Showing 48001 words to 51000 words out of 69565 words
duba ka gani" daga mai rigat ta tai ta nuna mai qirjin ta da gefen cikin ta, anan ta juya wajen Saudat tace" Saudat nuna mai cikin ki kema" nuna mai tai itama tana kuka," me ke faruwa haka" Abban ya fada cikin tashin hankali ganin da yai Suwaiba ta zama Nonoless, " Abba mazajen da muka aura ta dalilin mugun son kudin mu, da influence na Goggo, Abba yan qungiyat shan jini ne su" ta qarashe cikin qunar rai da dacin da take ji a wuyan ta, a zabure Abban su yace " me kk ce? Shan jini fa Suwaiba, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Ya Allah, wannan wace irin rayuwa ce haka? Ya salam" zama yai ya dafe kan shi," to sanar dani me ya sami qirjin ki da kuma gefen cikin ki gaba dayan ku ke da yar uwar ki?" Kwashe komai tai ta fada mai, cikin kidima da tashin hankali ya miqe ranshi ya gama baci da jin abinda ya samu yaran shi, duk ta dalilin matar shi da ta kasa taimaka mai wajen ba yaran shi tarbiyya, ficewa yai a dakin ya nufi dakin Goggo," hankalin ki ya kwanta, Saratu hankalin ku ya kwanta nace, an mai damin Yara marasa haihuwa, ba zan taba ganin jikokina ba ta bangaren su, ke baki saki jiki kin haifa min yaran ba,ga shi kin ja sanadin son kudi da abin duniyan ki ya sa jikokin nawa ma zasu zama ragaggu, ban manta wa ke da kan ki ki kai kutunkutun ki ka tsaida haihuwa, wai yaran sun ishe ki, wace irin mace ce ke? Ki duba kiga Suwaiba an yanke mata nono gaba daya, banda jinin yaran nan da ake diba duk wata, tsahon wata takwas, ina zaki kai alhakin su?" A wannan lokacin Abba kuka yake, Goggo kuka , yaran kuka, Mama Bilki hawayen tausayin yanda rayuwar gidan na su cikin qanqanin lokaci ta koma take, wannan rayuwa ! Goggo ta kasa cewa komai, bakin ta rawa kawai yake, sai zatai magana sai ta ji bazata iya cewa komai ba, Suwaiba ce ta katse su da cewar" Abba ina neman izinin ka barni nai mana daki a ta can wajen, dan ba zan iya ci gaba da zama da Goggo a daki daya ba" murmushin takaici Abban su yai yace" kinji ? Kinji da kunnen ki, Yar ki ba zata iya zama dake ba? Kar ki damu Suwaiba, wannan kudin bai kamata ki amfani da su ba, kamata yai a bada sadakar su, ina da qasa, da ciment, dan dama ina da aniyat yin daki dan ku, koda kun zo ganin gida, dan haka da kaina zan yi" juyawa yai ya fita, kamar abun wasa Abban su ya fata hada qasa da komai, nan da nan Suwaiba da yan uwanta suka hadu suna taimakawa mahaifin su wajen yin ginin, harda mai ciki, Ammar ne ya tako dugui2, ya isa wajen su ya debo qasar a hannun shi ya miqawa Abban su, dariya sukai gaba dayan su, a haka Ammar ya zama shi ne ke saka su nishadi har yamma ta gabato Mama Bilki ko tana can tana masu girki har ta kammala, Goggo ba wanda ya kula da yin ta, ko kukan ta, sun maida hankali akan son yin dakin da zasu nesanta kan su