Showing 6001 words to 9000 words out of 69565 words

Chapter 3 - 'Yan Abuja comeplat Hausa novel

HAERMEE   

13 May 2025

2215

baci, yana jin haushin ta, daga nan an samu matsala, ita kuma mace son zuciyar ta shine kwadayin abun da mijin ta baida hali, dan ta gani a maqota kama daga sutura, abinci, da abin hawa, sai ta fara nuna halaye na sin zuciya wataran har ya kai ga tana sabon Allah dan ta samu kudin wadannan , kinga kenan ta biye wa son zuciya daga nan aure sai ya lalace azo ana samun matsaloli, zan barku anan saboda dare nayi kuma na san amarya ta gaji tana buqatar hutu ko ba haka ba?" Murmushi tai mai sauti tace"Mun gode Allah ya saka da alkairi" Ameen" suka amsa gaba daya, anan wani abokin su kuma ya amsa yai masu addua mai yawa wadda zatai masu matuqar amfani a rayuwa in Allah ya amsa masu, a haka ne suka ce bari su tafi, ya tashi zai raka su, yana miqewa ya bige da jikin kujera, yar qara yai ta shagwaba kamar wani mace, tai sauri ta dago tana mai sannu, ido abokan shi suka zuba mata suna mamakin kyau na qaramar yarinya haka, nan gaba ta qara girma ya zata koma?πŸ€” ganin haka ne yasa yai sauri yai gaba yana "to kuzo mu tafi mana"😠 ( wai kishi ana kalle mai mata lolsπŸ˜‚) fita sukai suna zuwa soron gidan yace "to guys ni zan koma na gode Allah ya bat mana zumuncin mu da amana" Ameen" suka amsa, wani ne a cikin su yace " kai dai ba sai ka kore mu ba muma sauri muke , dan na kula ko second uku.ba ka son qarawa anan" dariya sukai yai wuf ya shige yana daga masu hannu. Zaune take ta hade kai da quiwar qafa taji shigowar shi, bayan yai sallama ta amsa ne ya je kusa da ita ya tsugunna, yanda nungashin shi ke sauka a kan hannayen ta daya riqe sai da ya sa zuciyar ta sauri, ga tsoro ga wani feelings sabo da ke shigar ta, " Princess kin ga ya da kkai kyau kuwa? Ba dan kar nai qarya ba sai nace tinda nake ban taba ganin kyakkyawa irin ki ba" Kai Yah Jabeer wannan kowa yaji yasan dadin baki ne kawai" matsawa ya qarayi sosai fuskar ta na saman tashi, amma kusancin su ba mai yawa bane daya qara matsawa hancin su zai hadu, sannan yace" Hmmm ke kk ga hakan amma ni iya gaskiya ta na fada" wani irin abu taji ya bi qafar ta har kanta, bata taba jin wannan feelings din ba" wannan shine auren dama" My Goodness, this is going to be awsome, da na zaci wata azabar ake sha kamar yanda qawar ta shamsiyya da akaiwa aure wata uku da suka wuce take fada masu," me kk tinani haka" ya fada a jikin leben ta da ya qarasa kai bakin shi jiki, da sauri ta miqe tsaye tai breaking kiss din da yaso ya mata, ta hau kame2 tama rasa ina zata shiga, daki zata ko waje zatayi, kamo kafadun ta yai dika ya hade ta da bangon da take tsaye kusa da bed room din su" calm down my princess, is not like i am gonna hurt u or something" murmushi tai na yaqe tace" Yah bacci nake ji jikina ciwo yake" " Ok to muje ki alwala mui nafila sai ki samu ki rage kayan jikin ki mu kwanta zan maki tausa ma" baki na rawa tana sauri cike da in-ina tace" Aaaa..... bama....bama sai .. ka min tausaaa ba " dari yai ganin yanda hankalin ta ya tashi kamar wadda yai wa wani abun already, he just almost kissed herπŸ™„, alwala sukai sukai salla