Showing 54001 words to 57000 words out of 69565 words
Salihu da tinani, wata zuciyar na kwadaita mai ci gaba da rayuwar hutu, daya ban garen na nuna mai illar hakan, in ya ci gaba da zama dan qungiya yakai soyayyar Suwaiba inaa? Kaiii daya rasa abar son shi gwara ya hakura da qungiyar nan Allah zai kawo mai wata hanyar, miqewa yai, yana miqewa wayar shi ta hau ringing, dubawa yai yaga kiran Alhj Kallah, tsaki yai kamar ba zai dauka ba, dan abin da ya mai dazu ya sosai ran shi sosai, amma sai yandaga yaji ko ya canja ra'yi ne zasu fita tare, yana dagawa yaji wata muryar daban da bai san ta waye ba" waye kai ina mai wayar?" " ranka ya dade mai wayar Allah ya mai cikawa yanzunnan ya samu hatsari wanda gaba daya kan shi ya fashe, sannann qafar shi ta dama ta karye" " innalillahi wa inna ilaihirra ji'un" kalmar da yake maimaitawa kenan, ya kashe wayar ya zauna, qarar message ne yashi, cikin tashin hanakali ya duba sai yaga address din inda Kalla yai hatsari aka turo mai, kamqr wanda aka ma allura haka ya miqe yana fadin" Allah na tuba ka yafeni, Allah ka gafarta min ni Salihu daga yau nai alqawarin tuba daga zunubaina na daina harkar nan ko zan rasa raina ne" kuka hake matuqa haka ya kai ga motar shi ya tada yai inda aka kwatanta masa, wayar shi ce ta qara ringing " Oga Zaks" shine abinda ya gani, tsaki yai ya daga" Salihu kaji abinda wani ta fadan? Kana ina yanzu haka, da gaske ne Kalla ya mutu?" " nima ban sani ba sai na isa wajen na gani, ka oashe na kusa isa ga mutane can dai an taru.a wajen sosai" kashe wayar yai ya qarasa, yanda ya ga abokin nashi take ya yanke jiki ya fadi, wasu je a gefe suka taimaka mai da ruwa ya farfado, yai wajen shi a guje yana kuka, riqe shi mutanen wajen sukai suna bashi hakuri, umarni ya basu akan su taimaka mai su daga gawar akai masallaci mafi kusa a mai wanka a binne, kawai dan basu da kowa, haka ko akai , waya ya zaro ya sanar da Oga zaks, jikin Oga zaks yai sanyi amma dake zuciyar ta dake ko kuka bai ba, sai dai ma kawai ya mai taaziyya ne kawai yace in an kai shi yaje yana son ganin shi, kashe wayat shi yai yace" ba dole ma na fita ba, ai ko ba komai Kalla yai wa qungiya hidima, ya cancanci azo kan gawar shi a mai addua amma wai in an kai shi na je, ko baka ce ba zaka ganni kuwa" share hawayen shi yai shima yabi bayan yan tsiratun mutanen da suka gama rife Kalla a makwancin shi na gaskiya,mota ya fada yai gidan shi, tattaro duk wata dukiya tashi yai, yaje ya dakko ATM cards din shi, da makullan motar shi, da takaddun filaye da gidajen shi kamfani da komai ya zuba a motar, ya sa kai, bai zame ko ina ba sai qofar gidan Oga Zaks, yana isa a ka ya tsaya ma Oga Zaks , " ya haka Salihu, zaka zo ka tsayan akai kamar wani sanda" " miqa mai komai yao da suke a wani akwati, ya ce" Oga ina son barin qungiya ba dan komai ba sai dan ina son na koma tsaftatacciyar rayuwa, abinda ya faru da Kalla ya qaran son barin qungiya" take ya kwarorowa Oga Zaks duk abinda ya faru da Kalla da shi kafin hatsarin da yai, nqn danan jikin Oga Zaks ya dau rawa, qaton cikin nan kamar ana buga ganga haka yake qara, maganganun sun shige shi sosai, " To salihu ba za ai haka ba ka fita kai daya, yau kuma a yanzu zan tara mutanen mu, na sanar da su, wanda yaga zai fita ya biyo mu dan nima fita zan, wanda yaga zai zauna ga waje, amma zan so yanda ni ne na assasa wannan qungiya na rusa ta, dan ko na tafi zunubin xai bini" wani dadi ne ya lillibe Salihu dan bai zaci hakan ba, ya