Showing 30001 words to 33000 words out of 69565 words
game da warin gaba" " Oh k wannan, dama muna magana ne akan macen da take fama da warin gaba na farko dai akwai na lalura, akwai wanda mace da kanta take jawo wa kanta" "hhhhhh kaji Matar yaya wai mace ta jawo wa kanta kamar yaya? Kana sane kabar jiki yaita tsami" dariya sukai sosai suka tafa, " Allah da gaske nake, yanzu misali Nafee, ke ce kin tashi a rana kin wuni da pant daya a jikin ki, kin je fitsari kin yi fitsari baki wanke wajen sosai ba kin maka pant kin mayar, kin yi bayan gida kin maka kin mayar, sannan da jiqar da komai kk mayar wa, ki fadan pant din dan uwan ku ne da zai qi wari?" " hhhhhhh wallahi dole yayi amma dai misalin nan dama ba dani aka buga shi ba a canja gaskiya a saka Salma" " wulaqanci yayar tawa, Allah sarki mutan Abuja ana can ana shan dadi an manta da dangi" " hmmm ke dai bari buri ya cika, Allah muma ya sada mu da mafi alkairi" " Ameen dai" " to yanzu fadan ya za ai ai maganin wannan warin dan Allah dan akwai yar makarantar mu, kin zauna kusa da ita sai kinji wannan warin, dan ba zanji kunyar fada mata ba, da azo ana ta gulmar ta tana jin haushi" " Allah sarki, aiko gwanda ki sanar da ita, dan aboki na gari ke wayar da kan abokin shi, kina ji ba, a rana a baki canja pant a ki canja sau uku, ya zama na kina da tsimma ko towel qarami a toilet din ki wanda in kikai fitsari ko bayan gida zaki tsane wannan ruwan, sannan in kin zo tsarki ki fara da gaba ko da baki komai ba, sannan baya, karki hade wajen wajen wankewa, in kk gama kk goge wajen sai ki maida pant din ki, in rana tayi kikai wanka sai ki canja, da dare ma haka, ba yanda za a same ki da wari ko da baki shafa misk, balle a same ki kina wanke wajen da ruwa mai dumi da kk zuba zuma asalin me kyau, wannan wanke gaba da ruwan zuma ya samo asali ne daga Annabin rahama yana daga taskar magungunan daya bayar muna amfani da shi, bake ba warin gaba in dai kina wanke wa da ruwan zuma kina saka misk, kina tsanewa in kinyi bayan gida, ina fatan na amsa tambayoyin ki Hajiya tambai" " hhhhh wallahi kin biya ni kin amsa har da wanda ban ma zata ba ke dai Allah ya barki da yaya, ya sauke ki lfy" cikin jin dadi tana shafa cikin ta ta amsa, tashi tai ta tafi bayi da butar ta a hannu, bayan ta fito ne take ce ma nafee" Nafee gobe ne kin san ranar gyaran jikina ina zan samu dankalin turawa pls na wa ya qare" karki damu zan samo maki kan gobe, ji cikin ki ya fa girma amma kk maganar gyaran jiki, ki bari ki haihu mana" " Tab aa ni dai ki samo min, in babu ma ina da zuma da sugar kawai ki samon lemon zaqi ko daya ne ko biyu" " to Allah ya kaimu, bari nai wanka na fita makaranta" "to Allah ya bada sa'a, bari na dan huta nima".
