Showing 66001 words to 69000 words out of 69565 words
mashi,tana goge masa zufa ne tare da jera mishi sannu da zuwa cikin rattausan lafazi, umartar ta yai ta kira yayar tata,miqewa tai ta tafi, ta kira Goggo Sarai da tai zurfin a cikin tinanin baya, yanzu da hankali ke qara shigar ta, ba qaramin kunyar Mama Bilki take ba, tasowa tai kamar wadda kwai ya fashe ma a cik, ta biyo ta, " Gamu Abban su" dagowa yai ya kalle su cikin sha'awar yanda suka koma a nitse ba hayaniya ko mummunan kishinnan, Ammar ne yaje wajen Goggo Sarai ya zauna a cinyar ta, shafa kanshi tai tana mai murmushi, Abba labar ta masu komai yai sannaj ya sanar da su Tallen na qofar gida ma yanzu, haquri ya ba Goggo Sarai da yaga ranta ya baci, yama juyawa yaga fuskar Mama Bilki ma a bace, domin shi mijin Salma shima ba qaramin azzalumi bane kwantar masi hankali tai da dadadan kalamai sannan suka hakura, aika Ammar yai yace yaje ya shigo da baqon nan, tafiya yai ya sanar da shi, Talle ya shigo qafa duk ta sage mai saboda tsaiwa, waje Abba ya matsa mai kan tabarma, tayin abincin ya mai Goggo Sarai ce ta qaro ruwan sha da wani abincin, ci sukai suka qoshi, sannan Abba ya kira su again, " da farko dai ina son sanar da kai dukkan mu nan iyayen Salma mun yafe maka, kuma muna saka ran itama ta yafe maka, tabbas ka cutar mana da yarinya, ka zalumce ta, amma duba da cewar muma masu zunubi ne a wajen Allah kuma mu roqe shi ya yafe mana, banga dalilin qin yafe maka da zamui ba, daga qarshe ina mai sanar maka yanzu haka Salma na Abuja gidan kudi gidan hutu ita da yaran ka dan biyu ta haifa, kuma ta samu miji saurayi ya dauki yaran kamar mallakin shi, ni ba zan sanar da kai ina Salma take ba a yanzu dan ta fara samun farin......." " ban katsi nunfashin ka ba Abba, amma tabbas nima ba zan so abinda zai hana ta farin ciki ba a daidai wannan lokacin, tabbas, na amince su ci gaba da rainon yara na, lokaci zuwa lokaci zan dinga zuwa nan din, ana gaisawa,ga address dina saboda wataran ko za a buqaci hakan," takardardaya rubuto tun a gida ya zaro ya miqa ma Abba, idon shi ya kada yai jawurr, tabbas har yanzu akwai son Salma a ran shi, wanda tin da ya dauka sha'awa ce kawai, miqawa Abba ledar Hannun shi yai ya mai sallama dan komai dare gida yai, ya ma yaran shi addua, an nuna mai hotunan su, inda Mama Bilki ta dakko mai wasu ajiyayyu tin na jarirantar su,har randa zasu tafi, hawaye kawai yake sharewa, duk yaran shi ba mai kyaun wadannan da ya koro, dan duk macen da ya aura in zata tafi sai ta dire mai da ko yar shi, ko in taje gida ta haihu zata dawo mai da shi, Haule ce kawai take itama kyakkyawa saboda uwar ta, yana tina ta sai zuciyar shi ta qara tsinkewa,ya kula yara uku ya bari yanzu, amma wannan na daga cikin horon da Allah zai masa ya raba shi da yaran da yafi qauna, tashi yai bayan ya sake masu sallama ya isar da saqon su Huwaila,godiya suma sukai masa, ya kama hanya sai qauyen su.
