Showing 81001 words to 84000 words out of 92699 words
Tura mishi baki nayi cikn masifa nace.
"Baby tana cikin Rahilah, nima addu'a nake nima. Allah ya bani cikin na tarerayi abuna cike da soyayya da kaunarshi."
Dariya ya gintse kamar da gaske yace.
"Kika son cikin ne?"
"Eh mana waye zaiki kyautar Allah, nibisu Rahilah na basu wata huɗu fa kuma gashi itama Rahimah har tasami nata cikin, wai idan nace musu toh ni yaushe zan sami cikin sai suyita min dariya wai har yanzun ban girma bane, shi yasa nske wauta."
Kifa kanshi yayi a hannunshi yana dariya har da tintsirawa ya ɗago kai, cikin nutsuwa yace.
"Kinyi karama da ɗaukar ciki maryama namiji ma ai sai mara imani ne zai far miki shekarunki sun kasa dayawa, ki bari inda kika shiga 20yrs sai na nima miki ciki ko nima zan san yanda ake nima koda kasar waje ne sai na je dan niman ciki."
"Don Allah Daddy da gaske kake, lallai kuwa da na caɓa, kaga kuwa zan shirya mishi abubuwa dayawa idan yazo."
Nan nayita shirya mishi sakarci da shiririta da shirme.
Shiru yayi yana kallona, a zuciyarshi yace.
*Maryam bazan taɓa barinki ɗaukar ciki ba, bazan taɓa niman hakkina ba sai kin isa wacce zata iya ɗaukar damuwar namiji*
"Daddy baka ji ba, nace taya ake ɗaukar ciki?" lumshe idanunshi yayi tare da murmushi yace.
"Toh Maryam taya zan sani bayan nima ban taɓa ɗauka ba sai dai na ajiy.."
Shiru yayi yana kallona, sabida jin zai ɓaro babbar magana, can yace..
"Baku yi biology bane, kuma ai naga ke yar sciences class ce, kuma shime kike tambayana."
Shiru nayi tare da mika nayi hamma nace.
"Daddy mubar wannan maganar a ina zan kwana."
Kinsan karfe tara likita zai shigo zoki kwanta a kan cinyana.
"Nifa bana son kwanciya a jikin namiji dan..." turo kofar da likita yayi sai da na duba agogo yana zuwa ya mishi allura da bashi magani. Sannan suka fita.
Tashi yayi ɓa gyara gadon sannan ya koma, jan kujera nayi na kwantar da kaina akan gadon.
A hankali ya mike ya ksshe wutar buɗe idanuna nayi naji ya kara karfin Ac, cak yayi sama dani ya kwantar dani ya raɓa gefena, tuni barci yayi gaba dani a jikinshi sai da yaga barcina yayi nauyi sannan ya mike ya fita zuwa ofishin likitan, nan ya zauna yayi mishi bayani halin da yake ciki shiru likitan yayi sannan yace.
"Zan baka maganin da zai rage maka kaifin desire ɗinka in ba haka ba gaskiya zakwai matsala kuma ai naga kana da amarya aiko?"
Murmushi Mai nasara yayi sannan yace.
"Tayi karama da yawa, idan nace zanyi wani abu da ita wallahi xan cutar da kuruciyarta kaga kuwa banyiwa Huda adalci ba, dama takai 19 ne da sauki amma 17yrs ba sai next month zata kai 18 haba dubi al'amarin dukda tana da abinda na jima ina nima amma ban taɓa jin naraba da kuruciyarta ba, kamata yayi yanxun tana kokarin shiga jami'a."
Yanda mai nasara yayitawa Dr Femi bayani sai ka rantse da Allah bayahude isra'ila ne tsabar tsantsauran ra'ayi shifa har yau bai taɓa ganin kuskuren da suke takawa a gidanshi ba asalima, ganin kaman freedom ne shiyasa yake son sauya min ɗabi'a irin nasi.
