Showing 1 words to 3000 words out of 59470 words

Chapter 1 - UWA KO UKUBA MShakur HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

28 Mar 2025

3073

[03/01, 07:38] +234 806 292 7511: 💫 UWA KO UKUBA?💫

✍💫M SHAKUR

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJIN KAI!

EPISODE 1️⃣💫
Office dinshi da aka rubuta Dr Musty ajikin kofan yabude yashiga daidai wayanshi na ringing ta hanyar
flashlight dake motsi yana kunna kanshi da kashewa dan wayan na silent, wucewa gaban desk nashi yayi
inda wayan take a kwance yakalli wayan hannunshi yasa dasauri yadauki wayan ganin Mamie ajiki yakai
wayan kunnenshi, cikin muryanshi dake nuna natsuwa da girmamawa anatse yace “Mamie” daga tachan
bangaren muryan wata yar dattijuwan mace kamilalla mai tarin natsuwa tace “Assalamu Alaykum
Mustapa kaga Hamadi ke zazzabi jikinshi zafi kaman wuta kuma yaki tashi mutaho asibitin ku, yaki
gayamin meke damunshi, banmasan baida lafiya ba wlh kaji jikin kuwa” anatse Mustapa yazaga yazauna
kan kujeran wajen cus maganan Mamie captures attention nashi sosai batare daya nuna damuwa ba
yace “zai iya magana”? Mamie da hankalinta yatashi tace “koni bayama maganan balle yamaka, koda
yake zai iya maka” anatse Dr yace “Hameed fa?” Mami tace “yatafi wajen aikinshi tun kafin 8 kuma bai
gayamin Hamadi bayida lafiya ba shima na tabbata bai sani ba” dan ijiyan zuciya yasauke anatse yace
“ganinan zuwa, kisa towel a ruwa ki goggogemai jiki, don’t worry Mamie he will be fine” anatse Mamie
ta sauke ijiyan zuciya dayaji daga wayan tace “toh Allah yasa saikazo” ta katse wayan.

Ijiye wayan yayi yamike tsaye yadauki key motanshi da wayanshi magidanci ne dan he looks like
43/42yrs old guy din nan, phamarcy hospital dinsu ya shiga da kanshi ya debi magungunan da drip da
allurai ya ijiye komi gaban accountant nasu yabiya da kati aka samai a leda yafito yashiga wata mota mai
kyau fara benz yaja motan zuwa gidansu.
Babban gida ne anan jan bulo but tsohon gida irin gidan masu kudin da din nan, babban gidane sosai ga
maroon gate ajiki, horn yayi wani dan matashin mai gadi daya fara washe baki ya budemai kofa shiga
cikin gidan yayi, babban dankareren flat ne babban gaske guda daya a compound din, ta gefe kuma
kaman lambu ga bishiyoyin guava mangwaro da cashew gakuma flowers, akwai fili sosai da space a

compound din, sauka yayi daga motan yafito yanabin ko’ina da kallo, motoci biyune parke wajen parking
din sai wata machine fara lipan irin wayyo kudina din nan kal kal dashi, wucewa yayi flat din tun kafin
yabude kofa kamshin turare kemai sallama, ahankali yabude falon babu kowa a falo sai Lami dake goge
goge dasauri tace “Ina kwana Baban Akram” “lafiya lau” ya amsata, falon nada kyau ga carpet zagaye
ko’ina da katuwar tv a bango, falon nada fadi gawani katon picture frame da wata dattijuwan mace da
namiji dattijo shima ke zaune suna sanye da manyan kaya sai yara maza biyar tsaye abayansu dukansu
fuskansu ya nuna banda mutum daya daya juya kaman zai gudu ne sai Mahaifiyar takama hannunshi
tarike ahaka akai hoton sai hoton bayanshi babu na fuskanshi. Staircase yawuce yayi sama direct wani
daki dashine first room anan saman yayi.

