wasa da dariya.
****
A zaria kuwa sai da aka dangana da Aman asibiti, sabida jininshi da yayi masifar hawa, a daren suka kai shi, gari na wayewa, ya farka wajen karfe tara nasafe ya gabatar da sallah yana idarwa ya juya ga Ahmad, yace.
"Abokina ka yarda dani wallahi ban aikata abinda hindu ta faɗa ba, asalima kwato yarinyar nayi daga mugun hannun, Abokin.."
"Toh mr romeo, aimunsan da haka, kawai ka rufe mana bakinka ka tashi mu wucce kaduna dan karfe biyu da rabi za'a aura maka jinjirar da kake suma akanta." Inji Mai nasara,
Mikewa Aman yayi ya naɗe abin sallar Ahmad ya amsa, sannan ya koma bakin gadon ya zauna, ɗago jajayen idanunshi yace.
"Ba auren yarinyar bace mafita, fahimtar Mamie shine mafita, dan nasan halinta akan wannan abun zata iya daina min magana."
Shigowar likita yasasu sukayi shiru mika musu hannu yayi sukayi musabaha,, yace.
"Mr Mandara ko zaka iya kwanciya a dubaka."
Kwanciya yayi likitan ya,shiga duba lafiyarshi, ya tabbatar musu da kome lafiya sai dai ya kiyayye ɓacin rai,
Sannan ya sallamesu, daga nan ko minti ɗaya basu kara ba, sai kaduna, kwantar da kujeran yayi ya lumshe idanunshi, cikin tsananin damuwa yace.
"Dole na rabu da Hindu, dan haka ne mafi alkhairi a gareni."
"Hmm aikuwa a jaridar Aminiya za'a wallafaka wani yasaki matarshi sabida zai auri jinjira waccw bata fara kirgan dangi ba," Inji mai nasara,
Juyawa yayi ya kalli Ahmad da yake tuki, sai danne dariyarshi yake, juyawa Aman yayi ya kalle Mai Nasara cikin jin haushi yace.
"Eh gwara ni, jaririya zan aura kai da katara, jakuna a matsayin mata fa, wallahi mai nasara zan danna maka bahagon ashariya, wallahi ka kar kureni yanzun nasa Ahmad ya tsayida motar mu bawa Hammata iska,"
"Haba ina ba dani zakayi haka ba ka kwantar da hankalinka ka kusan bawa jinjira iska da cinyoyinka." ya faɗa mishi,
"Ahmad sauke ni naci uban wannan gaye, zai rena min hankali ɗan iska, wanda girman kai da miskilanci ya hanashi gyara gidanshi."
"Naji ango baby."
Haka mai nasara yayita kuna Aman har suka isa gidansu Aman, aka sauke shi ko kallon inda suke baiyi ba ya banka kofar motar, yayi gaba abinshi sauke glass Mai nasara yayi yace.
"Sauka lafiya ango jinjira,"
Cak Aman ya tsaya, a fusace yayi kam motar, ya buɗe inda mai Nasara yake cikin huci da ɓacin rai ya caccumo Mai nasara zuwa waje.
"Dan Ubanka mi kake nufi dani ne."
Fitowa Ahmad yayi daga motar yana raba tsakaninsu, luuuuuu Aman ya tafi zai faɗi, suka tare shi, cikin tashin hankali Mai Nasara yace.
"Wallahi bana nufinka da kome, asalima zolayarka nake, don Allah ka yafe min, ɓata maka rai da nayi."
Lumshe idanunshi yayi yana jinsu suka ɗauke shi a kafaɗa har cikn gidansu,, Mamie na falon tana waya da yan uwanta da suka taso tun jiya, dan tun da abin ya faru, taci alwashin aurawa Aman Rahilah, ta kira Babban Yayansu Sale Goni, ta faɗa mishi, dake suma gidansu malamai ne, da asuba ya kirata yace aure fa zai tabbata, insha Allah karta ɗaga hankalinta zasu cigaba da addu'a,
Yanzun ma da yayarta mace suke magana sun kusan isowa, dan samako sukayi,
Shigowarsu Ahmad yasa ta yanke kiran ta zuba musu,ido take suka shiga kame kame, dakyar Mai Nasara yace.
"Bashi da lafiyane, jininshi ya hawu sosai, amm..."
"Toh mi yasa baku kai shi gidanshi ba, sai nan."
Tsagalgalesu tayi sannan tasa mi aikinta ta gyara mishi tsohon ɗakinshi aka sake har su zanin gado, da labule da duk wani abin bukata,, sannan ta kira family dr ɗinsu, tace.
"Ku kaishi tsohon ɗakinshi,dake wancan koridon"
Daukarshi sukayi zuwa ɗakin dake zuba kamshi da sanyi daɗi kamar ya.
Suna zaune likitan yazo ya duba shi, yasa mishi ruwa da allurai da kuma magunguna.
