Showing 15001 words to 18000 words out of 92699 words

Chapter 6 - MATAR SO BOOK 1

06 Sep 2025

848

mukayi muna mata fifita, sai ajiyar zuciya take saukewa,

   D'akinmƴ Aunty gausiya ta zauna tana kuka, sai yanzun take dan danasanin kashe aurenta da tayi, gashi tun ba'a jekoina ba tafara kuka,

             Tunda muka samu Mama Amarya tayi bacci, muka dawo ɗakinmu, ni da Rahilah muka koma ɗakin Umma Rahimah ta koma ɗakin Mama da zama haka muka mata watsewar zaɓi.

  
         ****,Aslinmu,
      Mu yan kasar nijar ne, Malam da Umma, Asalin sunan Malam Omer Harzuka, ɗan asalin Damagarane bazabarme ne, Gidansu malamai ne, a damagaran wanda ake ji dasu malam yana da yan'uwan shi nacan,

          Rigimar cikin gida ya haɗashi da Yan uwanshi, wanda haka yasashi yayi fushi yabar gida,

Malam shine babba a cikin gidan sai ya zamana a gidan ɗakuna ukune, akwai ɗakin Uwar gidan mahaifiyar Malam Mairama,sai Dakin Kyauta, sai dakin Halima wacce suke kira Hali dubu, Kakanmu malan Hayatu yana da yan kadarorinshi na kiwo, irinsu shanu, sai rakumai da tumakai,.

Gidansu suna yawa maza da mata,, ɗakinsu Malam yana da kane, guda biyu yan biyune suma,

Dakinsu basu da wani fitina kamar sauran ɗakunan, Hassana da Hussaina am musu aure acan nijar ɗin amma suna zuwa mana.

Dalilin barinshi gida ya farune bayan auren Umma yar abokin Babanshi, inda kakanmu ya ɗauki wasu daga cikin dabobinshi yabawa Malam, sai kanen suka tada rigima akan mi zai bada Omer su bai basu ba, faɗa yayi musu yace wannan kason da yabawa Omer yabashine dan rabonshine na kiwo da yake mishi.

Tunda suka ji haka sai sukayu shiru,dan Malam kaɗai ke masa kiwon dabobin.

Bayan anyi haka da kwana biyu, aka samu ɓullowar cutar amai da gudawa wanda yayi sanadin rasuwar kakanmu.

Bayan rasuwarsa yan uwan malam suka buɗe mishi wuta, akan sai ya bada dabobinshi araba bai damu ba dake yaba son fitina, sai ya mika musu da aka raba ya ɗauki Iya kakarmu da Umma suka bar nijar inda yazo maraɗi ya sai da dababinshi ya shiga motar katsina, daga sun zauna a katsina har na tsawon shekara, kafin ya dawo kaduna yazo ya kama haya, ya shiga makarantar markazi na malam mahmud gumi, dake yana da iliminshi tun can sai karatun bai bashi wahala ba.

A lokacine Umma tasami cikin Yaya Hayatu, cikin me matukar laulayi, ita da Iya sukayita fama har ta sauka lafiya,

Shagon saida litattafan addini ya buɗea kasuwar barci, kuma sai Allah yasaka mishi luɗifi a cikin shagon take ya bunkasa, Yaya nada shekara uku aka turashi madina yayi karatunshi acan,

Cike da farin ciki yazo ya faɗawa Umma da Iyarshi, aikuwa sukaita murna,, dake shi ɗaya zai tafi sai yabar shagonshi ga yaronshi yana cirewasu Umma kuɗin abinci da na haya,

Allah cikin ikonshi Naziru yarike su Umma da Amana har tsawon shekara biyar kafin malam ya dawo lokacin shagon ya kara bunkasa, Naziru ɗan nan kaduna ne, kuma maraya ne, amma mutune mai gaskiya da amana,

Bayan dawowar Malam ya maida Naziru makaranta dama bai gama scndry ba, dan yana aji biyu ya ajiye karatu gashi ynx yana niman shekaru ashirin, da buga buga malam ya turashi makaranta,

Dawowar malam aka sami cikin Aunty Shema'a, wacce cikinta baibawa umma wahala ba. Bayan haihuwar umma Malam ya fito da maganar karin aure Iya ce ta taushe Umma har aka kawo Mama Amarya,

Lokacin Aunty shema'u babu inda bata shiga, dan sai aka ɗauki shekara ɗaya da rabi kafin akayi auren, dukkansu malam ya kwashe ya zuba a makaranta high islamic,

Sun cire kishi a ransu sun rungume hidimar mijinsu, fiye da kima.