" Alhj wannan itace mata ta da kuka karba min auren ta a garin kano, dama na dawo da ita nan ne dan na dinga samun kulawa, zama ni dayan ba dadi" Talle kenan ya fada yana sosa qeya, murmushi uban gidan na shi yai yace" Allah sarki ai ba damuwa, hakan da kai kayi tinani, kuma ka kyauta, ina maku fatan alkairi, Allah ya bada zuri'a dayyiba" " Ameen" gaida shi salma tai kanta a qasa tana wasa da gyalen ta, ya amsa ba tare da ya kalli in da take ba, kudi ya qirgo dubu goma ya bata, yace gashi ta sai wasu abubuwan da take buqata, amsa tai hannu na rawa, rabon data riqe kudi haka ai ta manta, tashi sukai suka fito, suna isa daki ya miqa mata hannu, fuskar nan ba walwala," me zan maka kuma" ta fada cikin tsiwa, " dan uban ki ni kk tambaya me zaki min, to in baki san me zaki min ba bari na fada maki, kawo su nan" alamun da ta gani na ba wasa yasa ta miqa mai tana hawayen baqin cikin ga samu ga rashi, murmushi ya fara yi jin dumus da yai," Ko ke fa salameme na, yanzu ai kin ga ko dari biyar na baki ai yafi na qattin qauye masu baki dari da hamsin ko" juyo wa tai cike da bala'i tana kallon shi kuma sai ta fasa dan wani tsoron shi daya kamata, gani tai yana cire kayan shi, ita ko bata shirya ba, ga ciwon jiki da take fama da shi, gashi shi in ya fara abu bai san ya bari a huta ba, sai ya gajiyar da mutum, kuka ta fara tana" ni na barma dari biyar din dan Allah ka bari sai nan da kwana uku, na gaji banda lfy" dariya yai sosai ya maida kayan shi" da kyau matar manya matar Dan Abuja kenan, ku baku da buqatar kudi ai, ni na fita to ga wannan ki leqa waje akwai shago ki siyo kwaki da sugar ki sha, ina jin har canjin gyada zaki samu ma" nera dari ya wurga mata ya fice yana wata tafiyar yan duniya a shagide, kuka ta durqusa tana yi, " wai ni ina yan uwana ne, suna can suna jin dadin su sun manya da rayuwa ta, basu san a halin danake ciki ba,Oh Allah ka kawon dauki, na tuba, Juwairah kin huta, dabaki zabin aure ina zaki ba, gani ina cin ubana a garin da na taso da kwadayin yin aure cikin shi" kuka take mai ban tausayi, yunwar dake cin ta ce ta dawo da ita daga tinanin da take, tashi tai ta wanke fuskar ta, ta saka mayafi ta je ta siyo garin ta da sugar da gyada, hadawa tai tana sha tana kuka,ganin duk talaucin su ba su shan gari a gidan su amma yau gata da gari, share hawayen ta tai, ta jingina da katifar su, a haka baccin wuya ya dauke ta.
" Adda Suwaiba ya kamata fa mu je ganin gida yanzu haka, haba tinda muka zo yau watan mu na takwas kenan fa, muna cikin na tara, bamu taba zuwa gida ba, ba a taba zuwa mana ba, ga labarin Salma shiru, har yanzu" " hakane kam ya kamata muje muga ya su Goggo suke, batun Salma ki daina damun kanki tana can suna cin amarcin su, kin san mijin ta ma ba laifi akwai kudi, wataqila ma basa qasar nan" " haka ne Allah ya jiyar da mu alkairi, amma nikam na tambaye ki?" Ina jin ki" " dan Allah baki zargin komai game da mazan nan namu kuwa?" Kamar ya fa?" Tina wa da tai in ta sake Suwaiba ta san me ake ciki kashin su ya bushe ya sa tai saurin kauda zancen ta basar tace" ba komai yanzu dai mu tambaye su, yaishe zamu gida" " Ba rana balle wata" amsar da suka ji kenan ana basu bayan an bude qofa an shigo, " ke tashi mu tafi gida, ai an sada zumuncin haka, ku da kuke son Abuja kamar ran ku, in ban manta ba, Saudat kan mui aure cewa kikai, in Allah ya baki miji kuka tare a Abuja sai kin shekara biyar baki je ganin gida ba, ko ba ai haka ba?" Cikin qunar rai da kwallar da ta maqale mata tace" anyi haka, amma a da ai ban da isasshen sanin ya Abujan take kuma gani nake zan iya amma ni yanzu gaskiya gidan mu nake son zuwa naga uwata" wani hatsabibin kallo ya watsa mata, ba ta san sanda ta durgusa ta dau jakar ta ba tai hanyar fita, sallama yai wa abokin shi wanda daga jin warin da suke sai da suka biya sukai tatul, nikam nace Saude Allah shi kyauta karki daku yauma.......😂
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
MAMAN YOUSUP
