Showing 21001 words to 24000 words out of 92699 words
Murmushi yayi ya dawo dasu gida, ya mika mata Firdausi wacce suke kira da Jannart yace.
"Allah yana kallonki, idan kin gadama ki bata hakkinta idan baki gadama ba kibarta ta mutu, kece da asara ni, da zaran nayi wani auren zan samu yara dayawa,"
Dukda bata saduda ba, haka ta cigaba da rokon yar, tsana da tsangwama hr yarinyar ta cika shekara ɗaya, bai bari takara kwana ɗaya ba, ya kaita katsina, gurin Umminshi zuwan yarinyar Umminshi dmta kira fsisal tace.
"Faisal duba min, yarinysr nan kamar bata da lafiya."
Daukar yarinyar yayi zuwa asibiti aka dubata, anan aka samu yunwa na damunta, magunguna ya haɗo ya kawo mata, tare da abincin da ake bawa yara,
A cikin wata shida yarinyar ta dawo lafiya. Wani irin kulawa Ummi take bata wanda yasa yarinyar manta da wasu iyayenta,
......
Tsakanin Ahmad da Hafsat sai ido, dake yar duniya ce ita tasan kan abinta tuni ta lallaɓashi suka koma ruwa, wani sabon halin da ta tsiro shine na tagaji, ciwon baya musaman idan suka zo rayuwar aure, nan zatayi ta mita har yaji haushi ya sauka bai gama ba,
Sai ɗan banza yawo biki ko bana danginta ba, tana gurin da ita za'ayi shi, hatta suna ba'a barta a baya ba dukda irin wadatar da mijinta yake dashi bai hanata hango wasu ba, Ahamad nada matukar kokari bashi ba har sauran abokanshi duk wani kayan yayi tare suke sawaya matansu, musaman Mai nasara dukda miskilancinshi yana son yaga matarshi ta caɓa ado, abin takaici idan kaga kwalliyarsu, zasu event, ita kuma farida zata gurin raba kayanta, madan banki ce mai sayawa, asavar da lahadi har gwara balkisu tana kokarin kaman tawa, tunda ita bata kome.
Duk wani kayan kawa na yayi kafin a gani a jikin wasu toh sai matansu da yaransu sunyi yayinshi, a ɓangare hindu koda Aman ya kawo mata, sayarwa take taci kuɗin da ya fahimci haka sai ya daina kashe dukiyarshi a iska, sai yaje ya sayo mata masu araha ya jefa mata, dan ko min tsadar kaya idan tasaka sau ɗaya toh ya tashi aikin,...
****
Yau Alhamis tun safe muka tashi da wuri sabida zamu raka Umma zaria, walimah ce kawai sai azahar zamu tafi mun dawo makaranta,
Ana tashinmu muka dawo, ɗakin Mama mu kashiga Aunty gausiya nacan na darzan wanki, kayan Mama har da zanin gado, "Sannu Mama ya gida,"
Nacewa mama, "Uwata lafiya lau ya karatu,"
"Alhamdulillah, basu dawo bane? Naga sunce zasu rigani dawowa."
Su rahilah nake tambaya, dake makarantarmu ba ɗaya ba, gudun karmu haɗu muki maida hankali aka raba mana makaranta, rahimah makarantarta daban haka ni ma, sai Rahilah itama ha,
Muna cikin maganarsu sai gasu nan sun shigo, mika min kaya Mama tayi a cikin laida tace.
"Gashi na bikin da zakuje, wai akwai walimah da Arabiya night,,"
Shiru nayi sam bana son hidimar bidi'a, shigowar Rahilah yasa na ɗago kai nace.
"Hmmm kuje bikin kawai ni babu inda zani,"
Kallon Mama tayi alamun tana jiran karin bayani, nan mama ta faɗa mata, tace.
"Bana son shashanci ku shirya ku dan ta kusan shigowa, kuma drvn hajiya falmata shi zaizo tafiya daku."