Watan Mama goma sha ɗaya ta haifi Aunty Asma'u wacce take aure, a Abia mijinta ma'aikacin banki ne,

Aunty Asmau watanta goma sha uku, sai ga cikin Aunty Hamdiya wanda lokacin Umma kama da tsohon cikin Ya kabir wanda yake bautar kasan shi a Edo,

Mama na fama da karamin cikinta, sosai suke fama da kansu ga Uwar mijinsu. Da ba lafiya watan guda tsakani Umma ta haifi ya kabiru, sati biyu da haihuwarshi Iya ta rasu, sun kaɗu sosai har na tsawon wata biyu, ana haka akayiwa malam tallar gida a tudun wada layin yan kosai, ba tare da wani damuwa ba yaje yasayi gidan me ɗauke da ɗauka bakwai ciki da falo da ban ɗaki guda uku, ciki ɗaya ɗaya, da ban ɗaki guda biyu sai ciki ɗaya babu ban ɗaki a cikinsu sai a haraba, nan malam ya ajiyewa yaranshi maza,

Ciki biyun da ban ɗaki na yara mata,

Bayan wani lokaci Mama ta haifi Hamdiya, lokaci Yaya kabir yayi kwari sosai, gidanmu ruwa biyune ɗakin Umma mu bakakene sai ɗakin Mama su kuma farare ne.

Sai da Aunty Hamdiya tayi shekara ɗaya da wata biyar aka sami cikin Aunty Gausiya, tunda Umma tasami cikinta ciwon Asthma ya shigeta da an ɗauka wank ciwo nadaban ne sai da aka tsananta bincike aka gano Asthma ce, dakyar dakyar cikin ya kai wata bakwai karshe tiyata aka mata, aka ciro babyn yar karama, umma ce ke hidima dasu har suka shekara dan Mama ciwo tayi sosai,.

Gashi gausiya ta tashi garau, sonda Mama ke nunawa Gausiya ya ɓaci tun bata da wayo har ta fahimci da zaran ta tsalla ihu Mama zata birkice, sai ta tsiro da fitina kala kala, ga faɗa da zagi haka Umma zata rufe ido ta zaneta, tun mama bata nuna bacin ranta har ta farawa Umma ba'a a wasa inda take cewa.
"Yaya da dai kin daina dukar zuciyar mamanta dan ji nake da ita kamar tsoka ɗaya a miya."

Tunda ta faɗi haka umma ta kame hannunta a jikin yarinya amma kiri kiri, umma ta ware gausiya a cikin yara, tun malam bai fahimta ba har ya ɗago wariyar yayiwa Umma magana tace.
"Ita zata iya rike sauran yaran dan a hannunta aka haifesu ita kuma gausiya yar soce taje Uwarta ta riketa."


Suna haka kwatsam Mama tasami cikin shkura shima tasha wuya dan har cirewa aka so yi Allah bai nufa, aka haifeta lafiya,

Bayan shekaru ashirin cif, yaran umma huɗu har dani da sai na mama Amarya shida, bayan shekaru aka sami cikinmu inda aka haifeni bakwaini, su Rahilah sai da suka cika wataninsu cif, ina da wata huɗu aka haifesu, mune kananu dan yayunmu duk sun girma har ana batun aurar da Aunty Shema'u Yaya Hayat yana karatu a ɗan fodio Uni.. Sokoto gausiya da shukra sune yan mata kananu,

Shema'u da Asma'u aka aurar dasu rana ɗaya, Aunty Shema tana auren wani ɗalibin Malam ne, sai mijin Asmau shima babanshi abokin malam ne,

Bayan shekara uku aka aurar da Hamdiya da iya kar yaran gidanmu scndry, daga nan magana ya kare,

Halayar gausiya ba daɗi, gashi sai rashin ɗa'a take a unguwarmu, yayinda shukra tafita.

Haka suma suka cigaba da karatu, har suka gama scndry shukra ta sami wani malamin jami'a anan kasu ya fito nimanta,

Gausiya wani yaro ta makalewa, ganin tana shirin lalacewa Malam ya hanata fita ga fitsara da rashin mutunci, babu me shiga shirginta har muma kanenta, ganin idan akace xa'a jirata ɓata lokacine akayi bikin Aunty Shukra.

Lokacin da Yaya Hayat ya gama karatunshi na likitanci, ya dawo gida nan ya gano gausiya na fita ya kamata yayi mata mugun duka,


Ranar malam na kasuwa Naziru yazo mishi, ya zama babba malami shima yana koyarwa a A.b.u, cikin farin ciki suka zo gida yaci abinci.

