Showing 3001 words to 6000 words out of 92699 words
Allah ki barmu muyi barci,"
"Eh nifa wayar muku dakai nake."
"Ina wayar dakai anan, zaki lalata mana rayuwa don Allah Rahila jeki kwanta ubangiji ya kawo miki shiriya a cikin barcinki."
Rahima na gama faɗar haka ta juya mata baya, ita kuwa mi zatayi mana banda dariya har da rike cikinta.
Dukka dukka shekarunmu basu wucce sha bakwai ba, da watannin amma rahila tasan iya karance karance, gyara kwanciyana, ina nazartan maganarta baki ɗaya bansan iya lokacin da na ɗauka ba, har barci yayi gaba dani.
........ Buga mana kofa Mama Amarya tayi dakyar na buɗe idanuna, wanda suke cike da barci mika nayi tare da salati nace.
"Yau fa asabar ne! Ai sai abarmu mu huta."
Kallona Rahima tayi bayan tashigo ɗakin nace.
"A ina kika kwana.?"
"Hmmm! Ai Allah ya takaita mana ne, jiya Asthmar Mama Amarya ya tashi ina kwance bayan kunyi baci sai ga, bakona yazo shine na tashi nashiga banɗakinmu naga baruwa, sai na ɗauki Pad da kuma pant ɗina na shige gurinta nasamu tana ta fama, gashi inhelarta ya kare, sai danaje na bugawa Malam kofa dan yana ajiye dasu, muna zuwa har idanunta sun fara hawa sama, kaii Allah ya isa mana tsakaninmu da Aunty Gausiya dan itace sanadin tada asthmar Mamanmu."
Fita mukayi nida Rahila, har muna ture juna, muka samu tana sallah, a ɗ'akin mukayi sallar muna idarwa muka zuɓe a jikinta tare da sake kuka, rungumeta mukayi sai kuka muke, kamar wani abu zai sameta.
Shafa kanmu tayi, cikin nutsuwa tace.
"Ya isa haka! Yan ukuna bagani nan a raye ba. Toh ya isa haka ba kuka zakuyi addu'a zaku tayi min Allah ya kara min lafiya."
Kallonta Rahila tayi cikin kuka, sannan tace.
"Wato da Rahima, bata shigo ba dashi knn sai dai musa mi mugun sako, Don Allah Mama ki daina saka damuwa a ranki."
Shafa kanmu tayi cikin jin daɗi tace.
"Toh nadaina."
"Toh karya mana ita zakuyi, Auta da yan biyu."
Mikewa mukayi, muna dariya dan Babban Yayan Hayat na ya shigo rike da basket, zama yayi cikin nutsuwa. Mikewa nayi na amshi basket ɗin na kai kusada ita, gaisheshi mukayi ya amsa, yana murmushi yace.
"Mama ashe abinda ya faru knn? Amma ai an gaya miki ki rage iza damuwa cikin ranki, banda kwanarki na gaba Allah ya kawo Rahima ai da bamu kai labari ba, don Allah ki cire al'amarin Gausiya, a ranki ko muma Yaranki zamu sami nutsuwa."
"Yayansu! Ai ba wai narike damuwarta bane kawai ciwone ya tashi min, amma zan kiyayye gaba."
Lekowa Umma tayi tana kallonmu yanda mukayi rashe rashe, a cinyar Mama.
"Mmm! Zaman jiranku zanyi ne? Ko kun manta kuna da mkrantane. Ga wanke wanke can."
Da sauri muka mike, zuwa waje aikinmu kowa ya kama, dan munsan da aikin.
Nike wanke wanke da shirya kayan karyawa, Rahila sharan ɗakunan Iyayenmu da wanke ban ɗakinsu da kuma namu, Rahima kuwa da ita ake girki, shima juya abin ake, turn by turn.
Karfe bakwai da arba'in muka gama kome, sai wanka muka shiga ni na tafi ɗakin Mama Amarya, Rahila ɗakinmu rahima ɗakin Umma, dan a kowani ɗakin muna ajiye kayanmu, cikin sauri muka fito dan karyawa Umma da Mama suna ɗaki.
Shigowar Malam yasa muka juya gareshi cikin nutsuwa muka ce.