da ita, ginin ya masu nisa sosai, a haka suka bar wa gobe sukai wanka, suka zauna bangaren Mama Bilki, suka zauna gaba dayan su, a babban faranti ta zuba masu, kowa ya saka hannu har Abban su suka fara ci, Mama Bilki ce ta miqe Abba ya kalle ta" Ina zaki kuma Sarauniya ta?" " Abban su zanje na kira Yaya ne, mu ci abincin dika" cikin zare hannayen su dika, tare da turo baki alamar basu yarda ba suke kallon ta" kin samu amsar ki a wajen su dan haka zauna mu ci bincin mu" komawq tai ta zauna, suka gama ci suka wanke hannaye suka sha ruwa, wanke kwanon Saudat tai ta aje ta dawo suka zauna suna ta hira, suna wasa da Ammar" Mama Ammar ya girma yai wayo sosai" " aiko dai kinga dik sa'annin shi ya fisu girma da wayo" " lallai kam" " Suwaiba, Saudat, Salma" daga kai sukai suka kalle ta jin yanda ta ambaci sunan su alamar ba wsa, amsawa sukai gaba dayan su suka zuba mata ido" ina son na baku shawara a matsayina na uwa, sannan ina son ku duba abinda zan fada maku da da kyau, ku qoqarta amfani da shi, kun ga da farko dai uwa ba kamar ta a rayuwar duniya, Allah ya ce abi shi sannan abi iyaye, Annabin rahama ya jaddada bin uwa sau uku kan uba, dan haka ni ina son ku yafe ma mahaifiyar ku abinda tai maku, tabbas bata kasance uwa ta gari ba, mai ba yaranta tarbiyyar da musulunci ya tanadar, amma ta baku so, ta nuna maku qauna, na uwa da yaranta, in kun kula ita a tinanin ta tayi abinda ya dace daku ne, amma koma dai menene ina son ku sani, wanda bai yafe ma wani ba, shima ya ji tsoron kar Allah ya qi yafe mai nashi laifukan, dan haka nake mai baku hakuri a madadin ta, ku taimaka ku yafe mata, kar kuja wani ciwon ya kama ta dan Allah na roqe ku" cikin kuka suka matsa kusa da ita suka rungume ta, Suwaiba ce tai magana a cikim su" Mama Bilki ke alkhairi ce a rayuwar mu, ki yafe mana abubuwan da mukai maki a baya, tabbas mun cutar da ke sa kalaman mu, da ayyukan mu, bamu zama yara masu biyayya ba, ki hakuri ki yafe mana" " indai nice na yafe maku baku ce man komai game da Yaya ba?" Salma ce ta amsa masu dan Suwaiba da Saudat har yanzu akwai daci da wata irin qiyayya da suke ji game da mahaifiyar tasu, amma sun sani dole su yafe mata, sui hakuri da abinda ta musu" mun yafe mata Mama Bilki Allah ya yafe mana" " to ya kamata kuje ku sanar da ita kar ta kwana cikin damuwa" Suwaiba ce tai saurin miqewa" ni dai Mama ba zan iya zuwa yau ba, dan Allah kar ki tirsasa ni yin abinda ban jin zan iya yin shi a yanzu" ta qarasa cikin kuka,"Bilkisu Allah ya miki albarka, amma ki bar su haka, zuqatan su cike yake da abinda ta musu, daga baya a hankali komai zai warware masu" " to Allah ya kaimu, Allah kuma yansanyaya zuqatan ku ku yafe mata gaba daya" amsawa sukai dika da " Ameen" hankalin Goggo kam ya kai qololuwa wajen tashi, Wanj duhu take gani ya rufe mata ido......
