Showing 27001 words to 30000 words out of 69565 words
soko bane kamar ka, zai iya gane wa" kada mata kai yai alamar zai kiyaye, shigewa tai, Salma amarya ana can ana soyewa ita da me gida, Sun yi nisa ba sa jin kira, komai ya kankama, har ya fara aiki, suna cikin yi ne sukaji motsi ana sanda, gaba daya Talle ya cika wajen na su da gurnanin shi, Marka kamar ta mutu dan kishi, ga wani irin feelings da take ji, sai matse qafa take ta kai ta dawo, ta kuma kaiwa ta dawo, tana jin motsin tace," Alhamdu lilLAAH" ai ko ta manna kan ta a jikin qofa taji ya za a kaya, " Salame bude qofar mana na iso, me kk yi ne baki riga kin bude ba sai na zo ina bugawa sun ji kamar rannan, so kk wannan shegiyar kishiyar taki mai baqin tsiya taji ta leqo irin na rannan, Salame ya dai naji ki shiru, dan Allah ki sauri mana ki bude muyi mu gama na tafi a matse na zo yau" Talle da ya gama jin komai wani shaqa yai ma Salma da idon ta ya firfito waje, amma da sauri ya sake ta ya sauka , ya saka wando jin da yai ba a daina taba qofar ba,kuma ba a daina kiran Salma ba, ai ko mai maganar da ya leqa ta bular da yake hango su yaga yana ta howa da gudu ya kwasa yai waje, ya fito da hanzari yaga an gilma da gudun tsiya komawa yai dakin, dan ya san laifin ta ne koma wane, kan yaje ta zura rigat ta tana ta kukan wannan masifa da ake neman jefa ta, " Marka" shine abin da ta furta,dafe kan ta tai, da ta sani da bata tsuye ta ba ta bat su da halin su, gashi yanzu ta jawa kanta,dukan ta ya fara ko ta ina tana ihu tana ya tsaya yaji me ya faru, ba ta da laifi, inaaa dukan ta yake tin tana kuka tana bashi hakuri sai da ta koma ajiyar zuciya, sai da ya tabbatar ta kasa motsa ko da ya tsan ta ne sannan ya futa dakin Marka, tana bude qofar ta wani azababben mari ya maka mata, " Dan uban ki kin san hakan na faruwa ashe kk munafurcen baki gayan ba ko da ta wayar yarannan ne? Ga shi kwarton na ta ya ce kin gansu" kuma ta fara dan marin ya matuqar shigar ta" inna fada maka ba yarda za kai ba cewa zakai kishi ne, shiyasa nace Allah ya nuna maka da kan ka ka gani" kwafa yai yace zata ci uban ta na san maganin ta ai,komawa yai ya kwanta, a dakin markan, nan take jarabar ta ta motsa, musamman d ta gan shi ba riga,matsawa tai da zummar kwanciya gefen shi, da dabara ta goga qirjin ta a bayanshi, wata ajiyar zuciya ya sake ya finciko ta, da zafi zafiya ya fara aika mata saqonnin shi cikin huce haushi, marka tun ana na dadi tana kukan dadi, sai da ta fara kukan wuya, roqon shi ta ke Allah Anna bi ya kyale ta amma inaaa yai nisa, sai da ta gwammace ba tau wa Salma mugunta ba ranar, fadi yake yana" duk sai kunci uban ku, zan maganin kowa a cikin ku, ki min shiru abin da kk so nake baki ko na farfasa maki baki" ya kaiwa bakin ta duka, dip tai bata qara kokawa ba sai kukan zuci, da sassafe ya shirya ya daukar wa Salma kayan ta suka wuce cikin garin Abuja, Marka kamar ta mutu dan haushi, ita da ta so a barta ta zauna da su amma shine aka tafi da ita, kai wannan abin haushi da yawa yake.
Sun isa Cikin garin Abuja da rana wajen 12pm, gidan Alhjn shi ya kaita, sun qara yin tafiya, amma wannan karon dakin shi na gidan nan ya kaita, ya aje ta , yai ficewar shi, miqewa tai fuska ta kumbura sintim da kyar take gani, ta jingina da ginj ta rungume guiwowin ta tana kuka mai bam tausayi, nadamar zuwan ta ABUJA kam ta yi ta ba iyaka, wato in baka iya kama barawo ba ya kama ka, wannan shine ya faru tsakanin ta da su Marka.
