Showing 60001 words to 63000 words out of 69565 words
mero, sai ta bangaren Innar mu, suma biyu, Innar Fateema, da Inna Aishe, sai wata aminiyar Innar mu wato Baba Maryam, ba su isa kebbi ba sai takwas na dare, gaba dayan su jikin ta qaura yai la'asar, tun Nafee na irin abun amaren nan a mota tini ta janye mayafin a fuska ta sake, tambaya ko tafi nawa tana ma, abokin angon dake tuqi, dan motar daga ita sai abokin angon dake tuqa su sai wani a gefe sannan ita da angon, mota uku sukai, janyo ta mijin ta yai jikin shi ta kwace a kunyace tin suna Gusau, da wahala tai wahala da kanta ta dora kanta jikin shi ta sha baccin ta, ko da ta farka ta zaci zataga sun kusa isa amma taji shiru, kai na taqaice maku sai da Nafee ta matse kwalla, tinanin ta daga Kebbi Nigeria ta qare,lokacin da suka isa ana ta kiraye2n sallar isha'i ne, suna zuwa gidan dake unguwar Alieru Quaters, a bangaren Three bed rooms a nan aka aje ta, fasalin nasu gidan daban ne dana sauran, ya tsaru iya tsarin zamani, kana kallo zaka san gidan masu hali ne, yan uwan ta kam sai san barka suke, da mata addu'ar Allah ya zaunar, kwanan su biyu aka tashi juyowa da su, Saudat kuka tasa data tuno hanyar da suka kwaso, sai lallashin ta ake abokin angon daya tuqo su yana ta mata dariya" a gaskiya zan fada ma Umar farouq ya shirya matat shi raguwa ce" ai tana jin haka ta miqe ta goge hawayen ta tare da zabga mai harara" inji wa? Ni kar ka wani fada mai mu tafi" dariya aka saka dukka wajen banda Nafee da take rabe a gefen mijin ta tai kalar tausayi, ai ko suna sa kai ta fashe da nata kuka, bayan sun fita ne suma suna cike da tausayin ta angon ta ya dauke ta cak yai ciki da ita yana lallashi, su Saudat sun kama hanya sun baro nafi, wajen mijin ta mai matuqar so da kulawa, tare da tausayin matar shi, dake tashin qarfe bakwai da rabi sukai sun iso kano qarfe wajen uku na rana ne kowa sai da aka aje ta gidan su, drivern daya kawi su Mama Bilki ne ya tsaida Saudat, " ba daban Farouq ya rigani ba kuma yana matuqar son ki, tabbas dana kawo kaina nima, amma ba zan iya tafiya bam sanar dake sirrin dake raina ba, na kamu da son ki a kwanakin nan da mukai kusan wuni a tare daku, ina maki fatan alkairi, Allah ya baku zaman lafiya da zuria mumina saliha" taji dadin fahimtar shi da kuma yabawa da hankalin shi sosai dan haka ne ma yasa tace mai," na gode sosai da siyayyar ka a gare ni, ina ma ka fatan alkairi, Allah ya baka wadda ta fini, tabbas abotar ku akwai amana kuna da halin manya," murmushi sukai sannan daga baya ya mata sallama ya ja ya tafi.
Kwana biyar tsakani, bayan waya da musayar saqwanni dake tsakanin masoyan hudu, sai gashi wata lahadi da yamma, wasu dattijai suka zo gidan Abba Baballe, da nemawa Farouq da Salmanu auren su Saudat din, a wasu maka2n motocu suka zo, wanda yasa Abba jin tsoron kar a maimaita yar gidan jiya fa, amma saka makon bayani da suka samu shi da Baba Balarabe, da kuma shaidu sun tabbatar da cewar tabbas mutanen kirki ne, a nan take suka roqi arziqin a daura auren in ba damuwa, saboda ba a kusa suke ba, kowa da garin da yake aiki, shi Abban su Farouq mazaunin Abuja ne, sai qanin shi dake lagos, dayan kuma a kebbi yake, Abba Baballe sawa yai a kira wani kawun su daya rage masu da abokin shi babba, nan take aka daura auren su Saudat da Farouq, Salma da Salmanu, akan sadaki dubu hamsin hamsin, tare da alqawarin Salmanu zai riqe yaran Salma kamar nashi in sun masu izini, su Abban Suwaiba sun yarda amma sun qara da cewa in ba takura, suka jaddada masu, cewa shi Salmanu ba Salma kawai yake so ba, har da Yaran ta ya gani ya kamu da qaunar su dika, Abban Suwaiba yaji dadin hakan sosai, a haka taron ya tashi cikin farin ciki da yarjeje niyar sanda Amaren da angwayen suka shirya a tsakanin su ayi tarewa.
