Showing 42001 words to 45000 words out of 69565 words
a duniya na kula yana son abunnan" " wai sosai ma kuwa, bakigan shi bane yana satar danwake a tukunyar Innar mu da dai kin sha dariya, Innar mu in ta kama shi sadaf2 take tafiya ta damqe hannun shi da ludayin tsamar danwaken, yai ta ihu ta qi saki" dariya sukai tayi sosai tinawa da wannan kabarin, miqewa sukai suka fara gyara dankalin, suka yanka veges harda na lambun nata, ta debi dan alayyahu kadan, da albasa mai ganye, suka gama yankawa sai ta soya dankalin nan ta dakko dafaffen naman ta da suka yanka qanana ta soya sama2 ta aje gefe, sannan ta rage man suyar ta dakko jajjagaggen kayan miyar ta, da ba timatir sosai guda biyu kawai tasa ba manya ba suma sosai, ta saka da tafarnuwa da kayan qamshi ta soya ta saka maggi da dan gishiri, sannan ta dakko wannan veges din ta zuba akai bayan ya fara soyuwa, ta juya suka tirara, sai ta juye akan wannan dankalin da daman, ta juya su, suka hade, dakko dafaffen kwanta tai shima bayan ta bare ta hada da shi ba tare da ta yanka ba, ta juya su tare,flask din ta ta dakko ta zuba wannan hadin ta rufe ta rage masu nasu, dakko flour tai naga ta dakko wani gari" Matar yayah wannan garin meye?" " to tambaya an fara ne, garin wake ne na markada da yar dawa kadan, sai alabo, na niqo su shine zan hada da flour din yafi dadi sosai" " Auuuuhooooo, to ai sai ana yi ana tambaya ko kinga laifina?" " Aa aa matambayi baya bata ai" murmushi sukai ta debo kuka, mai dan yawa yanda zai santsi, ta dakko ruwan kanwar ta, ta zuba ta hada da wani ruwan dan bata son ta cika kanwa da yawa, ta kwaba yai laushi kwabin, ba tauri sosai ba ruwa, haka ta kwaba ruwan na tafara ta fara jefawa qanana, dan yafi dad, bayan ta gama ta tsame a ruwa mai kyau ta hada mai nashi a flask, ta miqe ta barma Nafee ta qarasa ita timatir daya ta dakko nunanne, ta fada mai sugar a tsakiya bayan ta yanka, ta hau goge fuskar ta da shi, sai da ga baya kuma ta dau rabin ta saka xuma ta goge fuskar shima, nan da nan wani duhun murhu da rana ya bace fuska ta dau kyalli da kyau, bayan ta gama kuma ta dakko lallen ta, ta saka mai man kwakwa kadan ta kwaba shi, ta hau murge jikin ta duk inda hannun ta ya kai musamman fuskar ta, kafin kace me Juwairere tai kamar ba ita ba," tab lallai Yayah na shan dadi aradu, yau fa ba ranar gyaran jikin ki bane, bama ki dade da yi ba amma ji yanda kk koma kamar wata tauraruwa" " Nafee kenan, ai ita mace ana son in mijin ta yai tafiya ko na kwana daya ne ya dawo yaga ta canja kawai ko ta ina, balle wannan da kk gane we ar talking about Yah Jabeer, My love, everything" dariya sukai, Nafee nata tsokanar ta ta gama ta shiga wanka, shigar da yake matuqar so tayi ta dakko kayan ta fara sakawa, doguwar rigar material ne aka mata irin na masi ciki, an daure sama kamar bra akai mata sai hannun ya zamana a wuya aka daure shi, cikin nan ya sha mai da gyara, sai kyalli yake gwanin sha'awa, sai dogon wando da akai mai fadi sosai ta zura, ta dakko kayan gyaran gashin ta, ta tsaga daga gefe, ta kwantar da shi, ta daure in a ponytail style, qamshi kam ranar kamar an barin turare, fuskar ta daga powder sai lipstick, ta gyara girar ta, ta saka kwalli,( kwalli na da matuqar tasiri ga mace, macen da ta saka kwalli ta iya kallo ta yi a rayuwa, in baki iya ba koyi ki fara)dogon hijab ta saka, tai sallar magrib ta zauna, tai azkar din ta, ta fara karanta qur'ani, ana kiran sallar isha'i ta tashi ta fara, Sallama yai ya shigo, yana ganin tana salla ya aje kayan shi yai alwala shima ya tafi masjid, tana idarwa qara gyara jikin ta tai duk da ba abin da yai, ta qara turare, ta gama, dauke kayan da ya shigo da su tai, na ajewa a kitchen ta kai ta fito da kayan nashi,masu datti ta fitar wamda bai