Showing 33001 words to 36000 words out of 92699 words
ji, ku yan matan nan idan na faɗa muku, zaku iya lalacewa kawai ku sharw batun amma abin ba'a cewa kome dan naga zahirin Yaren novel."
Tana gama faɗar haka tajuya musu baya, can barci yayi gaba da ita, suma mikewa sukayi suka gudu gida, sabida Umma ta kirasu idan tasani xata iya saka musu kuka,
Sau uku mamie na lekowa ɗakin, bata tashi ba.
****
Tunda ya isa gurin aikinsu yake ta doka murmushi, Ahmad ne yace.
"Kaiii Ango, da alamu ka sha gara kenan."
Lumshe idanunshi yayi a hankali daren jiya ya shiga dawowa mishi, hango surata yake, ji yake kaman yaje ya saceta yayi ɓoye.
"Baxaka gane bane Ahmad akwai banbanci tsakanin kananu da manya, zan maka fatan samun irinta."
Tunda suka fara maganar mai nasara ya ɗago ya kallesu daga haka bai kuma ba, dan yasan sai ya iya janyo da baisan yanda zai da ita ba,
......
Biyu da rabi, ta farka ta zauna yanzun kan bata jin kome, ban ɗaki tashiga tayi alola da wanka tazo ta gabatar da sallah, tana idarwa Mamie na shigowa, ajiye mata abinci khalisat tayi, ta fita zama mamie tayi tace.
"Dauki madaran nan ki fara sha."
Kofin madaran ta ɗauka ta shanye, abincin mamie ta bata taci a nutse, tana idarwa ta mika mata, fruit wanda aka, aka zuba mishi zuma da madaara.
Sosai tasha fruit ɗin, sannan mamie ta shiga ban ɗaki ta haɗa mata ruwa tayi wanka wanda aka zuba sinadarin kamshi tana gama ta turata ciki,
Ta jima tana wanka sannan tafito, mika mata humra tayi ta cigaba da shafawa goga wanan share wanca, tsuguna anan, kafin su gama la'asar tayi alola tasake tayi sallah kafin me kwalliya tazo tayi mata, wani shegen lace aka bata tasaka riga da zani, royal blue, ɗinki buba, yayiwa rahila mugun kyau, ga kwallaiya,
Karfe biyar aka gama mata, sai gasu Sajida suma sunzo, tare da wasu yan uwansu, Walimah akayi a gidan,
Sai shida aka watse, shida da rabi su sajida suka bar gidan, inds suka rabu da kuka,
Karfe takwas Aman ya shigo ya gaida Mamie da yan uwsnta,
Mikewa yayi ya tafi falon Babanshi, a can suka zauna suka sha hiransu, shigowar Mamie da Rahilah ya ɗauke mishi hankali.
Tunda tashiga kanta da lulluɓe, ta gaida Abba bata sake ɗago kai ba, nasiha aka musu mai shiga jiki sannan mamie ta maida Rahilah cikin yan uwanta wato ɗakinta sabida Aman😂
Haka aman ya sato jiki zaui musu kdnapper Rahilah yasamu mamie ta toshe hanyar.
*****
A can gidanshi na g,r,a akayiwa Rahilah jere dukda akwai kome cire na gidan akayi aja jera mata nata, suna fitowa, Hindu tace.
"Sannu karuwai, kunzo kunjera kayan karuwar kanwarkun ce, bayan yagama tsince budurcin tun a waje."7
Ta zata zasu tayata hauka ne sai taga sunbawa iska ajiyarta haka suka fita suka barta.
Babu wanda ya faɗawa Iyayensu dubi da halin da Amarya ke ciki.
.........
Washi gari yan maiduguri suka fara shiri, sai ga kayan gara daga gidansu rahila.
Abin ya burgesu haka mamie ta ware musu nasu suka tafi da shi.
**** Sosai mamie ke gyara Rahila ciki da waje ta murje tayi kyau, musaman da take shan fruit
Kwana goma dayin bikin mamie ta koma, islamiya, dama tunda ta koreshi bai sake dawowa ba sai yau daga gurin aiki ya shiga unguwar sayayya yayo mata,
Murmushine ya kwace masa tunawa da yayi....,.