Jabeer ne yai sallama ya shigo fuskar shi cike da fara'a kamar wanda yai tsintuwar dimond...........[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ๐
๐ผ 'YAN ABUJA ๐
๐ผ
BY HAERMEEBRAERH
Hey guys thank you so very much for everything. Na ji dadi sosai da kulawa da nuna damuwar ku, na ji sauqi sosai. ๐๐ป Alhamdu lilLAAH. Love u da yawaโค
Page 16:
Shiga yai hannun shi buyu boye a bayan shi, ita kuma ta sowa tai da niyyar mishi sannu da zuwa yanda suka saba, sai taga ya maqale a jikin gini yana mata dariya, daga girar ta daya tai tare da lumshe cikin wani salon daukar hankali" me kk boyewa baka son na ganiiii" " matso kusa ki gani to" matsawa tai, kusa da shi sosai, in ta matsa yace ta qara, haka har saida jikin ta ya zama gaba daya a nashi, sannan ya fidda hanneyen shi ta bayan ta, ya rungume, yai kissing din ta sosai, sannan ya kama ta suka zauna, miqa mata leda yai ya tallabe fuskar shi yana kallon ta da murmushi, bude ledar tai itama tana murmushi tana kallon shi tana kuma kallon ledar, tana budewa taga wayar da zatai dubu sha biyar, bude baki tai cikin murna da tsalle, ta dane shi tana mai kisses ko ta ina, kama ta yai ya riqe kafadun ta, " My princess ki nutsu kina girgiza mana bby, so kk kuji ciwo?" " Kaiiii amma mine na gode, na gode , na gode, Allah ya saka maka da alkairi, Allah ya sama dukiyar ka albarka da rayuwar ka gaba daya, Allah ya jiqan iyayen ka ya sa su cika da imani" " Shhhhhhh wai wannan godiya haka kamar na sai maki mota?" " hmmmm kai ka ga bai kai ai.wannan godiyar ba, kai ma kasan ina da son waya, a matsayina na wacce ba ta taba riqewa ba yau na samu ai sai godiya ko, beside macen kwarai dole ne ko tsinke mijin ta ya kawo ya bata ta nuna mai godiya da murnar ta, in ba haka ba taiwa kanta baqin ciki dan gaba ba zai ci qwarin guiwar kawo wa ba" " wannan haka yake macen kwarai, mace daga cikin matan aljanna, Juwairah in dai ta dalilin miji ake shiga aljanna na maki alqawarin na yarje maki" wani irin hawaye mai dumi ne ya ke bin fuskar ta na tsantsanr farin ciki da nishadi, ga wani son shi da ke ratsa shi, " Yah Jabeer, na gode sosai Allah ya bar mu tare , mu je aljannar tare, domin kaima ka shiga cikin alqawarin Allah duk mai kyautata wa iyalin shi zai shiga aljanna, kana daya daga cikin mazan da suke koyi da halayen Annabin rahama da sahabbai" haka sukai tai ma junan su dadadan kalamai, ( abinda aka rasa a wannan zamani kenan, saurayi zai tai ma budurwar shi daddadan zance kan aure, amma da anyi kwanaki ya daina kenan, itama haka, sai a dawo kowa na dana sanin auren dan uwan shi, auren duk da muke ganin yana dadewa wallahi ba sa dai na neman junan su kamar ranar suka fara haduwa, kowa a kullum yana son ya fidda sabon salon da zai faran ta ran dan uwan shi ne, dan haka mu ci gaba da nemawa juna farin ciki sai auren mu yai qarko).
Bayan an kwana biyu Suwaiba da Saudat sun fara sabawa da wannan mummunan labarin da suka juyo wa kansu, Saudat ta fara neman dalilin da zai sa ta san me ne ne silar rashin haihuwar su, watarana Alhj Kalla zasu tafi meeting gidan Oga Zaks , domin a wannan yana yin da ake ciki ta fuskanci ko su su waye, sai dai ta qi gayawa Suwaiba dan ita akwai wauta, da ta sani zata fasa kowa ya san sun sani, ta ko jawo masu masifa, sai da ta gama jin komai wani member suka samu da zai shiga qungiyar tasu amma bai san location ba, take Alhj Kalla ya fara bashi address, Saudat na kwafewa, tana gamawa zata tura riga Alhj Kalla ya fito, gaban ta ya fadi amma ta dake, ta ci gaba kamar tana gyaran rigat ne," Ohhh mata kenan, daga kwalliya sai saka kayan ado, sai gyare2 kawai kar dai aga munin ku" dariya sukai gaba dayan su," ina ta kiran ki ina palo banji kin amsa ba" take ta gane wayo yake son mata," ai ban jiba Alhj na, ni da nake nan kana can,wataqila ma da ka daga murya dana jiyo ka, tinda kai ba zakai amfani da waya kana kirana