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
BY HERMEEBRAERH
Page 27:
Kuka kawai talle yake ya kasa tsaida hawayen shi, wannan rayuwar ba wanda ya ja ma su ita face shi, mugayen halayen shi ne da yi ma yaran mutane sakin wulaqanci, da zinace2n shi ne ya kai su ga haka, gashi tsabar lalacewa Yayan shi ke neman matar shi ta sunna, Yaran yayan shi na neman na shi yaran, kaiii jama'a wannan wace irin musiba ce ta sauko mana a wannan zamani, Marka kam irin kukan qabilun nan take, tai girgiza tai girgiza tai kukan sai kuma tai dif ta cigaba da gyada kai, abun ya shigeta sosai ba kadan ba, jummala ta mutu sakamakon yunqurin zubda ciki, ga Hawaila tana kallo a gaban ta da ciki dan kuyat a gaba, itama ga nata farkan a gefe, wace irin rayuwa suka jefa kansu a ciki? Maqota ba mai zama wai da sunan makoki, ko sun shigo yada magana ne yake kawo su, wasu daga ciki zakuji suna cewa" Tohhhh abinda ya faru kenan hmmmm Allah dai ya jiqan ta amma zunubu kam an kwasa" ire2n kalaman mutane kenan ana yi ana kyabe baki, wasu kuma bayan sunyi gaisuwar sai sun dora da" ikon Allah kamar ciki nake gani a jikin Huwaila, ni dai bani da labarin auren ta, sannan mun san ba a shan ciki a ruwa, hmmmm Allah ya kyauta,gidan Talle kenan, gidan uwa ba kwaba ya ba hantara" kowa da abinda yake furtawa, baqin ciki kamar ya kashe Haule, wai yanzu nan ne gidan ubanta, gidan da ba tarbiyya ba kwaba, yanzu itama tambarin ya shafeta, ai kuwa da an gama arba'in guduwa zatai qauyen da taji wata qawar Marka da tazo kwanaki ta fada da sunan wata mata a matsayin mahaifiya gareta, mai suna Husai, qauyen yana nan kusa da su, in ta zauna a gidannan ko mashinshini rasawa za tai, in ko ta koma can ko sunqi karbar ta ba zata dawo nan ba, kwalla ta share ta ja hanci, tana kallon su cike da tsana, da tsanar halayen su, tashi tai daha wajen kwata2 tai shigewar ta daki,addu'a take taima 'Yar uwar ta a ranta na Allah ya yafe mata, Yayan Talle kuwa zaman daki ya kama shi, bai da damar fita waje dan abin kunyar da suka aikata, by now kowa ya san meke faruwa a gidan Talle, ba kowa a qofar gidan yan karbar gaisuwa ko yan gaisuwan, sai su Baban gida da Badamasin, Talle kallon su yake kamar ya shaqe su, amma yasan a iskancin da sukai shi yayi ninkin nasu sau ba adadi, nade tabarmar da yake kai yai ya shigo, fakam2 ya tsaya kan Huwaila, kwalama su Baban gida kira yai, suma shigowa sukai da tabarmin su a hannu, kai a qasa kamar munafukai," a cikin ku waye me cikin Huwaila?" Badamasi ne ya nuna Bangis, shi kuma ya qara duqar da kai qasa," Yanzu yarannan wai har kunyi girman dirkama wata ciki? Ko dake maganar wai kun yi girma ma bata taso ba tinda ga misali kun bayar, kun yi sanadin mutuwar daya, ga daya nan da tambarin abin kunyar da zai bi zuri'ar mu har abada, dan haka sai ka bari ta haihu a maku aure kun renu dan shegen cikin gidan da kuka samar tare," cikin tsananin qunan rai yake maganar, ita dai Marka bata cewa umm bare Aa, tai dif sai hawayen nadamar rayuwar su ke fita mata, a cikin zuciyar ta tana ayyana wannan lamari ba laifin kowa bane face nashi, daya tsaya ya tsare mata sha'awar ta da buqatun ta da batai zina da auren