"Barka da Safiya, Malam ya mi jiki ya zafi."
Murmushi yayi cikin dattako ya zauna a kusadamu ya amshi cokalin hannun Rahima yace.
"Kice da hannu kamar Yan uwanki, yafi albarka."
Kaman zatayi kuka tasaka hannunta, a cikin jollof ɗin taliya da dankalin turawa ta fara ci, kunshe dariyarmu mukayi dan tana da matukar tsaginagini( kyama ko kyankyami) amai ta fara niman yi muka ɗaga kwanonmu da saurinta taje gurin wanke wanke, tana amai.
Lekowa Umma tayi cikin ta ɗaga labule, tace.
"Amma ai kinsan baki cin abinci da hannu matukar ba tsarki kike ba."
Kunyar malam yasa na tsame hannuna na ɗauki tea na shige ɗakinta, Rahila kuwa ko a jikinta sai ma murmushin da take dokawa mun bar mata abinci.
Cikin harshen zabarmanci Umma ke ɗaya mishi aiga abinda yasata amai, dariya yayi cikin hausa yace.
"Kinga kuwa nine na kwace mata cokalinta."
Wanke gurinda ta ɓata tayi, sannan ta ɗauki tea ɗinta ta shigo ɗakinmu,
..... Takwas muka shirya tsaf muka fito, kallonmu Umma tayi muna sanye da unifoam, ruwan toka sai nikk'af da muka rufe idanunmu da shi.
Mika min hand out Umma tayi tace min.
"Yau bazan shigo ba, ki duba idan hajiya Falmata tazo ki bata sai kuma yan ajina ki kara musu, karatu inda suka tsaya."
D'aga nikk'af ɗin nayi ina kallon Umma nayi idanuna cike da kwalla, bakina na rawa nace.
"Umma ni.."
"Ke nace, kishiga ajina ki musu kari."
Kamar kazar da kwai ya fashe mata haka nafito, daga ɗakinta sallama muka musu....
**** Tsit kake ji banda Mai Nasara da tafita zuwa masalaci babu alamun akwai mutane a gidan, shima da ya dawo ɗakinshi ya wucce, me girkin gidan ya gaishe shi cikin girmamawa yace.
"Sir mi za'a girka,"
"Anything."
Ya bashi amsa a takaice, sannan ya shige.
Shiru mi girkin, yayi cike da damuwa yasan yau kam sai yayi girki sama da kala goma dan kowacce mata sai ta tsiro da abinda zata ci,
Shigewa ciki yayi ya fara aiki, shigowar Aneesa, a gurguje tace.
"Mr Johson a haɗa min, abinci cikin gaggawa ina da meeting yau."
"Ok Mah."
Cikin sauri ya haɗa mata, makaroni da kayan ciki, wanda yasha curry da tymer, juye mata yayi ya kai gurin cin abinci,
Ya dawo ya cigaba da aikinshi.
A gurguje ta fito zata karya lokacin Mai Nasara shima ya fito, wave ɗinshi tayi da hannun sannan ta fara cin abinci wanda ta ɗiba a cikin ɗan karamin bowl,ruwan khal ta ɗiga a abincin sannan ta fara ci,
Ko cokali biyar batayi ba, ta mike gurinshi tazo tana goge bakinta da tissue ta ɗan rungume shi, sama sama tace.
"Barka da safiya, Mai nasara ina da meeting sai four zan shigo gida da fatan babu matsala."
(😹 Don Allah kuji wata rayuwa tana tambayarshi bayi da matsala)
Riketa yayi ya daidaita tsayuwarsu, sannan yasaka bakinshi a kunnenta yace.
"Ina da matsala, i need U."
Agogon hannunta ta kalla da sauri ta raba tsakaninsu tana yake tace.
"My Dear, ina da meeting ne fa kayi hakuri na dawo sai nasan abin..."
"Jeki Allah yabada sa'a."
Sake bashi wani kiss tayi ta juya da sauri tana cewa.
"Bye baby."
(Ni a tunanina gatse yayi mata, amma dake sakarya ce ko a jikinta)
D'akin balkisu ya nufa, tana cikin uwar ɗaka, har can yabita tana kwance tunda ta idar da sallar asuba, ta koma ta kwanta, baiyi wata wata ba, ya haye gadon ya cire rigar jikinsa ya kwanta tare da janyota jikinshi.