Mutan Gwambe ina godiya sosai da nuna so da qauna, kuma saqo daga Salamemen Talle tace a sanar dake bata da qawa sama dake tana son ki sai kin isa ABUJA adama da ke😂😝 ME LOVE U XOXO❤
Page 18:
Goggo Sarai ce ta qame kan kujera tsabar ba a iya samun wajen ba ma, da nuna ita bata gaji arziqi ba, iyakar wajen ta aka shata aka gyara, baqin cikin da kanta da kanta take, dan ko ba wanda ya kula da ita, ita amma gani take all eyes on her, ita a dole ga uwar masu kudi, mijin Salma kawai take jira su dawo daga waje a yo mata kabakin arziqi na waje, Ammar na hango yana tafiya dugui2, dan ba wai ta gama kwari bane, ya zo wajen randar ruwan Mama Bilki, da dikkan alamu qishirwa yake ji, Mama Bilki na daka tana baccin tsakanin azahar da la'asar( bacci ne da in bawa yayi shi yake samun lada daga wajen Allah) ita ko hakimae ana zane ana kora jus da meatpie, ga mafici a hannu irin wanda ake kamar zuge shi dinnan ta kwama uban baqin glass a ido na ba mutunci dinnan, Abban su shi ke da bangaren ta yau amma gudun wulaqanci sai dare yake shigowa, kan tace ita ke ci da gidan, ko makamancin haka, dan haka yana qofar gida, Ammar ne ya dakko cup yai ta buqawa a jikin randar," Yauwa yaro fasa wa uwar ka dan arziqin da ya rage mata ka huta gadon mugun abu kawai" bata gama rufe baki ba ya saki fitsari, gangarowa yai qofar ta, habaaa ai kamar an watsa mata ruwan zafi, ta miqe kafin ta isa ya fara qoqarin tafiya yana kuka, da alama ba iya fitsarin zai ba, daidai fitowar Mama Bilki da shigowar Abban su, hannu ta sa ta wanke Ammar da wani lafiyayyen marin da ko Maman akai wa sai jikin ta ya gaya mata," ganin wannan kini babbun iyayen naka masu son abin duniya da har suke ganin Da namiji ya fi Ya mace daraja ba zai hani cin uban ka ba, in banda baqin ciki da aka koyawa yaro qarami tin yana ciki, duba fa ku ga yanda ya tsanyaran fitsari a qofata yai gaba, to ba zan lamunta ba" Ammar tsabar kuka ya gigice sai ga kashin ya biyo baya, zuciyar Mama Bilki tafasa kawai take ba iyaka, tin da Abban su yake da ita bai taba ganin bacin ranta haka ba, ita kanta Goggo Sarai ta tsorata , wandon Ammar Mama Bilki ta cire ta wurga a jikin qofar da aka canja wa Goggo Sarai, qofa ce irin ta qarfen nan mai kauri milk color, ta aje Ammar din ta isa jikin qofar ta samu wandon ta goga sosai har labulayen, sannan ta dawo ta daga hannu zata wanka mata mari, amma sai naga ta tsaya,( nace kash dama kin qarasa mun sha kallo💃🏻) me ya tsaida ta oho, daukar Ammar tai da yake ta kuka yaqi shiru ta je ta fara gyara shi sai da ta gama taje ta dauke wandon nashi ta wanke ta shanya, sannan ta qara wanke mai jiki dika, ta bashi ruwa da abinci ta goya shi sai bacci, yana yi yana ajiyat zuciya, wata irin wuta aka dauke a gidan gaba daya , ba mai iya cewa komai, Goggo Sarai na tsoron tace kanzil yanda Mama Bilki ta bata rai bata san me zai je ya zo ba, ita kuma Mama Bilki ta fasa marin ta ne ganin datajar Abban su dake bayan ta, shi kuma ya fuskanci hakan, sannan ya yi shiru ne saboda kar ya bata damar magana ya san kuka zatai dan zuciyar ta cike take da baqin ciki, sai da ya tabbatar ta fara sauka tinda ta ci gaba da yan aikace2n tsakar gida sannan yace" kin ban mamaki Sarai ba kadan ba, ki duba kiga abinda kk aikata, yanzu marin da kk wa yaron nan ko ni ki kaiwa ai sai naji a jikina ba shi ba ma, dubi yanda yatsunki suka kwanta a kan fuskar shi, kamar quna, haba dan Allah, kin kyauta kenan, baki taba ganin fushin Bilkisu haka ba , to ina mai tabbatar maki ki kiyayi sakata a irin fushin nan bana kusa, dan duk abinda ta aiwatar akan ki ke kk jawo, kinga misalin hakan ai dazu ko?" A sannan ne ta samu bakin magana, " eh tinda kun haifi dan gwal, dole mana ku fifita shi akan komai, to da dan da uwar na san meye matsalar ku, baqin ciki, kuma nan gani nan bari dumamen mayya in dai nice ni da Yayana yan albarka" juyawa tai fuuuu ta hau cire labulayen dika aka watso su tsakar gida ta dau daya ta goge qofar dakin da shi, ta saka ruwa ta wanke, ta qara gogewa da labulen masu kyau din, da su ta gyara wajen, duk kyau da tsadar labulayen