Nan yake faɗawa Malam ai zuwanshi hutu yayan Mamanshi daga Maiduguri yazo ya ɗaukeshi suka tafi can, dake suna da buɗi sai suka nima mishi takardu ya tafi sudan, har ya auri yar uwanshi bata jima da rasuwa ba gurin haihuwarta na uku, Malam ya tausaya mishi, ya tambaya Yaya hayat da shema'u anan malam ke faɗa mishi ai gidan ya cika, shigowa malam yayi ya faɗawa su Umma,

Komawa yayi gurinshi suka shigo gidan, inda farkon shigowarshi yayi tozali da Aunty gausiya,

Bayan anyi gaishe gaishe, akayi yaushe gamo, anan yake shaida musu Ai yaron shi babba sunan Malam ne ana kiranshi faruq, sai takwaran Iya Maryam,

Sosai malam yaji daɗi,, da zai tafi ya saukewa malam kayan masarufi,

Bayan sati biyu sai gashi nan yaxo ya gaida malam, wasa wasa ya maida gidanmu gurin zuwanshi, har karatun dare da na safiyar da ake, duk yana zuwa kai da yaga zai cutu ya fito ya faɗi abinda ke damunshi,

Malam yayi farin ciki, ya sami Umma da mana ya faɗa musu suma murna sukayi da aka faɗa mata katsaye tace.
"Lallai fa ni bana sonshi."

Babu wanda ya saurareta, har aka fara maganar tayi karfi, sannan Baban faruq ya fara zuwa gurinta duk fitarta sai ta mishi rashin ɗa'a har akayi auren cin mutunci da wulakanci, cikin yaranta rabone kawai ya ratsa dan sai sun raba hali ya gwada mata karfi yake karɓan hakkinshi sai rabo ta ratsa,

Gashi Allah ya haɗata da munafukar makociya ita ke ɗaurata Kan kome, bayan aurenta akayi bikin yaya shida matarsa da suke zaune a doctors quarts anan kaduna, har da yaransu biyu Hasina wacce suke kira da Afren sai Atika wacce suke kira da Ihsan,


Tunda aka fara maganar auren Aunty ciwon Mama ke tashi har zuwa yanzun da ta kaso auren,
.......
Cikin tausayawa na share kwallar dake bin fuskana. Bayan sallar isha muka sake lekata tana bacci sannan muka koma ɗakin Umma.

****
Washi gari...
Muna tashi muka fito zamu fara aiki malam yace.
"Kuje mu kwanta, Gausiya ta fito."
Jikinta na rawa tafito ya fara aiki, dakyar Umma tashawo kan malam ya barta tayi abin karyawa muka ci, bamu zauna ba sai makaranta.

Koda muka dawo an gama abinci, zama mukayi abinmu ko kulata bamuyi ba, muna gama cin abinci muka kai mata kwanon gurin wanke wanke muka shige ɗakin Mama , aka buɗe hira banu fito ba sai da azahar.

****
Kamar jiya yau ma shi yayi abin karyawa kuma ya cinye abinshi dan bata tashi, yana gamawa ya shiga ɗakin motse jikinshi yana idarwa Ahmad ya kirashi a kune ya saka wayar can kasa makoshi yace.
"Barka angon Hafsat."

Yana sauke numfashi, dariya Ahmad yayi yace.
"Shege kana rage gajiyane na tsinke maka jin daɗinka toh idan kagama muna jiranka a officer."

Katse kiran Ahmad yayi a gurguje ya shirya sanye da bakin jeans da farin shirt an rubuta Armania mai dogon hannun.

Yana isa officer din Ahmad ya sakashi a gaba da dariya......
[8/25, 2:59 PM] Real Mai Dambu: 🌹🌹🍀
         *MATAR SO*
                 🌷🌷🌻

*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER'S ASSO*
(HWA)

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....

Dedicater To Hafsat Abubakar💋

  _Idan kinsan baki saya karki karanta sabida na kuɗine, idan kika samu an sato toh karki faɗa min maganar banza dan zan iya miki Allah ya isa, duk wacce ta fitar min Na barta da Allah_

*BOOK ONE👈*

*Page.6*

     "Yau wani ya hucce gajiyarshi akan wata toh sannu Allah yasa kwallon ya faɗa raga, nan da watannin muzo cikin shinkafa."  Duka Aman ya kai mishi yana murmushi dan dama Ahmad ya fito ɗan kazar kazar.

    Kallon Agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunshi yayi, kafin ya ɗago kai taɓe baki yayi cikin nutsuwa yace.
"Wannan mutumin kome sai yasaka mana african time ne."

