Showing 33001 words to 36000 words out of 69565 words

Chapter 12 - 'Yan Abuja comeplat Hausa novel

HAERMEE   

13 May 2025

2226

" inna kama ka a yau a gidannan ka fara tsallen kwado,da kaji ka shiga hannu na" tana ta huci ita a dole an tsokane ta, dariya yake harda riqe ciki dayaga ta gaji ta nemi waje ta zauna, zuwa yai kamar yana son yai tsallen kwado a gaban ta," Haba Babyn Yaya, kiyi hakuri, in dai nine i promise i will never do dat again ever, ya fada yana watsa hannu alamun yayi nadama yana karya wuya" na hakura amma ka jawa kan ka kai zaka kaini toilet a hannun ka ka dawo da ni, dama na kula tinda cikin nan yai girma sai dai ka tallebe ni ta gefe baka daukata, bazan lamunta ba ehe" " an gama ranki ya dade da imani" murmushi sukai a tare suka furta" I love u" wucewa yai ya je ya hada ruwa mai dan sauqin zafi ba wani mai yawa ba yaje ya dauke ta kan su fita tace ina zuwa zan dau wayata, a hakan ya kaita daki ta miqa hannu ta dau wayar, " Kashhhh ashe ma Nafee bata da waya, bari inna fito na leqa na karbo dankalin in ta gama hada min din" kai ta yai ya dauraye mata wannan danqon, sai ga jikin ta yana wani laushi da haske, kamar wata matat masu kudi, fatar taji hutu, sun fito kenan yana dauke da ita ya bada baya ya shihe daki Nafee tai sallama, dakata wa tai, sai da aka bata izini sannan ta shiga,baje ta tadda Juwaira a kujera, " me ciki, ๐Ÿ™Š Ooupsy ! Ga dankalin na mai da shi yai laushin kamar yanda kk ce na saka lalle dakwai amma ba dikan na juye ba bayan na kada kamar dai yanda kk ce gishiri da kuma manjan, sai kin ci dariya Innarmu cewa take wani abun dadin ne, wai Nafee, irin abun rannan zaku mana mai kwai?" ๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚dariya suka saka harda jabeer, sai da sukai mai isar su sannan ya bata rai" ya ishe ku Innata ce fa" dariya suka qara tintsirewa harda shi din," Feena taso ayi wannan dake, kuma kiyi a hankali karki ji ma mata ta ciwo" " masu mata" ta fusta a hankali" me kk ce?" " niiiii me na isa cewa, ba abinda na ce ko nake shirin fada" dariya suka ba Juwairah tai ta yi kuwa, daga naya suka samu wannan hadin sukai ta murza mata a jiki kamar dilka, kafin kace me juwairah ta yi kamar wata amarya, suna cikin yi Nafee ta miqe ta dakko ayaba daya, da kwai, sai zuma da markadadden dankalin hausan da markade yai laushi, hade su tai har ayabar sukai laushi sosai ta koka ta saman kan ta tana tsagawa tana shafawa a can qasan kanta, shi kuma yana mata dilka, bayan ta kusa gama wan ne Juwairah tace" Amma dai Nafee baki saka albasa a hadin yau ba ko? Dan naji ba wari" " eh ban saka ba na san ba zaki so ba mayb ya saka ki amai"" kaiiii amma ko na gode