zaci zai sha wahala kafin ya amince mai, waya yasa ya kira mutanen su,kusan awa biyu sika dauka kan kowa ya hallara, ganin fuskar Salihu da ta sha kuka ya badu mamaki, nan take ko Oga Zaks ya fara zayyana masu komai, cikin qanqanin lokaci wasu da dama suka aje makaman yaqin su, wasu kuwa suna ganin ai su akwai sauran lokacin tuba,tsawar da Oga Zaks ya daka masu ce ta dawo dasu daga cece kucen da suke ta yi" na yake hukunci wannan qungiya rushe ta zan, wanda ya sake kafata shi ya sani, amma ni kam na gama , dan haka daga gobe zan rushe ta, tsakanina da dodo ko kashe ni yai na kubuta da ikon Allah, fatana Allah ya gafarta min, ya ba wa wadan da na zalinta ikon yafe man a filin qiyama" sai ga Oga Zaks na kukan nadama, basu rufe baki ba suka ji gidan na wani irin qara, mai firgitarwa, haba mana xo kuga gudu, kowa na gudun ceton rai, Salihu ne ya ke qoqarin taimaka wa Oga zaks su gudu, amma ya dakatar da shi" Salihu kai ta kan ka kawai, ni nasan tawa ta qare, da wannan uban tumbin nawa kk tsammanin samun gudu a gareni? Ka dube ni fa ka gani nayi ka bakwai, ka barni kawai, abin da na aikata zan girba, i am willing to give my life for urs, coz i started everything, i think it has to end with me, just go, run for ur lyf, and pls don't forget to pray for me, ask Allah to have mercy on me" tura Salihu yai da qatfi a daidai lokacin da wani qaton baqin zaki ya fito daga wani baqin daki, yayo kansu, Salihu diba yai da gudu ya bar wajen, Oga Zaks salati kawai yake, ya cika wando da fitsari shataf, tsoro da tashin hankali ya ganshi qarara, tinawa yai ashe haka wadanda suke ba dodon suke ji kan su mutu, take yaji qirjin shi na wani mugun bugu, cafka zakin nan ya kaiwa wuyan shi ya hau cinye shi, Oga Zaks kam an tafu inda Kalla ya tafi, Salihu kuwa gudu yake kamar me , mota ya gani da makulli jiki me ita wataqila tsabar tsorata ne ya hana shi ci gaba da tada ta, dan harda takalmi qafa daya a ciki, da alamar danshi a sit din, maybe fitsarin shima ya sake🤔 take Salihu ya tada motar ya debi hanyanyat kano.
Sin gama gyara gidan tsaf, sun ma iyayen nasu girki, wanka sukai, suka gyara jikin su, jikin Suwaiba duk ba kwari haka take jin faduwar gaba, Saudat kam ita in banda sharar dakin su ba abinda ta tsinana, komai kusan Salma da Suwaiba ne sukai, gaban ta sai tsananta bugawa yake, amma sai tai ta maimaita addu'o'i a bakin ta, haka itama Suwaiba, bayan sun shirya ne suka dauki hanyat gidan Juwairah me jego, sun isa daidai Jabeer ya fito riqe da towel din da yake gasa mata jiki musamman cikin ta da bayan ta da shi, kallo suka bi shi da shi , saka makon ganin Juwairah ta fito tana" Ni dai gaskiya a canja min me yin wanka, kai gaba daya kamar ba wankan ne ke kai ka.......... " maganar ta maqale dan ganin yayun nata na shigowa, niyyar ta ta koma bandakin dan juyawa tai tare da damqe bakin ta, zata shige, Saudat ce ta ruqo ta da sauri tana dariya," Me Yah Jabeer din ke maki? In kina son a canja maki mai wanka sai na dinga maki, amma ni sai ruwan ya tafasa sau uku sannan zan amfani da shi" zaro ido tai waje tace" A'a Adda Saudat a barmin Yah Jabeer din mu lallaba a hakan" dariya suka kwashe da shi, Jabeer yace" kuji yarinyar nan fa, wai zata lallaba a haka sai kace wani mugunyar nake mata" Nafee ce ta amshe da" Hmmmm Yah ai shiru kawai da wannan maganar amma ko dazu naji qarar ta" hararar ta yai yace " Suwaiba ku shiga ciki mana kuka tsaya a waje" shiga sukai har me jegon, Nafee ce ta miqe sakamakon