Bayan wannan daddadan labarin ya iske su Juwairah ne ta roqi Jabeer akan ya barta har tagama batun tarewar Yan uwan ta kan ta koma, ya amince amma shi da yamma zai koma Abuja sabida aiki, sun bari akan in ta kammala ta sanar da shi sai su koma tare, kudi ya bar mata mai yawa a hannun ta kan ya tafi, tin kan tafiyar kuma sai tai tajin ba dadi zai tafi ya barta, bata son abin da zai raba ta da mijin ta , musamman wannan bata san kwana nawa ba zai dauka, shima gaba daya bai som rabuwar tasu amma dole ya qarfafa mata guiwa , haka suka rabu kowa na kewar dan uwan shi. Ta dawo daga raka shi ne taji wayar ta na ringing dake kan fridge din ta, dauka tai taga Nafee ce, bayan sallama da gaisuwa ne tare da tambayar bayan rabuwa Nafee tace" matar yaya kunyi min mntuwa fa, kun manta tsimi na ba a sako da shi ba" " Subhanaka ya raheem, ai ko kinga har yanzu ba wanda ya kula, ba damuwa ai kinga yanda na hada maki wancan, ki hada wani wannan na ba su Adda Saudat, keee an daura auren su ma jiya, tarewa kuma ance ba yanzu ba sai sun shirya magana da mazajen su, iyayen sunce basu buqatar komai sai matan yaran su za a kai masu" cikin murna Nafee ke addu'a, bayan gama murnar ne tace" nifa matar Yaya na manta wasu abubuwan dan sake fadan mana pls" " kai Nafee ko angon ya kwashi romo har da basirar ki ne?" Dariya sukai Nafee tace cikin shauqin son mijin nata" matat yaya wato My love daya ne tamkar da ba iyaka acikin maza" " Oh ni Juwarah yarinya ta fitsare bari nayi na gama fada maki na kashe wayata, ina nan ina tausayin ki ashe ke kin gama.zama yar hannu ma abin ki, " dariya sukai tayi kafin Juwairah ta lissafa mata kayan hadawar da suka qunshi" kanin fari kadan zaki saka ba mai yawa ba saboda masu magungunan gargajiya sun tabbatar da shan shi da yawa na kawo ciwon hanta, dan haka ki saka kadan sai citta mai dan yawa, minannas, sai ki matse ruwan rake mai yawa, ba a qara wani ruwan fa da wannan ruwn raken iya adadin yawan dakk so da shi zaki amfani, sai ki samo zuma mai kyau sosai ki saka sai ki dake kayan qamshin nan ki saka a ciki, sai kin ga yai kauri kadan ma'ana bai irin ruwa tsululu ba, zumar ce zata saka yai kaurin, ki dinga sha da yamma,amma pls wajen nemo zumar ku tabbatar me kyau ce kin san yanzu an bata zuma, na ba su Adda saudat wannan nakin nima na dan sha" " na gode matar yaya sai an jima ki shan fan bbyna, ina gaida yaya" nima ina gaida angon ki" .
Wahse gari sallama taiwa Innar mu ta tafi gidan su ba zata dawo ba sai an gama tarewar yayun ta, ta kaiwa Yayun nata wannan tsumin, sannan tun da suka fada mata mazan su sunce ai nan da kwana biyar za a kaisu su tare, nan da nan ta hau taya su gyaran jiki kala2, sai ga su sun fito amare sak, itama sai da ta gyara dan a cewar ta itan ma amarya ce, tin da taje, take ma su kwadon zogalen daya sha timatir dahuwar ruwa2 haka take kwashewa, timatir mai yawan gaske take saka masu gulin yaji kayan qamshi,(wannan hadin ga masu son hips din su ya fito zasu na ci sosai har su samu biyan buqata ko su saka zogalen a danyen shi bayan sun wanke shi sai su mai hadin, sannan ana iya yin hadin da alayyahu ma) sannan ta samu kabewa tai ta hada masu da madara da zuma suna sha,( wannan kuma yana gyara masu skin din su ba kadan ba)lokaci ne na mangwaro ta dake da siyo masu mangwaro suna sha ba qaqqautawa( mangwaro na qarawa mace ni'ima sosai da dumin jiki) ga tsarki da hadin ta na musamma da baya wuce ta, isu isu suke abin su, Goggo Sarai gaba daya jikin ta yai sanyai,bata taba nadamar rayuwa irin ta yan kwanakin nan, ganin cewa tabbas Allah shine mai yi ba mutum ba, duba da cewar gashi dai duk bala'in son kudin ta, ta kai yaran Abujar kuma sun wahala, babbar ma har da nakasa, finally gashi yanzu Allah ya basu ' YAN ABUJA na kwarai, hawayen da take qoqarin mayar wa ne wani ya gangaro," Yaya ki daina kuka, in yaran nan suka gani zaki daga masu hankali" " Hmmm Bilki dole abun ya damen, bam zamo uwa ta gari ba, na tsani rayuwa da turbar dana dora yarana akai a baya" " haka ne Yaya kinyi kuskure babba, amma yanzu ai ya wuce, ya zama tatihi,kuma in shaa Allah hutun da kk nema masu su ji shi," cikin gyada kai da yarda da maganar ta ta dauki kwanon abincin ta isa dakin su ta miqa masu ta fice..........