yar uwa"( wannan hadin na dankalin turawa da lalle da kwai d manja kadan da gishiri ko baqar mace ce take yi tana haske , tana fitar da kalar ta mai kyau, ga laushin jiki, shi kuma hadin dan kalin hausa ana yin zallah na albasa madadin dankalin ko dan kali madadin albasa, kowanne yana fidda gashi sosai kuma ya hana shi karyewa, yai laushi da santsi, sai dai na albasa na da wari, dan haka in uwargida ta gama ana son ta samu abun wanke kai mai qamshi sosai ta wanke kuma in an saka ana son ai massaging scalf din sosai ya shiga ko ina) ba su suka gama ba sai wajen azahar, tayi bacci kan su gama, tashi yai yana miqa" wai gayu da dadi da wuya" " hhhhh Yah to ai kai zaka mora gwanda ka taba yau kaji ya take ji da da take yi ita daya" " waya fada maki da din ban taya ta wasu qana nan abubuwan? Ban dai taba irin wannan bane, ashe haka take shan wuya duk dan ta burgeni baiwar Allah" ya fada yana shafa gefen fuskar ta, bude idon ta tai" what ar u two talking about" nan da nan ta tsargu da qibar da tai suke, aiki hde fuska tai, Nafee da ta gane dariya ce taso kwace mata, amma tace bari nasan me zan" Ni dai daya fafa cewa nai ba ruwana in kk ji, dan haka ba ruwana yanzun ma zance na tafi innar mu na kirana, Yah ka fada mata" kama baki yai yana mamakin sharrin da yarinyar ke sn hada mai, kan yai yunqurin wani abu yaji ta janyo hannun shi gaba daya ya zube agefen kujerar, hawaye ta fara ta dora kanta a qafar shi" shikenan dan nai qiba sai a dinga tsokana ta, ai ba muni nai ba", tana yi tana shan majina, rasa me zai yai dan yasan sharri kam Nafee ta hada mai shi bai da hanyar fita, kamo ta yai ya hau massaging kafadun ta" kiyi hakuri princess, dama gani nai cikin yai girma sosai shinr nace ko yan biyu zaki haifa?" " cikin zumudi tace "Allah yasa yayana" " Ameen to tashi muje mui wanka an kusa kiran sallah" miqewa tai, a ranshi yace " wai that went well, Nafee Allah na son ki da ta burkicen yau sai kin wahala kema" wanka sukai ya gyara mata kan ta ya saka mata riga doguwa har qasa mai budadden qugu, ba qaranin kyau tai ba, kallon ta yake kamar kar ya daina, ita ko murmushi take , bayan sunyi sallah ne Innar mu ta aika masu da abinci suka ci, tin da ya saka mata ruwa ta sha ta bingire a zaunen ta hau bacci, daga ta yai ya kwantar shima ya kwanta, suka sha baccin su, Yah Jabeer kam ya dade kan ya samu wannann bacci, dan komai na shi nemaj kwace mai yai, ga rijiya da ruwa amma guga ta hana, ga princess din shi a kusa baccin me ciki ya hana shi more gayun da ta sha domin shi.ni ko nace sai kun tashi asha bacci laaaafiyaaa.......
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ๐Ÿ’…๐Ÿผ 'YAN ABUJA ๐Ÿ’…๐Ÿผ