*BAYAN SHEKARA BIYU*
Salma ce ke zaune da jaririya a hannu da suke kira da suna Faiha, gefe Juwairah ce tana riqe da hannun yaron ta qaqqarfa mai kuma barna, Salim, Sai Suwaiba da ke ma Abrar kitso a lallausan gashin ta mai tsaho, gefe kuma a kwance a kujera Saudat ce ke latsa waya tana ta doka murmushi, Maganar Juwairah ce ta katse shirun nasu" In baka tsaya ba Salim zan kira Daddyn ka ya dauke ka ku tafi kona huta," da sauri yaron ya zauna a cinyr ta ya nutsu, dan a cewar shi Daddy is no fun to be with, amma Mummy, yana son zama da Mummyn shi ko da duka zatai mai in yai halin nashi na barna, ' Yan biyu ne sika shigo da gudu, suna haki" Mummy Daddyna yace wai ki bada Faiha, Salim da Abrar mu je park" kowa a cikin su daidai lokacin da kowa yace Daddyna sun kalli juna da harara,ba su fada a tsakanin su sai akan abu biyu, chocolate da kuma Daddyn su, sai kace kaya haka ake rabon shi a tsakanin su, wannan yace nashi ne wannan yace nashi ne, fatima ce tace" kaiii wannan Muhammad din sai son yi min kwace kk kullum for how long zaka gane cewa Mummy ce taka ni kuma Daddy nawa" " Fateema ke ce baki san komai ba hat yanzu" ya fada yana mata kallo wai shi harara, dan kwata2 bai kaita wayo ba, ga shi fadan ma bai iya ba" kai ni ku karbe ta sarakan rabon iyaye,kada Allah yasa ku zaben din ga Faiha in ta girma zata zaben ai" miqa masu ita tai suka karbe ta,dariya saudat tai sosai tace" Mummy ar u jelouse ?" Dariya dika suka dauka, Juwaira ta sauke Salim ya bisu,daidai an gamawa Abrar kiston ta, miqewa tai tace" Tanx Mum" tai kissing kuncin Suwaiba ta fita a guje, murmushi tai mai nuna alamun jin dadi ta bita da"ku dawo lfy kui adduar fita daga gida kan ku fita, kar a manta da yin addua in zaku dawo," daga nesa ta amsa mata da" inshaa Allah mum, i love u," " i love u too baby" nan ma Saudat ce dake ta Chatting da mijin ta ta sake dagawa tace" lovers kenan" nan ma dariya sukai, juwairah ce ke kallon ta da Yan uwan ta cikin farin ciki da nishadin da Allah ne kadai yasan iyakar shi," to ya kamata mu ma muje Shopping, akwai wasu abubuwan danake so mu siyo yau" ta fada tana kashe masu ido, Saudat ce ta diro da sauri ta dage hannaye sama tana murna" Yeeeeehhhhh shopping" " u always act like a kid Saudat," inji Salma, pilon kusa da ita ta wurga mata, " eh din anyi,my husband always treat me like one," ta qarasa tana murguda baki, dariya suka saka, Juwairah tace" yeh u ar always his baby" " and u ar more like baby to me than she is always my love" juyawa tai taga Jabeer ya shigo cikin qananan kaya, tare da mijin Saudat, tsallen murna Juwairah ta daka taje ta rungume shi,wanda dama yana fada hannun shi is open, rungume ta yai kamar su kadai ne a wajen,gyaran murya mijin Saudat yau yace,babban Yaya muje ki, tinda shi wancan Baban yaran ya debe su muma mu kai su shopping din kawai, kallin juna sukai matan, ba haka suka so ba, akwai dan abubuwan su na mata da suka so kwasa, amma ba damuwa sun taya su zaba ma, dakko hijaban su sukai,Juwairah har da Niqab Yah Jabeer yake sata sakawa, haka suka fita, gwanin sha'awa, waya sukai ma mijin Salma ya same su a Sahad dake can ABJ din, aiko Salma da tana jin ta out of place sai murn,sa riya sukai mata, a can suka hadu da yaran da mijin Salma siyayya sukai sosai kafin kowa ya nufi gidan shi, Suwaiba gidan Jabeer zata kwana kafin wase gari mijin ta yazo su tafi.
