Showing 12001 words to 15000 words out of 69565 words

Chapter 5 - 'Yan Abuja comeplat Hausa novel

HAERMEE   

13 May 2025

2216

tare ba saboda maybe yanayin gidan naku, sai saka mai ruwan ki kai masa da kayan wanka, sannan ki saka mai toothpast a brush ki aje mai a kusa, ba yanda za ai ya qi musammab yaga kin saka maku tare, kinga ba zai zargi kina jin wari bane daga wajen shi, har yai feeling bad kuzo kuna samun sabani) bayan ta mai wankan yayi brush daki suka koma, ta gyara mai jiki tare sa feshe shi da tirare, palo ta dawo da shi yana biye da ita kamar raqumu da akala, abinci ta zaunar da shi ta bashi, yana ta santi" kaiiiii amma ba qaramin birge ni kkai ba, kin san rabona da faten wake har na manta kuwa?" " naji dadi da yabawar ka Hubby" " kusa da ita ya matso" ke din ta daban ce, komai naki daban ne,Allah ya barmu tare" murmushi sukai dika, kiran sallar magrib ne ya katse su suka tsaya suka saurara sannan suka bi suma, bayan an idar ne sukai adduar da ake yi ba yan idar da kiran sallah, Allahumma rabba hadhihidda'awatittammah, wassalatil qa'ima, a ti muhammadal wasilata wal fadeela waddarajatirrafee'a wab'athhu maqamam mahmudan lladhi wa adtah, innaka la tukhliful mi'ad, sannan suka dora da salatin annabi ingantacce, addua suka daga hannayen su sama sukai a tare ita da shi, suna idarwa suka tashi sukai alwala, shi ya tafi masjid ita tai a gida, bayan ta idar ne tayi azkar din bayan kowacce sallah ne, sai ta samu tai kuma azkar din yamma, tana idar wa ta miqe ta je tai wanka ta dawo dan ragowar abincin nasu ta juyo masu ta kawo ta hado da ruwa da komai ta aje a gefe, daki taje ta saka rigar baccin ta mai matuqar kyau da daukan hankali, sai ta dora zani akai, da hijab tana jiran sallar isha'i bayan tayi sallar ne da minti 15 ya shigo, sai da ya biya wajen Innar mu ya gaida su, baban shi na ta sa mai albarka, ita ko ta cinkishe fuska tana hura hanci, daya tambaye ta sai tai qaryar kanta ke ciwo, dan yau wuni tai da yunwa, can sai ta saki fuska " kasan da yake bana son faten wake, kuma bana son bawa yar albarkar nan aiki shiyasa, amma da shinkafa zan bata ko gwangwani dayar nan ne ta dafa min, tinda Nafee ita har yau bata iya tsantseni irin na Juwairah ba" ba komai Inmar mu kawo na kai mata za tai maki ai, ba zai yu ku kwan da yunwa ba" da sallama ya isa daidai Juwairah ta fito daga daki ta cire zanin ta da hijab din ta, tana qarasa shafa mai a cinyar ta, ko da ya higo tini ta sauya salon shafawar, sake baki yai kamar dolo yana kallon ta, qarasa shigowa yai ya aje ledar still idon shi a kanta, juyawa tai ta koma daki tana tafe tana juya bayan ta tana waigowa tana mai wani kallo da murmushi, ni dai tin da ya shiga suka ja qofar bam qara ganin me suke aikatawa ba sai dai kunnuwa na sun jiyo man Jabeer na sambatu da bana gane yaren da yake, sayyarar qafa ta na ja nai wajeπŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€

Qarfe hudu na asuba suka fito sukai wanka tare da alwala mai kyau suka koma, bayan sun shirya ne suka fara habatar da nawafeel, kowa ya fara addu'ar shi, Jabeer ne ke hango baqi, a gefen shi dan ba wuta sai ta wayar shi suka kunna, miqa hannu yai yaga meye, dagawar nan da zai yaga shinkafar da Innarmu ta bashi ce jiya a dafa mata, " Ya salam ! Tab lallai da safe na shiga magana wajen innarmu, aiko ni tai na kawo ki dafa mata wai yunwa take ji, tin safe bata ci komai ba, bata cin faten wake, shine gaba daya na manta" " haba Yah Jabeer bai kamata ka manta da wannan mahimmin abu ba kuwa, domin yunwa ba ta da mahadi" a qasan ranta kuwa jinjina wa Innar mu take wajen iya hada makirci, matar da taci ta tande kwano, har ta aiko wai a dada mata in akwai, tace babu shine take cewa ba ta ci, ikon Allah, lallai Allah mai jin qan bawan sa mai tinawa da shi a kiwanne hali yake, da bata zama mai neman taimakon Allah a kimai ba da bai taimaka mata jiya ba da bama ta san me ake shirin kulla mata ba, kiran sallar asuba ne ya katse su ya fita masjid an yi sallah, ya dawo, ita kuma tayi tata a gida tai azkar tai karatun asuba da take yi kullum ba fashi komai aikin da ke gaban ta sai tayi ko rabin shafi ne kan ta tashi, tana rufe qur'ani ya shigo, lokacin gari ya dan waye, miqewa sukai akan zasu maida bacci, dan Nafeesa ke abin karyawa a gidan, in ba arziqin abin karyawan ma da dama koko kawai zasu dama su sha, sallama sukaji anyi..........