BY HAERMEEBRAERH



QAWAYEN ARZIQI
Widad Ummu Hafeezah
My Roumie ๐Ÿ’–
Sis Ramlat
Baba larens
Aunty Ummu
Buzu nawa๐Ÿ˜‚
Aseeya Ahmad Bunzu
Aisha Ali Garkuwar mu
Zahrah muhammad
Maryam( Mero tsokana๐Ÿ˜) Maryam Alkali( Autan Hajiya)
Fateema( Mum Sultan)
Aisha Bizzy
Zeenour Mustapha
Hussaina Cute one( kwaila๐Ÿ˜‚)
And so many more of my good and loving freinds, that i can't write ur names, kuna da yawa, kun san kan ku na san ku, ina son ku sosai, Allah ya barmu tare da alkairi mai yawa, ya kare mu daga dikkan sharrin zaman tare. Haermeen Haermma love u XoXo๐Ÿ’–.






Page 19:





Da asuba yau Salma ta tashi da matsanancin ciwon kai da mara, in da Talle hankalin shi ya tashi ba kadan ba, kar 'Yar mutane ta mutu a hannun shi, shi dai Allah ya gani ba wani son ta yake ba dama, kuma shi ba zai yarda ya kashe 'yan kudaden dayake tarawa ba in sun rabu ya baro wata sabuwa ya dirza ba, tabbbb yaushe ma zai yarda ya taba bayan neman auren ma ya kankama, kuma yanzu haka dama wa'adi ya debar mata," kawai bari Alhj ya fita nan dai da Kano na auna ta gida, nace sai nazo ba shikenan ba" yana maganar zucin nan ne ya ji Alhjn na kiran shi, da gudu ya fita, " To ga wannan a kula da gida, ni zan tafi , wannan karon xan dan kwana biyu gaskiya wataqila bam dawo ba, dan amaryata kasan na fada maka ta samu qaruwar diya mace, so ina ganin zan dan jima kadan fiye da yanda aka saba, a kula da gida, kar na dawo na ji shigen labaran dana saba ji, ba zamu kwashe da kyau ba Talle" gyada kai yake kamar qadangare, Allah Allah kawai yake ya tafi ya kai Salma tasha ya dawo, kar ta mutu a hannun shi, " Allah ya kiyaye Oga ba zaka taba samun wani labari mara dadi ba" daga kafada Alhj yai alamar" ruwan ka" yana fita bayan ya rufe gate din ne ya koma dakin da gudu, samu yai ta dan samu dama ba kamar yanda ya barta ba, ta fito daga toilet da alama amai tai," ke hada kayan ki yau zaki ganin gida" cikin kaduwa da murna a gefe kuma kunya da tashin hankalin da wanne ido zata kalli su Juwairah da Mama Bilki? Uwa uba Goggon ta, tace mata waye mijin ta, driver? Ko gate man? Zubewa tai a katifa," Nikam Sweet na fasa ba yanzu ba ka bari na murmure, sannan mu dan samu kudi, ko a haka zan tafi ai sai a zage ka" "a zage ki dai yo ni meye nawa in zaki miqe ki miqe ki kwashi dan abinda zaki iya dan kin ga ni daga yanzu ma barin gidanan zn ko kin dawo ba ganina zaki ba nima na bar aiki anan daga yau, dan na kwashi rabona wajen Alhj, qauye zan koma, na ji da iyalina, kuma ba yanda zaki ki san qauyen mu nan ma tinda ko sunan baki sani ba, ba kuma ki san hanyar bama, so in kin tafi ki manta mai suna Talle, ko Alhj Mansur da kk taba aura, ki manta kin sanni, sai dai in kin tashi tuna ni ki min godiya a ranki na sama maki hanyar zuwa ABUJA, harda qauyen ta ma, dan haka ga wannan" takarda da kudi dubu goma cass ya miqa mata, a zaunen ta daskare, bata gaskata me ake fada mata ba sai da taji tsawar shi yana maimaita mata da kuma bata umarnin tana bata mai lokaci zai fita ya gudu shi,( qarya yake mata ba inda zai gudu kawai sanin bata ko san sunan inda suke ba shi ya sa shi fadin haka, baya son ta yi tinanin dawowa ma) miqewa tai da taimakon shi, take ciwon kan ta ya dawo sabo, wani jiri ke diban ta, haka ta gama komai, ko nace ya gama hada mata komai, yana bata a hannu tana riqewa, idon