Showing 15001 words to 18000 words out of 46406 words
ɓangaren Abbu kuwa a cikin zuciyar sa yanajin son yayi bincike kamar yadda yafaɗa haka kawai kuma sai yaji yakasa ai watar da hakan,a ɓangaren Mamie ma haka abun yake tanajin abun a ranta sai dai bata iya furtashi a baki .......!★
Mommyn twins ce
Haka rayuwa yaci gaba da tafiya,
kamar yadda kuka sani yanzu rayuwar tafiya kawai take,dare babu wuyan yayi haka gari bawuyan ya waye,koda gudun da kwana da yini suke ya'ishi ɗan adam yayi wa kansa hisabi,
domin kuwa rayuwar mu tafiya kawai take yanzu...★
haka naka narika rainon cikin Mama tana iya bakin kokarin ta wajen kula da Ni da abun da ke cikina,
lokacin da cikin yakai wata bakwai da watan yakai karshe, tun daga lokacin nazamo abun tausayi bana iya yin bacci dazarar dare yayi to bacci yakaura ce min ina so nayi amma babu hali,dazaran na kwanta sai naji kamar na kwanta kan kaya duk inda na juya babu daɗi,
ban isa na kwanta ba sai dai na jingina da jikin garu kokuma na zauna sakankanin buhuhuna natokare gefe da gefe na,a haka zan samu naɗanyi gyangyaɗi,
cikin ga masifar nauyi da girma ni kaina yanzu ina ganin girman cikin da Mama take faɗa.
a haka har watan yakare,ina cikin wannan halin...
Cikin ikon Allah yau cikin yashiga wata 8 dai-dai.
kamar ko wani lokacin zuwa awo na idan yayi da sassafe Mama ke tashi na mutafi yauma hakan take,
kasan cewar natafi da wuri da wuri nafito daga asibitin,
da kyar nake ɗaga kafata nanufi gida,
ina tafiyar ina hutawa har na isa gidan.
azaune na iske Mama kan kujera ƴar tsuguno,tana ganina tamike taɗau taburma tashin fiɗa tana faɗin
"Zauna ki mike kafafun ki sannu kinji".
Kai na gyaɗa nazauna ina sauke numfashi,cikin tausaya wa ta dubi cikin ta cigaba da faɗin
"Kai wannan ciki naga alama shi yake janki Ni sai gani nake kamar ma cikin yafi karfin ki".
kallon cikin nayi tare da yin murmushi,
tamike ta kawo min abinci da kunun tsamiya tace
"Ci sai ki kwan ta ko zaki samu ki ɗan yi bacci".
nace To...
Ina gama ci Mama tamike tace
bari ta kawo min pillow na mike a nan dan yafi iska, nace to.
tana shiga ɗaki aka fara kwaɗa sallama da karfi-karfi murya naɗaga na'am sa sallamar da nake jin sa kamar ihu acikin kunnena.
mirgina wa nayi da kyar na mike nanufi kofar gida,
wani katon mutum na gane
a tsaye daf da kofar gidan, kallon mutumin nayi dan na gane shi ganina da shi na biyu kenan
gaishe sa nayi ya amsa fuska a turnuke sannan yace
"Fasuma tana ciki?".
nace "Eh".
fuska yadaɗa turnike wa ya turo tunbi gaba yace "Je kice mata Alhji Mamman ne yazo".
nace to. najuya nako ma ciki
Mama na sun kuye tana gyara min pillow da ta dauko min na karaso in da take tace
"Yau wa zo ki kwanta ko Allah zai sa ki Sami bacci ko bakiyi da daddaren ba zai zo da sauki".
nace "To, Mama wai Alhaji Mamman yazo".
cak ta sai da hannunta daga abun da take,ido naɗan tsura mata ganin yanayin da ta shiga daga faɗa mata wan da yazo ɗin, tana sunkuye kanta a kasa bata kuma aje pillow'n dake hannunta ba.
karo na uku kenan aduk san da Alhaji Mamman yazo ina lura da ita irin wannan yanayin take shiga,
"Ko me yasa?". nayi tambayar azuciya ta,a sanyaye ta ɗago ta nufi ɗaki can tafito da mayafi da kuma kuɗi a hannunta,
tanufi kofar gida.
Daga in da nake zaune inajuyo sautin Muryar Alhaji Mamman sai dai bana fahimtar abun da yake faɗa,
taɓa lokaci kafin tashigo,ido na bita da shi har takara so in da nake,
kan kujera ƴar tsuguno ta zauna jiki ba kwari,
tadube ni nima ita nake kallo kallo ɗaya zaka yi mata kasan cikin muguwar damuwa take,
"To wanene shi?".
nakuma yi tan bayar a zuciya ta, wan da bansan har ya fito ba sai da naji tace
"Hmm wan mai gida nane ubansu ɗaya".
da sauri na kuma duban ta taci gaba da faɗin
"Shi ne mai wannan gidan zaman haya dama muke aciki,
to bayan rasuwar sa sai nauyin yadawo kaina ni nake biyan kuɗin hayar to yanzu yana bina kuɗin shekara 2 ne da ban samu na biya ba shine yake ta sintirin karɓa,
ƴan kuɗaɗen da suke hannuna na kai masa kafin na samu wasu na kara masa yaki karɓa,
wai sai na haɗa masa duka na shekara biyun,
yanzu dai na basa hakuri yatafi,
to bari mu gani mu ɗan taɓa sana'ar na ɗan kwana biyu ko Allah zai za a samu ɗan wani abu sai a haɗa abashi".
tau sayin Mama ya kama ni kwarai nace
"Allah yasa a samu acikin satin nan ma sai a basa".
tace "Amin"...