............
....
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ 'YAN ABUJA. πŸ’…πŸΌ


BY HAERMEEBRAERH





Page 8:





Nafeesa ce ta shigo," Yah Jabeer Innarmu tace ka bada shinkafar tin da tayi wuyar dahuwa" πŸ™ˆ " inna lillahi, ni gaba daya mantawa nai shaf dana shigo, dan Allah ki bata hakuri kice yanzu za a dafa" tace in ka fadi haka na amso ka bata ta fasa wataran an dafa" "My goodness, yau ya zan na je gaida Innar mu, yq kk ga fuskar ta tai fushi ko?" 😱 " hmmmm ba kadan ba kuwa Yah, amma tace kar na fada maka tai fushi" Juwairah a ranta tace" ina fa zata so ya sani tinda tana son nakasani ta qarqashin qasa"πŸ™„ dauka yai ya miqa mata, yace ta bata hakuri sosai kan ya shigo, fita tai da ita tana mai dariyar zaka amsa ne in ka shigo.
Bayan sun taba baccin su ne sun tashi wanka sukai sukai brush su ka shirya, hijab ta dora akan kayan ta matsattsu da tai ma mijin ta kwalliya da su kan ya fita, sun shiga bangaren na su Innar mu lokacin ta gama.raba abin karyawa, tace akai masu sai ga su sun shigo, duqawa Juwairah tai har qasa suka gaisa," Ya jikin Nafeesa tace bakiji dadi bane yasa ya aje bai baki ba" zare ido tai cikin duqar da kai," da sauqi Innarmu na ji dama sosai" to Allah ya qara lfy, yasa amarya za ai min ko ango, danni na gaji da lfy sa banga qaho ba aure wata na biyar kenan shiru ba magana" ta fada in a form of wasa take, amma duk wanda ya kula ya san magana take fada mata, murmushi tai sosai tace" Innar mu karki damu komai lokaci ne amare za a samo maki masu yawa da masu kawo cefane har sai kince sun isa haka" tana fada ta miqe tai wajen Baba Balarabe ta gaida shi, sake baki Innar mu tai, shiko gogan be gane magana suka sakar wa juna ba, dadi yake ji wai Innar shi da matar shi akwai shaquwa, har suna magana irin wannan a gaban shi, matsawa yai yana" akwai abinda zan taya ki ne Innata?" Murmushin qarfin hali tai ta ce eh ba a rasa ba, dan dai kawai kar ya koma wajen da matar shi take, " Baba ina kwana?" Lfy qalaou diyar albarka, kina lf" " lfy qalaou babana" " to madallah, Juwairah ina son ki ta hakuri da wannan Innar taku, wani hali ta dakko d ni kaina ta canja min kwata2 ba kamar yanda na santa ba, dan haka kema sai kinyi hakuri, abotakar ta da Goggon ku ba abu ne mai kyau ba, na yi nayi na raba su amma abun yaqi" " Ba komai Baba , ai uwa ce a wajena Innar mu ko da ba matar ka bace, mahaifiyar Yah Jabeer uwa ce a wajena, tinda ita ta haife shi, kuma shi din mijina ne, in ban so mahaifiyar shi a tawa ba ni kaina ba zan samu kwanciyar hankalin gidan aure ba, rikicin yawa zai min, da mahaifiya ma ana samun sabani dan haka ita ma a hakan na dauke ta, watarana ba zatai ba" " Allah ya miki albarka , halayyar mahaifin ki da mahaifiyar ki ba wanda kk bari" murmushi sukai dik, bayan sun gama gaishe2n su suka koma suka karya ," to ni zan wuce sai na dawo, ki kular min da kanki, kar ki wahal da kanki " tasowa tai ta zagaye hannayen ta a wuyan shi shi kuma ya zagaye qugun ta sukai ma juna kiss sosai, da kyar ta kwace kanta, sai wani shinshina ta yakeπŸ™„ " Yah zaka makara fa, ka tafi cikin amincin Allah, Allah ya bada kasuwa mai yawa mai albarka, ya kare ka daga haramun komai qanqantar ta, Allah ya hada ka da halal komai qanqantar ta, ka kular min da kan ka, ka tsaida sallah akan lokaci, in kaji yunwa ka taimakeni kaci abinci, kaga yanzu ba da bane ba abubuwan da sai na ci gaba da dafa maka kana tafiya da shi, karka barmin kan ka da yunwa kaji?" " Karki damu an gama ur higness" ya dan duqa alamar gaisuwa, dariya sukai ta raka shi har waje, ta dawo daki ta hau gyara wajen da suka ci abinci.