Shiru tayi taki kulashi, haka yayita kiɗanshi da rawanshi ko tari batayi ba, kamar zai saka kuka ya kalleta yace.
"Laifin mi nayi mukune haka? Da kuke azabtar dani akan abinda Allah ya haltamin shiknn bazan sake zuwa, tunda na fahimci zina kuke son na fara."
Mikewa yayi, ya sanya kayanshi ya bar ɗakinta, taɓe baki tayi ta tattara bargon ta shige banɗaki tayi wanka sannan tafito tana karamin tsaki, ita sam bata da lokacin..........
😹😹😹😹
```Abin dariya ko? Wasu matan sai addu'a```
[8/25, 2:59 PM] Real Mai Dambu: 🌹🌹🍀
*MATAR SO*
🌷🌷🌻
*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER'S ASSO*
(HWA)
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai....
Dedicater To Hafsat Abubakar💋
*Toh makaranta nan na kawo muku karshen free page ina da sauki kuma ina da zafi bazan cutar da kai ba kuma karkayi yunkurin cutar dani, Don Allah idan kinsan zaki saya ki fitar min Wallahi na yafe miki basai kin saya ba idan duniya da gaskiya ku duba girman Buk ɗin da Ciwo A rayuwata karku cutar dani, tunda nayi muku adalci duk wanda ya shiga hakkina Akwai Allah*
*Ga musu saya ga number acct ɗina Gtbank:0472282105 sai phone number:08130269641 na idan ka tura kuɗin sai kayi min screen short kuɗin Book 300# sannan zaku iya turo rechg card na MTN Nagode Allah yasa Mudace*
*BOOK ONE*
Pagen karshe.....03
Tsaki take jerawa yafi a kirga, sabida tsabar son jiki da gajiyan da ya tara mata, ita a ganinta ya takura matane.
Tunda ya shiga ɗakinshi yasakarwa kanshi ruwa yake bin ko ina na jikinshi, dafe kanshi yayi cike da bakin ciki da damuwa yaushe zai samu sallama a gidanshine. Yaushe zai samu abubuwan da kowa ke fatan samu, dafe goshinsa yayi dakyar yayi wanka ya fito tsame jikinshi yayi ya fito, ɗaure da towel goge jikinshi yayi ya ɗauki man shafawarshi ya shafa, sannan ya buɗe gurin kayanshi ya ɗauko riga da wandon jamfa, ya saka shadda ce dark blue, wacce aka mishi aikin surfani, da farin zare da ratsin baki da sky blue, sai hular kanshi wanda shima kusan haka ce, takalminshi ya saka fari baki wanda ya dace da kayan, agogon azurfa wanda aka kawatashi da kwalbar Demand, a nutse yafito ya kalli kanshi a madubi, abinka da farin fata sai gashi yayi sharrr dashi, ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗauki jakar computer ɗinshi da wayoyinshi da key motarshi, ya fito.
D'akin Balkisu ya leka tana nan inda ya barta, fuskarshi ba yabo ba fallasa yace.
"Zan lekasu hajiyata."
Kaman bazata amsa ba tace.
"A dawo lfy,"
D'akin Fareeda ya leka tana kwance abinta, shiga yayi ya ɗauki, takarda da biro ya rubuta mata, *Na tafi zaria*
Yana gamawa ya ajiye, ya fito ɗakin yaranshi ya shiga yasamesu suna barci sumbatar goshin huda yayi, wacce take kan gadonta na sama, ya gyara mata lulluɓenta, sannan ya isa gurin Mufida itama sumbatarta yayi, sannan ya isa gurin Sameer da yake can nashi gefe, ya sumbaceshi juyawar da zaiyi yaga Huda ta mike, tace.
"Daddy! tafiya xakayi?"
D'aga mata yayi,ba tare da damuwa ba ta diro daga gadon sai da ya tareta yana kallon inda ta diro, sunkuyar da kai tayi tace.
"Sowiee, bazan kuma ba,"
Murmushi yayi zai fita, da hanzari tace.
"Daddy zan bika."
Kura mata ido yayi sannan ya kalle agogon hannunshi kafin yace.