[8/25, 2:59 PM] Real Mai Dambu: Cigaban page 9....
Kishingiɗe yake a falonshi ya saka laptop ɗinshi a gaba, yana buda abubuwan bukatar da zasuyi amfani dashi, a china wayoyi ukune a gabanshi ɗaya ce karama sosai, duk sauran biyun manyane.
Karamar cikin ce tayi kara ya ɗaga, ya kara a kunne cikin sanyin murya yace.
"Barka da hutawa Alhaji."
"Yawwa Babana gani a kaduna abin arziki ya kawoni da fatan bazaka watsa mana kasa a ido ba, idan ka sami lokaci kazo gidan da Abokinka aman ya auri yarinya mun gama magana akan sauran Yan matan nida Alhaji Saminu bature Kawun abokinka mun nima muku auren Yan matan kai mun nima maka Maryam Sajida, ita Hassana Rahimah wa Ahmad, nan da wata uku."
"Hmm" iya abinda ya cewa Alhajinsu knn,
Yayi jifa da wayar ranshi a ɓace, *Ba dai yan uwan jinjiran da Aman ya aura ba, amma gayen nan anyi ɗan kutm ɗan iskan mutum yajanyo min reno.*
Abinda mai nasara yake faɗa knn yana nanatawa, karshe kashe laptop ɗin yayi ya mike zuwa ban ɗaki.
****
Tuna baya...
"A gaskiya Hajiya anci mutuncin yaran nan da mahaifiyarsu, ni dama Bakar nake so mai nasara ya samu ko za'ayi dace ta sauya mana alkiblashi." Inji Mama kilishi.
"Naji bakin cikin abinda ya faru, sam yaranmu aure suke ba tare da sunsan matan suka dace ba dasu, kalli tijaran da Yarinyar nan tayi gashi abin ya juye mata ta kare da kishiya."
Haka suka cigaba da tattaunawa, har Alhajinsu Mai nasara ya shigo nan suka mika mishi bukatarsu na nimawa mai nasara auren maryam sajida,.
Zama yayi yasa aka masa bincike akansu sannan ya tafi nimawa mai nasara aurenta yana zuwa sai ga kawun Ahmad wanda Hajiya firdausi ta turoshi nimawa Ahmad auren rahimah an tsaida magana nan da wata uku.
****
Bayan tafiyarsu muka shigo gida zama nayi a kusada Mama Amarya kaina a kafaɗarta nace.
" Mama ku barmu muje gidan two mana,"
Murmushi Mama tayi cikiɓ kewar Yartata tace.
"Babu ruwana, ai kinji abinda Malam yace."
Shiru mukayi Rahimah ta kalleni kallon geran kayan niman aure nayi nace.
"Mama auren waza akuma."
Kai tsaye tace.
"Keda Rahimah."
Mikewa mukayi sai ɗakinmu muka zauna, muna jimamin Rahilah ashe namu na tafe.
****
Parking mota Aman yayi ya fito, a hankali sanye yake da london suit, wani dark blue har wani haske yake suit ɗin rigar cikin suit ɗin sky blue, takalmin kafarshi bakine sai a gogon da yake ɗaure a tsintsiyar hannun na arzufane,
Kwaso kayan yayi ya shige cikin gida, tana zaune a falon ita ɗaya tana cire lallen hannunta ya shigo da sallama, mikewa tayi ta fara kokarin saka hijab ɗinta,
Sannan ta amsa sallamar tare da cewa.
"Barka da zuwa, Ya Aman."
Lumshe idanu yayi sakamakon karewa jikinta kallo tana sanye da, doguwar riga na English wear mai dogon hannu, karɓan kayan ta isa gabanshi zatayi ya ajiye a gurin ya rungumeta, tare da sunsunar kamshinta wanda yake tafiya da nutsuwarshi.
Kanshi ya ɗaura, a kanta yace.
"Barka dai Cutie. Ya kwana biyu ko kiyi kewana, kin barni can inata azabtuwa da kewarki."