" kai jama'a wai dan tsabar baqin ciki na aje flask din nan anan an kai min shi can, ko uban wa ya ce a tavan kaya oho, shikenan mutum in yana haushin talaucin da yai mai katutu sai ya dinga taba kayan da ba nashi ba yana canja masu waje? Oh ni sarai na ga abin da ya ishen yau" kamar ba zata amsa ta ba amma taga dacewar bata amsar" Hmmmm Allah nawa inji bamaguje, to ai dai har yau wata kusan biyar ban ga daya daga YAN ABUJAN sun yi koda waya bane balle nace ko an yi maki wani aike na azo a gani, ana nan dai yanda ake, ba wani hura hanci da za ai mana kuma " haba kamar ta ari baki dan masifat da ta taso mata lokaci daya ta yunquro,sai bala'i take tana gore2n ai abinci ma wataran ita ke taimakawa, Mama tace daga yau in ta haifu karta qara taimakawar taga in bazata rayu ba ita da danta? Ammar ne ya kama hannun maman shi yana kuka, dan baya son hayaniya shi sam, daukar shi tai sukai daki sika bar Goggo na kumfar baki.








Oga Zaks na gani sun fito daga wani daki mai duhu sosai, Alh Kalla dauke da Saudat
Alh Salihu dauke da Suwaiba, suna fitiwa, " to ku maida masu sabbin kayan da kuka zo da su kuyi gida,nan da awa uku zasu farka, kuma ku kwanta gefen su a matsayin bacci kukai, domin wannan magungunan da sukai ta sha zasu sa masu kasala da ciwon jiki, na kammala duk wani aiki da za ai akan su, kudi kuma sai kun ce sun ishe ku, dan mahaifar su na da kyau sosai, Dodo yayi farincikin samun ta, ba a taba kawo mata irin wannan ba, nima kuma shaida neπŸ˜‹, hahhahaahhha" godiya sukai suka canja masu kaya sukai mota da su sai cikin.garin.Abuja, kowa ya dau hanyar gidan shi, fadar kyau da tsaruwar gidajen nasu bata baki ne kawai, readers ku hango kowanne gida mai kyau kawai a idon ku, a gado suka aje su suka kwanta gefen su sukai ta baccin asara, basu suka farka ba sai wajen lq'asar, miqa Suwaiba tai, tana hamma, tana kallon dakin nata, ko ta ina dakin ya ruda ta, ko tunanin komai ba tai ba sai na bari taga wannan gidan na ta mai dimbin kyau, tashi tazo yi taji wani.ciwo a cikin ta komawa tai.ta zauna, tana "wasssshhhhhh Allahna, me ya samen a ciki kum? Duk jikina ciwo yake" kamar a tare suke wannan maganar da Saudat domin tafi Suwaiba raki harda kuka, a rude mazan suka tashi kamar ba abinda ya faru" me ya same ki Sweetheart?" Cikina" dagawa yai ya gani," Ayya kiyi hakuri zai warke a hankali hatsari muka samu a hanya, ke da yar uwar ki kwalbar cup din da kuke shan drinks ta cake ku a ciki, amma mun kaiku babban asibiti an dinke wajen, so a hankali zamu jira ya warke mu ci gaba da shan amarcin mu ko" ya fada tare sa jawo ta jikin shi yana shafa ta, kwantar da kanta tai a jikin shi kamar ba ita ba, tashi yai ya je ya hado mata abinci tana daga gadon ya aje mata, ya zauna yana bata a baki, wani dadi ne ya lillibe Suwaiba yau mafarkin su ya zama gaske, tana gama wa ta dau waya ta kira Goggon ta, wayar a kashe take ta kunna ta tanakiran ta ko bugu daya ta dauka kamar jira take, " haba yar nan yau wata biyar da kwana uku, kun tafi shiru ba magana ba aike" wata biyar da kwana uku??????............
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ 'YAN ABUJA πŸ’…πŸΌ




BY HAERMEEBRAERH







Page 9:












Tinani ta ke son tayi, amma kanta ya kulle sai pounding yake, nan da nan ciwon kan da take ya qaru sosai, komawa tai ta kwanta, tai qoqarin daina tinanin" Babe what us wrong?" " kana ke ciwo sosai, so nake na tina abubuwan da suka faru a tsakanin wannan watannin da akai auren mu gaba daya ban sani ba" " ki dena yawan tinani likita ya hana, saboda zai jawo maki ciwon kai mai tsanani, ki kwantar da hankalin ki kinji, aikin da akai maku ne yasa kuka kai wadannan watannin ba tare da sanin inda kan ku yake ba, nj dinnan da kk ganni sai da nai sati uku a asibiti, abokina kuma wata daya da sati biyu, kafin mukaji sauqi" tausayin kansu ne ya kamata, lallai ashe hatsarin babba ne? A haka bacci ya dauke ta shi kuma yai palo yana murmushin samun nasara, waya sukai da Alh Kalla, " aboki ya ka qare da wannan 'yan rigimar?" Komai ya tafi as planed, ban samu matsala ba, wannan shegiyar uwar tasu ce taso sawa mata ta tinani, na kawar da shi, yanzu haka bacci take" dariya suka.saka, " ai ni tashi tai tana min shagwaba naji kamar na manta da ciwon na dan more ta kadan, dan sai ta min kyau sosai" " shegen sama, ana halin neman yanda za ai a rufawa kai asiri kana neman kayan dadi" dariya sukai tayi" anyway na mata dabaru irin namu na manya ta bar zance fatan ta Allah ya bata lfy, kasan har yanzu maganin bai gama.sakin su ba, bacci take tayi" " haka ne, to sai dare in mun hade a gidan Oga, yau akwai meeting" k to ba damuwa sai daren" kashe wayar sukai kowa na jinndadin samun nasarar da sukai, yanzu tinanin su bai wuce yanda zasuna samun jini da aka ce suna kawo wa duk wata ba daga matan nasu, dan su ba sa son suna satar yayan mutane, ana tsafi da su, aikin zai basu wahala, kuma kar wataran a kama su, dabara ce ta fado mai na yanda zasu na samun jinin daga wajen su, murmushi yai sosai, " dan ta rashin haihuwa me sauqi ne, tunda ba ni aka cirewa mahaifa ba bare na damu, 'ya'ya dama takura ne, sanda na so haihuwa na nemo matar da zan haihu da ita, dariya.ya dingayi kamar mahaukaci sabon kamu. Ni ko nace hmmmmm kwadayi mabudin wahala. " Ni dai marka na gani da yin abinci kullum nai na talla nai na gida ?" " nima haka gaskiya, wannan yar rainin kullum sai dai mu dafa mu bata, ga Baban ma ya tafi har yau bai dawo ba " tab ai ko yau ita zatai tuwon dare ko taji a jikin ta, ni hutu ya samen, dan ba zai yu.na nemo na tuqa kuma na bata ba inaaaa" "sai Markaaaa, uwar gidan Talle, an buga an barki" yaran suka fada cikin hada baki da dariya da shewa, ita kuma ta wani dage qafa tana zaune a qasa ta turo dankwali gaba, tana kada qafarta da tai fururu, " je ki kiran ita Huwaila" da hanzari ta miqe tana gyara daurin qirjin ta, tana tafe tana banqaro qirji, qugun kamar an daurawa tabarya zani, " Amarya ki zo Marka na son magana da ke" kamar ba zata amsa ba da dan duk.tana jin su, ga wani mugun tsoron su da take ji yanzu, dan duk wani rashin mutunci da yake faruwa a kunnen ta, yau da gobe duk tana jin su, fitowa tai dan ta tsira da jikin ta, dan yanda suke ikirarin dukan ta kullum tasan za su aikata, " kinzo ba zaki magana ba ma?" " gani" " to ki bude kunne da kyau ki ji, daga yanzu ke zaki dinga girkin gida, su yaran sj ji da na siyarwa, ba zai yu nai ta wahala ba a gidannan, ke kina nade a gado, saidai na dafa na miqa maki, ki cinye ki gyara daki ki wanka ki koma ki kwanta, ai ba abinda ya kawo ki kenan ba, bautar aure kika zo, dan haka kula da yaran tsakar gidannan ma yana ciki, tsarkin kashin su da masu wanki, duk naki ne yanzu, in dai hutun amarci ne sati daya budurwa, bazawara kwana uku, ke ko ban san ame zan saki ba, tsabar adalci irin nawa wata biyar da kwana hudu na baki kika huta, dan haka daga yanzunnaj ba sai anjima ba ki dau aikin ki" " wo ke wo ke markan Talle" yaran suka dauka suna ta mata kirari tana kada qafa tana hura hanci su kuma suna dariya, " banji kin amsa ba " " to" ta ce ta juya zata tafi taji wani daga yaran yana " Naaa gaaamaaa" wani kuka ne ya taso mata, tinawa da tai tinda take bata taba daukan Ammar ba balle ta kai ta ga mai tsarki, gashi yau za taiwa dan wasu, kuma an maida hakan aikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login