Dukda likitan kirista ne sai da ya jinjina bokon Mai nasara yana da shekaru haka yasami karamar yarinya ɗanya jabga ina zai bar banza tasha shi, magani ya rubuta mishi. Sannan ya fita, bayan fitar Mai nasara likitan yashiga tunanin yanda zai haɗu dani.
Zama yayi yana hango yanda nake tafiya dukda hijab ɗina har kasane bai hana shi, shaiɗaniyar zuciyarshi hango mishi ni ba.
Koda ya dawo kwanciya yayi ya tura hannunshi cikin rigana tare da sauke ajiyar zuciya.
........Da asuba kuwa ina ganin yayi wanka cike da bin didigi nace.
"Daddy Wanka da safe, haka lafiya kayi wanka."
Murmushi yayi ya tadda sallah yana idarwa sai ga Dr Femi ya shigo allura yayiwa mai nasara, ya koma bakin gado ya zauna kallon da likitan yake min yasani komawa kusada mai nasara na lafe. A hankali barci mai karfi yayi gaba dashi. Gyara mishi kwanciya nayi ina kallonshi, sai yayi kamar zai buɗe ido sai kuma ya rufe.
Ban san likitan na dakin ba sai danaji an yaye min hijab ta baya tare da rarumana, ina juyawa na falle ɗan iska da mari dariya yayi ya shafa gurin ya sumbata.
Cikin gurɓatacciyar hausarshi yace.
"Yaro mijinka yace bazai pumpi ɗinka ba kaga ni zanyi maka kuma na baka kuɗiiii."
Yana magana yana lasar bakinshi bansan lokacin da na kare kirjina ba tare da ɗaukar karfen da ake karin ruwa nace.
"Idan kayi gigin taɓa ni sai na kasheka kuma sai nasaka an kona asibitin, baka san waye yake kwance bako zan yi maganinka."
Duk wannan hayaniyar ds muke yana jin mu, kusan mintuna ashirin muna kaura rikice, ji nayi an janyoni juyawa nayi naga Msi nasara ne yarda karfe nayi tare da juyawa na rungume shi ina son kuka, "Shiii maryama ya isa haka ai jinin mijinki ba kowa keda irinshi ba, duk karfin magani mintuna aagrin yake a jinina ya gama aiki, Dr Femi ka gama aiki a garin kaduna salin alin kabar garin nan dan dama asibitin bana ka bane ɗaukar ka Dr Zulaihart rano tayi tayi kuma ka gama aiki daga yau."
Zuɓe gwiwarshi yayi yana rokon mai nasara,amma fir yaki karshe koranshi yayi daga ɗakin, jin yanda nake kuka mi cin rai,
Shiru yayi wato abinda kai ka rena sai Allah ya nuna maka cewa, wani na niman kamar wanda kasamu bai samu ba.
*Wallahi Rayuwarmu akwai gyara ainun gashi mai nasara ya rena maryam akan bazata iya ɗaukar nauyinshi ba sai gashi Allah ya nuna mishi arne yana niman kamarta bai damu ba, koda karfin tsiya zai raɓeta ba iya mai nasara kaɗai keda Wannan halayar ba anfi samu a cikinmu Matan hausa don Allah karku ɗauki Abin burgewa na Novel ku ɗauki darasin dake ciki, awallahi ya tsunmi ba ɗaya bane sannan rayuwar novel ba dukka bane reality dukda akwai true amma mu tuna cewa ba dukkan abinda muke nima muke samu ba musamsn rayuwarmu na Arewa komu ma Marubutan nan muna fuskartan kalubalen rayuwar aurenmu kuma wasu suna tunanin cewa abinda muke sawa kamar dagsk ne A'a ba haka bane munayi ne dan gyara labarinmu nagode sosai da bibiyar labarin👏👏👏*
[8/25, 3:00 PM] Real Mai Dambu: 🌹🌹🍀
*MATAR SO*
🌷🌷🌻
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER'S ASSO*
(HWA)
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....
Sadaukarwa Ga Yan grp ɗin Matar So....
Dedicater To Hafsat Abubakar💋
_Wannan buk ɗin hakk'in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_
*BOOK 1👈*
Sorrƴ for the typing erorr.
