Showing 69001 words to 72000 words out of 92699 words
tsamiya ta kawo min dazafinshi na amsa, cike da kunya nace.
"Nagode Hajiyarmu."
"Dama irin zaman da kuke kenan baki faɗa min ba ayi mishi iyaka dake ba kin zauna kamar mara wayo yana dukarki miye amfanin haka dubi yanda yayi miki lahani, sai kace mara galihu wallahi banji daɗin haka ba."
Kasa nayi da kaina cikin muryan kuka nace.
"Hajiya nice nayi mishi laifi, shi kuma ya fusata ba sai kinyi fushi da shi, bazan kuma ba ki bashi hakuri."
Mamakine ya kamata, juyawa tayi ta fita,
....... D'akin mama kilishi ya shiga tare da dafe goshinsa, kanshi a kasa. "Yanzun Yunus abinda kayi ka kyauta sami yar mutane ka zaneta haka, aiko huda ban taɓa ganin ka taɓa lafiyarta wato ga baiwa, wacce aka maka dole ka zauna da ita shine kasa belt ka zaneta, Yayi kyau sai kaje ka sami hajiyarku da takardan sakin Maryam dan tace idan baka saketa ba zata maka Allah Ya is..."
Manyan idanunshi ya ɗaga a razane ya zuba mata, jikinshi na rawa ga wani bugun da zuciyarshi keyi yace.
"Mama yanzun akan dukar hajiya zata min Allah ya isa?"
"Yo kashe musu y'a zakayi muna kallonka duka har kan nono, tsabar rashin hankali zaka kashe musu y'a tashi ka fitan min a falo kaje kuma ka bata sakin Yar mutane babu abinda ya dame ni, tunda kai baka san kara ba ai duk abinda Maryam zata maka bazaka taɓa ɗaga hannu ka daketa ba, amma dake kai bakasan darajar da muka nema maka ba shine ka zane musu y'a. Har gudanawa Maryam take yarinyar da shekara uku tabaiwa Huda. Ashe yanda ka daketa zaka iya dukar huda haka ni fitar min a falo."
[8/25, 3:00 PM] Real Mai Dambu: 🌹🌹🍀
*MATAR SO*
🌷🌷🌻
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER'S ASSO*
(HWA)
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....
Sadaukarwa Ga Yan grp ɗin Matar So....
Dedicater To Hafsat Abubakar💋
_Wannan buk ɗin hakk'in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_
*BOOK 1👈*
Page....22
Tashi yayi jikinshi yayi sanyi sosai ganin rashin dacewa dukar da yayi min yake, ɗakin Hajiyarshi ya nufa huda na ganinshi ta mike ta shige inda nake.
Shigowar Sulaiman da magunguna yasa shi ɗago kanshi mika mishi hannu yayi suka gaisa, sannan shima ya zauna fitowa Huda tayi cikin murmushi tace.
"Uncle Man ka kawo magungunar Aunty mom ɗine."
"Eh gashi akwai, Neurogesic shi ana shafa shine a bugu kowani gurin dake ciwo sai wannan magungunar su na ciwon jikine, Wai ita Maryam ɗin mi yasameta ne haka.? Dan hajiya taki min bayani sai dai tace min na kawowa Maryam maganin ciwon jiki dana sha da na shafawa."
Tura baki tayi tare da kauda kanta ga barin inda Uban yake tace.
"Daddyne ya mata dukar mutuwa gata can a ɗaki sai Amai take, cikinta da kirjinta kamar zasu fashe da ciwo, Nima Allah yasa wani yayi min irin dukar da kai mata kaji yanda abin yake."
Tana gama faɗar haka ta juya ta shige ɗakin.
Ina cikin bargo sai rawan sanyi nake, ɓalla min maganin tayi ta bani sannan ta guda na shafawar ta mika min ta fita a hankali na kwaɓe rigar na shiga shafawa da farko akwai sanyi sai da ga baya zafin ya fara ratsani, kuka nake wiwi, tare da cire rigar sabida zafin inda na shafa man.