Shiru tayi kanta na kirjinshi, jin sautin bugun zuciyarshi take, a can kasan makoshinsa yace.
"Taimaka min ki cire min wannan kayan nauyin, na gaji sosai."
Bottums ɗin rigar ta shiga cirewa, dukkansu kanta asunkuye ɗago kanta yayi ya bata karamin sumbata a goshi, sannan ya riko hannunta suka cire nitie ɗinshi zarewa yayi ya ajiye a gefe, sannan ya riketa sosai yana kallon yanda ta rufe idanunta yanda gashin idanunta dana giranta suka kwanta, sai goshinta suma sun kwanta luff, gwani ban sha'awa.
"Yunwa nake ji," ya faɗa mata a hankali.
Sake shi tayi, jiknta na tsuma, sabida kwana biyu haka kawai take jin wani feelings sosai musaman idan ta tuna, ranar da ya rutsata sai taji tsigar jikinta na mikewa,
Abinci ta haɗo mashi, da duk wani abun bukata ta kawo mishii, zama yayi tayi serving ɗinshi tuwon shinkafa miyar eguse, sai farfasun bindin saniya.
Zubawa cokalin da tasaka mishi yayi ido kafin ya ɗago yace.
"Plss ki bani naci."
Mikewa tayi ta koma kitchen ta wanko hannunta, zama tayi ta shiga bashi abincin lomar farko ya rike mata hannu da hakorinshi.
Sakewa yayi ganin wani shu'umin murmushi da tayi mishi, a haka tayita bashi abincin, daga ya rike mata hannu sai ya tsiri tsotsan hannunta, a haka har suka gama ta kwashe kayan zuwa kitchan, wanke hannunta take sonyi amma sai ta tsinci kanta da lashe hannunta itama tare da tsotse hannun.
Rungumeta yayi ta baya, tare da saka kanshi wuyarta a hankali yace.
"Kina son lasar hannunki shine baki faɗa min ba, nabar miki."
Yana maganar tare da goga mata hancinsa a wuyarta, rike hannunshi tayi gam sabida sakonshi dake shiga jikinta, juyata yayi ya haɗe bakinsu yayi ya shiga bata wasu irin kiss, wanda masu matukar shiga jiki.
Zare hajib ɗin yayi ya wurga kasa, a hankali yayi sama da ita, sai ɗakinta ya direta a gado runtsa idanunta tayi, ɓalle shirt ɗin rigarshi yayi ya rufa mata, sosai yake juyata son ranshi,
Shiru tayi tana rike da kanshi da yake wuyarta, duk tafita hayacinta sabida maganin da Mamie take bata ya gama bin jiknta sosai, wani irin yanayi take ji, mara misaltuwa dakyar take jan numfashi tare da rumgumeshi.
Jin karan get yasashi mikewa da sauri ya fita ya gyara kayanshi kafin mamie tashigo, zama yayi kaman maraya har mamie tashigo kallonshi tayi tsaf ta hango rashin gaskiyarsaa kitchen ta nufa taga Hijab ɗin Rahilah a kasa.
Fitowa tayi ta zabga mishi harara sannan tace.
"Bana ce sai na nime ka ba,"
"Eh mamie na kawo mata wayartane." ɗaukar jakar yayi a ajiye sannan ya saka takalminshi yace.
"Sai anjima."
"Malam kuɗin turarena"
Juyawa yayi yace.
"Ai tuntuni na turo miki."
Fita yayi yana murmushin saura kwana huɗu yayi kidnafi(😹)
****
Kusan kwana uku kenan tunda aka kawo tambayarmu da sadaki babu wanda yazo a ɓangare maneman. Duk mun addabi kanmu da tsoro da fargaba, kullum Nasiha Mama ke mana, domin Umma tace tayi mana bata da lokacin mana wani abu,
Gashi wani tsirfa ada ke mana nasamu lalle,yana gogewa zamuyu wani.
.......
Zaune yake shidasu Aman yana son faɗa musu amma yasan dariya sasu mishi wayar Ahmad ne tayi kara, ya ɗauka, sabida ganin First lady.