raka'a biyu bayan sun idar ne ya kama kanta, ya fata kwararo adduoin da suka zo a sunna, na ma'aurata kamar haka" Allahumma innee as'aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha a laihi wa a'udhu bika min sharri ha wa sharri ma jabaltaha alaihi" bayan sun gama ne ya koma palo ya dakko ledar da abokan shi suka aje mai, ya dawo da plate da cu daya, juye masu kaza yai a ciki da chips din da yasha hadin hanta da kayan kamshi, ga attaruhu da albasa, an mata yanka mai kyau, kamshi je ya karade dakin daya motsa mata da yinwar da take tare da ita, ga kumaadara mai sanyi a gefe da jus din exotic na Dansa, niyyar ta ta qi ci, dan qawayen ta sunce in an bata kar ta ci, in taci sai ta biya shi da jikin ta, inaaaa yunwar ta ta motsa" Allah yana ban amshewa zan me yai zafi, iyaka na fara kuka nasan zai hakura" πŸ˜™ aiko yana miqowa daidai bakin ta cikin jin kunya ta amshe, tana are ido dan dadi, a haka ya na bata yana ci suka gama, bayan sun gama ne ya fara qoqarin rage mata kayan jikin ta, bayan ya dakko mata na barcin da zata saka, wuga ido ta fara ko ta ina, ga shi sun ciko da hawaye taf, "Yah Ka bar ni nai da kaina" OkπŸ€—" ya ja baya yaje ya cire nashi ya saka na bacci a gaban ta, lokacin da ya cire rigar da wandon ya cire vest da sauri ta juya,tana kwalalo ido wajeπŸ‘€ hankalin ta ya tashi gano yanda jikin shi yake, take jikin ta ya fara bari," like what u see? " d hanzari tace " no i don't infact banga komai ba" murya na rawa, " gaskiya Naseer ya kyauta danai wanka kan mu zo amma da bnsan ya zan ba yanzu dan a matse nake zuwa wankannan batan lokaci zai" zaro ido ta qara kamar su fadi qasaπŸ‘€ " Yah to kaje toilet mana tinda ka matsu?" Hmmmm gama ki ga me nake nufi" yana kashe mata ido dayaπŸ˜‰ take hankalin ta ya tashi dan ta gano shi yanzu, a hankali ta dau kayan tai palo ta canjo ta dawo yanzu kam she is crying like a bby, zuwa tai ta kwanta a hankali dan tai wa Inna Deeje alqawarin bazata giji mijin ta ba , zata bashi duk abinda ta nema mudin bai sabawa Allah ba, janyo ta yai jikin shi, yana shinshina qamshin ta, " kaiii amma princess gaba daya qamshin nan ya sa na qara qaguwa na kusanta da ke" shafa ta ya fara yana mata salon da ita kanta ba zata so ya daina ba, a wannan lokacin Yah Jabeer ya fara qoqarin cika aiki, addua taji ya fara ta saduwa da iyali, kamar haka" Bismillahi Allahumma janibna shhaidana wa jannibasshaidana ma razaqtana" kukan da take son yi ta mayar ta hadiye, bata qaunain da zai bata ranshi ya fasa, kuka da roqo da komai tayi mashi a ranar, har cewa tai tama fasa son nashi, tinda haka ne πŸ˜™ bayan komai ya dawo masu daidai ne ya mannata da qirjin shi yana mata adduoi da saka albarka, sannan yana nuna mata mahimmancin kawi mai budurcin ta da tai , da illar da zata same ta da bata kawo ba din, kuka take qasa qasa, tashi yai ya saka kayan shi ya fita ya hada mata ruwa mai dumi ya kaita bayin su ja su kadai a sata ciki taji dadiin ruwan sosai bayan sun gama sukai wankan tsarki suka fito suna zuwa zama. Tai dan lokacin qarfe 3:30 sallolin nafilar ta tai ta fara bacci a wajen,sai shi ya daga ta bayan ya idar da nashi, sukai baccin su.

