Shigowa yayi ɗakin, ya tsaya a bakin kofa maganar da Sulaiman ya gaya mishine yayi matukar kashe masa jiki. Tsurawa kirjina ido yayi yaga yanda suka koma ga sabida sunsha dukarshi.
Takawa yayi har bakin gadon ya zauna, ɗago kai nayi muka haɗa idanun, jan bargon nayi na rufe jikina. Ina ja da baya.
Janye bargon yayi, tare da tsare ni da ido yayi, sannan ya kai bakinshi ya fara hura min iska, wanda yake ratsa raɗaɗin da nake ji, ajiyar zuciya na shiga saukewa dan nafara jin dama dama.
"Yunus zaka fitan min a ɗakina, kafin na saɓa maka kaje Yarinyar da ka zalinta tabarka da Allah, kuma ka sake musu yar mutane kafin kabar garin nan ko kuma na makaka kotun musulunci a maka shegen dukarda kayi mata. Get out,"
Inji Hajiyarshi.
Zugwai zugwai ya fice bai iya ce mata komi ba yana fita ta koma kaina cike da masifa tace.
"Sannu lusara ya gama jibgarki yazo zai lallaɓaki, har da barinshi ko Maryam ke wacce irin mutun ce da bazaki rama abinda aka miki."
..... A hankali kuka na yake fitowa, kaina a kasa nace.
"Toh bansan yanda zan rama bane, kuma tsoronshi nake ji."
Tsaki tayi cike da masifa tace.
"Kwatar kankine sai nakoya miki, ko tsiwar ma baki iya ba, Amma Malama ta cutar dake ainun, wallahi wannan wani irin tarbiya ce haka da yaro bazai kwaci yancin shi ba. Toh zauna zan koyq miki yanda zaki rama."
Tana gama faɗar haka tafita tabar ɗakin, ni kuwa na cigaba da kukana.
Ban kuma ganinta ba har barci yayi gaba dani, cikin barci naji kaman ana lasar nonuwana a hankali, ina buɗe ido sai akan Mai Nasara kurr nayi mishi a hankali naja da baya tare da juya mishi baya.
Haurowa yayi samar gadon ya shiga janye bargon bance mishi komi ba na barshi ya janye, nace.
"Kazo ganin illar da kai min ne? Ko kazo latsa kazama ce, banziyar wofi, Hhhhh Yunus kenan kana taɓani yanda kake so kuma bai hanaka faɗa min magana ba, dukda haka bai maka ba kasa belt ka zane ni dubi yanda ka maida min da nonuwana wai in tambayeka kasan darajar Aure kuwa? Kasan darajar Mace kuwa? Duk wanda yasan wannan darajojin bazai taɓa wulakanta mace ba, daga Yau kasake taɓa jikina Allah ya isa min, kaje kasan darajar mace kuma dan rashin kirki Har Mahaifiyarka tace karka kara zuwa inda nake ka ɗibe kafafunka kazo dalla fitar min a ɗaki, taɓa ni da akayi na kwanaki akaci bulus ban yafe ba, kuma Aurenka ko ta masifa ce banayi koda shine abinda zanyi na karshe a rayuwata dalla fitar min a ɗaki wanda baida yakana kawai."
"Sajidaaaaaaaaaaaa" ya daka min tsawa wallahi sai da cikina ya kaɗa, amma na wani ɓata rai tace.
"Saura zare belt a zaneni, tunda na faɗa maka magana hotiho kawai lusar.."
A fusace ya ɗaga hannunshi sama kuma ya gaza saukewa, murmushi nayi nace.
"Try it mana! Wallahi ka gama dukana kenan, kuma ka kuskura kace zaka taɓa ni! Ka taɓs aurenka dan dama sai ka sake dan ni ba baiwarka bace, tunda na taso Umma bata taɓa dukana ba, balle Malam wanda muka gado hakuri a gurinshi, kafita bana son ganinka in kuwa kaki zan maka ihu k'orto."