Gaisawa sukayi da umminshi sannan yayi shiru sai murmushi yake dokawa, kallon Aman yayi godiya ya shiga zuba mata sannan ya katse kiran.
Cikin wani irin murmushi yace.
"Kaiii mutumina, ashe mun kusan zama ango, kaji an nima min auren kanwar matanka."
Tsume fuska mai nasara yayi dan kar ahmad sakoshi cikin zance dariya Aman yayi yace.
"Ina passport ɗin matata, tunda tafiyar ta amjima ce, gara na rike abuna a hannuna. Kafin nasatota."
Murmushi ahmad yayi sannan yace.
"Ai bani ɗaya bane har da Mai nasara aka nimawa maryam."
Mikewa yayi a fusace zai bar gurin Aman ya ɗaga murya yace.
"Ango jaririya har zaka tafine Allah ya nuna mana karshen miskilanci."
Ko ɗaga kai bayi ba haka ya shiga motarshi yabarsu a gurin...
......Karfe bakwai da rabi yana zaune a gaban Abbanshi suna hira Mamie ta shigo gaisheta yayi sannan yace.
"Mamie ina son kai Rahilah, gida ta gaishesu naga kamar tana kewan gidan."..
Shiru tayi kafin tace.
"Eh nima ɗazun nasameta tana kuka amma tace min wai babu kome."
Bari nasata ta shirya sai kutafi.
Mikewa ta fita, murmushi yayi sannan yace.
"Abbana nagode da bani wannan shawaran, kaga gashi ta faɗa tarkona."
"Karka nuna rawan jikinka akan tafiya da yarinyar kawai ka matse."
Dariya sukayi sannan Abbanshi ya cigaba da mishi nasiha har ta shigo tace.
"Tana falo."
ok kawai yace sannan ya fita a falon, sanye take da wata faran atamfa, mai jar fulawa da Bakin, hijab dinta fari sai tayi kyau.
Sakata yayi a gaba suka fita, ya buɗe mata gaban motar ta zauna, sannan ya koma ya shiga, sai da suka biya kasuwar zamani yayiwa su Umma da mu siyayya, sannan ya kawota har ciki suka ya shigo muka gaisa sannan ya fita nan muka sakata a gaba muna kallonta, ita kuma tana jikin Umma tana shagwaɓa dakyar tashiga ɗakin Mama nan kaman mi, ɗakinmu muka shiga, Inda Aunty gausiya ke ciki duk ta lalace babu me kulata sai Ya Hayat.
Auntynce take faɗa mata an turo niman aurenmu, sosai tayi murna har da ce mana.
"Yara kun kusan shigowa, yasen idan aka kama kirjin yarinya sai tayi jinya."
Zaro ido mukayi cike da tsoro anan take kwankatsa mana, ai kowannemu ya nemi maɓoya dariya tayi sosai har da rike cikinta.
Karfe tara na dare yazo ya ɗauketa, daga nan airport suka wucce, inda ya mika mata nikk'af, suna isa ta ɗaura suka shiga ciki tana son tambayarshi amma yaki bada fuska,
Kamansu ake jira, ganin yanda take ɗari ɗari yashi janyota kallonshi tayi a cikin nik'af ɗin yace.
"Kalle hanya"..
A hankali suka shige cikin jirgin ta rike mishi riga, zaunar da ita yayi ya ɗaura mata belt, ana gama sanarwa jirgin ya tashi.
Rike hannunta yayi gam, ɗaura kanta tayi a kafaɗarshi.......
[8/25, 2:59 PM] Real Mai Dambu: 🌹🌹🍀
*MATAR SO*
🌷🌷🌻
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER'S ASSO*
(HWA)
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....
Dedicater To Hafsat Abubakar💋
_Idan kinsan baki saya karki karanta sabida na kuɗine, idan kika samu an sato toh karki faɗa min maganar banza dan zan iya miki Allah ya isa, duk wacce ta fitar min Na barta da Allah_
*BOOK ONE👈*
*Page...10*
Shafa fuskarta yayi cikin sanyi murya yace.