ba , sai kai ta kira in ban ji ba kace nai laifi" murmushi yai a ranshi ya tabbatar bata ji komai ba, "k shikenan je ku dakkon ruwa na sha anjima kadan zan fita" tashi tai tana kada jiki tana yauqi tana isa kitchen ta qarasa da hanzari ta ciro takardar ta wulla a bayan fridge din dan ya fi kusa, motsin shi ta ji ya biyo ta, budewa tai kan ya qaraso ta dakko ruwan da cup, yana isowa tace" hmmmm Alhj na kana sona da yawa na kula 'yan kwanakin nan kamar ka maidani rigar sawa ko ina zaka sai dani" murmushi yai yace" ai ke kk koma haka shiyasa na koma hakan" ya karbi cup din ya hade da hannun ta, ya matse saida tai qara, ya zaro mata idon shi jajaye yace" ki kiyayi bincike domin yana kai maiyin shi ga halaka" " Bannnn......ban ganee...baaa" " dalla malama rufen baki, ji kk ban san kina bin waya ta ba? Ko in da na fita, ki gani? Ina nake zuwa me nake yi? Me kk son sani yau na sanar dake? Dan ba tsoron ku muke ji ba? Auren kwadayi auren kudi kukai, kuma kuna samu, to meye na sai kun ji kwakwaf?" Jikin Saudat sai rawa yake wani ruwa2 taji na tsattsafo mata ta qafart ta batai aune ba taji ya kwada mata bari" Dan uban ki fitsari kikai a tsaye? Ji yanda kk batan takalmi ni da zan fita? Me kk sani game da mu?" " Alhj ban san komai ba, sai dai zargi da nake" aje cup din yai ya zaunar da ita a kujerar dinning dake kitchen din " ehen ina jin ki zargin me kk?" " dama ina zarkin ko ku yan damfara ne, kai da Alhj Salihu" " kin tabbata zargin da kk kenan?" "Allah shine" " to bari kiji, zargin ki ya tabbata, amma idan na ji wannan maganar ko a wajen waccan doluwar yayar taki da ba abinda ta sani sai barin zance, da soj kudi, kin mutu, kinji ko baki ji ba" cikin tsawa ya qarasa zancen," Nnnnaaajii..."" Good,ni na fita, miqon takardar da kk boye kan na karya ki" tashi tai ta dakko ta miqa mai, ficewa yai ya barta ta durqushe tana ta kuka, lallai yau data gaya mai abin da ta gano game da shi da fa shikenan kashe ta zasui, yanzu ta gudu ma nan ma har gidan su zashi wataqila ma ta jawa uwar su a hada da ita a kashe, ta zauna tai shiru sui ta cin kudin haram kudin jini, "kaiiiiii wannan Abuja ba tai ba, inaaaa" ni dana sani a Damaturu nai aure na ma" ta fada tana share majina.
Salma ido ya kumbure dga zaunen tai baccin wuya ba shi ya dawo ba sai wajen la'asar, riqe da koko da qosai dan yamman nan da ake yi, sai wata leda mai kaya a ciki kala uku da takalmi kala biyu sai jaka daya, da yan kayan kwalliya da ba a rasa ba, miqa mata yai, ta tashi ta isa ta karba, leqawa tai ta yamutsa fuska, " baki daku ba kenan ko, gar da zan baki abun da ban sai wa Marka a shekara goma ba, ke kin samu ma kk kyabe baki ko" a tsorace tace" na gode" ta tashi ta shiga dan bandakin dake maqale a dakin tai wanka ta canja kayan ta fito, koko da qosan ta dauka ta ci ta sha, sannan ta koma ta zauna, " kin iya cewa wani yai sallah amma ke bata dame ki ba, ji kk ban gane ki ba, wa'azi a baki amma ke baki aiki da shi munafuka, irin kune kuna da yara kuna sa su sallah su qi, to basu ga kuna yi ba" miqewa tai zalo zalo taje tai alwala tai sallar ta koma ta zauna," zuwa gobe ogana zai dawo shi kadai yake zama anan, matan shi suna maiduguri, aiki ke kawo shi nan, dan haka in ya dawo da yamma ki shirya muje mu gaida shi, in muka dawo na gan ki a waje ko kusa da wajen dakinnan kin mutu ranar, dan na san ki idon ki idon kudi, kice zaki maqale ma bawan Allahn da bai san neman mata ba, na kula akan kudi komai yi zaki, tinda an iya bin qattin qauye masu bada dari da hamsin" hawaye take sosai sunqi tsayawa, haushin ta bai wuce yanda yama qi ya saurare ta ba sam, ya tsaya ta mai baya ni yaqi, kawai sai ta maida kanta ta kwanta, bata qara furta komai ba har ya shirya ya fice, kuka take mai ban tausayi" Oh ni Salma na saiwa kaina wahala daga yar shawarma da motar dana gani duk na rude ga inda na kawo kaina, Abuja ko wahala?"