ta a tsaye, hawaye na zuba, haka ya gama ya sata gaba ya kulle qofar ya dau wata jaka dan tsabar ya raina mata wayo ta zaci tare zasu bar gidan, mota suka dauka ya saka ta suka bar gidan kifa kanya tai a cinyar ta tai ta kuka sun isa ta tasha a bakin tashar ya sauke ta yai gaba ko waiwaye bai ba, a haka ta samu ta isa bata ko magana, in da taji ana kiran Kano nan ta isa ta shiga wata mota sauran mutum biyu, tana shiga wata arniya ta shiga itama, sunayen su aka basu su rubuta, amma ita tai shiru, kudi suka buqata ta miqa masu ko da ya qirgi kudin shi ya miqa mata sauran ta nade a hannun ta, tafiya sukai ta awanni haka ta zauna idon ta ya bushe qayau, har suka iso kano, adaidaita sahu ta dauka ya kaita har gida ta miqa mai kudi ya bata canji, har tai gaba ya bita ya miqa mata a hannun ta, yai gaba, yana " Allah ya kyauta" shiga tai ba ko sallama, Goggo Sarai tana zaune hakimar ana kada qafa akan kujera, tana hango Salma sai da ta kusa tintsirawa, da gudun ta zani na warwarewa tana gyarawa ta taro ta" Lafiya ? Me nake gani haka? Ina mijin naki? Daga wace qasar kuka dawo haka? Fashi akai muku? " duk wannan tambayoyin ne jere a bakin ta tana qoqarin shiga da ita daki, har Mama Bilki zata fita, Abba ya riqe ta, yace bassu, ni na je , yanzj da kinje kin ja magana,cewa za tai gulma ta kai ki" " To Abban su Allah ya jiyar da mu alkairi" " Ameen" fita yai ya isa dakin, zaune Salma take, idon ta na kallon waje daya kawai, ko qiftawa bata yi, kukan kuma ya tsaya, tambayar duniya taqi magana, Goggo banda kuka ba abinda take, " Subhanallahi, me ke faruwa ne, kin saka yarinya a gaba kina ta kuka haka? Ke Salma ki mana bayani, me aka miki, ina mijin naki kuma? Daga ina kk haka?" A sannan ne Salma ta saki wani kuka mai cin rai, ta dakko takardar ta miqawa Abban nata, dan yanzu haushin Goggo take sosai, duk ita ce bata basu tarbiyya mai kyau ba, uban su na son basu ta musu hudubar shedan,ta hana su saurara, wannan wace irin rayuwa ce haka, Salati sukaji ya sake ya aje takardar ya zauna" Malam me ya faru? Ku sanar dani ko hankalina ya kwanta" " mijin nata na can garin ABUJAN NE YA SAKE TA SAKI UKU" dora hannu a ka tai ta kurma ihu, ta hau jibgar Salma tana" Shegiyar yarinya me kk mai ya sakon ke, kk kama asara haka, mutumin da kuka fita qasar waje? Kuke shaqatawar ku cikin jin dadin rayuwa, ki zalunce ni ki zalunci kanki, ki sa ya sako ki, da dukkan alamu ma ciki ne da ke, amma ba zaki bar dan ki ya taso cikin jin dadi ba" kalmar ciki ne ya razana Salma kenan, tasan Talle ya mata illa, dan ko giyar wake ta sha, a yanda ta san waye Talle ba ma zatai gigin ta haihu ba ta kai dan ta qayen su, ai kamar yanda yace sun rabu ta manta da shi hakan za tai,ture hannun Goggo tai a jikin ta ta je gaban Abban ta ta durqusa," Abba na ka yafe min, ka ji tausayi na ba dan halayyata mummuna da nai a baya ba, ka duba girman Allah da soyayyae da da iyayen shi, ka yafen, ka tausaya ma abinda ke cikina in ya tabbata ina dauke da cikin kenan, karkai fushi da mu, ka bamu wajen zama a gidannan karka kori abinda zan samu, zan wahala ta hanyar halal na kula da abinda Allah zai ban, amma kar ka ce za a sake daga zancen uban dannan na gama shafin shi, sabon shafi nake son budewa" kuka ne yaci qarfin ta sosai, wanda yasan ya Abban su hawayen tausayawa diyar