Mikewa nayi na fita sam raina baiso zuwa bikin ba, haka mukayi wanka, muka ci abinci muna zaune sai ga Umma tashigo nan muka gaisheta, ɗaki tashiga tayi sallah sannan taci abinci, karfe biyu da arba'in sai ga Hajiya Falmata da drvnt a motarsi sienna, nan mukayiwa Mama sallama muka nufi waje,
Tunda muka ɗauki hanya zuciyata bata da sukuni, haka nake jina sukusuku, har muka isa gidan galadimah Zazzau inda ake bikin kenan.
Muna shiga aka fara bin motarmu da ido, fita mukayi daga motar a hankali ganin yanda ake mana kallon kurilla yasa na ɓata fuskana kamar zanyi kuka,
"Laaaa Mamie barka da zuwa, Malama sannunku da Zuwa yan uku. Kuxo mu shiga gurin Ammy tana cikin gida."
Inji wata yar budurwa wacce bazata wucce tsararmu ba, kallon fuskarta nake kaman nasanta, har cikin falon Mahaifiyarta ta kaimu, ta shiga cikn ɗakin da tasamu da mutane tace.
"Ammy kizo ga Mamie Falmata tazo tare da Malama Hasina, suna falo."
"Toh manyan bakina sun iso, Rahama jeki basu abin taɓawaa gani nan fitowa,"
Ai wasu daga cikin kawayenta da suka san Umma da Hajiya falmata tare suka fito dake suna haɗuwa a,aikin tafiya da'awa, nan aka shiga gaishe gaishe, wata a cikin matan irin mugayen yan bokon nan ne, tace.
"Malama Hasina, Yarankine suka girma haka sun kusan tafiya jami'a kenan."
Murmushi Umma tayi tana taɓa goran ruwan hannunta, tace.
"Sune muka barsu iya ss3 sabida basu da jikin girma, amma duk yayunsu mata a ss2 suke waec da neco, suje gidan mazajensu su cigaba, malam yana tsaya musu."
Taɓe baki wata tayi tace.
"Ni nafi gane, yarinyata ta fara jami'a kafin aure."
"Eh dukda haka, auren bai hana karatu idan mukayi dubi da yanda zamani ya koma, ɗan yau baka shedanshi kina ɗakinki tana ɗakinta, wasu zasu lalata miki su, karewa ko kawaye bamu basu damar tarawa ba, sabida sha'anin rayuwa, sune sukayi jinkirin rashin samun miji da wuri amma yan uwansi sha shida muke aurar dasu, shema'u ta haɗa degree a islamic law, Asma'u ta haɗa degree dinta, Edication, Hamdiya itama nurse ce, Shukrah tana karatu, a nan kasu sai Gausiya itama a nan zaria take deplomarta a bank and industrie. Yayansu Hayat yana aikin likintaci, ga Kabiru yana master, sukuma suna scndry, mi muke nima a boko kuma ga addini ga boko ka haɗa gishirin rayuwa, kuma bani ds haufi akan yarana dan nasan ko dattijo suka aura zasu iya zama dashi balle kuma matashi daga talatin zuwa sama."
D'if falon yayi shiru ganinmu cikin manyan hijab yasa ake mana kallon, wasu kauyawa jin irin tamu iyawar yasa kowa ya shiga faɗin masha Allah,
Abinci aka kawo mana, muka kasa ci sai juyawa muke, tsabar kunyar idanun mutane Hajiya Iyami uwar Amarya takira Rahama ta kaimu ɗakinsu anan ma akwai yan mata irin masu rawan kan nan, karshe tsakuran abincin mukayi,
Da yamma muka shirya cikin riga da zani, na Englishi mai ratsin lemon green muka nufi gurin Walima,, dake bamu fito da wuri ba su Umma har sun tafi, daga mu sai Hajiya Falmata, kiran Aman tayi tace yazo ya kaimu,
Toh da yazo yace mata gashi nan, muka fito zubawa rahilah ido yayi kusan sati biyu da kwanaki amma har ynz gizo take mishi, fitowa yayi ya buɗewa Mamien shi gaba ta zauna mu kuma muka shiga baya, saita madubin motar yayi da kyau, a daidai inda Rahila ta zauna.