Arziqi ya wadata a zuri'ar gidan Abba Baballiya, gidan kuma 'YAN ABUJA, albarkar Allah ta sauka masu, ko ta ina,inda a tsakanin Jabeer da yake dan su da surukan su, kowa qoqarin yi ma iyayen abun da zasuji dadi suke, an canja fasalin gidajen iyayen daga na qasa zuwa na cement, da kayan alatu kala2, ga shaguna da suka bude masu, na saida kayan masarufi suka saka amintattun yara suke kula da wajen, shiko Yah Jabeer kasuwancin shi yana nan da kamfanin jakunkuna na AF2 dake malaysia, abun ba a cewa. Komai sai godiyar Allah,makaranta mazajen dika ke tinanin maida iyalan nasu nan kusa su ci gaba da neman ilimi har sai sun ce ya ishe su, Suwaiba nonoless tin bata son saka bra din acuci maza irin ta Cutie har ta fara, mijin ta ya masu gini a unguwar Kabuga, qaton gida, yanzu harkar gwanjo ta bude sosai, Talle arziqi ba laifi, ana nan an zama manyan ustazai masu ma wasu wa'azi musamman da basu misali da rayuwar su, Saudat da mijin ta, sun fawwala ma Allah dukkan lamuran su, na rashin haihuwa, ba sa damuwa a ransu ko adan, tin ana zuga mijin ta yai aure har an gaji, domin soyayyar su suke sha, da shaquwa ga fahimtat juna dake tsakanin su.
Allah ya albarkaci rayuwar mu baki daya.
*Masoya novel na 'YAN ABUJA ku dakace ni gobe domin jin wasu bayanai da sharhi da zan akan wannan novel da inshaa Allah nake saka ran zai amfanar kuma zakuji dadin shi da yardae Allah, ina roqon ku da kuma fatan duk abinda na fada daidai kuma kuka san abin koyi ne da ku qoqarta saka wa a ayyukan ku, sannan wanda nai kuskure ku yafe ni akai, ina jiran gyaran ku akai daga yau zuwa gobe inshaa Allah na gode. Me love u XoXoโค*
[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: ๐
๐ผ 'YAN ABUJA ๐
๐ผ
BY HAERMEEBRAERH
*Assalamu alaikum Jama aree bandi raabe am, yidibee novel 'YAN ABUJA, mido yetta on masin,beyeddi on holli am haa dow defteream, mido yeela ko end jangi pat end habdai end naftira bemai koo na pat ba end habda ko sedda on, mido usa mido yetta on walama bana fulbe haa on woni fu ha duniya do miyetti, walama bana yare IBRA, end doo woondi inshaa Allah, mido yidimon*โค
*Ina kuma riqon duk wanda Allah yasa ta fara bin wannan novel daga farko ko ta riski wannan page din koda bata bi daga farko ba ta daure ta karanta wataqila ta samu koda abu daya ne mai amfani a ciki*
Page 36:
Zan yi sharhi ne akan wannan novel namu na yan abuja, inna gama nawa wataqila ba zai yu na fidda komai ba ina son kuma makaranta ku fiddo man da naku hakan zai sa naji dadi maybe gaba na sake mana wani novel din๐
1- da farko dai gaba daya a kuma dungule nai magana akan iyaye da tarbiyya ne, yanda iyaye in Allah ya basu yara ya zasu saka su akan hanya mai kyau wace tarbiyya zasu basu, me yaka mata su saka masu a zuqatan sh saboda gudun kar su tashi ba akan tarbiyya mai kyau ba.
2- sannan nai magana akan kwadayi, mahaifiyar su Suwai nonoless ta taso da su akan kwadaryi sa burin zuwa inda ba lallai ne arziqin su na can ba, unlike Juwairah da suka raina ta akan auren Yah Jabeer.