'YAN ABUJA kuwa bayan sun isa wani katafaren hotel suka sauka mai suna Chelsea hotel.................
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ 'YAN ABUJA πŸ’…πŸΌ


BY HAERMEEBRAERH




Hey guys, i want u to know that i really and truelly apriciate ur love, Allah ya barmu tare, as for those of u that ar requesting for this novel ta prive dan Allah kui hakuri na kai page 5 as u can see wayata riqewa zatai in ina tura novel da yawa abun ba mutum daya ba, so dan Allah ai hakuri da ni.Tanx.


I dedicated this page to all it's fans, and WATA UWAR's fans. ANA MUGUN TARE. ME LOVE U XOXO❀




Page 5:








Tinda suka je farfajiyar wajen bakunan su Suwaiba yaqi rufuwa, ganin irin manyan motocin da suka gani, wasu sai a American movies suka taba gani, wasu ma basu taba ji ko ganin su ba, ( abun ku da masu idon cin nera) hankalin su ya kai qololuwa wajen kwadayin son suga mahallin su, sun shiga wajen da ake gabatar da dinner, inda suka qarasa wajen hight table din su hudun su, iya ganin su iya ganin jajayen hulina ne, sai fararen kaya da sirkin ja, daga matan har mazan shigar kenan, sune kadai suka saka baqin lace da ratsin baqi, mazan su ma farin shadda da jan aiki a jiki da jar hula ne akan su, wani mutum babba suka gani a gefe mutane kowa ya shiga sai ya gaida shi, ya hakim ce a wata qatuwar kujera, suma tashi sukai suka kai mai gaisuwa sannan suka koma mazaunin su an fara gidanar da dinner lfy, inda daga baya aka umarci kowa yake yai serving kan shi abin da zai ci wajen maza daban wajen mata daban, wani irin nama ne na daban da aka zo dafawa aka mai dahuwar laushi sosai duk abin mutum ba zai gane na meye ba, matan kuwa kaji ne da sauran tarkace abinci kala2 a wajen har da na qasashen waje, sunci sun sha, daga baya akai ta rabawa mazan wani ruwa a wata kwalba mai duhun kala, jikin su har rawa yake dan murna, kowa ana bashi ya kafa kai tas suka shanye, suka aje kwalbar, bayan an yanka cake ne da sauran bidi'o'i aka tashi daga wajen inda angwayen suna shiga mota suka bama matan wani ruwa a cups masu kyau da sirkin wani magani a ciki, suna sha take bacci ya dauke su, madadin su yi gidajen su da su sai naga sun dauki wata hanya kamar za a bar garin, wani katafaren gida ne suka isa mai gate guda uku manya, katangar gidan duk maitar mutum na ya gudu ba zai samu dama ba, suna isa wasu qattai ne naga sun fito murdaddu sun sha baqaqen kaya da neck tie red, daukar su Suwaiba sukai a hannu suka shiga da su gidan a wani qaton falon nan anan suka aje su kan kujeru suka juya zasu fita, ji sukai wata qatuwar murya tai magana, kai min ko wacce daki, ka hada su a gado daya, wani turmusheshen mutum ne ya fito ba riga daga shi sai gajeren wando, i have been wondering were on earth do they found his sizeπŸ€” God he is huge😱 ga tsaho ga qiba, ga tumbi, ga sanqo, ga gashin baki, ga hammatar nan cunkus, ga idonnan jawur, ga ga ga....... my goodness, i can not describe this guy, kawai gashi nan dai, haka ya tako da fataken qafafun shi ya kalle su suka duqa, alamun gaisuwa, daga masu kai yai ya ce" kuje sai nan da sati biyu ku dawo,dan ban taba ganin mata masu kyau irin wannan ba" yana lashe baki, daga kai sukai suka amsa da " to oga zaks, fita sukai kowa hankalin shi kwance dan sun san samun su zai rubanyu da yawa, Nicon hotel suka wuce su hole abun su, dan su dama sunyi auren ne dan gudun maganar mutane, amma ba dan sun damu da auren ba, tinda a cewar su mata na nan kamar jamfa a jos.








Shigar Oga Zaks dakin keda wuya ya isa gaban gadon, yana lashe baki, kashe wutar yai ya kunna bed sid lamp, cire masu kaya yai ya dakko wani magani ya shaqa masu, maganin bacci ne, wanda zai kai su kwana bakwai cif suna bacci ba tashi, ina ganin zai zame rugegen gajeren wandonnan nai gaba da gudu πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€πŸƒπŸ»β€β™€.


Ba shi ya fito daga dakin nan ba tin daren sai qarfe tara na safe hamma yake yana miqa yai wani bangare ya shiga wani daki, waya yai naji yana " ku shigo, ya aje wayar ya shiga wanka, wasu mata ne dattijai suka shigo, dakin da su Suwai ba suke nan suka shiga, gyara su suke, suna tausaya masu, amma dayar tace" hmmmm wama ya sani ko garin shegen son abun duniyar su ne suka hadu da su, ai kinga ban ga laifin su ba kwadayi mabudin wahala" haka ne kam" tafiya sukai bayan sun kammata, a palo suka hadu da shi yana zaune, ya baza uban tumbi yana kwasar girki, " daga yau duk wata shegiyar tsohuwa a cikin ku da ta qara gulma akan matan da suke shigowa gidannan sai na mai daku matana kuma ta inda baku tsammata ba tana zan na amfani da ku, munafukan banza da wofi" jiki na rawa baki na kyarma suka hau bashi hakuri, korar su yai ya barke da wata mahaukaciyar dariya.