Yana tuki yana satar kallonta, garin haka har ta kamashi sunkuyar da kanta tayi ta danki hannuna ina jin yanda jiknta ke rawa,
Faɗamin tayi, dama nikam najima da sanin haka, murmushi nayi mata, kawai dan naga dacewarsu.
Koda muka isa muka fita juyowa yayi ya kalleta, fuskarshi a tsume yace.
"Baki iya gaisuwa ba ko."
Duk bakin rahilah sai gata muryanta narawa tace..
"Ina wuni."..
"Bar abinki bana bukata." yace mata da sauri ta fita.
Kallonsu Hajiya falmata tayi, tace.
"Rahila tazo muje rabu dashi yaje can gurin matarshi ai tare suka zo."
Dukda bai faɗa ba, amna ts hango bakon yanayi a tare da ɗanta, kuma batayi bakin ciki ba, sai ma farin ciki, idan hasashenta ya zama gaskiya,
Taron walimah yayi kyau, inda Umma tayi bayani akan rayuwar aure da ma'aura, musaman yanda aure ya koma a wannan zamanin,
Da tazo magana akan Matar So, kuwa har wani take tayu musu...
MATAR SO SUNANE DA KOWACE KE SON AKIRATA DA SHI
. Babban gishirin Zaman aure Wanda zai kaiki da mallakar zuciyansa tamakar kin wanke kin bashi ne.
1.Hakuri,
2 .juriya,.
3. ladabi da biyayya. Sai kin jure Zaki Iya hakuri Sai Kuma kinada hankuri zakiya may Ladabi da biyayya.
Babban makamin mace agidan miji Kuma sune
ADDUA ADDUA ADDUA DA MIKA LAMARINKI GA ALLAH.
*BABBAN HANYAR MALLAKA KUMA*
1. Iya girki (ba indomie ko spaghetti ba nope
2. Iya sarrafa Shi a shimfida (Iya jima'i) karki/ka zama lusari
3. Iya Magana. Kisan irin kalaman da Zaki dinga furtawa. Iya mu'ala da mutane. Yin adalci kyautata zato da Kuma yin uzuri.
Ta cigaba da cewa.
"A wannan zamanin iyaye muna sakaci da yawa yarinya ta girma har tayi aure baki nusar da ita rayuwar aure da rayuwar da zatayi anan gaba ba, maxan ysnzun basu damu da ki musu, wani abin azo a gani matuƙar zaki riƙe girki iya sarrafa harshe, ya sarafashi a gado, mutunta danginshi maida damuwarshi naki, ki kambama alamarinshi fiye dana kowa,
Karki ce ya cika fushi ko yana da miskilanci a'a ke zaki koya mishi sakewa dake dakuma sauran mutane, Matar fari itace ke fara lalata alamarin namiji duk yanda kika ɗaurashi haka zai mike, sannan akwai kura kuran damuke aikatawa, rashin yin kwalliya a gidajenmu sai zamu fita unguwa, zan muku misali dani kaina, Hasinah banda wannan yadin hijab dake jikina wanda duk inda zanje dashi nake fita, toh bana iya sakewa ko jagira nayi nafita dashi toh waye zanwa a waje bayan ina da wanda ya ajiyeni namishi, wannan ɗabi'ar tasamu mazauni a cikin zukatar Yarana baki ɗaya, idan mace takai mace kuma ta amsa mace babu malamar da zata zauna da ita tace mata ga yanda zatabi da namiji, sabida rayuwarshi kamar na ɗan shekara ukune, da zaran ya tada rigimar shi, sai ki duba dabi'ar karamin yaro ki gani, da zaran ya fara kuka zan faɗi a kasa yayita shureshure, a lokacin zai baki haushi kaman ki jibgeshi amma idan kika tuna da, cewa kukanshi kara miki zafin kai zaiyi, niman alewa ko wani abu zaki fara dan kurabu lafiya,
Toh namiji ma haka shi bazai faɗi ba, amma zai koma gefe yayita huci idan kina da wayo, a lokacin sai ki saukar da kai ki bashi hakuri, idan kika ga yaki sa shi a gaba kita rarrashinsa, wanda idan kinga zaki iya saka mishi fitinanne kuka shi akawa laifin tuni zai manta da wani rigima ya sauko, toh a lokacin sai kiyi amfani da damar haka ki bashi hakuri dan zai damu shi akawa laifi ke kuma kike kuka, Mata muna da matsala a rayuwarmu sosai bazamu iya rarrashin miji ba amna zamu iya rarrashin mai saida ɗan kunne dan yayi mana sauki,, haba mata ina hikimar tamu take ina kwarewar tamu take, tunda Asiyah ta iya bawa fir'auna shawara ya ɗauka waye ne mijin naki da bazai ɗauka ba,
Ummu Salma an karɓo daga gare a hadisin da buhari da musulin suka rawaito.