Page....25
Sauka yayi daga gadon jiri na ɗibanshi ya ɗauki hijab ya saka min, kallon yanda na makale a jikinshi naki rabuwa dashi yasa shi kara rungumana, wayata ya amsa ya kira Aman rahilah ce ta ɗauka ya ce.
"Kicewa Aman yazo yanzun."
Toh tace.
Takira Aman da yake bangare hindu, ta faɗa mishi da sauri ya nufi asibiti koda ya isa ganin yanda nake kuka gashi na makale mai nasara, sai abin ya bashi mamaki yace.
"Man lafiya?"
Dakyar mai nasara yayi mishi bayani. Hmmm tashin balagan tsintsiye fita Aman yayi yaje gurin babba likintan yayi mishi bayani abinda dr Femi, kuma yau zaisa a rufe asibiti.
Kafin seven na safe manya da kananu na asibitin sun taru ana meeting, dakyar aka shawo kan Aman dan Mai nasara yace sai kotuce za rabasu da dr Femi.
Su kuma asibitin suna ɓoye maganar ne dan kar siyasa tashiga a rufe musu asibiti musaman da suka san Waye Mai nasara.
Abinda sai da aka haɗa da Mahaifin Aman sannan suka hakura, har lokaci ina jikinshi dan gani yake ko ya-ya ya kyale ni wani zai kaimu hari.
Karshe dakatar da Dr Femi akayi na wata shida da hanashi albashin watanin.
Can gurin 8 aka kawo mana kunun tsamiya, da soyayyen dankalin turawa sai farfesun zabuwa ina jin kamshi na dira a jikinshi dan kamshin girkin Mama Amarya ce, gaida ya Kabir nayi wanda yazo ganin gida dan aikinshi a abuja ne, hira sukayi da mai nasara da Aman bayan tafiyar Ya kabir, Mai nasara ya wani tsuke fuska, yana hararana kuma abinci nake zuba mishi fa,
"Kee dawo nan."
Ya buga min tsawa, sake abincin nayi na koma jikinshi na lafe, har da kifa kaina a kirjinshi suka cigaba da hiransu.
Abincin da banci bakenan shima kuma bai ci ba, nayi barci har Aman ya tafi bai tashe ni ba.
Sai kallon fuskana yake yana shafawa a hankali.
A cikin kwanaki huɗu da mukayi a cikin asibitin, naga kayan takaici dan tsakani da Allah mai nasara ya hanani walwala a gaban mutane. Wani shegen kishi ya tsiro mara ma'ana.
Ranar na rakasu Mama Amarya da suka zo gaishi, na jiyo zan koma cikin asibitin sai ji nayi ance.
"Maryam Omer Hayat."
Juyawa nayi naga Uncle Mustapha na makarantarmu, cikn sakin fuska na gaidashi nace.
"Uncle waye kazo dubawa."
"Mata ta ce tahaihu shine na kawo musu abinci."
"Ayya muje naga matartaka."
Haka muka tafi har inda aka kwantar da matar ina zuwa naga babyn naɗe a showel pink ɗauka babyn yayi ya mika min, na kalle matan na gaisheta ina murmushi nace.
"Masha Allah barkallah."
Addu'ar da akewa jarirai nayi mata sannan nace.
"Uncle babyn da Mamienta take kama fa bada kai ba."
Dariya yayi sannan yace.
"Allah ko?ke waye kika kawo asibiti?"
Mikawa matar babyn nayi cikin kunya nace.
"Mijina ne ba lafiya, amma ina ganin anjima zamu sami sallama,"
Sake kallon pink lips ɗin babyn nayi,
"Ayya Allah ya bashi lafiya, zan bi ki nagaida shi." yace min,
Sallama nayi musu sannan muka fita har ɗakin da mai nasara yake, cikin mutunci suka gaisa da uncle yayi mishi ya jiki, a fakaice kuwa hararata yake da wutsiyar idanunshi, har uncle ya fita na mishi rakiya waje tare da godiya yace.
