Showing 75001 words to 78000 words out of 92699 words
kana son Maryama amma kake bawa kanka wahala."
"Kaii Wallahi ko sau ɗaya bana sonta, dai ina jin ba daɗine akan rashinta, ka yarda dani."
Wani irin kallo Aman yayi mishi, me ɗauke da renin sense, ga soyayya kuru kuru har da rantsewarshi taɓe baki yayi ya buɗe motar zai fita.
Mai nasara yace.
"Aman kaima juya min baya zakayi?"
Murmushin gefen baki Aman yayi sannan yace."Kowani cuta da maganinshi sai dai mituwa ce babu maganinta Yunus You are in love amma kake musanta min magana well zan baka shawara kaje zaria ka samo kanta idan haka ta faru zan baka final shawara."
Yana gama faɗa haka ya juya yafita,
Jan motarshi yayi sai zaria,nan ya tarda kwandon bala'i har sai da ya kusan zubda kwalla.
"Wato dan ka maida mu marasa mutunci shine muka nemi sakin kaki bada ko Yunus ka bani sakin Yar mutane ko na saɓa maka, wai shin mi kaida Mutane ne abokan wasanka har kana sake ɗayar matarka muda muka ce ka bamu sakin maryam sai ka saki Fareeda toh bani takardan Yar mutane mara mutunci saɓo tumaki ɓallo jaki bani, kaje mugun halinka ya taimakeka."..
Shi kanshi abin duniya ya dame shi, muka ya kasa magana mikewa yayi ya bar falon Alhaji, zuwa falon Hajiyarsu nan yayita raba ido bai gani ba,
Karewa mikewa yayi zuwa ɗakin hajiya ya sami ɗakin Wayam, babu ni babu alamata.
Gurin Mama ya dawo tace.
"Kazo dubawa kotana nan ne? Toh mun ɗagata daga gidan nan kafin ka shiga rayuwarta."
"Amma..."
"Dakata fitan min a ɗaki kaje can..."
Fata fata suka mishi dawows kaduna yayi ya kira Aman ya faɗa mishi, halin da Yake ciki.
Dariya Aman yayi yace.
"Ka wucce gidansu kasami Iyayenta da maganar, zaka sha mamaki yau duk inda Maryama take a chest ɗinka zata kwana.".
Kashe kiran yayi ya nufi, tudun wada, a kofar gida yayi parkin ya tura yaro akan mijin Maryam ya zo.
Ya kabiru ne yazo ya shiga dashi cikin gidan, aka shimfiɗa mishi taburma ya zauna, gaisawa sukayi da Umma da Mama.
Cikin nutsuwa ya faɗa musu halinda yake ciki, tare da nuna musu shine da laifi amma iyayenshi sunce ya sake maryam don Allah ayi hakuri bazai kuma ba.
D'aga labule umma tayi taga karfe biyu da rabi, kallonshi tayi kafin tace.
"Zuwa karfe shida na yamma Kabir zai kiraka."
Godiya yayi sosai sannan ya tashi zai tafi ya ciro kuɗi zai ajiye tace.
"Yunus ɗauki abinka, mu y'a muka baka ba abin hannunka muka duba ba."
Duk yanda yaso ta amsa amma fir suka ki karɓa koda suka fita da Ya kabir sun taɓa hira har zuwa matakin karatu, mika mishi card ɗinshi yace.
"Kazo da takardunka, dama muna niman wanda zai zauna mana a kamfaninmu na Abuja kuma mun samu."
Godiya kabir yake kaman yayi ihu dan murna, haka sukayi sallama,
....... A cikin gida kuwa ɗaukar waya Umma tayi takira Mamie suka gaisa, cikin tsautsayi Mamie tace.
"Maryam Sajida, duba min miyar nan nakan gas,"
"Toh Mamie"
Aikuwa kashe kiran Umma tayi tasaka hijab dinta sai gidan Mamie, muna tsaka da hira mamie na faɗa min.Umma takira fa, take naji yan hanjina sun kaɗa.