Tace manzon Allah yana zama yayi shawari dasu, akan alamuran addini ko, kuma wani yaki, indai manzon Allah zaiyi shawara da matarshi ke wacece da bazaki bawa mijinki lokacinki ba, ina kira gareku mata yan boko karki cr aiki ya hanaki kula da miji, zakiyi kuka nan gaba idan ya auro undergrad, kina ji kina gani zai, mai dake gefe ya saka wancar a gabanshi idan bai yi haka ba toh yar aikin gidanki da kika bar mata gidan ita zai aura, idan mai tunani da tsoron Allah kenan idan kuma aka rasa haka, kina ji kina gani zai na bin yar aikinki suna masha'arsu, ko kuma yaje waje nima, wallahi muji tsoron Allah, wai tsabar rashin daraja a gurin mace mijinta zai raba gurin kwanciya da ita, sabida tanq wari da hamami, wai nikam mi kuke shirin zamane matan arewa, tun a gida zaki koya mata gyaran jiki girki tareraya, iya magana, sabida sha'anin rayuwa baki san inda xata zauna ba, amna ina sai dai ki koya mata shan maganin mata, can yayi kyau amma rayuwarta ba kyau, kwanakin baya naje kasuwar ganye sayar wani ganye da ake amfani dashi gurin taimakawa yaro sabida kurga, sai naga wasu yan mata guda biyu ɗaya take cewa.
"Ita tagaji dashan maganin mata, dan mijinta baya wani sonta sabida bata iya girki ba, inda take samun saukinshi sai gurin jima'i, Ya ilahi wai sabida mi bazamu koya musu girki ba, sai na kasa hakuri na mata magana harna gabatar mata kaina, take kunya ya kamata janta gefe nayi muka tattauna, nasata ta roki mijinta ya sakata a islamiyana, da kuma ajin Hajiya Falmata, na koyar da girki da gyaran jiki, hmm yau sai ga yarinyar da mijinta kafin nazo ɗin nak ta biya min Umrah, tana kuka tace.
"Malama a'a ke ba malama bace ke uwata ce kin bani farin ciki wanda uwar da ta haifeni bata bani ba, malama Mama, ga takardun zuwa umra na baki, zamu je ofishin Alhazai dake a karasa miki aikinki"
Na rasa mi zancewa yarinyar, bawai dan bantaɓa zuwa ɗakin Allah bane a'a sai dan gani nayi ɗan abu kalilan ya janyo min alkhairi, sai nakira mai gidan na faɗa mishi yace jeki na baki izini, Iyaye wallahi bama kyautawa itace tun yana ɗanye ake ɗan kwarashi, anan zan tsayq Amarya zakiya idan gidanki ya lalace babu ruwan Hajiya Iyami, da Hajiya Falmata da ni Hasinah sabida kina cikin ɗaliban Da'awa, idan gidanki yayi kyau abin alfaharinmu ne.
Da haka nake miki nasiha ki gyara rayuwar aurenki kija mijinki da danginshi a jiki wani sabon salo wai kuna kiran iyayen miji da ulcer ko hawan jini, a'a kuskure ne, ke zaki rushe dangantsrku ke zaki gini, ina da suruka, naki na saka ido akanta da mijinta, ina da yara mata baxan so nimaa cutar min dasu ba, akan Yan ukuna zan kwaɓe hijab da rigar malamta na gurzawa surukina rashin kirki, dan ni nasan abinda na bashi, idan yace min bata da kunya shi xan fara tuhumq kafin na tuhumeta, sabida karfe ɗaya baya amo sai da wani a kusa da shi,"
Daga nan ta,rufe da Addu'a, daɗin abinda tayi sai shi ana ta,tururuwan zama a kusada mu, kafin atashi mun zama celebritys.😂
Haka muka dawo daga gurin, nan umma tace zata koma kirikiri nace zan bita, nan suma rahila suka ce zasu bita, ai nan hajiya falmata tace.