haka ta saka hijab din ta ta fita waje ta watsar ta dawo, tana wani isa da taqama taje ta canja wasu," a hayyyeeeeee ayyuuuuririiiiii, to bari kuji sau goma wannan shegen tsinanne yana bata qofa sau go........bata ida fadin me take so ba ji tai qummmmmm a bakin ta, ludayin hannun Mama Bilki ne ta saita shi a bakin Goggo Sarai, ihu ta saka, ita kuwa ta je ta durqusa ta dau abin ta ta juya ta ci gaba da aikin ta, Abban su mai zai in ba dariya ba, " Kai amma Gimbiya yau kam sai dai ace na zama munafukin mata, amma kin burgeni, ke kuma da dai da kk kira shege, duniya ta san ni ne uban shi, sannan, tsinanne da kk kira min da ba zakiga tsinewa a 'ya'yana ba inshaa Allah ina mai musu addu'a ko keme abin qi Allah zai karen su, sai dai kiga tsinewar a kan kan ki dan ba yau na fara jin kin kira min Da da wannann sunan ba, ke yanzu ba abin kunya bane ace yar haka ta fara shiga tsakanin ku? To ina qara gargadin ki ki kiyayi randa bana gida ki taba wannann baiwar Allah ina tausaya maki" ya qarasa maganar cikin dariya ya fita qofar gida, duk abinnan da ake Mama bata ce uppan ba aikin ta take kawai, Goggo baki ya haye sama, abinka da farar mace fatar tai jawur, daki ta shiga ta dau waya ta danna Number n su Suwaiba, dannawa tai tayi ana turanci, gashi yau harda Malam din akai fadan ba mai duba mata yaji me ake fada, kama kan ta tai da taji yana ciwo ta hau kuka, zama tai gefen tamfatsetsen gadon ta da ta sake mai matuqar kyau da girma, kukan ta tasha ta miqe ta kwanta, yau ita Bilki ke bigewa baki da luddai??? Oh duniya, da kudin ka da komai ba za a ji tsoron ka ba yanda taga ana yi wa masu kudi, to kwarjini ne bata da shi ko me, miqewa tai taje gaban madubi, ta kalli kanta daga sama har qasa, ga atampa nan mai tsada sarqar gwal.da zobuna, komai ya ji, dubawa tai taga ashe fa har yanzu ko umara bata taba zuwa ba balle Hajji? Murmushi tai tace " Gaskiya mana, to ai ko kashin ku ya bude dan kuwa dole ne wannan shekarar a sake farali da ni naga ta raini" komawa tai ta kwanta, bacci ya dauke ta, cike da mafarkai kala2 na ban tsoro, ta dade tana irin mafarkan nan, 'Ya'yan ta na cikin matsala, amma sai ta dangan ta shinda sharrin maqiya, in suka dawo za su je neman taimako.
Yau ce ranar da Juwairah ta wate domin gyaran jikin ta, Yah Jabeer din ta na gida, in da ba zata iya kaiwa ba shi yake taimaka bata ya mata, misali yanzu ba dika take iya wanke bayan ta ba, to ga wannan abin gyaran jikin da zatai yana buqatar taimako, da farko na ga ta hada lemon zaqi a wani kwano qarami, ta zuba sugar cokali daya, da zuma cokali daya, sai ta saka lemon tsami daya, ta juya su sai da sugar n ya narke sannan ta dakko soson ta, ta miqa mai daga shi sai gajeren wando( yammaza zasui aiki😂) gani nai zai tsoma soson a wannan hadin kan ya tsoma da sauri ta riqe hannun shi" Yah pls i want some ya ban sha'awa" tana turo baki, gaba cike da shagwaba" ke fa kk ce kin ware kwanon nan na gyaran jiki ne ko abu za a debo kin dinga kyankyami kenan shine yai zaki sha abun ciki?" Cike da mamaki," ni dai zan sha , plsssss" miqa mata yai a spoon din, aiko ido alumshe ta shanye kusan sai da ta shanye rabi yace " tsaya za mui abunnan ko na dawo ta gaba na qarasa baki ki shanye?" Kada kai tai alamar Aa su ci gaba da gyaran jikin, sai sude bakin take, fara wanke mata fuskar ta yai, da wuyan ta da bayan ta , da wannan hadin da soson, zuwa hammatar ta, sai ya dawo ta gaba ya wanke mata tsakanin cinyoyin ta zuwa cinyoyin ta, guiwar ta a haka saida ya hade kaf jikin ta, bayan sun gama ne tai mai godiya, tare da furta mai kalmar da ta zama masu al'ada wato" I love u" maimaita mata shima yai ya daga ta, " wai wai wai Babyna gaba daya kinyi nauyi yanzu, da gyar fa na dago ki" turo baki tai kamar zatai kuka, dama yasani tsokana ce, dariya ya fara yana kame bakin shi, tura hannun shi tai daga kafadat ta zata fara tafiya, " Mai ciki ihmmm ganinan tafe, me ciki, wallahi bani son sunan nan" juyo watai ta biyo shi suka fara zagaye bangaren su tana kukan shagwaba,