"Mintuna 30 na baki."
Da gudu ta shiga ban ɗaki, wanka tayi da brush sannan tafito tasamu baya nan, kayanta ta ɗauka kala biyu tasaka, duba lokacin tayi sannan tayi sallah asuba a lokacin.
Tana idarwa ta ɗauki yar karamar jakanta, ta rataya sannan ta wucce kitchen wani kula ta ɗauka ta ɗebi abinci da ruwa da juice ta fita, ɗakin uwar ta shiga ta kalleta, tace.
"Mommy zanbi daddy."
Juyawa tayi abinda dan tasan ba kulata zatayi ba, tana fitowa taga Laraba da Hasana tace.
"Idan su Mufy suntashi kuce nabi daddy Zaria."
Da sauri tafita yana cikin motarshi a zaune, gaba ta buɗe tq zauna sannan drvn yajasu suka fita, ganin yana aiki yasa bata dameshi ba tap ɗinta ta ciro ta fara game.
****
Tunda muka shigo makaranta Rahila ke dariya taɓani tayi tace.
"Kee ga malam mus'ab can sai doka miki murmushi yake.?
Kyaleta nayi dan bana son hayaniya, wuccewa mukayi zuwa azuzzukar da muke koyarwa, musaman yau da nake da aji biyu gana umma ganawa.
Ajin umma na fara shiga, sabida ajina akwai malam Hafiz a ciki, ina shiga suka shiga murna nikuwa haushinsu nake ji dan sun iya tambayar renin hankali, suran da suka tsaya nace su nanata min sai na musu kari.
Daga aya ta arba'in na suratu bakar suka ɗauka har aya ta hamsin, ɗaga nikk'af ɗina nayi sannan na shiga musu kari, aya goma har suka rike kasancewansu matan aure na jinjina jan da brain ɗinsu yake, muna gamawa na mike dan na hango malam nafi'u zai shigo.
D'aura nikk'af ɗina nayi nace.
"Ko akwai tambaya ne?"
"A'a malama maryam Sadija."
Suka faɗa min, can wata mata daga baya tace min.
"Maryam Sajida,ina tambaya."
"Ina jinki." na faɗa mata a takaice.
"Hmmm dama, tambaya ce misali mace ta kwana da miji, sai asuba yayi, toh sai jinin haila yazo mata, shin zatayi wankan janabane ko zata jirkinta har ta gama hailarta.?"
Shiru nayi kamar ruwa ya cinyeni, tsabar kunyar amsar da zan bata kaina a sunkuye nace mata.
"Wankar janaba ya hau kanta, idan muka duba wasu ruwayoyi da kuma litattafan fiqhu Allah yasa mudace."
Na fita da sauri dan karsu kara tsayi dani, dariya matar tayi tana cewa.
"Wannan Yar malama Hasinan akwai kunya."
Shigan malam Hafiz yasasu shiru, inda ya fara musu da hadisi.
Ina shiga ajina nasamesu sunyi dandazo, Rahila tana karanta musu, Zubar gado girgiza kai nayi kafin nace musu.
"Malama Rahila kije ajinki ɗalibanki na jiranki."
Muryan Sadiqa naji tana cewa.
"Malama Rahila! Kin karanta gidan karuwai bugu ɗin Ya haɗu, idan kina karantawa dole ma kiji kina niman abokin rayuwa, dan ana bayani sosai akan sex."
"Rahila fitan min a class nace." na daka musu tsawa,
D'aga min hannu tayi cike da takaici ta kalle Sadeeka tace.
"Kuma idan baki sami abokin rayuwa ba ya kike ji a lokacin?"
Cike da son basu labari tace.
"Wallahi idan ina karantawa matse cinyoyina nake, sabida tashin hankali, dan wani mugun sha'awa yake bijiro min."
"Hmm toh bari na faɗa miki abinda baki sani ba, matuƙar kika cigaba da bin ire iren wannan buks ɗin zaki wayi gari duk irin kokarin da namiji zaiyi akanki bazaki taɓa gamsuwa ba, sufa sun rubutane dan ayi aiki dashi, akan mi kike ɗaura zuciyarki ga damuwa, wallahi ki daina."
Murmushi yarinyar tayi cike da rashin damuwa tace.