"Yan uku ai zama zakuyi sai jibi zan mai daku."
A gaban mutane bai hanani saka kuka ba, tsakanina da Allah, haka kawai, za'a barmu a bakon guri Mama kilishi da tun dawowarmu take bina da ido murmushi tayi kafin tace.
"Malama anya Yan ukunku zasu zauna a gidajensu kuwa nan da kaduna suna kuka kaman yara, koda yake ai autotine."
"Eh hajiya Rukayya haka nake fama dasu ko gidan yayunsu basa zuwa hutu, idan basa gurina toh suna gurin Malama Atika, gwara ni ina gurxa musu faɗa, daga malam har malama babu ruwansu da faɗa, toh Hajiya ga Amanar yan ukuna, don Allah jibi su dawo da wuri sabida akwai islsmiyan safe kuma sune malaman."
Tana gama faɗar haka, ta mike haka muma muka mike, har gurin motar da zai maida ita gida muka je, muna share kwalla tsabar sakalci, ko irin ta kallemu dan matukar ta kallemu zamu iya karya mata zuciya, haka ta suka tafi muna, kallo sai kuka dariya Rahama tayi ta mana, tace.
"Kutt wallahi kun cika shagwaɓa, ina zaria ina kaduna, da kuke kuka."
Haka hajiya falmata tasamu a gaba muka koma cikin gida, a ɗakin yan matan duk mun taru mun cure, dakyar sukayi ta janmu har muka sake jikinmu....
.......
Da dare, ana ta shirin arabiya night amma banda mu, sabida dukkanmu muna jin kewar gida dakyar muka shirya da faɗar da hajiya Falmata tayi mana sannan ta ɗaura mana da rarrashi, Rahma tayi mana kwalliya dake ta iya, muka yafa abayarmu, su rahmah sun rigamu fita. Duk mutane sun tafi jin muryan Hajiya falmata yasa muka leka ɗakin da take, muka ce.
"Mun shirya Hajiya."
"Toh kuje Yayanku na waje ina zuwa." tace mana,
Muns fita Mahaifiyar Ahmad tace.
"Nifa zan zo kaduna, cikin sati me zuwa, duk yanda kikayi da ita ki faɗa min, babu wanda zaiki haɗs zuri'a da Malama Hasina, kiga irin shakuwar dake tsakaninta ds yaranta ki dube yaran mana da sauran yan matan ko iya kallonka basayi, tsabar tarbiya da Addini ya shige su."
"Toh ke hajiya firdausi, Ahmad ya nuna miki yana da bukatar aurene?" Inji Hajiya Iyami,
Dariya tayi sannan tace.
"Aini ce nake hanashi yanzun kuma nice zan sashi."
Haka sukayitq tattaunawarsu....
***
Muna fitowa muka sameshi sanye da jallaɓiya har da hirami, dake ango duk abokinsune, kafarshi ɗaya na ciki ɗaya na waje, ɗago kai yayi ya kallemu, sannnan ya janye idanunshi yace.
"Maryam Sajida keda Husaina kushiga baya Hassana ta shigo gaba."
Fuska yayi kaman bashi ba, shiga baya mukayi nida Rahimah Rahilah taja kafa zuwa gaban motar ta zauna, shiru motar yayi can ya juya ya kalleta a sace sannan yace.
"Mi ƴasa kika saka turare?"
D'ago kanta tayi kaman zata fasa ihu, sunkuyar da kanta tayi bata ce mishi kome ba, shiru ya biyo tsakaninsu nida Rahimah muna kallon abu, can yace.
"Ba tambayarki nayi ba? Ko kinfi son zuwa cikin maza kina kamshi, karshe duk inda kika ratsa duk wanda yaji kamshi alhakina kanki."