Hannu yasa yabude kofan dakin, dakin nada girma shima ko’ina a gyare tsaf, gadaje biyu ne adakin
dsame size kowanne tareda desk da chair a gefe, ga wata yar dattijuwa da zatakai maybe 57yrs haka
zaune bakin gadon kusa dawani dogon matashi fari sol dake kwance akan gadon da akalla zaiyi 33yrs ko
34yrs yana sanye dawani black joggers ba riga ajikinshi sai singlet fari kal, yanada very huge chest da
muscles masu girma, idanunshi a rufe ruf Mamie ta daura karamin towel asaman goshinsa, yanada
dogon hanci ga lips very pinkish and so meaty, ga gashi akanshi sosai sunyi coils sun nannade kaman
bature, dukansu basuji motsin Ya Mustapa ba saida yakaraso wajen gadon Mamie tajuyo dasauri
takalleshi tace “Doctor ka iso” anatse yazo gaban gadon yasa hannunshi yadauki towel din daga goshinsa
sannan ya karbi na hannun Mamie yaduka gaban gadon ahankali yana kallon matashin yace “Hamad!
Hamadi!” Kadan kadan matashin yake bude idanunshi kafin yabude idanunshi duka da suka kankance
sukai ja sabida rashin lafiya Ya Allah wasu irin wild black eyes yakeda shi da black eyelid ka kalleshi zaka
rantse kasake rantsewa yasaka kwalli kuma baitaba sa kwalli ba haka Mamie ta haifeshi da idanu ahaka,
anatse Mustapha dake kallonshi yace “meke damunka”? Shiru yayi kaman ba shi akema magana ba,
shima Dr ya tsaya yana nazarinsa kafin ya yajuyo yakalli Mamie yace “Mamie yaci abinci?” Girgiza kai
Mamie tayi tace “banjin ko abincin dare yaci ba, Hameed yahada ya cinye I’m sure” ahankali yace
“kawomin breakfast dinshi Mamie he needs to eat” tashi Mami tayi tace “toh Allah gamu gareka bari
naje nakawo” Mamie tai maganan tana tashi ta wuce kofa tafita tarufo musu, juyodakai Dr yayi
yakalleshi tareda zama abakin gadon babu alamun wasa kan fuskanshi strictly yace “meke maka ciwo”?
Dan kallon yayanshi yayi saikuma gently yanunamai wajen maranshi da hannunshi tareda dan lumshe
idanu yadan fuzar da iska kadan, ahankali Dr yakai hannayenshi yadaga singlet nashi sama six packs
dinshi suka bayyana hannu yakai yadanja wandonshi kasa kadan white CK boxer nashi ya bayyana fari kal,
hannunshi Dr yasa yasauke boxer kasa kadan dasauri yace “yaushe wajen da akamaka aiki yafara rash
din nan? Why didn’t you tell me?” Daidai lokacin aka bude kofan tareda shigowa dawani sauri yaja
labcoat din yayanshi yarufe maranshi da cikinshi da bala’in sauri, chak itama Mamie ta tsaya cus taga
abinda suke, Dr ya kalleshi da yanda yarufe kanshi da labcoat dinshi kawai sai yajuyo yakalli Mamie
ahankali yace “Mamie” dasauri Mamie tace “ai bansan abu kukeyi ba, bari naje inkun gama ku kirani”
tajuya tafita da tray abincin tareda rufo musu kofa, Dr Mustapa yajuyo yakalleshi yace “you have
infection awajen i will dress it now sainaje nataho maka da antibiotics probably abinda ya sakinma
zazzabi kenan” yayi maganan yana karban labcoat dinsa daga hannunshi ya tashi yace “bari na dauko
dressing kit” tashi yayi zai wuce, dudda zazzabi na cinsa amman saida yakai hannu ya rike lab coat dinshi