Haushi ne ya cika shi ya fisgo ni tare da haɗa bakinshi da nawa aikuwa na kama lips ɗinshi na ciza, ya maza ya ɗaga yana huci nace.
"Da kenan kaci banza kana taɓa ni zan nuna maka ni jinjirace mara mutunci get out Yunus dama ban taɓa jin sonka ba balle kuma sha'awarka an cuce ni an haɗa ni da tsohon hannu comman love bai iya ba sai dukar mace ai wannan jahilcin tun 1999 Ka daina kai da ka dawo dashi kaje gurin tumakan matanka subaka abinda kakw bi a jikin kazama."
Tsaki naja mishi na shige ban ɗaki dagani sai Pant dama rigar na zameta, oho dai na canza always ɗin na fito da gayya, nake tafiya ina girgiza nonuwar da ya taɓa lafiyarsu, jarababbe idanunshi na kai na haye gadona na kwanta, nace.
"Kwlelen kare da hantar kura."
Na gyara kwanciyata addu'a nayi na shafa.
Yau naga masifa sam kamar mara zuciya ina kwanciya shima ya cire rigarshi ya kwanta a bayana har da ɗaura hannunshi akan nonuwar,
"Kan Uban can, Ni zaka renawa hankali ka jibge ni akan nonona kazo ka nanuke min, kayi na kuɗinka " na mike zubur.
Na ware murya nace.
"Wayyo Allah na, xai kashe ni Hajiya kizo, wayyo Umma na shiga uku na lalace, karka sake dukana wayyo, Wayyo ku taimake ni Mama kizo na shiga uku na banu Huda."
. Gabaki ɗaya na birkita gadon da shikanshi na tukunkuye shi, ta yanda kowa yazo zai zarge shi.
Aikuwa dake dare yayi sai ga Mama da Huda, a guje sun danno ɗakin, ina ganinsu na fauce a jikinshi har ina hatsilawa, gashi babu kaya jikina zanin gadon Huda taja ta rufa min, sunawa Mai nasara wani irin kallo.
Gashi na cika musu kunne da kuka, Hajiyace ta shigo ɗakin cikin rawan jiki taxo ta rungume ni, nace.
"Hajiya dan girman Allah ki maidani gurin Ummana bata taɓa dukana ba, Amma daddy ya same ni kamar jaka, indai haka ake auren na yafe ban taɓa ganin Malam ya daki su Umma ba, amma yana shigowa ya rike min kunnena na shiga uku nafasa auren sai na fadawa Ummana."
Shiru sukayi har shi gyara muryan Alhajinsu yasa su juya da baya, yace.
"Lafiya?"
"Hmm Alhaji na zata zan iya kashe wutar kiyayyar da Yunƴsa ya kunnawa zuciyar Maryama, ashe ba haka bane, ynz ma ya shigo zai kashe musu yar mutane Alhaji mugun dukar da Yunusa yayiwa Maryama, Ko Yarsa gata nan bai taɓa mata ba ya farfasa mata jiki ya ilata musu Y'a don Girman.Allah kasashi ya sake musu y'a tun a cikin mutunci kafin ya janyo mana abinda zamu gaza kare kanmu a idon duniya."
Yana zaune a bakin gado ya haɗa kanshi da hannayenshi, ya rasa abinyi.
"Ku fito."
Inji Alhj.
Koda suka fita kayana aka barni nasaka, sai a lokacin ya mike yasa rigarshi gabana yazo ya rungumeni a hankali yace.
"Nagode maryam Sajida, Amma bazan sake ki ba ko da zan rasa komi nawa ne, zan fanshe shi dake koda kuwa da numfashina aka saka akan ki zan bada, amma ki sauya tunani rabuwarmu ba sauki."
Shafa min cikina yayi zuwa cibiyana yana min tafiyar tsutsa, rike hannunshi nayi gam, ina sauke numfashi dakyar nace.
"Na,shirya rabuwa dakai ta kowani fuska."
"Karki yi abinda zai ɓata miki suna da rayuwa kina kasa da sha takwas, kuma kina harin zawarci, bayan baki san daɗin auren ba."