Tunda aka samu yayi barci su kuma Ahmad suka tafi gidajensu da niyyar shiryawa zuwa masalaci,
****
Bayan sallar juma'a alummar musaulmin dasukayi sallar juma'a suka shaida Auren Husaina Omer Hayat, tare da Angonta Dr Aman Mohmud Mandara, auren da yazo bazata a cikin unguwarmu dama, yan unguwar suna mana lakabi da bama auren kananun mutane sai manya,
Tunda aka shigo akace Alhamdulillah, an ɗaura auren Rahilah sai gata tana shirin zuɓewa a kasa, sai da aka tareta wani fitinannen kuka tasaka wanda ya taɓa zuciyar kowa a gidan, mukan ai ba'a cewa kome,
Shigar da ita Umma tayi ɗakin Mama Amarya wacce itama ta kunshe kanta a ban ɗaki tana kuka. Kwantar dani Umma tayi a bakin gadon mama,
Buga kofar ban ɗakin Umma tayi, sai gata tafito kanta a sunkuye tana goge kwallarta murmushi Umma tayi tace.
"Gata nan, igiya ukun Aman ya ɗauru akanta, nayi iya nawa sai ki kara mata da wanda zaki kara, amma maganar gaskiya karki bari taga kwallarki dan zaki karya mata kwarin gwiwa,,"
Gyaɗa kai Mama tayi, sannan Umma tafita tsakar gida, inda tasamu ana shigo da kaya cike da mamaki, ganin Yayar Mamie Aman yasa ta sake murmushi tace.
"Hajja Yanah kece a garinmu? Barka da zuwa, ku basu guri su shiga ciki."
Dariya Hajja Yanah tayi tace.
"Malama Hasina,har yanzun kina nan da halinki na karɓan baki, fa mungode da abun arziki na bamu kyautar na musaman mungode."
Murmushi Umma tayi, cikin jin daɗi tace.
"Ai bakonka sarkin ka, batun aure kuma karawa zumuncinmu karfine mune da godiya, wanda zai auri Yarka ai ya gama maka komi, a wannan zamanin da mazan suke tsada, mune da godiya bawai dan yaran sun mana yawa ba, sai dan nasan Hajiya falmata zata iya rike mana Rahilah."
(Da fatan kun fahimci maganar Umma, kalma ɗaya mai kunshe da harshen damo bawai dan yaran sun mana yawa ba, nufinta ba wai muna niman kai da Rahilah bane ko sauran yaran, sai tasan ko babu auratayya Hajiya falmata zata rike Rahilah a matsayin Yarta🔛)
Godiya sukayi sannan suka shiga buɗe kaya, ɗaya daga cikin Auntys ɗin Aman tace.
"Ga kayan nan, amma bana lafe bane, kayan da muke na al'adace wanda akewa Uwar amarya da Uban amarya da danginta, bawai mun kawo dan ku biya mu baɓe, ai kun gama biyanmu tunds kuka ɗauki lu'ulu'u kuka bamu ko hka ma ya ishemu fatanmu nan da wata tara cif abin arziki ya sake taramu, dan mici daɗi, yanda take Husaina Allah yasa tana shiga ta juye mana, huɗu duk shekara muzo suna wallahi bazamu ki ba, ai abin daɗine haka."
Dariya akayi sannan aka musu godiya, tare da abin arziki Umma ta basu.
Har zasu fita, Kanwar Baban Aman Hajja Qoise tace,
"Mu dai bama bukatar, kayan ɗaki idan da gaske ɗaya muke, toh mun yafe, Yarmu muke bukata."
"A'a Hajja ku faɗa mana, inda za'a kai mata, kayanta koda bazatayi amfani dashi ba, itama tayi alfahari da kayan da iyayenta suka mata" Inji Umma,
Haka suka rabu cikin mutunci da fahimtar juna,
*Yaseen nasha fura da nono ya kahe min jiki idan naga da hali zuwa dare na muku amma banyi alkawarin ba* 👐👐
[8/25, 2:59 PM] Real Mai Dambu: Cigaban 8page......
Zama sukayi aka shiga ware kayan, bandir ɗin shaddane masu shegen tsada, sai atamfofi suma haka g wasu manyan liffaya,
Abin gwanin burgewa, kowa sai san barka yakewa su Umma da Rahilah.
****
"Wai duk wannan shirin na zuwa ɗaurin auren Aman ne, duk wancan munafikine ya koya mishi niman mata, Allah yasa bayi nasara akanka ba Ahmad." Cewar Hafsat da take kallon Ahmad na sanya wata muguwar yadin maza.
(Wayyo mai nasara tara matanka yajanyo ana kirania da munahuki😜)
Ganin yaki kulata yasa ta koma gefe, zuciyarta na raya mata tunda Aman yayi aure tabbas Ahmad na hanya, shima.
Mikewa tayi ta isa bayanshi tana goga mishi kirjinta, juyowa yayi fuskarshi a haɗe ya tureta gefe, cikin dakakkiyar murya yace.