Muna cikin maganar ta shigo da sallama bayan Mamie na b'oya.
Tunda tayi sallama suka gaisa Mamie ta kama hannunta suka shige ɗaki,har kusan la'asar basu fito ba.
Koda suka gama kai ruwa rana, suka fito wani mugun kallo tayi min sannan tace.
"Rahilah da Rahimah kowacce tana makale a ɗakinta dan.rufin asiri shine dan kuskure irinta ɗan Adam kika, fito zaki kashe aurenki Hmmm Maryama ki zauna ai daɗin abin bake ɗaya na haifa ba."
Tana gama faɗar haka ta juya kan Mamie tace.
"Yanzun Yunus zaizo ɗaukarta."
"Wayyo Allah Umma kashe ni zaiyi."
"Allah ya jikan wanda ya rigamu gidan gaskiya, karewar kasheki ya jefa ki cikin rami."
Kuka nasaka da ihu har da birgima haushi ya kamata ta samu tayo kaina ta shiga niman dukana mamie ta shiga tsakaninmu tace.
"Wai don Allah ke baki da zuciyane dukarta yayi fa har akan nono kuma ana hukuntashi kice zaki maida mishi da ita."
"Hajiya Falmata knn mata dubu nawa maza suka na kasa, kinga sun taɓa barin gidajensu, yayi kuskure kuma ya gane hakan da yayi bai kyauta ba, tunda ya iya zuwa gurinmu ai yasan mune zamu saurareshi ba tare da duba girman abinda yayi ba, ki fahimceni akwai hujjana nayi haka, Wallahi matukar maryam ta koma ba zai taɓa ko farcenta ba, ina faɗa miki gaskiya ne ai ya kawo kanshi inda bazai iya fita ba, wallahi na ratse miki da Allah idan har maryam Yunus ya taɓata toh bani ce na haifeta ba, ta shirya zai zo yanzun."
Fita Umma tayi, na cigaba da kuka, Mamie na rarrashina tare da nasiha,
Umma tana isa gida ta saka kabir ya kirashi yaje ya ɗaukeni, a gidansu Aman.
Yana gurin cin abinci amma haka ya mike yabar abinci, bayan ya biya,
Kayana tsaf Mamie ta shirya min tare da karamin wasu turaruka tace.
"Mamanku na zaria tace na haɗa miki, kiyi hakuri zaki ga ribarshi nan gaba."
Muna cikin haka yayi sallama, kuka nasake, taramu Mamie tayi har da hannunka mai sanda.
Daukar jakana yayi duk biyu ya fita dasu, ina kuka mamie ta rakoni har jikin motar, tayi mana fatan alkhairi.
Muna fita, tunda muka hau hanya nake kuka, mai mugun karfi kaman zan cire mishi kunne, parking yayi a gefen titi, ya zuba min ido, ina jinshi ya kamo hannuna na fauce cike da tsiwa nace.
"Dalla malam shika min hannuna, Musa a fiska fir'auna a zu..."
Jnyoni yayi da karfi ya shiga sumbatar fuskana, aikuwa na ware muryana na fasa ihu, matseni yayi da jiknshi, yana sauke a jiyar zuciya.
Fitina nasaka mishi sosai dan haka yaja motar muka bar gurin, muna isa gidan na shige abuna nabarshi da dakon Kayana, kafin isa cikin gidan na share fuskana, sabida haɗuwa da nayi da Sameer.
Ina shiga nasamu tumakin sun zuba min ido irin."Maaaaaaaaaaah) ɗin nan dariya nayi a raina nace.
*Kaiiii Amma mutumin nan ya kurewa iskanci maneji, duk tulatulan matan nan na shine."
A fili nake dariya ina kallonsu na haye sama abuna, ina shiga falon sama na haɗu da wata bijimar saniyar, a kwance tsabar mulki sau ɗaya ta kalleni murmushi tayi min nima na maida mata da shi.
Buɗe ɗakin nayi naganshi a rufe, lekawa nayi cikin sakaltaciyyar murya nace.