"Kai sanin daɗin aure ya dama, ina dai dai da nashirya rayuwata kamar kowa, kuma kaga duk namijan da zan aura sai aureni a ɓagas ne yana min kallon rogo ina masa kallon kitse, tunda namiji bai take ni ba don Allah free me Mr Mai nasara."
Ina gama faɗar haka na fita ina murza idanuna da fake kwallar munafinci, da sauri na raɓe jikin Huda dama jikina da zafi take ta zabura tace.
"Aunty Mom kin sha magani kuwa." cikin fida wani munafikin kwalla nace," kunne ne yake min guɗa."
"Innalillahi....Alhaji ka gani ko na shiga uku ni Hauwa'u kashe musu y'a zaiyi fa." Inji Hajiya.
Kallon rashin Yarda Mama tayi min, irin anya Maryam, sunkuyar da kaina nayi jikina na rawa dan ba ɗabi'armu bane karya kuma ba'a ɗauramu akai ba.
Fitowa yayi a sanyayye, ya nemi guri ya zauna kanshi a sunkuye.
Kallona Alhaji yayi cikin lallashi yace.
"Maryama!!! Mi ya haɗaki da mijinki,"
Kallon Huda Mama tayi tace.
"Takwara bamu guri."
Mikewa tayi jikinta a sanyayye ganin yanda ubanta ya koma lokaci ɗaya,
Gabaki ɗaya jikina ɗaukar rawa nayi ina kallon fitar huda, sunkuyar da kaina nayi, cikin kuka nace.
"Baba nice na fasa mashi laptop ɗinshi wanda yake abubuwan kasuwancinshi garin yin game, kuma ya hanani ɗauka da yazo ya tambaya nayi mishi rashin kunya Amma wallahi baxan kuma ba karku faɗawa Ummana, zatayi fushi dani."
Na karshe maganar cikin kuka da yarfe hannuna, ina kuka wiwi.
Zaro ido yayi yana kallona, cike da mamaki, murmushi Mama kilishi tayi sannan tace.
"Alhaji ta tashi kawai taje, gurin Huda sukwana sai mu karasa maganar dashi."
"Tashi kije."
Ina mikewa tsabar tsoro kamar zan hantsila yayi maza ya mike zai tare ni, na faɗa jikin Mama by mistake na fama nonon kara nasaka tare da dafe gwiwarta na kifa kaina, ina sauke ajiyar zuciya kuka nake sonyi amma ganin yanda duk suka ɗaga hankalinsu ya sani mikewa ina murmushin dole nafita,
"Wallahi Yunus ka cuci kanka, dube yanda tayi karya dan ta kareka nayi Imani da Allah ba abinda tafaɗa bane ya faru mi tayi maka har kayi mata wannan dukar, fama kirjinta tayi fa, Gaskiya Alhaji kasashi yasake musu y'a dan girman Allah dan dole muje asibiti su duba kirjinta." Hajiya ta karshe maganar tana share kwalla.
"Koni ma na yarda da maganarki dan babu sisinshi a auren mune muka mishi kuma matar tamuce dan haka mun fasa ya sauta kawai." Inji Mama kilishi,
"Yunus Mi ya haɗaka da iyalinka kai mata irin wannan dukar, asanina kai mutum ne mai hakuri da biyayya da kuma bawa kowa hakkinshi. " Inji Alhj,
Gyara zama yayi cikin sanyi murya yace.
"Wallahi sharrin zuciya ce, kuma yarinyar ta cika fitinane bansan mi zan mata bane, kuma gata bata da wni wayewa dan sauran Yan uwanta su Fareeda ai ba'a taɓa jina dasu ba, abinda na.lura shine akwai gidadanci a tare da ita, amma ayi hakuri zan makaranta kuma gaskiya Alhaji ayi mata magana ta daina wannan kukan banzan da rashin kunya."