amfani da su ba ta mayar wajen kayan su, sai wata leda da bata taba ba ta aje a gefe,daga alamu tsaraba ne, ruwan wanka ta je ta hada mai mai dumi, ta dawo kenan zata zauna taji shi, bayan qofa taje ta maqale tana ta dariya qasa2, shigowa yai yana ta dube2 bai ganta ba, sai da ya kama qugu sannan yace" Juwaireren Mama ko ki fito ko na zauna a qasa naita kukan rashin ganin ki, in an shigo nace baki son gani na ne" kan ya rufe baki yaji ta mai wata iriyar runguma ta baya wadda tasa shi fidda sautin da bai san ta ya akai yayi shi ba,( rungume mutum ta baya akwai yanayin da mace ko miji zasui ya zama ba wata runguma da ta fita dadi, ana yin ta ne ta hanyar zuro hannu a hankali ka zagaye mutum sai ka ja shi baya cikin shauqi ka manna shi da jikin ka) juyawa yai gaba daya ya daga ta sama, suna ta dariya, kisses kam kun san ranar an yi bari da ruwan su, zaunar da ita yai a cinyar shi, yana shafa cikin ta, yana ma cikin surutu kamar wanda yake hira damutum babba, dariya kawai take yi ita kam, " sannu da zuwa hasken cikin gidana, tin da ja tafi kaga daya gidannan duhu ya mamaye shi, yau haske da ya bayyana daban ne, na gode Allah da ya ban kai a matsayin miji, Yah Jabeer ba zan iya rayuwa ba kai ba, i missed u so very much" ta qarasa tare da qanqame shi tana hawaye, dagota yai yana jin wani sabon qaunar ta na ratsa shi, dan yasan she meant every word, " Hushhh Husshhhh my princess, ki daina kuka, Yah Jabeer na Juwaireren Mama ne ita kadai, bana fatan na wayi gari baki kusa dani, u ar my happiness, i cant do without u, u ar everything that i ever wanted in my life, so don't be scared of loosing me, nine ya kamata naji wannan tsoron, amma ba zan damu ba dan nasan zuciyar ki, da ruhin ki , da gangar jikin ki nawa ne" wata runguma ta qara mashi da ta saka shi jin dadi sosai, daga shi tai ta ja hannun shi zuwa wanka ta taya shi yai wankan yai brush suka fito ta shirya shi bayan sun gama ne kan shimfidar da suke cin abinci ta jawo hannun shi ta zaunar da shi, shikk binta kawai yake kamar raqumi da akala, dan waken ta fara zubawa a gefe, wanda har wani kyalli yake dan santsi sannan ta zuba mai wannann hadin da tai na dankali, zobon da ta dafa da abarba, da cittta kaninfari, kai da kayan qamshi dai da suka dace dika, ta saka harda cocumber, ta sa sugar, ci yake yana lumshe ido kawai, yana wani gurnanin magana amma ba a ganewa me yake fada, daukan zobon da aka saka a randar sanyi yai dan basu da fridge yai ya kurba, saurin bude idon shi yai sannaj ya mayar ya kulle, " Yah menene, yayi daci ne jo wani bu?" Ta fada tana zaro ido waje dan a tinanin ta ko bai mai bane, " matso kiji me yai" yana dan yatsina fuska, ita kuma sai ta danji zuciyar ta ba dadi, saboda gani take ta bata xobon garin iyayin mai hade2, dan ba ta san dama ana saka cocumber ba qirqira tai, matsawa tai kanta a qasa, " sai kin rufe ido zaki iya shan wannan abun, matso sosai na baki da kaina kiji ya yai" matsawa ta sake yi, ta rufe idon, jitai ya kama lips din ta yana masu wani salon da ya sa ta magana a qasan maqoshi, saida ya dade kan ya sake ta, ta kasa bude ido, dan wasu taurari ke mata yawo a kai" bude idon mana Princess, ni ba mai kudi bane bare na maki kyautar wannan kayan dadin da kk ban yau, amma na san i will make u feel something special, with every part of me" daukr ta yai sukai daki, zan bisu aka bugon qofa,nace ba sai an karya ma Hammana hanci na ba, zan tafi malamai🙄😙😙😙😙
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: 💅🏼 ' YAN ABUJA 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
Page 24:
" Adda Saudat dan Allah ki ban dubu daya mana ina son in dan ja jari ne ko ba yawa, xaman haka baya min dadi,ke ma kuma ya kamata kafin kudin hannun ki su qare ki kama wata sana'ar saboda kin saba yanzu da kudi, randa kk da buqatar su kk rasa ba qaramin damuwa zaki shiga ba" tinani Saudat take mai zurfi, can ta nisa tace" gaskiya kin ce wani abu kema, zan baki dubu biyar ki ja jarin, ni kuma zan fara kasuwanci ta waya da naga qawaye na da nai a whatsapp da facebook sunayi, ana samu in ka riqe amanar mutane, sai kaga ka samu riba mai yawa kana daga zaune" " yauwa Adda, sannan ina son nuna maki kinga Mama Bilki mace ce mai kirki, tana matuqar son mu, sai dai tabbas tana kishi da Goggo, wanda wannan dole ne a zaman kishiyoyi dama,mu sai mu kau da kai akan wannan, tinda iyayen mu ne, ba ruwan mu da hurumin su ta wannan bangaren, ya zama wajibi mu masu biyayya dikkan su, su a matsayin iyayen mu, itq a matsayin matar Abban mu" shiru Saudat tai domin maganar qanwar ta ta yau tana shigar ta, amma akwai nau'i na girman kai, da kishi a zuciyar ta, " hmmmm zan duba na gani" ta miqe ta dakko mata kudin ta bata, akan idon Goggo kuwa, " habaaaa Salma ai innice ke yanda na canja uwa, yan uwan ma canja su zan, auhoooo ba zaki iya canja yan uwa ba saboda kin same su su masu arziqi ne ko? Zaki roqa za a baki ko" " ni fa Gogga ba haka bane, ya kamata ki bude idon ki ki gane inda gaskiya ta dosa, ki daina rufe idon ki akan abinda bai kamata ba" " rufen baki sallamammiya kawai, an yi asiri da tuggu kala2 an rabani dake, to kije nima na huta da dawainiya, da dan wani da zanyi" juyawa tai tabar wajen Salma kuwa cikin qunan rai da baqin cikin halayya ta uwar ta ra shige dakin Mama Bilki, wadda taji komai, fadawa kan cinyar ta tai tana kukan takaicin hali irin na uwar tasu, shafa kanta kawai Mama Bilki take, bata furta mata komai ba," Mama ni fa ba kwadayi ne ya sa na tambayi Adda Saudat kudi ba, na tambaye ta ne naga ko tirare bani da shi, ga shi yanzu sai da Alimun ko lemon tsami nake amfani a madadin tirare, ba dan komai ba sai babu da take neman ta min yawa,amma in ina sana'a kudin zasu taimakan wajen kula da abinda ke cikina, shine Goggo take fadan maganganu marasa dadi akaina" " hakuri zaki Salma uwa ba abin wasa bane, dole mui mata biyayya in ba inda za a sabawa Allah bane, dan haka ki hakuri tin da kin samu jarin yanzu me zaki na yi na siyarwa?" " Mama Bilki ni da ina son na fara saida Meatpie ne, naga kina da injin yin taliya, kuma na kula kayan flour ana cinikin su, in ba su ba ban san me zan iya yin sana'a akai ba" " hakan ma shawara ce mai kyau, Allah ya sanya albarka" " Ameen mamana" kwantar da kanta ta sake yi a jikin ta ita kuma tana shafa gashin ta.
Yau kusan sati daya da kwana uku kenan Suwaiba na kwance tana jinya, Alhj Salihu dayaga zata farka ya danna mata allurar bacci ta koma, ko ya shaqa mata wata powder ta koma baccin, a haka tai wadannan kwanakin, zai mata wanka, zai canja mata kaya,sannan ya saka mata drip dan tana samun abinci ta jikin shi, ya zama babban likita kawai a cikin gifan shi, a haka sai da ya kula wajen ya warke tas sannan ya kyale ta da allurai na bacci da yake mata, yau ne ranar data bude idon ta tana kallo. Wajen kamar sabon waje aka kaita, a hankali ta bude idon gaba daya, akan na Alhaj Salihu ta bude su, kanta ne taji ya mata nauyi,kwantar da kan ta sake yi a pillow, jikin ta a mace ta bude baki tai magana da kyar" Me ya samen Sweet? Me yasa nake jin zafi sama2 a qirjina kamar naji ciwo?" " Shiiiiiiii karkina nagana sosai, hatsari muka samu a gidan, yan fashi ne suka suka shigo, kina bacci suka yanke maki Nono, ni kuma dana dawo na ganki kin suma shine nake ta kula da ke" a firgice ta miqe daga kwanciyar," an cire man nono?" Ta fada tare da zaro ido waje wanda suka cika da kwalla mai dumi, " na shiga uku ni Suwaiba,ya zan rayu ba mahaifa ba nono, gaba me zan rasa kenan, Alhj na fa san kai