"Dama Yunus marafa ne mijinki, Ah na tayaki murna dan mutumin kirkine."
Gyaɗa kai nayi tare da godiya, sannan ya tafi ina shiga ɗakin yace min.
"Koma inda kika fito."
Kallonshi nayi cikin rashin fahimta nace.
"Kamar ya?"
Na tambaye shi.
Banza yayi dani, dan yaga zan rena mishi hankali.
Shiru nayi na nemi guri na zauna, amma ranshi na kara ɓaci.
Yo ni wallahi ban fahimci haushi yake jiba sai daya sake min magana a hasale.
"Tashi ki koma gurin sabon saurayin da kika yo, wato ni zaki mai da ɗan iska shine har da gayyato min kato kaina, hmm Allah ya bani lafiya zamu haɗu a gaban Ummanki."
Sororo nayi sannan na taɓe bakina na ɗaga kafaɗata nace.
"Wannan damuwarka, ban taso naga ana abu mara kyau a gidanmu ba balle afara a kaina, daga malaminmu yazo gaisheka sai ka nemi jifata da wasu maganarka marasa daɗi,su matanka da suke fita kusan tsirara baka taɓa ihu akansu ba sai ni da nake sanye da hijab da nik'af toh ba damuwa bari naje gurin sahibin ruhin na......"
Bansan wani irin tsalle yayi ba, sai jinshi nayi a kusadani yana huci. Dama kunsan wakiliyar tsoroce jikina ne ya ɗauki rawa.
Zare hijab ɗin yayi cikin wani mahaukacin kishi ya haɗi da bango ya shiga kokarin, ladabtar dani ta hanyar ya mutsa min jiki da zaffafan sakonshi.
Dake ina jin haushi sam banji komi ba sai dai shi da ya gama shirmenshi ya kyale ni, a gurin.
A ranar ya nemi sallama, muka nufi gida tun a hanya na ajiye ɓacin raina na shiga hankalina.
Koda muka isa gidan, ko ina ba daɗin shiga dan ma Ahmad yana sauke mu ya juya, murmushi nayi ganin falon har zai wucce nace mishi.
"Yau zaka ga amfanina."
Na haye sama, wanka nayi na sauya kaya dama nakan zo gida ɗaukar kayana, ko wani abu.
Gyara ɗakina da falona nayi na sauko kasa na gyara kitchen, na ɗaura taliya jallop da irish, sai bushashen kifi na haɗa zoɓo nasaka gwaiba da Qcumbe, gabaki ɗaya gidan ya ɗauki kamshi da turarena da girkina,
Saka zoɓo nayi a firij nasaka hijab ɗina, na fita waje gurin drvn gidan na bashi dubu ɗaya nace.
"Don Allah malam, yahya ko zaka sayo min bevi mix da tiara, na dukka kace su haɗa maka kaloli daban daban."
Karɓa yayi cikin mutuntawa ya fita, bai ɗauki mota basai nacewa Mai gadin ya kirashi na bashi kuɗin mashi yana lekawa ya dawo yace.
"Hajiya har ya tafi."
gyaɗa kai nayi na juya, sai akan idanunshi wallahi sai da gaba ya tsinke, Fareeda na tsaye a gurin, nazo na wucce bin bayana suka ina shiga falo yace.
"Maryam wallahi kina kure ni fa, zan miki shegen duka."
"Toh kayi hakuri bazan kuma ba." nace tare da wuccewa kitchen ɗina, kumfa naga yana fitowa a cikin tukunyar girkina buɗewar da,zanyi kamshi morning fresh ya dake ni. Lumshe idanuna nayi na sauke girkin na kashe gas ɗin, ajiye abincin nayi yayi sanyi sannan na juye a leda, nasaka a kwndon shara.
Wanke tukunyar nayi na ɗauki wata yar karama na dafa indomie da kifin dan raina naso na juye a filet na zauna jiran tiara na kaman ance na ɗauko zoɓon na duba shi kuma gishiri aka zuba min, wankewa nayi na zubar na fito kan dinner table na zauna ina cin indomie dan rashin kunya sai ga Sameer yazo wai "kee ki bani abincin da kike ci."