"Daddy ɗakin a rufe yake fa."
Gani nan zuwa, haka kawai naji a raina na bashi wahala zare hijab ɗina nayi dama rigar da ake min dilke ne, mara hannu, sauka nayi har inda yake na kalleshi da kyau na kalle step, dai dai fuskarshi naje har da d'igelgel nace.
"Wallahi goyani zakayi kuma ka ɗauki kayan dani."
Zaro ido yayi nima na ware mishi nawa tare da tura baki nace.
"Zan kira Hajiya kuwa."
Ba musu ya juya na ɗanne bayanshi, tare da aza kaina a kafaɗarshi nace.
"Kasam mi na tuna, hawa dokin da mukayi."
Mikewa Farida da Aneesah sukayi cike da mamaki kuma ya ɗauki bags ɗina, "Barka tulatulai kunsan sha'anin auren Yarinya karama knn musaman jinjira irina wacce bansan komi ba sai Yunus mai nasara ko My sweet bom."
Shiru yayi ya haye dani sama, muna zuwa kofar ɗakina na dira dan ina jin kunyar Balkisu, ko ba komi Mahaifiyar Huda tace.
Buɗe kofar ɗakin yayi na shiga ciki na fasa ihu tare da cewa.
"Home sweet home, muaaaaa mai room nayi miss ɗinku."
Tuɓe rigar nayi babu bra sai pant na shiga ban dakina na fara wankewa, sannan na fito na cire zanin gadon na gyara na share ɗakin, mika nayi a gabanshi tare da kallon fuskarshi a raina nace.
"An daina latsani a bati."
Towel na ciro a wardrob na ɗaura na fito karamin falona na gyara tass, sannan nabi falon da ɗakin da turarukan wuta sannan na wucce ban ɗakina nayi wanka.
Yana ɗakin, ni kuwa ina fitowa na zare towel ɗin na shirya akan idanunshi. Wani mai Mamie ta haɗa min ina shafawa jikin boons ɗin na shafe tasss abuna na tashi doguwar riga mai tsagu har cinya nasaka, da zan fita na kalleshi nace.
"Mr Man dasaka nayi ne a ɗakin."
Firgita yayi ya dawo hankalinshi, durkusawa nayi nasaka belt ɗin takalmina dan flat ne mai belt.
Sannan na fito nabarshi, kitchen ɗina na nufa na zauna na gyara komi na ciki. Sannan na ɗaura abinci, dai dai cikina sai gashi ya sauko wani tsare gida yayi shi nan baya son wargi ni kuwa na sake tsuke fuskana na cigaba da aikina dan na bar irish ya soma lalacewa dan ma yana kasanr.
"Zaki gyara min ɗakina." ya faɗa min, na ɗago da xumar mai da mishi magana naga inuwar mutum a dinner area mikewa nayi nazo na sumbaci fuskarshi nace.
"Ɗaukeni ka kaini ɗakin, ko kuma na fasa."
Ɓata rai yayi sosai na baya son reni, "ɗazun bana goyaki ba, ynz kuma na ɗauke ki, mi kike nufi."
"Eh toh sai nakira Hajiya na faɗa mata, kasa umma ta ɗsukoni bayan kunmin shegen dukan" na faɗa mishi babu wasa a fuskana.
Irin abinda ya tsana knn, kuma gashi nan za'a rena shi, ɓata fusks nayi tare da ta karkarewa na zabga ihu.
"Wayyo Allah na...."
Saɓani yayi kawai a kafaɗana, ya jingina kanshi da Ukwu, ɗina aikuwa na ɗaura kaina akan hannuna, nayi tagumi kamar yanda Piona tayiwa shrek, da ya ɗaukota daga gidan da aka ajiyeta.
Haka muka wucce su Aneesah har ɗakinshi ya kaini ya jbgeni a gadonshi nayi maza na sauka ya fincikoni tare da matsaeni da kirjinshi yana tsare fuska, tura mishi baki nayi nace.