hakan yasa Dr yakalleshi, dauke kanshi yayi cus baiso suyi having eye contact ahankali murya ciki ciki
dakeda bala’in dadi da zaki gata yar kankanuwa yace “don’t tell Mamie Yaya” tsayawa Mustapa yayi
yana kallonshi sai kawai ya girgiza kai ya karbe riganshi yawuce yafita daga dakin yafito yashiga sauka
kasa Mamie dake zaune afalo tana ganinshi tamike da sauri tace “meya sameshi Doctor? Gabana sai
faduwa yake wlh, kuma yaki fadamin abinda ke damunshi, nasan kai kadai zai iya gayamawa, halin
Hamadi sai shi” dan murmushi kadan Ya Mustapa yayi yace “kinsan Hamadi da kunya, but nothing to
worry, is just wajen da akamai aiki ne yasami infection is minor matsala, he’s probably shy to tell you
maybe bayaso ki attempting dubawa ne, ina zuwa Mamie bari na dauko abubuwan dressing daga mota”
yawuce yafita Mamie tabishi da kallo sai kawai ta girgiza kai, yanzu abinda kema yaron nan ciwo kenan
yaki fadamata? Lallai lamarin Hamadi sai addu’a.
Bai wani jima ba yashigo dawani hospital bag yayi sama yashiga dakin, yana kwance yanda ya barshi but
yasake sauke singlet ya maida komi na jikinshi daidai, jakan ya ijiye yabude yazare handglove yasake
sannan yadauko auduga yataso yasake daga rigan this time ya sauke boxer nashi kasa sosai sabida ya
gyara wajen har fine smooth wall nashi na showing dakeda wani scanty black hair haka, yadaura
audugan yafara sharewa, gently yasauke ijiyan zuciya yanadan yatsine fuska yana motsi da kafa, Dr yace
“sorry it’s painful I have to clean it yazama ciwo” ya sauke ijiyan zuciya yana cleaning wajen hakan yasa
yadan fuzar da iska hawaye na azaba suka gangaro daga idanunshi dasuke arufe, kallonshi Dr yayi
saiyadan dakata yace “dazafi sosai”? Batare daya bude idanunshi ba murya kasa kasa wacce ke fita da
kyar yace “no” murmushi Doc kawai yayi yacigaba da gogewa hannayenshi rawa suka shigayi baimasan
ya akayi ba kama hannun yayanshi yayi yarike cikinshi na motsi dasauri dasauri na numfashin jin zafi
yadan yunkuro da kanshi, Dr yasake kallonshi hawaye fita suke daga idanunshi, murya chan kasa yace
“nakira Mamie tarikeka maybe you will feel stronger, nakirata?” Girgiza mai kai yayi alamun a’a yana
sakin hannunshi, cigaba sukayi kusan 10mins sannan yagama yamai dressing wajen, yamai fixing drip
yahada allura yamai, yace “kadena bari ruwa natabashi or any soap and also kadena sa wando kana rufe
wajen” gyadamai kai yayi da kyar Dr yace “bari na karbo maka abinci kaci saina baka magani” yawuce
yafita chan yashigo tareda tray na abinci tea akamai dayasha kayan kamshi sai chips da egg sai kuma
tuwon shinkafa da miyan taushe ijiye tray yayi gently yadagoshi yasamai filo abaya ya zauna bakin gadon
kusada shi yadauki tray ya ijiye kan cinyanshi yamikamai tea yace “gashi sha” dan yatsine fuska yayi
hakan yasa Dr yace “I will not say it again” gently yamika hannu ya karba yakai bakinshi ya kurbi kadan
Dr yasa fork yadebi chips yakai bakinshi ahankali yabude bakinshi yakarba daidai Mamie tashigo danta
kasa daurewa tace “ai nasan idan kaine Doctor bazai maka gardama ba niko nayi kadan saiyamin
gardama zaici, bantaba ganin makiyin abinci irin Hamadi ba” daidai lokacin aka bude kofan wata
tsohuwa da zatakai 80 tashigo dakin tace “yanzu da Lami bata gayamin Hamadi ba lafiya ba da bazaki
sanar dani ba eh Batulaa wlh kinci amanata, kai Mijina meya sameka?” Tayi maganan tana karasowa
gaban gadon kaman zatai kuka takai hannu zata tabashi da sauri ya matsa baya shifa Mamie kadai yake
yarda ta tabashi, Dr yayi dan murmushi yace “Gwaggo baiso atabashi sanyi yakeji” zama Gwaggo tayi
akasan wajen tana kallon Hamadi kawai tafashe da kuka tace “ohh ni, Hamadi tausayi kake bani yaro sai
laulayi kaman mace mai danyen ciki, yau kwana bakwai dududu da yimai aiki amman jibe harya fara
wani cutan, nace ku banni naje kauye na hadomai y’ayan itatu amman kun maidani yar iska barinma kai
likita” dan dariya Dr yayi yace “nikuma Gwaggo ke dai da Abba” wankamai harara Gwaggo tayi tace “wlh
kai, kaike munafunci ka turence ubanku ahanani, kaine ke karantamai karatun magungunan hausa basu