[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
Page 33:
Washe gari angwaye zasu zo tafiya da amaren su, su Goggo Karima dai ana nan sune yan rakiya Abuja, yau shiga kasuwa, su kai har Juwairah,kudin da angwayen suka basu na siyan kayan lefen su da basu samu damar hada masu ba shi suka je suka hado, bayan sun gama ne sika fara siyan kayayyakin da in sunje zasu buqata wajen gyaran jiki ko ni'imar su, wadan da suke ganin ba samu zasui da sauqi ba a can, musamman hadin kayan qamshin da Juwairah ta basu shawarar niqa mai yawa su tafi da shi, dan ko shan shi da madara da zuma, zasu buqata, a gefe daya Juwairah ta lodarwa mijin ta kayayyaki kamar dangin qanan kaya, vest, boxers, da turaruka, sai takalma, da huluna biyu, masi kyau sosai, mamaki ne ya kama su suka kasa jurewa sai da Saudat tace" ke kuma ya naga kina ta siyan kayan maza ne, baki saiwa kanki komai ba sai tirare da kayan bacci," " Adda Saudat Yah Jabeer na debarwa, ba dan komai ba sai dan yanda shima yake man dukkan hidima da qarfi da iyawar shi, na sani komai zan mai ba kamar ya shi ba ne, sannan wannan abun da na siya already yana da su, amma kyautata wa juna na qara soyayya, kyauta tsakanin miji da mata musamman irin wannan ta tiraren da miji ya fi so, tana da matuqar tasiri a zuciyar namiji, shiyasa naga ya dace tinda ya wadata ni da kudi shima na sai mashi" " lallai Juwairere ke kin ma fi Mama Bilki iya tattalin miji, na rasa waya koya maki, ko kayan baccin ki da tiraren ki is for his on benefit" dariya sukayi" Salma ai gaba kin ga in ya tashi bani zai ban wanda yafi wannan tinda yasan ko me zan duk inda aka je aka dawo zai amfana shima in one way or another" tafiya suke suna jinjina wayo irin na qanwar tasu, a sama sukaji muryar ta"Adda Saudat ku daina mamaki na, kowacce mace tana da kaifin hankali da basirar zaman gidan miji, bambancin mu shine wata tana shiga kwakwalwa da zuciyar ta tai tinani, ta mafana da baiwar ta wasu su amfana, wata kuma dunkufe kanta take, bata son yin dogon tinani sam, bama ta son tana zurfafa tinanin ta akan komai, da matsala ta same ta sai tace sai ta nemi shawarar qawa, wani lokacin ai sa'a ta samu shawar qwarai wani lokacin sabanin haka, amma in da zamuna bude zuqatan mu da maza su ji dadin zama damu, aure daya rage mutuwa, da hakuri da sanin ya kamata ya wanzu gidan auren mu, Adda muna a garin da ba mu da iyaye acan mu ne iyayen junan mu mu zamu taimaki kan mu, dole sai mun zama masu irin wannan tinanin gudun shiga matsala kan dayan mu ya kai mana agaji" wani kallon so da qaunar qanwar tasu ke yawo a zuqatan su, a haka suka samu abin hawa bayan an masu niqan kayan qamshin, gida suka nifa a gajiye, wajen bayan azahar, alwala sukai sukai sallah, sannan sukai wanka suka ci abinci, sai baccin gajiya.