Murmushi nayi na ɓoye bacin raina nace.
"Kaje kitchen ka ɗauko fork kozo muci."
Dariya yayi sannan yace.
"Ashe kina da kirki ai Mommyna da Mufeeda suka zuba miki morninig fresh da gishiri a cikin a bincinki."
Juya idanuna nayi irin ba damuwar nan zomuci.
Kallon Uwarshi nayi wacce ta buga mishi tsawa sai da Uban yafito dake tarbiyan da suka aza yaron akai knn yace.
"Mommy ai ba karya bane morning fresh kuka zubawa bakuwar Dddy a cikin abincinta, har da drink ɗinta kuka sak..."
"Sameee."
Kallonta Mai nasara yayi cike mamaki, yace.
"Ki biyo ni ɗakina."
Ba musu ta bishi, ban san mi ya faru ba sai dai yanda na gan take tafiya yasani shiga ruɗu. Mi yayi mata take tafiya kamar Yar kaciya.
A ɗakinshi kuwa da ya kirata girma da arziki ya fara mata magana aikuwa ta shiga mishi ɗanye kai shine ya murɗa ya biya bukatarshi tare da doka mata gargaɗi, da kuma horon fita ko ina sai bayan sati biyu.
Ina zansan wainar da suke toyawa ba, sai dai sun fito min ta inda ban tsamanta ba, dan har takai Mufeeda takan iya kallon idanuna na tace min karuwa,
Ranar a gabansu Fareeda ta faɗa min.
"Karuwa kawai wacce take kazamta da Daddy ko an ce miki banga kina saka bakinki na nash...."
Faɗuwar abu muka ji a bayanmu ashe ya shigo gidan, wayarshi tana cikin vibrater zai ɗauka yaji abinda yarshi take faɗa sai da wayar ta tarwatse gida biyu, kaman zaki haka yayo kan Yarinyar ya shiga kwallo da ita tare da fincikar wayar kayan kallo ya shiga zabga mata inda yake shiga bana yanke fita ba, shegu munafukai guduwa sukayi, tun yarinyar na kiran Mommy kozo daddy zai kashe har tayi shiru bai fasa, haka uwar yarinyar tazo ya haɗa da ita da gudu tabar gurin.
Bayanshi naje na runguma tare da kwantar da kaina nace.
"Mai hakuri yana tare da Allah, duka ko zagi bashine tafarkin shiriya ba, addu'a da kai wa Ubangiji kuka shine jigon shirya, sai tarbiya tasamu yanda ake bukata."
Tsit ya tsayar da dukan tare da juyawa ya kamo hannuna ya kalle ni, cikin wani irin murya ya buɗi baki zai magana amma ya kasa, ɗakinshi na mai dashi na zaunar dashi, ruwa na ɗibo mishi na bashi yasha. Sannan na xauna ɗaura kanshi yayi akan cinyata jin ɗumin ruwa yasani shafa inda nake ji a she kwalla yake zubdawa.
Shafa kanshi na shiga yi, har naji yana sauke ajiyar zuciya, zuwa wani lokaci naji shiru kwantar da kanshi nayi a pillow na fita waje, babu wanda yayi yunkurin zuwa gurin yarinyar wacce ta suma, ruwa na ɗauki na watsa mata, ta fasa kara tare da ɗaga hannayeta, mikar da ita nayi na kaita ɗakina na haɗa mata ruwan wanka tana dawowa hankalinta taga nice..
"Muguwa azzaluma, karuwa na faɗa miki na kuma faɗa miki naga lokacin da Daddy yake taɓa nononki mayya...."
Bansan ya fito yabiyo ni ba, sai ganinshi nayi a tsakiyarmu, sabon kuka ne ya kamata, ya riko hannunta wanda tsabar rikon sai da tasake fitsari ya kaita ɗakin Uwarta ya cillata kan balkisun da suke Waya da Mama kilishi tana faɗa