da kyau, kalli Hamadi kullum ciwo idan yau baya mura gobe ciwon kai, jibi malaria, gata wuya, yaro gashi
bayacin abinci, banda Allah dake hurasa ai ina ganin da tsumagiya yafi Hamadi kiba, dayake shi girman
jiki na Allah ne saisa yake gabjeje, yanzu da wanne zanji? Narasa mijina, kaida karagemin kaima so kake
narasaka eh Hamadi na” tafashe dawani sabon kukan tana kallonsa sosai, da idanu Mustapa yamai
magana hakan yasa Hamadi yadan kalli Gwaggo for the first time yayi magana murya chan kasa yace
“Gwaggo” muryanshi is so husky and sweet and so dominating and captivating, gashi very calming
dasauri Gwaggo takalleshi tana kwalalo idanu dasuka jike da hawaye, sake kallon Dr Hamadi yayi kaman
mai karanta sako kan fuskansa, saikuma ya kalleta kasa kasa yace “ni lafiya na kalau” murya ciki ciki yace
“banson kuka” murmushi Gwaggo tayi tana washe baki tace “oh jibeshi ko maganan bai iyaba sai
Mustapha ya koyama,i ohh Allah kadubi jikan nan nawa shi kadaine matsala a aduniya wlh tallahi
kabashi lafiya kasamai son abinci, da magana, kaga kullum cin zalunsa yan uwansa suke amman Hamadi
ba uhm ba uhn uhm, kodan haka kabasa lpy, Allah baka lafiya kaji” Mamie tace “Ameen” lumshe idanu
yayi yana kauda kai daga cips din da Mustapa ke bashi Gwaggo tace “barshi hakanan Likita wlh nadade
rabon danaga yaci abinci haka ma ni, hakan ma mungode Allah” tashi Dr yayi yace “Gwaggo muje namai
allura bacci zaiyi yanzu” dasauri Gwaggo tace “a’a zan zauna dashi kudai kuje” kaman zaiyi kuka Hamadi
yace “Gwaggo kije” Mamie tace “Gwaggo kinsan shi idan muna nan bazaiyi baccin nan ba” Gwaggo tace
“hakane bari ina nan gaban daki kome kakeso ka kwalamin kira kaji” gyadamata kai yayi suka wuce Dr
yakalleshi yace “I will come anjima do you want anything?” Girgixamai kai yayi alamun a’a yana gyara
kwanciya Dr yajuya yafita shima.

Yana fitowa daga dakin yaga Gwaggo agaban dakin zaune ta ware kafafu tana bude idanu da kyar tana
kallon yar Nokia phone dinta, jin an bude kofa da sauri ta dago kanta tace “yauwa likita kaga kiramin
Abubakar” cikeda lallabawa Dr yace “Gwaggo dan Allah basai kin kira Abba ba kada ki dagamai hankali
yana kasuwa” “Lamiiii” Gwaggo ta kwalama yar aikinsu kira cikeda fada tace “daman kadadeda nunamin
ban isa in aikeka ba ko nasaka abu kayiba nagode ma Allah Lami ta iya karatu tafi dan jakan uba” ya
kalleta sai kawai ya kadakai yawuce abinsa, Lami ta hauro sama Gwaggo tabata wayan danta kiramata
Abba.