"Wai toh na girma aure nake so ance sai na gama jami'a ya zanyi."
A nan ne na amsa mata, nace.
"A'a fa karki dawo kina kuka da kanki wai nikan miye ribarki idan kika cigaba da karance karance buk ɗinda zasuna tada miki sha'awa, kisan illar haka kina shiga daga ciki sha'awarki ta kare karshe mijinki duk abinda yayi miki baki godiya musaman ta ɓangaren auratayya, better stop ita now."
Shiru sukayi sannan na kora Rahila ajinta ni kuma na cigaba da koyarmusu da alkur'ani bayan mun gama muka ɗaura da tafsirin, muna gamawa suka farq jefo min tambaya ina amsa musu, sai karfe sha ɗaya muka tashi,
****
Fitowa yayi yaga gidan ba'a cewa kome, tsintsiya ya ɗauka ya share falon sannan ya isa kitchen tsabar tashin hankali sai da yaji kaman zai kwara amai, mask ya ɗauko ya toshe hancinshi sannan ya fara juye ruɓaɓɓen abincin wasu ma har sun fara tsutsa, dakyar Aman ya gyara kitchen ɗin ya wanke kayan da ya tafi yabari,
Sannan ya ɗauko Indomie da Bushashen kifi, wanke kifin yayi ds ruwan zafi da lemon tsami, sannan ya farfasa ya zuba a wani kwano daban.
Attarubu ya ɗauko da albasa ya yanyanka, sannan ya buɗe ma'ajiyin kayan spice ya zuba, sabida karnin kifin, sai man gyaɗa da ya ɗiga kaɗan, murmushi yayi yana tuna rayuwarsu ta jami'a, ruwan na tafasa ya juye Indomie sannan ya fita zuwa ɗakinshi bayan ya ragw karfin wutan gas ɗin.
..... Ɗakin Hindu ya leka ya sameta kwance daga ita sai rigar barci shima yayi sama, sai naked ɗinta bakyan gani,ko ɗan irin shaving ɗin nan batayi ga suma yacika tuuu, kauda kanshi yayi yana bin ɗakin da kallo ko ina kaca kaca, ga wani hamami da yake badawa, toilet ɗinta ya leka yasamu kayan amai, kome nan, ba daɗin gani, zuwa yayi kanta ya ɗake cinyarta da duka, firgit ta mike ta zauna, hararanshi tayi cike da tsiwa tace.
"Akan mi zaka dakeni?"
"Akan kazantarki na gaji na baki nan da awa guda ki gyara ɗakinki in ba haka ba wallahi yau zan sake ki."
Bata san lokacin da ta sauko ba ta tura baki gaba, ta shiga tattara kayan ɗakinki ta gabanshi tazo wuccewa amma abin takaici sai da ya toshe hancinsa, ya fita daga ɗakin ganin ya fita ta shiga kintsa ɗakin dakyar, tana gamawa ta faɗa ban ɗakinta shima haka ta tattara, dakyar tayi tana kukan zuci.
Bakinta ta wanke sallah kan ai ba'a maganar shi, falo ta fito tasameshi ya juye abincin a tire, yasaka spoon yana ci, haɗiye yawu tayi ta shiga kitchen ɗin ta ɗauko spoon , zama tayi ta fara cin abinci, mikewa tayi ta ciro wayarta dake chaji, ta kunna hoton abincin ta ɗauka sannan ta ɗaura, a status da karamin sharhi.
*Aikin Mijina knn, sai ni matar so💃 wacce bata da miji haushi ya kasheta da oho ba*
Still bai isheta ba ta ɗaura a grp nan aka shiga mata reply dake ta kware a karya sai cewa tayi.
"Hmm wallahi ina bacci fa yaje ya ɗagoni ya min wanka, kusan wkend ne shi yayi kome na gidan hmm baku ga yanda jiya ya barkice min yana son yaji shi sweety ɗina."
Rahila da wata admin ta dawo da ita taga abinda tace murmushi ta ɗaura mata a maganarta, dake ta sauya sunanta zuwa Oum Muwaddatu.
Cike da kuri tace.
"Oum Muwaddatu wallahi dagske jiya nasha wuya, ya durje ni son ranshi