ta ba,( dik d wannan ba hujja bace ga matan da suke ganin dan mijin su baya sauke haqqin shi akan su bari su bazama neman mazan waje, ko su fara aikata wani abun da ya kauce hanya, su sani Allah zai masu hukunci daidai da abinda suka aikata ne shima mijin Allah zai mai hukuncin abinda ya aikata, so ni a ganina ba dabara banw hakan, wadda ke da matsala haka maganij ta ya kamata su zauna suyi in ya gagara su tattauna da mijim to ta nemi waliyyan su su shiga lamarin haka islam ya tsara,bai halatta ta fada halaka ba da sunan rashin kulawar miji mu kiyaye)miqewa marka tai zata shiga dakin ta, ya dakatar da ita, " Marka ina neman yafiyar ki akan dikkan abubuwan da suka faru tabbas laifi nane, da na tsaya na zama namijin kirki da duk haka bata faru ba, ki yafe min mu dawo mu gyara rayuwar mu,"kauda kan ta tai saboda kukan da yake neman cin qarfin ta ga wani haushin shi da take ji na jefa su wahala da yai, Yayan shi ne ya fito daga dan qaramin dakin shi ya zube akan guiwowin shi" Talle qanina ka yafeni na biye wa son zuciya, da rudin shedan na aikata mummunan abun da ko mutuwa mukai sai yabi zuri'ar mu, ka taimaka ba dan ni ba domin Allah da zumunci ka yafen" kuka ya kifa hannayen shi a fuskar yana yi, Talle daga shi yai kawai ya dan daki kafadar shi dan shima kukan yake ji, kauda kai yai zai shige daki yaji maganar yayan nashi," a gaskiya sai mun gyata rayuwar gidannan namu kan komai ya tafi daidai, na farko yanayin yanda iyalin ka take yawo a tsakar gidannan ya jawo min matsananciyar sha'awar kasancewa da ita, dan zakaga tana yawo ba isasshen kayan da ya rufe dikkan jikin ta, tana tafe tana juya dikkan jikin ta, sannan ga maganganun ta danake jiyo wa yawancin su na batsa ne, wajen kallon ta da maganar ta bata kiyayewa, wadannan abubuwan sun ja ra'ayina matuqa, dan haka in muna son mu samu kwanciyar hankali da kiyaye war zinace2 a tsakanin mu sai mun kiyaye, sakewa yarannan da mukai shima ya jawo wannan bala'i da muka shiga har yai sanadin mutumar Jummai, ( sakacin iyayen yanzu da kusan nace kowanne gida hakan na faruwa,sai ace cousen din tane ai, kaji tana yayana ne, ko yana qanwata ce, amma da sun samu sarari su biyun su zai zauna ya lalube ta tsaf ya miqe, ita kuma tai dif da bakin ta, da wuya kaga cousens din da a wannan zamanin suke gida daya ko suke yawan ziyartae juna wata barna ba ta gilmawa, wanj sa'in gaba ga iyayen zakuga suna kallon yanda Yarinya ke mannewa namijin amma sai su dau hakan a wayewa, kuga tana wasan banza da namiji sai ace ai yayan ta ne ba komai,sai barna ta faru a zo ana dana sani wasu ma ba a sanin barna ta faru sai sun aurar da yaran, za a duba yarinya bata kai budurcin ta gidan miji ba cousen ya dauke a cikin gida, maybe ma a dakin uwar ta, can u imagen, wannan wace irin rayuwar zinace2 muka shiga? Mu yawaita nemawa kan mu tsari akan zina yan uwa Allah ya kare mu) Talle ne ya amshe maganar da gaskata yayan nashi, kuna ya basu tabbacin dawowar shi qauye da zama, don ya gama xaman birni kenan, murna kam Marka ta yi ta da jin wannan zance, amma ba ta ce komai ba har yanzu, a haka suka watse kowa ya kama inda zai yi cike da alhinin mutuwar Jummala.