ne sanadin rasa nono na Saudat ta fadan ban ji ba ban yarda ba, saboda ina son ka, ko da ina son kudin ka, ya zan rayu yanzu ba nono ba mahaifa" rushewa tai da wani kuka mai ban tausayi, cikin tausaya mata Alhj ya fara magana" ki yi hakuri Baby yau zan........ ka tse shi tai cike da bala'i" don't baby me again, i hate u, i hate u, i hate u" ta qarasa tana kuka mai ban tausayi, matsawa yai ya kamo ta ta zame," Don't touch me u monster, if u touch me again i swear i will cut ur balls too" cike da fushin da bai san tana da shi ba, wani shakkar ta yaji ta shige shi, miqewa tai cike da jiri, zata fita, " ina zaki kuma" " gidan mu zani, na gama auren ka, na gama aure a ABUJA daga yau daga rana mai kamar ta yau" " lallai ma Suwaiba, abinda baki sanj ba shine, ba inda zaki qara fita ko nam da can ne, kina tare da ni, dan yanzu ba zan iya rayuwa ba ke ba" ka mutu to, dan ba abinda zai hana ni barin gidannan, ko kana so ko baka so, in ka barni na tafi lafiya,ba hukumar da zan hadaka da ita, amma in ka hanani ba abinda zai hana ni hadaka da hukuma" wani murmushin rainin hankali ya mata ya ce" baki san wani abu ba, qungiyata babbar qungiya ce, manyan gwamnati da yan kasuwa ba wanda bab a ciki, ba yanda za ai ki hadani da hukuma kuma a samu hukunta ni din, mata dubin ki mun masu wannan aikin balle ke, dan haka hakuri zaki kawai mu qarasa rayuwa dake, in kin tafi wa zai na baki abun dadin danake baki?wa zaina debe maki kewa?wa zai zauna dake ba nono? Hakura zaki kawai mu zauna a haka" yana fada yana dhafa mata wuya, gaba daya ta qame ta dauke kantadaga ganin shi hawaye kawai take, ga wani tsoron shi a qasan zuciyar ta da take ji, yau ya zatai,kuka ne ya kwace mata sosai take yin kukan, key din motar shi ya dauka ya fice, anan ta durqushe tana kuka mai ban tausayi.
Talle kam ya saka marka a tsaka mai wuya ita da yayan shi, dan baya son maganar ta fita waje, gonar shi ta daji mai shegen nisa ya ke sasu zuwa gyaran ta, duba da cewar damuna ta kusa, kullum can suke tafiya ba abinci ba ruwa, amma shi zai je a machine din shi, da abincin shi da ruwan shi, saboda ya dinga ganin me suke masa, kar a masa ba daidai ba, su kuma su Baban gida gonar shi ta can wani qauyen dake kusa da su ya tura su, saboda ya yi yarjejeniya da su akan hakan, in ba haka ba ya kaisu birni ga hukuma, Kan kuce me Marka ta fita hayyacin ta, 'yan duwaiwakan nan duk sun zube, tai qashin wuya da jiki, yan gari sai gulma suke amma sunnrasa dalilin Talle nayin hakan, da dama sai suka alaqanta hakan da tsantsar rashin mutuncin shi, su Huwaila kuwa kullum sai sun yi surfen abinda za ai tuwo da shi sun dake da hannun su sun mayar gari, sannan sui tuwon, ga aikin qannen su da ya dora masu, wahaka kamar zata kashe su,ga qaramin ciki. Jummala ce ta fito daga dakin tana riqe da cikin ta, tana ta murqususu, " ke meye hakan zaki zo kina ma mutane kuka, kin gama aikin da na saka ki?"cikin kuka da tashin hankalin da take ji a jikin ta ne hasa ta budi baki zatai magana amma ta kasa, saboda wani abu da taji ya taho da gudu zai fita ta qasan ta, jini ne ya tsinke mata, nann d nan ta suma dan wuya, a gigice marka tai kanta,shi kanshi uban gayyar ya tsorata, daukar ta yai a hannu ya kai kan machin din shi, marka ma ta hau ta riqe ta, asinitin qauyen suka kaita, nan da nan aka tabbatar masu da bari tai, saboda ta sha wani magani na zubda ciki, ga jini yaqi daina zuba a jikin ta, suna buqatar a sai mata jini a qara mata zasui iya qoqarin su su tsaida jinin, Talle ne ya kalli matat shi, " sai ki fito da kudade da kk ajewa ai mata magani ko" ya fada cikin hade fuska, " to bari na koma gida" a qafa ta dibi hanyan duk tayi sanyi, ba cika da izzar nan ta da, kafin ta isa gidan ne ma likitan ta fito, take sanar