"Nikan ka kyaleni lokacin da kaxaneni bakayu tunanin zaka zo kana lallubar jikina ba, sai yanzun, dan ka ganin ni karama shine kake cutar dani, tunda nazo gidanka nake zubd...."
Tsit kuke ji, gam na rike rigarshi tare da rintsa idanuna, kwalla ne suka shiga sauka a idanuna, gyara min kwanciyar yayi jikinshi na rawa, taɓ nace a raina.
Lokaci ɗaya Mai nasara ya gigice, niman rabani da kayans yake, nayi maza na dakatar dashi da sauri,
"Kaga nifa ban isa ɗaukar namiji ba, hallo dai ni kazama ce.gashi na renaka bayan ka kusan haifana na don Allah ka rabu dani Mai Nasara Free me mana, dolene sai ka taɓa ni."
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya janye daga jikina, ina hango inuwar mutum ya gillama, tashi nayi na shiga gyara ɗakin, yana zaune a bakin gadon ɗakin harna gama nace zan gyara gadon ya mike, ban ɗaki na shiga naga yanda komi yake zaune da gindinshi fitowa nayi cikin tsiwa nace.
"Kawai period nake kasa bulala ka zane ni Inner wear ɗinka ma sai nice zan wanke maka."
Tsura min ido yayi a sanyaye. Bai ce komi ba na cigaba da cewa.
"Wallahi karka kuma kirana kazama dan kaima Babban kazamine, sai anyi magana kaita kallon mutane kaman anyi maka karya."
Cizon lips ɗinshi ysyi tare da kishingiɗa ya ɗaga min gira ɗaya, komawa nayi ina mita har na gama wankewa na fito da shanyar nabi ta kitchen ɗina akwai kofa naje inda na ɗaura igiya na shanya mishi kayansa na dawo, ganin gas ɗina nayi a kashe naga an juye abincin da ns girka dukka.
Karan spoon naji asama na haura Aneesah da Fareeda suka juye abincin suke ci.
Zuwa nayi na fauce abincina cike da tsiwa na juye nayi kasa dashi, tsabar ina cike dasu, na zauna na juye abina na cinye. Na rufo kitchen ɗin.
*****
Zaman gidan mai nasara wani irin rayuwa akw mai kama da ta dabbobi karku ga laifina dan na faɗi haka,babu addini sai boko zalla shima dai samakal, wani karamin banasaren ne,
Wani tashin hankalin da na fara fuskanta shine da zaran mun keɓe dashi zanga inuwar mutum a gurin a ɗakina ko anashi ko kitchen ya biyo ni dan ya sani wani abu za'a bibiye mu.
Ranar na shiga gyara mishi ɗaki, dake ɗakinshi akwai karamar korido, inda yake ajiye shoes ɗinshi.
Mura ke damunshi na masa farfasun kan rago, sai tea irin namu na yan nijar na kai mishi, sai kuma ruwan da zaisha magani, ina zaune ya mike na kawo mishi brush ya wanke bakinshi a wani roba na maida toilet, ina fitowa naga mutum a window komawa ban ɗaki nayi na taro ruwan zafi, na surka nazo na watsa a window dama na faɗawa Rahilah tace haka Hindu ke mata, sai da ta watsa mata ruwan zafi ta daina,
Aikuwa mufida ta fasa ihu.
Tare da yarda abu, da gudu ya fita yasamita fuskarta ta rike ga Tap ɗin Aneesah a kasa tana ɗaukarmu a video, ɗaukar tap ɗin yayi ya shiga duba ciki hotunarmu dashi da abinda yake min ne, a ciki komawa yayi da baya ya jingina da bango kamar zai faɗi nay maza na amshi tap ɗin, wasu kwalla ne ya cika min ido, na mika mishi tap ɗin zan fita yayi maza ya maidani cikin ɗakin yasa key ya rufe ni.
Dama ihun karya ce, tuni ta fita da gudu, munafukan na zaune a falo.
Ya fito daga shi sai wandon shadda, fara abinda na fahimta dashi mutum ne ma'abocin saka fararen kaya ko kaftani zai saka da farar riga zai haɗata.
