Showing 69001 words to 69565 words out of 69565 words
mai iya tarairayar miji, mai bashi haqqin shi na auratayya a koda yaushe, mai iya salo kala daban daban, ba tare da kauce hanya irin na matan yanzu da suka maida kallon turawa suna zina ya zama wai suna koyon style na auratayya wa'iyadhubillah, me ya kai ki ko me ya kai ka? Me suke da shi da mu bamu da shi, zuciya ce da kwakwalwa, muma muna da ita,a rana in kin so zakui style kala biyar ko fi, ku gamsar da juna,ba tare da kowa ya koya maki ba, to ku sani ni a nawa duk namijin da zai saka mana wani shirme mu kalla kafin sex ba namiji bane, rako su yazo in sun gama sabgar su ya bisu su koma, dan ba rashin zama na mijin da ya wuce ka kasa dagawa mace sha'awa sai kun ga wasu awaki na yi sannan ka samu ka take matar ka da ya fi wannan, ga illoli dake tattare da hakan, fushin Allah da tsinuwar shi akan ku dika, haihuwae yaran da ake cewa yanzu sun kashe iyayen su, sannan kuma ciwon makanta, sai mai wannan hali ya shirya masu in bai daina ba. Sannan illar kallon nan yanzu ta shine aka yawaita mata yan lessbians da maza gay dan musiba da qazanta Allah ya kare mu da zuriar mu.
16- Sadaukarwa, ka sadaukar da farin cikin ka dan wani musulmi ko dan uwan ka ya samu farin ciki shima, ga lada ga qarin arziqi da zai same ka, zaka samu da yardar Allah Allah ya mayar maka abunnan da ka sadaukar har da fin shi ma, kamar yanda Juwairah ta sadaukar da Abrar ma Suwaiba nonoless.
17- kowacce mace dangin miji ce ki kula da yanda zaki tafi da dangin mijin ki kema naki dangin mijin su kula dake in kika qi yin da kyau zaki ga ba kyau kema.
18- kula da tarbiyyar yara a tsakanin dangi, musamman cousens a wannan zamani, cousens sun ja an aurar da zawarwan yammata da yawa, ba tare da an sani ba, zaki ga suna wasan banza ba za a hana ba ace wai ai yayan ta ne, ba aure tsakanin su? Ke ko da aure yanda zamanin nan ya baci akwai limit na komai, ko kiga ya damu da ita da yawa,ko yaushe suna tare mamat2 ace ai suna matuqar shiri,kin tintibi dalilin shirin? Sannan kuma wajen bacci a bar yara sakaka ta nam wallahi cousens ke dada bata mana yara da qanne, dan haka mu kula dan kin tsaya akan yar ki baki laifin komai ba a duniya da lahira.
18- ina ma mata nasiha da qamshi, da kwalliya,tsafta girki iya magana musamman da yawan mu bamu iya kalamai ba da magana komai yabawa muke, ki iya kwanciya, kirsa, kwarkwasa, iya saka qananan kaya,da daura zani, iya kallo,shagwaba, wayyo da mata sun san me ke cikin ta da wataqila har makarantar koyar da ita an fara bude masu, ki iya girki, macen da ta iya girki mai aji ce ki ba ta da aure, ba raini tsakanin ta da kowa, ki zama mai sassauqan halin da kowa zai so mu'amala dake.
*ina riqon mu dab Allah ko daya mu qoqarta mu saka a aikin mu za a samu gyara da canji, wadda take da abinda na manta ban saka anan ba qofa a bude take da ta rubuto mana da sunan ta da komai dan mu qaru*