"Ki nutsu."
Sake kwantar da kanta tayi, tare da sauke ajiyar zuciya tsavar tsoro ko runtsawa batayi batayi ba har suka isa lagos.
Suna sauka ya shiga kasuwar zamani dake cikin airport ya saya mata kayan sawa sai na ciye ciye, da manyan rigunan sanyi sabida kakar sanyi ake a china,
Tana zaune wata matashiya tazo ta zauna a kusada ita, bata ɗago kai ta kalle yarinyar ba, sai da tace.
""Sannu ko? Kema china zaki?"
Gyaɗa mata kai Rahilah tayi, haka yarinyar tayita surutu, har Aman ya dawo ya zauna akusada ita ya riko hannunta, wanda suka sha gyaran mamie yace.
"Cutie ga abinci."
D'aga nik'af ɗin tayi xata mishi magana, buge hannun yayi tare da dalla mata harara, sunkuyar da kanta tayi, tace..
"Ya Aman na koshi."
Murmushi ya cigaba dayi yana kallon yanda mai nasara yayi crossing leg yana karanta jarida. Cigaba yayi da lallaɓata dan ya fara hango botsarewarta, ta hanyar share kwallarta da yace miye na kuka sai ta sake kukan tana cewa ita kam ya maidata gurin Mamie.
Ajiyar Zuciya ya sauke sannan yace.
"Naji zan mai daki, amma muje kirakani satiɗaya zamuyi kawai."
Can kuwa aka fara shirin tafiya, a first class Vip, suka zauna kome na gurin a tsare yake, bino bini yana kallon Ahmad da ya surkurkuce,
Mutane na gama shiga, jirgin ya tashi nan ma, rungumeta yayi har jirgin ya dai daita asama.
****2:03Pm In China
Karfe biyu da minti uku suka sauka a birnin Jon, na kasar china sanyi ake har da kankara, tun a jirgi yasaka mata rigan sanyi da takalmi safar hannun da na kafa, sai fuskarta yasa mata wani mask, mai nasara na ganin haka ya taɓa ahmad murmushi Ahmad yayi cikin karamar murya yace.
"Na mishi uzuri dan ina ganin ni tawa jaririyar, ɓoyeta zanyi har sai na gama gyara mata sittings."
Taɓe baki mai nasara yayi sannan ya kauda kanshi, koda suka sauka motar wani hotel mai suna royal hotel, yazo ɗaukarsi ɗaya nasu Aman ɗaya nasu Mai Nasara.
Tafiya kaɗan suka isa, hotel ɗin, inda aka shiga ɗiban kayansu zuwa cikin ɗakunansu,a online Ahmad yayi musu booking, makullar ɗakunan yana, hannun masu kwaso musu kaya, koda aka buɗe ɗakin farko nasu Aman shiga yayi da matarshi wacce sanyi ya gigitata, ya kunna room heater.
Kayansu ya karɓa ya jera a wardrob, sannan ya sake labulayen da suke ɗage, tana kwance a dukunkune ɗagata yayi ya ya gyara mata kwanciya ya shiga rabata da kayanta, sannan suka nufi ban ɗaki, wanka yayi mata idanunta a rufe, alola ya fita yabarta tayi, tana gamawa ta buɗe dirowar da ya ɗauki towe itama ta ɗauka kallon kanta tayi, ganin inda towel ɗin ya tsaya, take kunya ya rufeta taki fita sai da ya buɗe yaganta a tsaye.
Riko hannunta yayi ya bata doguwar riga tasaka, sannan ta hau abin sallah tayi sallar asuba, sannan tayi Azahar, tana idarwa ana kawo musu abinci zama yayi suka ci, sannan ya mike yace.
"Zoki tayani shiryawa, zan tafi meeting sai dare."
Mikewa tayi ta ciro mishi wani suit, neavy colour, ta taimaka mishi yasaka, abin dariya sai da yabarta tazo gyara mishi nitie ya taɓo, boons ɗinta a zabure tayi baya cike da fargaba, murmushi yayi ya shafa kanta bayan ta