Bayan kusan 1️⃣hr Mamie na tsaye kitchen tana gwadama masu girkinsu guda biyu abinda za’ayi taji
sallaman Abba dasauri tafito daga kitchen din amman haryahau kan staircase yana gyara babban rigan
jikinshi ya manyanta dan akalla zaikai 65yrs, irin dattawan arzikin nan ne yana sanye da hula mai kyau,
tajuya tace “ku cigaba ina zuwa” tafito tayi sama daidai Abba da Gwaggo sun shiga dakin Abba yayi
wajen gadon dasauri yana kallon Hamadi dake bacci peacefully mai nauyi hannunshi daya saman cikinshi
cikin whispering da anaji Gwaggo tace “Mustapa yamai allurai yabashi magani yasamai ruwan asibitin
nan shine yasami bacci” daidai lokacin Mamie tashigo dakin, dukawa Abba yayi yakai hannunshi ahankali
yadaura saman kan Hamadi yadan sauke ijiyan zuciya saikuma yadago yace “muje Gwaggo” Mamie
itama ta juya suka wuce falon sama Abba yace “mesa babu wanda ya sanar dani Hamad baida lafiya”
Gwaggo tace “nima awajen Lami naji bata sanar dani ba” anatse Mamie tace “koni ban sani ba wlh,
nashiga dakin naga baida lafiya and Hameed bai gayamin ba shima maybe bai sani ba kasan halin Hamad

da boye abu” dan shiru Abba yayi yace “Mustapa yabashi magani?” Gyadamai kai Mamie tayi tace “eh
yaci abinci kuma Alhamdulillah” dan ijiyan zuciya Abba yayi yace “okay bari nakoma za’a kawo fruits
anjima” yakalli Gwaggo yace “Gwaggo bari nakoma aiki kema kije ki kwanta kihuta” dasauri tace “ina
naga hutu jikana baida lafiya kaje ina nan harya tashi, idan dawani abu zan kiraka tunda naga kaima
bakada mai kiranka” Abba yawuce Mamie tabishi har wajen kofa murya chan kasa yace “me Al Mustapa
yace? Meke damunsa”? Ahankali Mami tace “wajen aikin da akamai ne yasami infection but kasan
Hamadi bazai taba nunamin ba, but Doctor yayi dressing yamai allura yatafi karka damu abinda yasamai
zazzabi kenan zai karamai dressing anjima” gyadamata kai Abba yayi yace “bari nakoma” yawuce yatafi
har zuwa motanshi yabude baya yashiga wani dreba yajashi dan yanzu baya iya tuki da kanshi.

Bai wani dade da shigowa hospital ba he’s changing dan yanada operation wayanshi yashiga ringing
kallon wayan yayi ganin Abdallah yasa yakai hannu yadauki wayan daga ta dayan bangaren wata
nutsassiyan murya yace “meya sami Hamadi Ya Musty?” Zare wayan yayi yasa a speaker ya ijiye kan
table yana chanza riga yace “waya gayama”? Da dan damuwa kan muryanshi yace “Gwaggo just called
me tafadamin” dan murmushi Dr yayi yace “don’t mind Gwaggo, is not serious abu, yama koma bacci
nikuma I’m back at work, nasan yanzun nan Faisal ma zai kirani Hameed ma haka zan shiga theatre
kasanar dasu he’s fine and concentrate a aiki okay” dan ijiyan zuciya yasauke yace “okay” good ya katse
wayan yasa wayan a DND yafito yarufe office nashi yawuce theatre.
[03/01, 07:38] +234 806 292 7511: 💫UWA KO UKUBA?💫

✍💫M SHAKUR

EPISODE 2️⃣💫
Wuraren 3 yashiga bude idanunshi asanyaye, alluran ko magungunan ne da Ya Mustapa ya bashi really
made him sleep, gently yatashi zaune yazare drip daga hannunshi daya kare, yadan shafa fuskanshi
sannan yasauke fararen tsaftatattun kafafunshi akasa yamike tsaye ahankali, he’s tall kusan yamafi Ya
Mustapa Dr tsayi kawai manyanta shi Dr zai nunamai dakuma shekaru da teba haka dan shi baida teba
kuma baida rama, wani irin full fitted body gareshi, bayinsu yashiga brush yasakeyi cus bayajin dadin
bakinshi at all, fitowa yayi ya chanza singlet na jikinshi yasaka wani yadauki wani black t-shirt yana
kokarin sawa aka shigo dakin dasauri yakalli kofa Mamie ce hakan yasa yayi sauri yakarasa saka rigan
yadan kalli Mami data tsaya saikuma ya sauke kanshi kasa murya chan kasa yace “Mamie” tahowa cikin