"Karki fara tunanin bazanyi aure ba, dan matukar Ummi ta amince min, hmm"
Takalminshi ya zaro ya ɗauki tissue ya goge sannan ya zura sahunshi ya fita.
Tunda yafita ta rasa inda ke mata daɗi, sai safa da marwa akan auren ahmad tabbas zata kona gidan bashi ba hatta amaryan, sai ta babbakasu sai dai tare a jail.
****
Ana gama aurin Auren Aman suka nufi gidansu, ta kofar baya suka shiga wanda Mamie tasa a buɗe sabida abokanshi.
Da sallama suka shiga ɗakin, kowa ya nemi guri ya zauna, kallonshi suke daga shi sai dogon wando da kuma singlet, yana rike da kofin shayi.
"Sannun Ango Husaina Allah ya bada zaman lafiya, kaima yabaka lafiya yanda zaka mike da kafarka."
Cewar Mai Nasara,
"Amin, Hmm dama idan kaji sauki akwai tafiya a gabanmu zuwa china, 4weeks xamu iya dawowa mubarka a can, ka karasa mana abubuwanmu." Kallon Ahmad yayi irin baka da hankalim nan, kauda kai yayi ya cigaba da zukar shanyinshi yace.
"Ina bukatar passport ɗinta, dan zan tafi da abata ce."
"karya kenan, mu da zamu kasuwanci kace zaka ɗauki mace aje da ita sai kace akanta zaka far..."
"Ya isa haka, Yunus bana so kabarni nayi abinda nake so, kai kayi wanda kake so, matata ce fa don Allah ko ban samu mutunci ba, tunda ina sonta katayani mutuntata."
Yana gama faɗar haka ajiye kofin yayi ya ɗauki towel ya shige ban ɗaki, bai fito ba sai da ya ɓata lokacinshi sannan ya fito, shigowa Aman yayi ya ajiye mishi ladar, shadda kala huɗi, farin cikin ya ɗauka yasaka bayan ya gama tsane jikinshi, ya shirya tsaf, bayan ya murza hularshi mai taken minister,.
Cikin gidansu suka shiga nan akayi gaishe gaishe, sannan suka nufi, gidansu Rahilah kallon Mai nasara yayi kafin yace.
"Ina son yan canji a hannuna, sabida shiga gidan biki sai da wani abu."
Mai nasara vai ki ba, ya kaishi banki suka cire kuɗi sannan suka nufo gidanmu, inda akewa Rahilah lalle ja, mai zanen fulawa, dake manyane sai gashi sun mata raɗa raɗa.
Muna ciki aka sheda angwaye sun zo, take gidan aka nutsu, suka shigo har ciki, aka fara gaishe gaishe, rahimah da take waje itace tasami ganinshi, ta window na leka naga ya faɗa, fuskarshi tayi fayau, sai murmushi suke dokawa. Juyawa nayi na kalleta yanda idanunta sukayi jajawur nace.
"Rahilah!!"
Haɗiye kukanta tayi tace.
"Kin manta ko scndry ban gama ba, balle nasan ciwon kaina"
"Haba Rahilah kefa mahaddaciyar alkur'anine fa, da wasu litattafan addini, mi zai ɗaga miki hankali."
"Babu my three." xama nayi a kusada ina jin ana zabga musu godiya sake lekawa nayi nasamu suna rabawa yaran yayunmu kuɗine, ina jin Umma musu ya isa hk, nan sukayi godiya suka tafita.
Bayan sun gama gaisuwar suka fita a kofar gida suka haɗu da Yayanmu nan Ahmad ya tambayeshi ko zasu sami kananun hotonta.
Ce musu yayi su jirashi ya shiga cikin gidan sai gashi da hotunan, mika musu yayi godiya sukayi sosai,
Sannan suka shiga motarsu, mikawa, Ahmad yayi hoton sannan yace.
"Gashi nan ku naima mata, visa china, da kuma dubai ko ni ku nema mata na ko ina ma."
Shiru sukayi babu wanda ya kuma kullashi.
.......
Kayanta da aka kaiwa tela tun dawowarmu aka amso dan har ta cire lallen..
Mikewa nayi zan fita, Aunty Shukura, tazo ta fita da ita komawa nayi na zauna, ɗakin mama Amarya suka mai ita,sabida ɗazun bata iya ce mata kome ba har tasa aka fitar da rahilah.
Tunda ta shiga Yayar Mama ta zuba mata ido, zama tayi kanta a sunkuye cikin hijab.
Mika mata, kofin tea sukayi dakyar ta amsa, ta fara sha, nan suka haɗu suka mata nasiha sosai duk abinda ake Mama bata ce kala ba, har suka gama, kanwar Mama ce ta dafata tace.
"Yaya Atika, kisa mata albarka dan anjima balallai bane a kawota."
Gyaɗa kai Mama tayi sannan tace.
"Allah ya Albarkaci rayuwar aurensu, da zuri'a ta gari ta kuma nutsu a ɗakinta shine alfarman da nake rokonta ,ta rufa mana asiri ta zauna a