Showing 3001 words to 6000 words out of 69565 words
ta tai murna na ratsa ta daya kira kanshi angon ta, ga hannun ta dayake murzawa a hankali, karbe hannun ta tai ta canja mazauni tana turo baki, ita a dole fushi take,Mama ce ta shigo dauke da kofi a hannun ta ta aje mai a gaban shi ta samu wajen zama," Mama kin ga wannan yar rigimar ta turo baki, lallai akwai magana yau" Aaa ni kam ba ruwana ina gefe ba a shiga tsakanin ku ai ku" komawa yai kusa da ita ya dago kanta" Juwairere na me ya faru?"to ba ga shi nan ba wai Juwairere๐ฅ ni Allah bana son sunan nan,gaba daya ka sa Nafee na tsokana ta, Kullum ta ganni sai ta hau ce man Juwairere ta qarasa yar kwallar ta na fita baki a gaba, dariya ta bashi ba kadan ba wauta da shagwabar ta na burge shi sosai" ki kwantar da hankalin ki princess ba zan qara fada ba inshaa Allah sai munyi aure" harara wasa ta mai tare da jin kunyar kalmar aure da ya ce ta fita a dakin da gudu tai tsakar gid tana dariya, kada kai Mama tai tace "Allah dariya kuke ban yaran nan ba kadan ba kun iya wauta" Mama kenan ba wauta bane da gaske auren ta nake son yi in Baba zai ban ita, itamma ba Abujan za a kaita ba, dan dalilin zuwana kenan, naji an kawi kudin wadan can marasa kunyar" hmmm haka ne Jabeer amma kasan ni ba ruwana da wannan kalmar ta yan unguwar nan ko, na cewar yaran gidan nan YAN ABUJA NE ba zasu auri kowa ba sai dan can, in su suna fda kuma sun yarda zasu aure su ni ban fada ba kuma ban ba yata izini ba , in da rabon can ne gidan auren ta yake Allah ya zaba mafi alkairi in ba can bane ni ko ina albarka na ke nema mata kullum" haka ne Mama, Allah ya shige mana gaba" Jabeer dan gidan Yaya Balarabe ne ya dawo daga bautar qasa inda aka tura shi illorin, ya kammala karatin shi bangare kasuwanci, to a yanzu haka yana taba saida jakunkuna da takalma, ba wani arziqi ne da shi ba, yayun ta sun so matuqa ace me kudi ne da sun aure shi ko dan kyaun shi, amma inaaaa talauci a cewar su ya dakushe tauraruwae shi.
A yan kwanakin nan kusan kullum sai ya zo, ana haka Salma tai wani saurayi mai kudi shina ya fada mata a Abuja yake da zama, kuna shi sana'ar saida motoci yake, kullum in zai zo ya vaza uwar riga ya shigo mota mai tsada ya zo amma fa ba ko sisi, wataran ne ma zai dan samu ya siyo mata yar shawarma kamar mayya tana rawar kai saurayi ya siyo mata abu ta amshe ta shigo,itama tini ta i sahun manyan ta amsar kudin maza da basu jiki ai tabe2 , alhajin dai dake son ta shima ya matsa zai turo sanda ya turo magabatan shi sun sha mamakin ganin daya daga kayan da ya taba zuw da su da motar, amma suka basar, a tinanin su wata qila anko sukai๐.........