Da kyar Marka ta miqe ta je ta hada wuta ta shiga ruwan dumi ta gasa jikin ta, komawa tai ta ci gaba da kwanciya, wani qaramin yaro ne shafi'u daya daga cikin yaran da Talle ke auri saki ya shigo zai kai shekara goma, baya jurar yunwa shi, dan ko da su Huwaila na baccin gajiyar iskancin su da suka sheqewa da dare, ita Marka takan tashi tai abin kari da wuri, to yau sunji shiru kowa dif a gidan, tura kai yai ta ware qafafu tana ta firfita da mafici," Marka yunwa muke ji" da sauri ta sake zanin ta juyo kan shi," me kace?" " cewa nai yunwa muke ji" habaaa ina wuta na saka wannan yaron, inji Marka, kiran shi tai tace zo ka karba, yana isa data damqe shi ta hau duka, tana" sai na fashe dukana akan ka, dan uban ka, banda wannan ta'annutin da uban ka ya min, har abinci kk tambaya? Ga shi tinda ya dauke waccan jaja amaren sai da na gan shi kuma, to ko xaka ci abinci har ka qoshi, amma na duka" dim dim dim kk ji" Marka lfy me ya miki haka" cewar Haule kenan, tana qoqarin kar bar shi, wani mari itana ta karba, kai na taqaice maku duk wanda ya shiga sai ta saki wani ta kama wani haka tai tayi kamar mahaukaciya, sai da ta gaji jikin ta yau laushi sannan ta kwanta tana kuka, ita ta shiga uku, ta hada sharri kuma ya zame mata tsiya......
[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: ๐
๐ผ ' YAN ABUJA ๐
๐ผ
BY HAERMEEBRAERH
Masoya novel din 'YAN ABUJA dan Allah ku min hakurin jina da bakuyi akai2 yanda na saba, inshaa Allahu in komai yai normal zan ci gaba ba da tsaya ba har sai na gama dika. Na gode. Love u allโค
Page 17:
" wa'alaikumussalam shigo shigo yar uwa kiga me yayana ya saimin" Juwairah ke fadin hakan cikin murna da kuma zumudi, Nafeesah ce ta qara sa shiga itama cike da dokin ganin me za a nuna mata, sanda ta gani itama yar qarar murna tai ta haye kujerar da Juwairah take" kaiiiii amma Allah ya saka ma Yah Jabeer da alkairi, ya sai mana waya mun daina leqen ta qawaye" " to malama ba wai an sai mana waya ba na dinga neman ta ina rasawa" " hhhhhh Allah baki hakuri ai wannan wayar inna dauke ta yanda kk san jariri sai kin nema na miqo maki, ko in tana buqatar a sa mata kudi" dariya suke sosai, " yauwa wai ni ruwan meye wancan a butar qarfe na ga kin saka a garwashi?" " Oh ban cire ba dama je ki sauken dan Allah ki dawo na fada maki hajiya tambaya" " ah to dan kin san in baki fadan ba baki da zaman lfy yau" fita tai ta sauke mata butar ta dora ruwan wankan ta , ta koma dakin, xama tai tare da tanqwashe qafa agaban Juwairah tace " To malama a bamu darasi, dan zama dake akwai diban ilimi" " ke ko, ke ko, hmmm kina raina sanin da Allah ya baki ne amma kin fini ilimi ai, kefa duba ki gani yanzu ci gaba da karatun ki kike ni fa ina zaune a gida kullum" " kema zaki ci gaba ne komai lokaci ne sis oya ina jin ki meye wancan a butar qarfe?" Dariya Juwairah tai sosai sannan tace" ke dai ba ki mantuwa to magani ne, maganin infection musamman na masu ciki, Mama Bilki naga ta yi lokacin cikin Ammar shine nayi, Oh har naji ina son ganin yaron nan wallah" " to naji magani ne amma ai baki fadan ya ake hada shi ba ko" haka ne, kinga dai da fari zaki samu ganyen garahuni, da 'ya'yan hulba ki tafasa su sosai sai ki bari ya sha iska sai kina tsarki da shi, da yawan masu ciki suna fama da infection sosai, mai fidda ruwa kala2, amma da zasuna amfani da wannan zai masu magani duk da ba wai yana dauke shi dika bane kwata2 amma yana ragewa sosai, in aka hada da wasu magungunan na sanyin" " yauwa ko ke fa ba ga shi kin qara min ilimi ba ni ina ma san wannan abun,in ba yanzu ba, yauwa rannan naji kina fadama shamsiyya wani abu lokacin na fita ban ji me kuke cewa ba