kiran ta da Innar mu ke yi, zuwa tai ta bata wani kwanika biyuo ta kawo wa juwairah, amsa tai tai ta tafi bangaren juwairah, sallama tai ta shiga suna ta hira kowa na yava kyaun jaririyar da sunan ta" wannan suna na yan gayu anya kowa zai iya fada" cewar Salma, dariya Nafee tai da ta qarasa aje kwanon gaban Juwairah dake shafa man kade a cikin ta," ai jiya sai kun sha dariya dan daga Innar mu har Abban mu basu itmya fada ba" " ai ko wannan suna zan so jin shi a bakin Goggo" cewar suwaiba, dariya suka bushe da ita dikkan si sun san a kwai case dib fadan Abrar a bakin Goggo sarai, Juwairah ce ta gama shiryawa Suwaiba ta daure mata cikin ta, sannan Jabeer ya shigo dauke da plate da Spoon da cup sai tea spoon, gaishe shi sukai dika ya amsa tare da yi masa barkar qaruwar da aka samu, godiya yai ya isa gun kwanukan ya bude, farfesu ne na naman qaramar dabba, yasha kayan qamshi irin na jiya harda ridi, gefe kuma kabewa ce innar mu ta dafe ta tai laushi ta dame ta tai kamar kunu, sannan ta zuba maya madarar shanu mai matuqar yawa sai zuma, zuba mata yai a cup din ya zuba mata naman a plate, " oya maza taso ki ci ki shanye, dan bana son kina zama da yunwa" turo baki tai gaba, " ni fa na qoshi, dazu da asussuba na qarasa naman jiya saboda yunwar dana tashi da ita, yarinyat nan ci gare ta kamar Innar ta Salma" dariya suka dauka da dikkan su" ai ko baki isa qoshi ba da dan ragowar naman nan, in baki matso kin fara ci ba zan maki dura gaban su, dan dora ki cinya zan na maki irin na kwanaki" zaro ido tai waje sai gata a qasa ta saka pilo ta hade qafafun ta waje daya ta miqe su( haka ake so mai haihuwa tana zama, kai ko ba haihuwa ba a son zaman nan na ware qafa, kabewa da madarar shanu da xuma duk wadda ta hada ta zata bada labari bazan ce komai ba🙊) kaiwa baki tai ta fara ci dadin da ya ziyatce ta bata san sanda ta cinye ba ta shanye kabewar dika, " just like a gud gurl" kissing din gefen fuskar ta yai ya dauke kwanukan zai fitar Salma tai saurin karba, " haba yayah muna nan ai sai ka bar mana aikin in mun tafi ka ci gaba" muemushi yai ya sakar mata yace" ni bari naje.na shirya zan wuce Abuja yau zuwa qarasa shirye2n komawar mu bayan suna" anan ya sanar da su komai game da aikin da ya samu, murna suka taya shi , da fatan alkairi, fita yai yai wanka, ya dawo zai shirya Juwairah ce ta tashi taje, yna shiryawa suna.hira tana hada mai kaya a jaka, duk da hana tan da yau.sai da ta hada masa, bayan ya gama ne ya dauki Abrar ya mata addu'a yau kissing din ta ya hade bbyn da maman ya rungume, daidai ya sake ta yai gaba ne ya dawo" Af nayi mantuwa" " me ka manta honey?" Matsawa yai kusa da ita ya janyo ta jikin shi yana mata kallo qasa2," No no no u can't do this now pls, Adda Suwai ba is here, Adda saudat is here, and Salma too, pls kai hakuri har ka dawo, kasan lips dina ja suke kuma zasu gane, ni dai dan Allah ka daina bani kunya," ta fada tana yar kwalla dan ya kyale ta, lake mata hanci yai yana" mun kusa komawa gidna mu mu uku, mu yi abinda muke so" dariya tai na samun nasara, ta mai addua ta rako shi suna zuwa palo tai fuska ta zauna kamar ba tare suke ba, kunya ce da ita kamar me, dariya suka mata Salma tace " kinji da shi ciwon ajali a dan yatsa, mu zaki layancewa," dukan wasa ta kai mata tace" Adda Suwaiba kin ganta ko" dariya sukai" ya kamata ki rage shagwaba yanzu kin haihu," cewar Nafee, murguda mata baki tai ta kauda kai.
Ahj Salihu ya iso kano da kyar ya gane gidan su suwaiba....
.