Su suwaiba sun kammala ginin dakin su tsaf, sai dai ba flasta, ba fenti, sai ledar daki da suka fara shimfida qaton buhu a qasa sannan suka saka ta, katifa biyu suka saka, babba da qarama daya, sai kayan sunda suka kwaso suka zuba ciki, daki yayi ba laifi, amma ba wani wadata da yalwa sai godiya kawai, kullum dare Suwaiba sai tai kukan rashin mijin ta da kuma yanda ta koma, yanzj wa zai aure ta? Yaushe Salihu zai aiko mata da takardar sakin ta? Ko yazo ma ta ganshi? Haka za tai ta saqe saqe har bacci barawo ya dauke ta. Goggo ta kamu da mummunan hawan jini, sakamakon sanya tinani da damuwa da tai, sannan yanda ta saba Yaran ta na manne da ita yanzu tsakanin su gaisuwa, in suka gaida ta sai dai tajiyo hayaniyar su da Mama Bilki tana koya masu abubuwan da ya dace, suna kuma wasa da Ammar kamar ciki daya suka fito, abun ba qaramin daga mata hankali yake ba, asibiti kam taje shi a kwanakin nan yafi sau nawa, dan sai kawai tana zaune taji wani jiri da duhu ya mamaye ta, sai suma, haka za su kaita a bata magani sui qoqarinnda zasui ta farfado si sallame ta Abba ya maido ta gida, takan ce a ranta " Oh ni Sarai naga duniya, Yarana danake taqama da su a idon duniya su suka juyan baya yanzu, Allah gani gare ka" yau Goggo ta tashi da matsanancin ciwon kai, in da ta dinga kiran Suwaiba ta na zaune tana jin ta tai shiru, Mama Bilki ce ta leqo ranta bace tace" Suwaiba kina son shiga aljanna kuwa? Mahaifiyar ki na kira kina ji ki shiru? Wallahi ki kiyayi Allah, ki kiyayi fushin uwa suwaiba, meyasa kk da ruqo ne, shi wancan mijin naki mai qaton ciki ba dan dan kyaun da yake da shi ba meye abin so a wajen shi, duk da wahalar da suka jefa ku kina nan kina faman son shi, kina begen shi, sai uwa wadda ta haife ki, itace baki san ki yafe wa ba ko? To na qara jin haka tana kiran ki kina ji ki zauna kiga ya zamu qare a gidannan da ke, shashasha kawai,kin miqe ko saina kwado maki wannan murfin kwanon?" A hanzarce ta miqe tana kallon hannun Mama Bilki mai kwanon, shigewa dakin Goggon tai tana zumbura baki" Gani" shine abinda tace ta ja ta tsaya, " Suwaiba nice fa Goggon ki, abar son ki, Suwaiba ba dan Adam din daya wuce kuskure, nayi kuskure, na yi nadama ku yafe ni ke da yan uwan ki, na san ban zama uwa ta gari ba,ko wannan ciwon da nake fama da shi ya ishen ciwon kai ba qaqqautawa, na rasa ya zan kuma duk.sanadin juyan baya da kukai ne, a tinani na a da rayuwa mai kyau nake baku, dan Allah suwaiba ku yafe wa Goggon ku kunji?" Kuka Suwaiba take sosai, harda majina, kusa da goggon ta taje ta zauna ta dora kanta kan cinyar goggon ita kuma ta hau shafawa, ba wanda ya qara cewa komai, nan take Goggo sarai taji kamar ana zare mata ciwon kanta, damuwar ta na raguwa.
Da saurin shi ya shigo gidan bakin shi washe kamar gonar audiga, qoqarin shi bai wuce yaje ga mahaifan shi ba da matat shi, shiga bangaren Innar mu yai yaga wayam an karo qofar ba kowa, bangaren su yai cike da doki da zumudi, durqushe ya ganta gaban ta robar da ta hada zuma da zamzam ne da taiwa fatiha qafa bakwai take sha tinda cikin ta yai wata takwas dan samun sauqin haihuwa, ta shan ye ya kai rabin robar, zufa ke karyo mata ko ta ina, sai addua take tana qarawa," Allahu Allahu Allahu rabbi la ushrika bihi shai'an wa huwassami'ul aleem" shine abinda take fada taja maimaitawa, da sauri ya isa gare ta, ruwa ya fashe mata tana wani nishi na son ta sillubo koma meye a tattare da