        Bai rufe baki ba, sai ga mai nasara ya turo hancin motarshi a haraban ma'aikatar, nima guri yayi ya parka sannan ya zuro kafar shi wanda yake cikin wani haf shoe, yafito sam bai cika damuwa da saka kaya kananu ba, duk kayan da zaka gani a jikinshi toh jamfane yau ma, jamfarce ruwa ashe sai takalmin shi haka ga baki ɗaya dai haɗin yau yayi tane fully, a hankali yake takowa fuskarshi a sake  ya shiga officer ɗin da sallama, amsawa sukayi  tare da mika mishi hannu musabaha yayi da Aman dan shi yake kusada, sai ya mikawa Ahmad suka gaisa tattaunawa sukayi  akan cigaban kamfanin da zasu buɗe,...

             *****
    Tunda muka ɗauko hanyar gida idanuna ya sauka akan mai saida ayaba, taɓa rahilah nayi cikin zolaya nace mata.
"Keee! Yaren novel can."

          Duka takaimin cike da jin haushi ta rausayar da kanta, dukda nikk'af ce a fuskarta sai da na hango murmushi akan fuskarta, a hankali tace.
"Insha Allah dakanki zaki kirani dan ɗaukar darasi, keee nifa mijina sai ya haukace akaina dan..."

    Kasa tayi da muryanta dai dai kunnena tace.
"Babu abinda baxan iya mishi ba, ke har ɗaukar hotona zan natura mishi."

    Zaro Ido Rahimah tayi tace.
"Mun shiga uku, Rahilah wato baki daina ba ko?"

    D'aga kafaɗarta tayi alamun oho, sannan tace.
"Ga wacce zaki tuhuma, bani ba ina zaman lafiyata ta kawo min maganar wai ga ayaba."

               Dariya nasaka har ina rike cikina, haka nayita tsokanar Rahilah ita kuma tana biye min har muka iso gida,..

    Da dare kuwa muna zaune a tsakar gida muma shan iska, Malam da Umma da kuma Mama suna hira Malam yace.
"Ina son Allah ya kawo min mazaje nagari da zasu aure min, Yan ukuna dan na lura Rahilah ta ɗan fisu, rawan kai addu'a nake musu ba dare ba rana."

   ... "Hmm Malam dama ina son magana dakai akan Maryam Sajida, Malam Mus'ab yayi min magana akanta nace sai na tuntuɓeka." Inji Umma knn,

   Shiru yayi na wani lokaci kaman bazai magana ba, ya kirani.
    Jikina har rawa yake na isa gurinshi, nace.
"Na'am malam."

         "Kina son Malam Mus'ab ne?" ya jefa min tambayar,

     A ruɗe kamar wacce akace tayi karya na shiga cewa.
"Wallahi na rantse da Allah ni bana kulashi ma, kuma malam ka tambayi su Rahilah babu ruwan da shi.."

   Kuka na saka musu ina rantse rantse, "Ya isa Mamana ban ce zan miki dole ba, dama tambayarki nake shin kina sonshi ne ko A'a."

        Cikin sauri nace.
"A'a ni bana sonshi."

         "Tashi kije Allah yayi muku albarka,"
    "Amin" su Umma suka ce suna min dariya,

     Dakin Umma na shige na kwanta, take su rahila suka biyo ni, suna rarrashina.

                Bayan tashinmu Umma take faɗawa Malam, "Na manta ban faɗa maka ba, Akwai Yar Amiran na da'awa zata aure yariman zazzau shine aka turo min da katin bikin, mi kagani akan tafiyar."

          Murmushi yayi sannan yace.
"Ba damuwa, Allah ya kaimu lokaci amma bake ɗaya zakiyi tafiyar ba ko?"

      "Eh zan ɗauki Yan uku muje dasu dan zasu taimaka min sosai." tace mishi.

           "Allah ya nuna mana lokacin." yace mata,

            Haka suka cigaba da hira ni kuma su rahila suka shiga rarrashina, kar a ɗakin muna kwana wannan ɗabi'armu ce da zaran abu yasami ɗaya toh kaman ya sami saurane.

     
            ****
  Yau alhamis muna tsakar gida wanki muke, malam ya shiga cikin raha yace.
"Yan uku gobe juma'a fa kar a manta da saukar da ake min."

       "Toh Malam Insha Allah zamuyi maka."
          
    Cikin ɗoki da muna muka gama wanki mun, kowacce ta ɗauki Alkur'ani muka fara karatu tun alhamis,

            Kafin dare munyi kusan izu goma goma, zuwa juma'a kuwa muka sauke mashi, cikin jin daɗi ya kiramu ya bamu dubu uku uku, duk lokacin da mukayi mishi sauka sai ya bamu kuɗi, haka ba karamin kara mana kwarin gwiwa da kaunar mahaifinmu muke ba,

 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login