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: ๐
๐ผ YAN ABUJA. ๐
๐ผ
BY HAERMEEBRAERH
Page 3:
A haka aka karbi kudin auren inda gaba daya aka saka ranar auren su nan da wata daya, gori kam da baqaqen maganganu ba irin wanda Juwairah.bata karba ba wajen yan uwan ta, tin tana kuka har ta kai ta daina sai dai ta kauda kai sui tayi ranta na quna, takanji kamar ta ce Ya Jabeer ya fito ai auren. Wata rana ta na zaune tana yanka alayyahu ma Maman ta sai Adda Suwaiba ta fito ita da Salma, " hhhhhhh Adda dan Allah ki ga yarinyar nan, a kyau dai duk gidanan albarka tafi kowa, ta tsaya ta mori kyaun na ta amma tanaiwa kanta baqin ciki tsabar mugunta , ban taba ganin irin wannan yarinya va" hmmm ina ruwan ki uwar kinibibi taje ta auri wanda ta gadama ma ba Jabeer ba, danni wallahi ba kyau ba ba ilimi ba in baka da farare bugun Abuja, sannan ba zaka auren ka kaini Abuja ba wallahi kayi kyaun banza da kyaun halin wofi, dan ba su zan ci ba" dariya sukai sina riqe baki, alamun sun ma ta rashin mutuncinnan, girgiza kai tai tace" Adda Suwai kenan, ina kyautata zaton kun manta wa keyi, sannan kun manta dawa kuke jayayya, wanda duk zai wa wani gorin talauci to y sani ba da wannan bawan yake ba da ubangijin bawan yake, beside ba fa kusan sana'ar mazajen ku ba gaba ki dayan ku damuwar ku kawai a kai ku Abuja, ku matan Abuja ne, matan manya, bana maku baqin ciki, zanfi murna ace kuna gidan hutu dan nima ina ma kaina fata, amma zan baqin ciki ace baku da alkibla saita kudi da son abun duniya, Allah ya kyauta, ammmm for ur information, ni haka nake son Ya Jabeer ba dan dukiyar shi ba ba dan komai ba , Son shi ni kaina ba zan ce ga daga in da ya fito ba, na tainci kaina da So da qaunar shi ne kawai dan haka wannan matsalar ku ce wai rashin kudin shi, tinda ya zama jinin jikina ba zan iya rayuwa ba shi ba kun ga ko ko a wanne hali yake zan iya zama da shi" Tafi taji ana yi mai cike da shauqi idon Jabeer tap kwallar dadi da murna, Mama na daka tana mamakin yar ta ta, lallai yau an kaita maqura,daga kai tai tagan shi yana qarasowa gaban.ta, wata irin kunya taji ta lullube ta da ko guduwa daga wajen ma kasawa tai, dan tinda suke bata taba zayyane mai yanda take son shi ba, wanda da damar masoya shi ke dakushe ma su amashin soyayyar su, kafadun ta ya riqe ya juya ya kalli su suwaiba, inda suka qame qam suna wurga idanu, " Princess wadannan kalaman naki sun qara dasa man zazzafar qaunar ku da son ku akan na da, ba zan iya rayuwa ba ke ba, dan haka nake roqon Abba da ya taimaka ya auran ke nima a hada gaba daya da na wadannan fitsararrun marasa tarbiyya, ba dan komai ba sai dan a kafa tarihi tare kar muzo lissafi yana kwace mana" murguda baki Suwai tayi tana qunquni tai daki, tsugunnawa yai ya ci gaba da taya ta aikin ita dai kunya ta ishe ta a haka suka gama yiwa mama girki ko leqawa gaida maman bai ba ita kuma ta kasa fitowa dan komai akan kunnen ta akai, Abba ne ya shigo da sallama bayan sun amsa ne yace" Aa Juwaira Jabeer yau kune kuke mana abincin daren? " yana fada yana dariya, sosa qeya yai ita kuna ta rufe fuska ta je ta amshi ledar hannun shi, tai dakin Mamar ta da yasha gyara yake qamshin tiraren wuta na tsinke, Maman ce ta zo ta wuce su da ruwa a bokiti kanta a qasa dan yai yaran sun bata kunya sosai, Jabeer ne yai dariya yace" Hajiya Maman mu yau kuma kunya ta kk ji ne? Shiyasa sai yanzu kk fitowa da kk ji Abba ko? Ai dana sani to tafiya nai da muka gama hirar tamu" sosain hannun ta ta wurga mai tana " wannan danneman tsikannen yaron wato duk kauda kaina sai ka nunan kai dan zamani ne ko? Ai gashi kun ja min makara yin wanka sai da Abban nasu ya dawo" dariya sukai dika Abban ke tambayar me ya faru da hanzari Juwaira tace" ba...ba..komai Abba" dariya Mama da Jabeer sukai Mama ta wuce su Jabeer yace "Abba ka huta akwai magana a bakinnan