dakin Mami tayi zuwa inda yake ta tsaya dab dashi hannunta tadaga ahankali takai fuskanshi ta shafa
gefen kuncinshi tace “yajikin? Meke maka ciwo yanzu eh?” Murya chan kasa yace “bakomi” shiru Mamie
tayi tana kallonshi sannan tace “salla zakayi bari na shimfida maka dadduma karka fita zuwa masallaci”
Mamie tasa hannu tadauki dadduman su dake kan stool ta shimfidamai tace “zoto kayi” tahowa yayi
yahau kan dadduman ya kabbarta salla itakuma Mamie ta zauna nan bakin gadon Hameed dan shine
close to dadduman tana kallonsa, from the way yake salla ahankali kasan wajen namai ciwo har yanzu,
idar da salla yayi yasake juyowa ya kalli Mamie sai kawai ya kwanto gently yadaura kanshi kan cinyan
Mamie yayi shiruuuu, shafamai kai tayi tace “mezan dafamaka? Akwai waina da miya zakaci?” Girgiza
mata kai yayi alamun no, murya chan kasa tace “tell me mezakaci” daidai lokacin aka bude kofan dakin
Gwaggo ne tashigo tareda wani matashi dake kama sosai da Hamad exactly shima fari ne saidai baida
idanu kaman na Hamad yana sanye da suit yana kallon Hamad da dan damuwa kan idanunshi, yana
ganinsu ya yunkura zai tashi Mamie ta hanashi Gwaggo tace “kaganshi babu wanda yakeso agidan nan
sai uwarsa, yafara mata kuskuskus kaman munafuki uwa shi kadai ta haifa” dauke kai yayi Mamie tayi
murmushi Hameed ya wuce Gwaggo dake tsaye nan koda yashigo cikin dakin zuwa gaban Hamad ya
duka tareda dafa kafadanshi, cikeda damuwa yace “wat happened to you Hamadi? Mesa baka fadamin
bakada lafiya ba? Meke maka ciwo?” Dauke kai Hamad yayi, murya chan kasa yace “I am fine” kallon
Mamie Hameed yayi da idanu Mamie ta girgizamai kai hakan yasa bai kara tambayanshi meke damunshi
ba yace “are you hungry? Tashi muje muci abinci a waje” ahankali ya yunkuro zaiyi magana Gwaggo tace
“wannan ne zai bika wani waje baki kawai kake batawa Hameed ai wlh saidai idan Mamarshi tasa baki
shine zai bika, ka manta ranan daka kaisa wani faty haka yaron nan yaşa kafa ahanya yadawo gida”
ahankali Mamie tace “Hameed barshi karku fita cus he can’t even walk properly bari zansa abinci
nakawo muku maybe idan zakuci tare zaidan ci” Mami ta yunkura zata tashi da sauri shima Hamad
yatashi, murmushi Hameed yayi shidai Hamad bayason Gwaggo tun suna yara, bawai ya tsaneta bane
kawai surutunta da ihu da maganganu ne bayaso, ganin yatashi yasa Mamie ta kalleshi tace “ina kuma
zaka”? Gwaggo tace “zai gudu mana ni Gwaggon shi dodo ina dakinsu” kin kallon Gwaggo yayi Mamie ita
kanta batason wannan dabi’an nashi na kin kakarsa, Hakan yasa tace “go back and seat! Can’t you see
she’s worried sick about you” Mamie tajuya tafita yawuce yazauna dab da Hameed duk Hameed na
kallonshi, baimaso ya zauna shi kadai kan gadonsa Gwaggo tazo ta zauna kusadashi, da ne abubuwan
Hamad ke damunshi but yanzu he’s so used to it wlh, yakalli Gwagggo dakebin Hamad da kallo duk sai
yaji ba dadi yace “Gwaggo ki zauna mana salon anjima kifara mana kuka da daddare kafafunki sun fara
zugi” zama tayi kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login