tashi, yarinya fara mai kyau duk 'ya'yan shi Juwairah ce kawai ta fisu komai, amma Salma na bayan ta, dubi yanda ta koma, ga qananan shekaru, har yau bata rufe ashirin din ba, daga ta yai tsaye ya rungume ta,aiko kamar jira take,dama she needs a shulder to cry on, ta rasa, for so long, ga strong and loving arms nan sun huging din ta, ya bazata ji gwarin guiwar fidda komai ba, kuka Abba ya barta tai har saida ta daina da kanta, yasan ta fidda koma meke cin ta a rai, zaunar da ita yai, yace ina zuwa, Mama Bilki ya kira bayan ya fada mata abinda ya faru, shigowa tai taje kusa da Salma, Salma na ganin ta taje da sauri ta rungume ta, tana neman gafarar ta, Mama Bilki yafe mata tai, ta zaunar da ita, " fada mana me ya faru" a cewar Mama Bilki, da gudu Goggo Sarai ta iso gaban Salma" yi shirun ki wannan sirrin mu ne karki magana a gaban maqiya" wani kallo dukkan su suka watsa mata, kowa da irin nashi, Salma magana ta fara, ta sanar da su komai da ya faru tin daga tafiyar ta har dawowar ta yau din, kuka sosai Abba keyi duk jarumtar shi, ya tausayawa diyar tashi,Mama Bilki ma haka, Goggo Sarai ga tausayi ga kunya itan ma kukan take, Salma ce ta juya ta kalle ta" Yanzu Goggo a wanne hali su Adda Suwaiba suke? Baki sani ba, kawai suna aiko maki da kudi kina ajewa, Goggo baki san ina ne Abuja ba, da tin tasowar mu kk kimsa mana son ta, yanda kk saka mana son abun duniya da hutu, da haka kk sa mana son ku kadai da muku biyayya da anyi yaran kirki,amma baki wannnan ba ba a kaiga dasa mana tsoron Allah da son Allah da ma Annabin rahama biyayya akan saqon da ya zo mana da shi ba, Goggo kin ci amanar kiwon da Allah ya baki, Abba na qoqari akan mu kina rusawa, ni yanzu ba zan zauna anan dakin ba, Mama Bilki ina riqon arziqin komawa wajen ki na zauna, dan tabbas nima ina zargin ciki garen yanzu watana kusan hudu bana ganin al'ada ga yawan ciwon kai da mara, sai zazzabi danake yawan yi, ki koyan dukkan irin tarbiyyar data kamata nima inna haifi nawa na basu,ba irin wannan tarbiyyat mara kyau da ma'ana ba" Goggo Sarai ce ta kwade mata baki," dan uban ki to ki dauki haihuwar ki da nai ma kice ita ce tai maki mana? Ku tashi ku fice man a daki gaba dayan ku bana buqatar kowa, yaran da suka san daraja ta da qimata za su zo su kula dani, dama ke tinda akai auren me kk tsinanan, baki tsaya kin nemi kamar na yan uwan ki ba , me kk samo banda wahala? Sai ku tattara ku je can, jikoki kuma yarannan biyu ba zan rasa su da ciki ba yanzu haka, dan ba zaman banza na aika su ba" miqewa sukai Mama na mata addu'ar shiriya a ranta, dakin ta ta kai Salma, abinci ta dakko ta bata, kamar mayya haka ta hau shi da ci tana hawaye, tana gama ci ta sha ruwa sai bacci, Mama Bilki ce ta gyara ta, tana tsananin tausayin ta, Abba sai godiya yake mata da sanya albarka.










Su kuwa yan Abuja ana can ana shanawa, hanakali kwance, suna zaune ana kasafin sassan jikin su.........
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ๐Ÿ’…๐Ÿผ 'YAN ABUJA ๐Ÿ’…๐Ÿผ




BY HAERMEEBRAERH





My Saerwwaermaerh
Ke ta daban ce Haermeen Hamma na son ki,

Billy shantali (Billisiou)
Hassana D
Ummul
And dikkan Surukaina na Tabital fullaku, har da surukar zamani๐Ÿ™„๐Ÿ˜™duk ina gaida ku ba adadi, ur love is daban in my qalbi๐Ÿ˜‚

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login