Salma matar me saida mota kuwa, wani qaton gida aka kaita a wata unguwa a gwarinpa, wani qaton gida ne mai kyau, ya tsaida motar, fita yai ya je ya bude gidan da kan shi, ya dawo ya shigar da motar fitowa sukai yana riqe da ita a jikin shi, bayan sin shiga ne take ta zare ido ganin dukiyar dake gidan, wani daki ya kaita mai kyau, suna shiga ya janyo ta ya fara aika mata saqinnin shi, dan shi dama bai wani more ta ba sosai, kuma ba laifi tana tare da budurcin ta, ba sallah ba salati ba godiya da Allah na daren farko na ma'aurata ba adduar komai haka ya maida ita mace, yasha kuka da zagi, dan ashar sai wanda ta manta, bayan sun kammala komai ne yai ta rarrashin ta, qasan zuciyar shi yana " zakici uban ki ne wannan zagin da dukan da kk mun duk sai na rama na fanshe abuna, yar me kwadayin tsiya" amma a fili wani lelen ta yake kamar kwai, a cikin sati dayan nan ya nuna mata gata sosai, wanda ta dinga hango gidan su tana ayyanawa a ranta" tab haka rayuwar Abuja take dama, ga miji gangariya na samu, ga kayan alatu na ci na sha na kwanta miji namin hidima, tab amma an bar Juwaira a baya ina tausaya ma rayuwar ta" " tinanin me kike haka ?" " ba komai, ina tinanin ka ne kawai" ta fada tana wani karairaya ta haye cinyar shi, " woww karki damu ai gani kome kk so naki ne, nema kawai zaki a baki" dariya tai tana shafa jikin shi tana limshe ido, " da gaske Alhaji na?" Da gaske mana tambayi ki ga aiki da cikawa" hmmm ni dama dubu dari biyu kawai nake so zan je na dan siyo kayan sawa na gida, dan na ga ba a kawon kayana nan ba, kace a bari inna zo gidan ka akwai amma ka hana ni shiga dakuna ukun can, sannan kuma in da nake ba wasu kayan kirki" ( yarinya wannan lokacin nake jira da zaki nemi wani abu a wajena) amma a fili cewa yai shirya muje na kaiki ki siyo kayan" da sauri ta sauka tana murna ta saka kaya ta dau jakar da tazo da ita ta fito, tsaf ta ganshi a tsaye yana mata shegen murmushi, fita sukai suka dau hanya, suna tafiya taga suna barin gari," ina zamu ne sweety?" Wani waje zan kai ki in kk ga wajen zaki ji dadi sosai" wooow u ar so romantic babe, i love u" I love u more dear" kiss yai wa hannun ta, a haka yana tuqi tai bacci, bata bude ido ba sai a wani qauyen da bata san ina bane, wani gidan qasa ne mai girman gaske, ko ta ina mata da yara qauyawa ne a ciki sai wasu dattijai a gefen wata bishiya, sina cin wani tuwo baqi miyar koriya sharrr da ita, da sauri ta miqe ta fara murza ido, a zaton ta mafarki take, " babe ina ne nan? Me muke yi anan? Ko mafarki nake ne?" Hhhhhhhh ba mafarki kk ba Salame, nan shine ya dace da ke, kuma nan ne gidan ki, na asali, can gidan gidan oga na ne daya karban auren ki, anyway , karki damu bangaren ki yafi na dika gidan kyau, da taimakon ogana, harda TV an sa maki, tin da ko gidan uwale da ubale ai babu su ko?" Ya fada yana wani shu'umin murmushi, ita ko ta dade da fara kuka harda majina, kuna take tana bashi hakuri ya maida ta ma Goggon ta ita ta fasa auren, wanka mata mari yai," dan uwar ki mai kwadayin nan an gaya maki wawa ne ni? Na kashe maki yan kudadeb nawa kice na maida ki gida, ai ke da gida sai kin haifi biyar a qalla, sai dangin ki sun manta dake , ba dai Abuja kk so ba, to ai nan ma Abuja ce, dan haka baki da damuwa,inna fita ku tabbatar kin biyo ni in ba haka ba gaban su zan fara ballaki, danni ba sabon abu bane wajena dukan mace" daga kai tai dan yanzu wani irin tsoron shi take ji ba kadan ba, hankailin tq in yai dubu to ya tafi yawo, musammab da ta shiga taga daki daya ne dakin nata da wata yar TV da kayan kallo, sai gado qarami da kujeru biyu, da yan kwanika da ledat daki, kai abun dai kamar wata mara gata, haka ta shiga tana kuka kamar ta suma, biyo ta yai yace ta biyo shi daki mai kallon nata, amsawa tai ta abishi kamar raquma, wani daki ne mai cike da tarkace da tsohon gado, sai wata uwar datti da aka tara a gefe na kayan wanki, ga poo din kashin yaro ba a zubar ba qazanta dai ta qarshen qarni kawai, wasu yammata ne a gefe an ci ma an yi fari ta fuska an dashe har fuskar tayi wani kampala kampala, ba kyaun gani, sun sha bra ta dame su anyi daurin qirji da yan wayoyi a hannu, manyan yayan shi ne, a qauyen da Talle aka san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login