nawa, ni dai in ke ba ki da abin cewa ni ina da shi" roqon shi take da ido ya bari sai gobe yau kuyar zata mata yawa, amma kanne ido daya yai yana mata kwalo sai ya fada yau, tura baki tai tai daki, bayan sun gama komai tayi wanka sunci abinci, in da wajen cin abincin ma Jabeer rashin ta ido ya so yi ta qi yarda, wai da sai dai suci a kwano daya, da taqi sai ya zauna kusa da ita, in ya faki idon kowa sai ya zura hannu a nata ya diba ya kai bakin shi yana lumshe ido, can sai yace" ke ni fa ban yarda ba ya akai naki ya fi dadi? " Kai Ya Jabeer da rigima kk, ni duk daya ne kai ne ka ji haka" to kawo mu canjen kwano in haka ne" miqa mai nata tai ya bata nashi daya ci gaba da ci ya qara zura hannu a wancan, " Tab in ba sai an qara canjawa ba me kk fakar idona kk sawa naki?" Yahhhhh" ta fada tana turo baki cike da shagwaba, " wai ni da kk wannan maganar ta ya akai kasan nata yafi dadi?" Saurin tashi zatai ya danne hannun ta da nashi, " Abba loma daidai nai a dikka" Allah yafi loma daya" ๐๐ " Hmmm Abban su dan allah ka rabu da shirgin yaran nan mu ci abincin mu bana son kana wasa da cin abinci kar wani ciwon ya kama mana kai" kashe mata ido Jabeer yai ya matsa kusa da ita, daidai kunnen ta" to kinji yanda ake wa miji ko, sauran mui aure kina raba mana kwan irin haka" dariya ta gimtse," hmmmmmm bariki, har da Yayan ake zaune ake iskanci a tsakar gida, sannan in nawa sun fita ace masu yan iska, to ai bahaushe yace, qazantar da baka gani ba tsafta ce" muryar Goggo Sarai kenan, "Subhanallahi, me kk fada ne ke ko agaban yara gasu gaba daya kin jawo su kun fito kun sani a gaba?" Eh abinda kaji na fada mana ko maimaici kk buqata na qara karanto maka?" To bari kiji mara kunya, Jabeer ya tabbatar man da auren Juwaira yake son yai, yana son a hada dana sauran ayi, dan haka wannan shirirtar taki da goregoren naki ya qare dan duk ina ji" Aiko ba wanda ya isa ya hada mana aure da wadannan yan maulan" kan ta rufe baki taji fauuu an make bakin da qarfi, saida bakin yai jini," kan uban nan Jabeer me suwaiban tamaka zaka mata wannan dukan, ko uwar ka Hansai ba zatai ma yata hukun ci ba balle Uban ka Balarabe" wani dukan ya kaiwa Saudat dake kusa da shi sosai mai qarfi saida ta kifa, " duk rashin kunyar da kikai ma Abba kan su zan huce ita kuma waccan hikuncin rashin kunyar da ta min ta karva" sannu uban su" inji Salma, aiko takalmin qafar shi ya cire ya murde hannun ta yaita maka mata, sai ihu take, Goggo ce taje da niyyar kwace ta, wani kallo ya mata da hantar cikin ta ta kada tai baya da sauri tana " Allah ya isan su baqin mugu kawai" sakin ta yai ya sa takalmin shi yai waje, Abba da Mama sai Juwaira da idon ta ya cika da hawaye suka shige daki suka rufe qofa suka bar su nan.
Washe gari sai ga Baba Balarabe yazo batin auren Juwaira da Jabeer, sadaki dubu ashirin, a taqaice dai dubu Hamsin ya miqa masu kudin komai dan iya su ya ke da, take ita ma aka shaida hada bikin su dana yan uwan ta, sunyi murna sosai, inda suka sha gorin cewar " dadin ta kudin auren ma kamar anje siyan yar tsana a gwanjo dan ko matsayin kasuwa ma ba a samu ba" suna yi suna dariyar rainin hankali, ba wanda ya kula su, sauran dubu darin da yake da ita kayan gado masu sauqin kudi yaje ya siyo mata da kujeru, irin na talakawannan, Jabeer yai qoqari sosai Abba na ta hana shi, yace Abba dama ai a musuluncu haqqin miji ne duk wadannan amma al'ada ta sauya abun, dan haka na bar ku da siyan yan kayayyakin kitchen, Allah ya hore mana mu samu aiki mai kyau Abba kasuwancin nawa ya bude, komai zai zama tarihi, addua sosai Abban ya mai da godiya. Daki aka gyara mata a main house din su ya kewaye mata guda biyu da dan wani qaramin waje a matsayin kitchen sai wani budadden bandaki mara rifi daga cikin kewayen nasu dai, ba laifi daidai talaka, yanzu jiran ranar biki sike nan da tan satika.