3- Ana son mace ta zama mai tarbiyya mai kyau, wadda ko ina ta shiga za ai sha'awar ta da halayen ta in bata nan ai kewar ta, ki iya zama da kowa da kyakkyawar mu'amalat, ki kasance wadda ko minti daya miji yai baku tare zaiji damuwa da tashin hankali, da duk wanda kk tare da shi ma.
4- Ana son mace ta zama mai tattali mai dabara in ba wannan a gida ta san ya zata hada wancan ya bada outcome mai kyau mai dadi, yanda ba mai gane ma rashi ne ya jawo hakan, sannan ta zama tana qoqarin dasa kowacce hanyar da zata kawo masu sauqi a gidan ta, kamar yanda Juwairah tai lambu a cikin gidan ta.
5- Mace mai rufawa mijin ta asiri a kowanne lokaci abar so ce ga kowa, ba namiji ma kadai ba ga kowa.
6- Mace ki zamo mai tsari, ya zamana kina da lokutan yin abubuwa, in kina haka za a same ki mai tsafta, baki kwaba wannan da wancan, misali, kina girki wannan bangaren zaki iya ci gaba da gyaran daki, sannan ko ya za ai mace in zaki wanki ki fara gyara dakin ki da gidan ki sai ki zuba wankin ki tayi, akwai wasu dana kula ko nace da dama, taqamar zasui wanki sai kiga gidan kamar bola da kin magana ace wanki zan shiyasa, yana daga cikin tsari ki ware ranar da zaki na ma gidan ki gyaran tsaf misali muce a qarshen sati ko sati biyu ko wata daya ki fitar da komai daga mahallin shi ki share ki wanke ko ki goge, sannan yana daga tsari ki ware ranar zuwa kitso da qunshi, sannan ranar yin gyaran jiki irin dai na Juwairah, in Allah yasa gidan ki kina da halin yin lambu kin yi to ki ware mai lokacin duba shi, in baki da lambu a sameki dai da wata shuka da kk kula da ita ga lada ga huce takaici ga amfani,musamman ZOGALE.
7- kar ki zama mai kwadayin abun hannun namiji, komai qanqantar shi komai yawan shi, in kk kasance mai kwadayi tabbas zaki wahala, wataqila ma a kwadayin qima da darajar ku ta zube son ki a hankali ya fita daga zuciyar shi, sannan qataqila in bakinda rabon zama da wani sassa na jikin ki ki rasa shi in d process of kwadayi, da roqo, kamar dai irin na Saudat mahaifaless.
8- A rayuwa kullum Namiji shine jagora shine uba shine yaya ko da kuwa qani je yana zama shugaba, ko abokin shawara, dan haka in baka kasance mai tausayi da tallafawa mace ba ka aje sunan ka a namiji ka daura dankwali ka bi layin matan aita buga cinya da kai, ku duba rayuwar Yah Jabeer da Abban su Salma , Yah Jabeer ba abinda bai taya matat shi, har da gyaran jikin, shaving, gyaran gashi, wanka, wanki, wajen haihuwa ma tare sukai komai, da ace mazan mu na zuwa dakin haihuwa suga azabar da mata ke sha, wataqila da sun rage ma mata rashin mutuncin da suke masu, sun tabbatar matan suna ta mata, suna matuqar qoqari, suna jarumta, da tausayi da sadaukarwa ya shiga zuqatan maza, da sun tarairayi abinda aka haifa masu da kyau da mutunci. Ta wani bangaren kunga yanda Abban su Salma ya dabbaqa sunnar Rasulullah yake kiran matan shi da suna masu dadi, kamar Gimbiya Da kuma Sarauta, wannan sunna ne ko mai tsufan ku soyayyar ku karta gushe,SO baya tsufa sai dai masoyan su tsufa ju jeme, amma soyayyar su na nan.