Tin da sassafe angwaye suka jera mota uku Jabeer kuma ya dakko hanya shima amma bai iso ba Adda Suwaiba da Innarmu sun zo suma, amare ana ta dan koke koken rabuwa da gida, Saudat kuwa tsoro ne fal cikin ta na komawa Abuja, ji take kamar ta fasa auren, amma ta dake, tana son tai wa mijin ta kyakkyawan zato, Adda Suwaiba anyi anyi tai rakiya tace ita da Abuja ko a film ba ta so taga Alihu a can ba, haka aka hakura aka barta she will come around wataran zata je ne, Jabeer ne ya iso, inda nan kai tsaye gidan su Juwairah ya sauka, ta sauke shi da abinci da komai na motsa baki, Amare sun daga sun bari akan in sun je zasu nemi gidan su, tin da Jabeer bai huta ba, haka suka tafi Goggo Sarai na ta zabga masu addua da Abba sannan Mama Bilki, kwalla kawai Goggo Sarai ke sharewa , bata san wannaj karon me zai faru ba," Adduar fatan alkairi zaki bisu da ita, ki daina zurfafa tunani, ki masu kyakkyawan zato Yaya," " To Bilki Allah ya kao su lfy, Allah ya zaunar da su da alkairai marasa yankewa" amsawa dukkan si sukai da" Ameen" suka koma ciki, inda Jabeer na dauke da Abrar, Ammar na wajen Suwaiba tana ta mai wasa, dan ya damu sosai da rashin Adda Calman shi, fitowa tai zata debo mai dambun naman da ya ragu a kitchen wanda akaiwa amare, giftawar ta Abrar ta gani ta ko sa kuka tana miqa hannu, komawa tai ta dauke ta, Yah Jabeer na mamakin soyayyar su, " haka suke , in dai Adda Suwaiba na kusa to pa ni na huta,sai mu yini ko Nono bata nema, sai dai tai ta bata kunun ta" " ikon Allah lallai akwai soyayya mai qarfi a tsakanin su", gama wa yai suka shirya komawa gidana su,inda suka tafi da Suwaiba itama, a motama Abrar na hannun ta, tayi bacci, sun isa gida Suwaiba da Innarmu suka tafi bangaren su , suma suka tafi nasu gidan, a hankali ta dorawa Juwairah Abrar a cinya amma juyawa tai ta qanqame ta, sai Jabeer ne yai dabara ya raba su, tafiya tai cike da qaunar yarinyar a ranta tana share hawayen baqin cikin rashin haihuwa, shafa marar ta tai daidai lokacin da ta shiga bangaren su, hawaye na fita mata masu dumi, Salihu ne dake gidan a zaune ya hangota ya tashi cikin hanzari ya isa gareta, rungume ta yai dan ya fahimci halin da take xiki, kuka ta saki mai ban tausayin mai sauraro" yanzu mine shikenan ba zan haihu ba, da ba zai taba samun mazauni a wannan marar ba? Ya zanyi da son yara dake addabar zuciyata?" Kuka shima yake sosai sai da sukai ma'ishi sukai shiru" kiyi hakuri ni na jawo maki wannan nakasar, ki gafarta min, nima ina cikin quncin rashin haihuwa,musamman inna kalli yanda Abrar ke son ki, take matuqar qaunar ki, sannan na san zaki haifamin yara kyawawa kamar ta, amma na mana mugunta, Allab wadaran rayuwata" rufe mai baki tai da sauri" pls don't say that again, Allah ya albarkaci rayuwar ka zaka ce, kabci gaba da gyara kurakuren ka na baya, ka duba ka ga ni fa yanda Allah ya maka albarka a kasuwancin nan, har fili ka siya, nan gaba kadan gida zamui mu koma, mu ci gaba da jin dadin rayuwar mu, to mene na daga hankali, Allah ke bada haihuwa ya ba wanda yaso,mu ba zamui kuka da Allah akan bai bamu ba,saboda mu da kan mu mukai wa kanmu mugunta dan haka hakuri zamu ci gaba da yi," Juwairah ce ta koma gidan ta da gudu tana kuka, garin Kayan qamshin da ta niqo wa Addan nata ta sake ya fadi a qasa, kuka take sosai har tana shessheka, wani irin tausayin su ne cike a zuciyar ta, Jabeer gaba daya ya rude" Babe me ya faru? Waya mutu, Ya Allah Sanar dani ko na sama maki kwanciyar hankali, ki sanar dani kome kk so na miki , kukan ki na daga hankalina" kwalla ce ta fito idon shi yai qoqarin mayarwa" Sweet one ka taimke ni ka bawa su Adda Suwaiba Abrar" maganar ta doke shi, kuma yaga tsantsan rashin hankalin ta,kyautar mutum sukutum, ya zai iya wannann kyauta? Amma duba da yanda take kuka sosai, hankalin ta a tashe ne yasa ya kama ta ya zaunar, ya umarce ta da ta sanar da shi akan wane dalilin zai ba da yarinyar shi guda daya tilo, bayanin komai ta mai cikin kuka bata rage komai ba, shi kanshi sai da ya share hawayen, " Tabbas roqon ki ya amsu,nima Allah ne ya ban ita ai ba ni naba wa kaina ba,dan haka na basu ita halak malak, ko bayan raina Abrar Hafsat Ta su Suwaiba da Salihu ce"sai ya kashe murya just to cheer her up"kinga da mun koma sai na sake wani zubin a nan wajen, na sama mana Abban ki ko" yana shafa marar ta" kai anan ma yau ba sai mu fara ba, har Allah ya sa a dace, kinga daga gobe sai a koma kiran ki Maman Abba" dariya ta saka ta kai mai dukan wasa ya goce ta bishi ta haye cinyar shi tana qoqarin sai ta hargitsa mai sumar kanshi yana qocewa, a haka