Sai farin singlet ya fito, ya mikawa Anesah tap ɗinta yace.
"Ku bani wayoyinku da laptop ɗinku, ynx nan kuma mata ta kuskura ta goge wani abu takwana da sanin abakin aurenta."
Mikewa sukayi kowacce ta mika mishi wyar kuma yabisu ya amshi, laptop ɗin ya shiga bincike abin takaici Aneesah ta ɗaura hotonmu a Whatsp tana faɗa musu kunga wani romantic.
Duk abinda yake min, ajiyar zuciya yayi sannan yace.
"............3186k kuka samu kuyi maneji zamu jone gobe😂😉 Iyalan Inna Wuro masu kaunar Raruka.........😂
[8/25, 3:00 PM] Real Mai Dambu: 🌹🌹🍀
*MATAR SO*
🌷🌷🌻
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER'S ASSO*
(HWA)
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....
Sadaukarwa Ga Yan grp ɗin Matar So....
Dedicater To Hafsat Abubakar💋
_Wannan buk ɗin hakk'in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_
*BOOK 1👈*
Page.....25
....Murmushi bakin ciki yayi yace.
"Daga yau na haramta muku fita ko ina sai kun faɗa min mi yasa kuke ɗaukar sirrin gidana, kuke ɗaurawa A media idan kuma bakuyi magana ba zan baku mamaki, sannan miye hujjarku nasaka Min Y'a irin wannan halin na rantse da Allah sai na baku mamaki, kune baku san halina ba, amma ku tambayi Maryam tafiku sanin waye ni."
Yana gama faɗar haka ya juya ɗakinshin, ina zaune a tsakiyar gadon na tusa kaina tsakiyar cinyoyina ina kuka,, sosai ranshine ya kara ɓaci yayi waje sama yayi inda ɗakin balkisu yake sameta a kan a yanda tasaba zamarta a karamin falonta mufida na uwar ɗaki.
Shiga yayi ganta a rakuɓe tana ganinshi ta fara kuka, sai ya rasa mi zai mata kawai, sai ya kyaleta yafito ya tsaya akan balkisu yace.
"Allah ya baki amanar Yaranki dan su zama hujja gareki ba hujja akanki ba, amma sam baki san da haka ba."
Yana gama faɗar haka ya juya yabarta a gurin.
.......Shigowa yayi ɗakin ya hauro gadon, tare da rungumeni yayi sosai na sake fashewa da kuka tabbas Mai nasara baya kaunata yafi sona yafi son Iyalinshi akaina.
Sai da muka kwashi sati kusan biyu bana iya sake jikina da kowa dama kuma kowa tsabgar gabanshi ya isheshi.
Zaman gidan ya gundireni sosai bana son shiga harkan kowa sai na gabana.
Shima bayida lokacinmu dan tunda ya warke ya fara tafiye tafiyen kasuwancinsa.
*****
Na zata matsalar ta kare min, tun daga wancar lokacin ashe da sauran rina akaba, abinda ake min shine sai ina kwance ko ina karatu za'a kure radio a gidan, ans jin majujala, ko ayita ihu da hayaniya.
Sau biyu ina musu magana basu saurare ni ba, sai na daina zama a falona sai na shige ɗakina.
Idan na fito kuwa Aneesah tace.
"Wallahi da kafarki zaki bar gidan nan dan sai na saki kuka. Kamar yanda kika ja min aka hanani zuwa aikina."
Murmushi nake mata na wucce abuna,
Bansan tsiyarsu takai haka ba, sai da suka rutsani a kitchen zasu dake ni, kowacce da bulalarta, sai gashi kaman wanda aka turo shi. Wallahi na gama tsorata sosai amma dake makiraine sai suka san yanda suka ɓoye abin sukayi nidai da Allah ya kwace ni na haɗa girkina suka fita, ina gamawa na saka mishi na wucce ɗakina.
Sam shima ya sake dawo da halinshi na, miskilanci da masifa dan kuskure kaɗan zanyi zai balbaleni