9- mace kar ta zama mai zazzafan kishi, zai lalata mata rayuwa da tarbiyyar yaran ta, zai sa miji duk son daya ke maki ya fara raguwa, sanan mutane ma masu hankali zasu fara tsanar ki, kuma daga baya kizo kina dana sani, lakin kar ki bari kishiya ta zama tana cin kashi akan ki,dan ko islam bai yarda ka zama mai sako2 yanda mutane zasu raina ka ba,kamar Mama Bilki, ta riqe zaman auren ta da amana ba mummunan kishi, tana da sanyin hali da hakuri,amma me bata yarda a taba yaran ta ba, ta tsaya masu, sannan kuma bata tsayawa ai hayaniya da ita in abu yai yawa action ta dauka, ๐ amma ban ce mace ki zama sarkin fada ba fa in dai tabbas zaki dau halin Mama Bilki sak to ratuwar ki da kishiya zaki samu sassaucin zama.
10- Qofofin Allah a bude suke ga bayin shi da suka yarda akwai shi kuma shi mai rahama ne, to duk zunubin da suka aikata ko da shirka ne, har dai in basu mutu akai ba suka tuba to Allah zai yafe masu,kamar yanda misali ya tabbata akan Kallah ya ce akwai lokacin tuba a gaba amma me yana fita mota ta mai lalata, ta dauke shi a duniyar, ai kunga ba lokaci kenan, mutuwa tana jikin skin din ku, at anytime zata iya cika mana aiki da izinin Allah dabularnin mala'ikan mutuwar, take za a zare ran mu, sannan shi Salihu daya tuban ga shi kudin dai yaoe dasu a bayan na haram daya tuba ya gyara ya sha wuya na dan lokaci na sana'a wan da a da bai san ya zai ba, daga baya kuma yai kudi ta hanyar halal.
11- Matan da basu taba haihuwa ba sui hakuri, Allah na sane da mu baki daya, ki zama kina wa kanki wannan adduar yar uwa" Ya Allah Ya rabbi ya khaliqu kulli shai'in Allah ina riqon ka, indan haihuwa alkairi ce a rayuwata da ta mijina da al'ummar musulmi da musulunci Allah ka bani, idan sabanin haka ne Allah ka samin hakuri da juriya tare da dangana, Allah kar ka bani, ka shiryar mana da sauran yaran musulmi su zama masu albarka" wallahi damuwar eashin haihuwa na maki alqawai in dai kinyi adduar nan da ikhlasi Allah ba zai barki haka ba sai ya maki zabij da kk nema.
12- Ta bangaren maza kuma in matar ka bata haihu ba ba shi zai sa ka juya mata baya ba, dan mace bata bawa kanta haihuwa, wataqila matsalar daga wajen ka ne, to misali ace ma daga wajen ka ne mace zata iya hakuri ta zauna da kai a haka, ka duva ka gani ba ta da wani namijin bayan kai amma zata zauna da kai, kuma ba shi zai hana kai ta maya rashin mutunci ba, amma kuma in ita ce mai matsalae wataqila ka sake ta, in ka barta kuma ka ce aure zakai ba zaka zauna da juya ba ita daya, ka gani mata ko yaushe su ake tauyewa duk inda aka je aka zo, me zai hana mazaje ku dage ku dabbaga sunna, ku kuma qoqar ta ku tabbatar ma duniya ba addinin da yaiwa mace martaba da qima sama da ISLAM?
13 - ko wanne stuation dayan ma'aurata ya shiga dayan ya nuna mai i am by ur side no matter what, duk daci duk zaqi ba zan barka ba tare muke a ciki.
14- soyayyar yan uwantaka abu ne mai matuqar mahimmanci sai da hadin kai bawa ke zama sarki, sai d hadin kai mayaqa kan samu nasara, in kanku a hade yake zuriar ku zata zama abin tsoro da kwarjini ga kowa, za ai tsoron taba dayan ku, za a na ganin ku as ka tabo daya goma ta shafe ka wa zai so?
15- mace ana son ku zamo