Ba Hajiya da Mama ba hatta Alhaji sake baki yayi yana kallon Mai nasara cikin takaici da bakin ciki, murmusawa Alhaji yayi cikin dattako yace.
"Toh ba damuwa mun ji korafinka shi knn ko akwai wani damuwar bayan haka."
Girgiza kanshi yayi alamun babu, gyara zama Alhaji yayi cike da mamaki da dariyar wautar Yunus, "Toh Yunus ko xaka iya bani takardan Maryama, ina son nanda karshen shekara na bawa Sulaiman Aurenta dan bazamuyi wasa da rasata cikin zuri'armu ba duk macen da tasan rufawa namiji asiri ba matar da za'aki bane, Idan mukayi dubi da kirsar Annabi Ibrahim (A.S)da matar Annabi Isma'il(A.S) lokacin da Annabi Ibrahim yayi zuwarshi na farko bayan barin Hajra da ɗanta sai yasami Annabi isma'il yayi aure, sai ya sami matar yace.
"Baiwar Allah ya halin maigidan nan yake."
Nan tashiga aibanta Annabi Isma'il, ai yayi kaza bayi kaza ba, tana gamawa, yayi mata godiya da zai tafi yace mata.
"Idan mai gidan ya dawo kice ya sauya kofar gidan nan bai dace da gidan ba."
Bayan mai gidan ya dawo wato Annabi Isma'il ta faɗa mishi wani tsoho mai kama kaza mai kala kaza ga abinda yace, aikuwa Annabi Isma'l yace mahaifina ne kuma yana min ishara da na rabu dake."
Next zuwanshi yasamu Annabi isma'il yayi wani auren daga zuwanshi matar ta tarɓeshi ta shiga mishi alkhairi da kyautata mishi haɗi da faɗar alkhairin Mijinta ta ɓoye sharrinsa ta nunawa kowa mijinta na kyautata mata sama da komi.....
Ban kawo maka wannan maganar dan ka zauna dole da Maryam ba dan nima nafi son ka saketa nabawa sulaimanu, ita shi zai iya zama da ita komin muni halinta, dan nasan shi ɗin mai biyayya ne da muradin Iyayenshi. Sati biyu jal na baka kawo min takardanta kaje ka zauna da wayayyun matan, sannan kuma kar na kuma ganin kafarka a cikin gidana indai ba da takardan saki ba, tashi ka tafi Allah ya bamu alkhairi."
Tashi yayi ya fita jikinshi a sanyayye, dan bai wani ji ba daɗi ba.
........Ni kuwa zafi jikina yayi sosai amma na boyewa huda har tayi barci amma ni na gaggara barci.
.......Shiru Alhaji yayi kafin yace.
"Miskili yana sonta bai san yanda zai janyo hankalinta bane amma bari muga gudun ruwanshi."
Mikewa sukayi kowa ya nufi inda zai kwana amma nikam barci yaki idanuna.
Har aka kira sallar asuba a lokacin jikin yayi zafi fiye da jiya, dan nonon sun kumbura sabida famasu da nayi ga zogi azaba, tun ina kuka har na daina na lumshe idanuna koda Huda ta tashi taɓa goshina tayi tajishi da zafi ta fita ta kira Mama, suna zuwa aka fito dani, shirya jikina sai da huda ta taimaka min, aka fadawa Alhaji,, asali bansan miye duka ba a rayuwata ba, kuma dukar da yayi min a kirjina ya haifar min da ciwo ga jikina da yayi mugun tsami.
Dakyar muka fito zuwa gurin motar Alhaji, dai dai shigowarshi daga masalaci kenan, tsura min ido yayi tare da lasar bushashiyar laɓɓashi, ɗago kaina nayi idanunmu ya sarkafe da juna, kwalla ce ta zubo daga idanuna na kauda kaina, shiga motar mukayi na kishingiɗa ina sauke ajiyar zuciya.
Yana son magana Amma Mama kilishi ta tsare gida, haka muka fita muka barshi a gurin, wani asibitin kuɗi aka kaini take, aka shiga bani taimakon gaggawa, daga allurai da drip.