A yau ne dimbin mutane manya masu manyan motoci da qanan mutane marasa abun hannun suka shaida daurin auren wadannan bayin Allah kamar haka, Suwai ba da Alhajin ta Salihu mai tumbin Nera, Saude da Alhaji Kalla na Abuja, Sai Salma da Alhaji Mansur, sannan kuma qaramar su Juwaira da Jabeer din ta, surutu kala2 ke yawo a tsakanin mutane wasu na sanya alkairi, wadan da suke bin bashin magana kuma suna gulmammaki akan su Suwaiba sun dakko ruwan dafa kan su ne basu sani ba, Salma kuwa bata da wayo, duk kyaun ta ta buge da auren talaka? Kowa dai da abinda yake fada, a haka aka tashi daga daurin aure, inda mazajen su Suwai ba suka ce su fa basu yarda ai komai a kano ba Abuja za a wuce ai dinna babba mai qayatar wa da abokan su, sai matan abokan su, ko dangin su ba za a dauki ko daya ba, shi dai mijin Salma shima cewa yai a bashi matar shi ya wuce da ita Abuja domin shi ba abokin mijin su Suwaiba bane, sun roqe shi akan yaje ai komai tare yaqi, dan haka kawai kauda maganar yai yace zasu tafi ba damuwa dangin shi da abokai na jiran shi za ai dinner, Ita kuma Juwaira sun yi yar walima kafin dare aka gama, YAN ABUJA KUWA jiki na rawa da daren nan, aka shirya su Goggo na kuka suna kuka aka fita aka daga sai ABUJA. Da dare kuma Juwaira na gaban Innar ta da tazo biki Inna Dije tana qara bata yan kayayyakin mata natural, wanda ta hada madara da zuma da ta sha dakakken kayan qamshi cikin babban kofi tace ta shanye, dama ta yini da yunwa tini ta shanye tsaf, ta qara mata da dafaffiyar kaza da ta sha kayan qamshi itama ta ci iya itawar ta, ( ita ni'imar mace ana son ta da dumi yan uwa, ba a son ni'ima da sanyi, dalilin haka ne ake sin muna yawai ta amfani da kayan qamshi su citta kaninfari masoro, da dai sauran su, suna saukar da dumi ga jikin mace, ko hadin su kankana da su cucumber korake mutum zai yana hadawa da wadannan, suna qara mai dadi da qamshi da amfani a jiki,) a haka aka sa ta gaba tai wanka me kyau da dan tiraren su na wanka dan duri, dan basu da arziqin siyan mai tsada, ta samu ruwan dumi mai hadin ganyen magarya da kaninfari kadan a ciki tai tsarki da shi sai qamshi ke tashi ko ta ina, tana fitowa Inna Dje ta bata misk mai kyau ta sa ta shafa a HQ, sannan ta miqa mata brush din ta ta wanke baki duk tana tsaye a kanta, ita ko kunya duk ta dame ta ga mutane ba a gama tafiya ba, ai ko tana gama wa ta sata tai alwala sukai daki batansa ta shafa wani kwalliya mai nauyi ba, iyaka ta gyara ta ta samata qanan kaya daga ciki riga da skirt masu matuqar kyau, sannan ta sa mata laffaya, ga qamshi na tashi ko ta ina, kunshin nan ya zanu kannan ya dau gyara na musamman , yan daukar amarya ne suka zo a mota biyu, tana kuja tana komai aka fiddata, wata goggon Su ce mai suna Kareema tace" yanzu Bilki ba wata yar nasiha haka za a fiddata baku mata ba ke da yaya?"" Hmmm Kareema kenan, ai Juwaira bata buqatar wannan, duk zaman ta tana nufin bata koyi komai ba a wajen mu? Ai ba zai mata amfani ba a yau ina jin taje da sawar albarkar mu a rayuwar su dika" a haka ta tafi daki ta zauna sai hawayen rabuwa da yarta take abar son ta, an kai Juwaira lafiya kuna kowa ya kama hanya ya dawo, an barta daga ita sai halin ta tana ta zare ido dan hawayen sun qare mata......
..
.....
[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: ๐
๐ผ 'YAN ABUJA ๐
๐ผ
Page 4:
Tana cikin wannan yanayi na tinanin Maman ta da Ammar taji hayaniyar maza na shigowa, sauri tai ta dawo palo ta zauna dan bata yarda wasu qarti su shiga mata har dakin baccin su ba da sunan abokan ango a daren farko, zama tai ta nade qafafun ta a kujera, ta rufe kanta har fuskar ta, Sallama sukai suka shigo, akwai wasu daga abokan shi da basu san ta ba dan ba garin suke ba, amsawa tai da muryar ta mai dadin sauraro, kanta a qasa, tana tsaka da jin dadin ba wuta ba zasu ganta sosai ba aka kawo wuta, haske ya gauraye ko ina, ai ko da sauri ta qara duqunqunewa, dariya sukai gaba dayan su" to amarya ki kwantar da hankalin ki mu ba zamu takura sai kin bude fuska ba, angok ki zai bude maki da kanshi in mun tafi, sai dai akwai wasu shawarwari da nake son baki, wanda na san kin san da dama daga abubuwan zamab aure, amma wannan mata da maza sun rasa su shiyasa ake samun sabani mai yawa a gidan aure, na farko dai akwai son zuciya, miji da an kwana biyu ya daina dokin amaryar shi sai son zuciya ya shige shi, ya fara fito mata da halayen shi mara kyau na kwadayin son ya zamana ta fara taimakawa gidan dan ya samu sauqi, ba a ce mace karta taimaka wa mijin ta ba hakan abune mai kyau, dan zai qara mata samun lada mai yawa, sannan zata samu soyayyar mijin ta da yawa, amma abinda ba a so miji ya sa son zuciya ya dinga especting din matar da hakan,in batai ba a zo rai na