[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: 💅🏼 'YAN ABUJA 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
Page 30:
Alhj Salihu ya iso gidan su Suwaiba da wajen bayan la'asar kadan, dai dai su kuma suna dawowa daga gidan Juwairah, daga nesa ta bayan da ya juya Suwaiba ta gane shi, ya rasa dan aike, kuma yana matuqar jin nauyi, kunya, da tsoron wacce karba za a mai, shin dalilin kafa kai da yai a jikin motar, wasu siraran hawayen nadamar rayuwar shi ke bin kuncin shi, ga rashin abokin shi da yai, kuma kusan a gaban shi zakin nan ya kaiwa Oga Zaks cafka a wuya, what if shima ya biyo shi? Ga Suwaiba da iyayen ta da 'yan uwan ta, maybe this is a bad idea for him to risk there life for his mistake, he was trying to walk away, when he hered her voice, calling out his name in a passionate way" Baby? kai ne? Kai ne da gaske nake gani? What are u doing here?" Qarasawa tai da gudu ta fada qirjin shi tana kukan missing din shi da tai, shima rungume ta yai kamar wani zai kwace mai ita, gyaran murya Salma tai masu," Adda a waje kuke fa, kn san halin mutane, ba za ai tunanin mijin ki bane, za a fara qananan maganganu" janyewa sukai daga yanda suke taja hannun shi zuwa cikin gidan su ta tsaida shi a soro, Saudat kam ta qame qam a wajen, dan zuciyar ta bugawa kawai take, ina nata mijin? Ya akai suka rabu yau? Bayan ta san ba sa rabuwa? Wannan tambayoyin Salihu ne kawai zai amsa mata su bayan ya samu nutsuwa, dan ta kula shima ba a nitse yake ba, Salma da tai gaba ne ta dawo baya ta ja hannun yayar tata sukai ciki, ta kula da cewar Saudat na cikin damuwa tin safe yanzu kuma data ga Salihu shi daya ba nata mijin abun ya qaru mata, ko ba komai tana son mijin ta kawai halayen shi ne yasa ta gudowa taqi komawa, what could possibly happen to him? Sun riga sunyi Sallah gidan Juwairah dan haka bayan sun shiga sanar da Abban su sukai Salihu yazo ga kuma a yanayin da suka gan shi, a da Abban was furious, amma da Mama Bilki ta taishe shi, akan ya tafi cikin nutsuwa ya bude ma Salihu zuciyar shi yaji me ke tafe dashi, in yazo da rainin hankali gidan su yazo, ta bashi goyon baya ya mao duk abin da yaso, kada kai yai cikin qunan rai ya fita amma sai ya danne bacin ran nashi, kamar yanda matar tashi ta bashi shawara, Sallama ya mai ya miqa mai hannu amma Salihu ya noqe, ya durqusa qasa yana mai kuka mai ban tausayi," Abba ni mai laifi ne ba a wajen ku ba har a wajen Allah, babban mai zunubi ne,na taso ban san menene ilimin addini ba, duniya kawai na saka a gaba, bani da ilimin addini daya ratsa zuciya ta da zai hana ni aikata dukkan abubuwan dana aikata, dan son ka da Allah da Annabin shi ka yafen abinda nai wa Suwaiba, ka yafewa abokina diban jinin Saudat da yai domin ya mutu, a dazu kan na iso nan, ta hanyar hatsarin mota" wani qarar kwanuka da qarar Saudat ne ya dawo da su daga maganar da suke, faduwa tai a wajen a sume, da gudu Abban su yai kanta, ya daga ta yai ciki da ita, ruwa suka yayyafa mata, a hankali take bude idon ta, ya sauka kan Salihu da ya shigo ba izini, kuka ta saka ta kai mai naushi a baki, " mugaye azzalimai, kashe shi kuka ko? Dan na san yanda Kalla ke sona zai biyo bayana ko bajima ko ba dade, shine kuka kashe shi?" " Saudat you have to calm down, u get it all wrong, ni da kk gani ni na shawarce shi akan mu fita daga qungiya dan son da muke maku, da kuma tsoron Allah daya shigeni, amma Kalla ya qi, ya mun bayanin shi akwai sauran lokacin tuba, na mai wa'azi da in mutuwa ta riske mu kan tuban fa, yace akwai lokaci, yana fita yai hatsari mummuna, kan shi ya fashe qafarshi ta......." " Stop it ! Stop it !" Saudat ce cikin tsawa take hana shi qarasawa, tare da fashewa da kuka mai ban tausayi, a nan dai ya qarasa labarta masu komai daya faru har a wajen Oga Zaks, Goggo dake gefe da ta fito cikin bala'i taji komai, sai jikin ta yai sanyi, ta koma kwallar tausayin yaran ta, ba laifin kowa bane illa laifin ta, ba su taba sanin Saudat na son mijin ta haka ba, kawai ta gudar wa mutuwa ne sai yau, daga ta Mama Bilki ta sa Abba yai ya kaita dakin su, ya kwantar da ita, kuka kawai take, Mama Bilki ce ta shiga bayan Abban su ya fito" Saudat ki hakuri , na san rashin masoyi akwai zafi, amma soyayyar da zaki nuna wa kalla a matsayin shi na mijin ki shine addua, tinda bai sake ki ba kk qi komawa, dan haka daga yau zaki fara takaba, har tsawon wata 4 (hudu) da kwana 10 ( goma) dan haka har abada mijin ki na buqatar adduar ki, baya buqatar kukan ki, kinji" ta qarasa tare da shafa kanta, cikin sakewar jiki ta dora kan ta a kan cinyar Mama Bilki hawaye masu zafi na fitowa saga idon ta, nan take ta hau kwarorowa mijin nata