Bayan sati biyu.
hakan yayi dai-dai da watannen cikina 8 da sati biyu, zaune nake a ɗaki bayan na idar da sallar azahar da sauri na yunkura na mike da kyar jin fitsari ya taho min lokaci guda kamar zai fito,da sauri na fita naje bayi nayi,nayi mamakin ɗan fitsarin da nayi bana kirkiba amma nake jin sa kamar zai fito kafin na isa bayin.
Na komo ɗaki ina zama bada jimawa ba nakuma jin irin fitsarin ɗazu, koda na koma bayin shima ba da yawa nayi ba,sai dai nayi irin haka har sau hudu,zuwa yanzu kam abun yafara damu na,yunkurin mikewa nake jin wani ya taho,amma nayi nayi na iya mike wan na kasa,
da kyar na tattaro ragowar karfi na na yunkura zan mike, ba shiri na koma zaune da sauri jin wani irin sarawar da bayana yayi da mugun karfi.
a take kuma marana shima ya amsa dayi min wani irin mummunar murɗa,
sulalewa kasan ɗakin nayi nashiga murkususu.
Cikin tsananin jin azaba da karfi na furta
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un!".
da sauri mama dake ai ki tsakar gida tashigo tun kan ta karaso take faɗin
"Yaya dai lafiya HAMDAH?".
cikin hanzari takaraso in da nake kwance ina juyi cikin azaba cikin tashin hankali tace
"Subhalallhi yaya dai HAMDAH".
kai nashiga juyawa cikin jin azaba da kyar na iya furta
"Wayyo Allah bayana marana wayyo Mama zan mutu".
a kiɗime ta
ɗa goni ta tallafo ni jikin ta tana faɗin
"Ikon Allah sannu ina ganin juyi ne dai dai lokacin haihuwa kam da saura sannu kinji"..
hannunta na kankame da karfi jin marana ya kuma murɗani sai naji fitsarin nan irin naɗa zu nan da nan jikina yakama rawa nadaɗa kankame Mama da karfi nabuɗe baki zanyi magana sai naji wani ɗumi yana bin kafata,
da mamaki Mama ke kallon kafata tace
"Ikon Allah ga alamar haihuwa kuma tun lokaci baiyi ba".
ni dai a sama nake jinta dan azabar da nake ji yanzu yafi min kama da nafitan rai duk da bansan zafin fitar raiba amma nasan babu abun da yakai shi zafi,
nagama sadakarwa raina ne zai fita dan azabar da nake ciki yanzu yawuci na kwatanta shi.
maganar ta nakuma ji a sama tana faɗin
"Tabbas haihuwa ce an ɓata da lissafin ne dai".
pillow ta janyo ta saka kai na a kai kana ta mike da sauri tafita,can an jima ta wado rike da kofi da ruwan hulba wan da ta tafasa shi ta tallafo kai na tasaka min kofin a baki tace
"Sha da zafin sa in sha Allahu zai zo miki da sauki".
da kyar na buɗe baki na soma sha nan take wani sabon zufa yashiga keto min..
Akai-akai tarika bani ruwan idan yaɗau sanyi sai taje ta ɗuma takuma bani nasha,zatona zan ji sauƙin kamar yadda tace amma me sai ji nake kamar ana daɗa hangizo ciwon ne,
kofin tamiko min tace "Karasa wannan sai na je na karo wani in Allah ya yar da yanzu zaki warke".
kuka na fashe dashi cikin muryar kuka nace
"Wayyo Allah Mama Ni dai idan nasha ciwon karuwa yake daɗa yi".
da sauri tace
"A'a yi shiru dai na kukan ba'a yin kuka a irin wannan ciwon ai karuwa ciwon yake yi idan kace zaka yi masa kuka,ko kina so ya karu ne?".
da sauri na girgiza kai tace
"To in kuwa haka ne kada ma kibari wani yaji kukan ki ko Ni da nake kusa dake in kuma ba haka ba to ciwon bazai taɓa bari ba sai dai ma yakaruwa addu'a zaki rika yi da salati nima kuma zan taya ki".
cikin jin tsoron abun da tafaɗa na haɗiye kukan sai juya kai nake cikin jin azaba...
abu kamar wasa sai daɗa zamowa gaskiya yake,tun azahar har la'asar ina abu guda faɗar kalar azabar da nake ciki bazai misaltu ba,
zuwa yanzu Mama ta fara shiga damuwa ganin an shari wasu ƴan awanni babu wani labari,ta dube ni cikin tausayawa tace bari taje gun Malam Musa ta amso min magani.
tafita da sauri,
batare da ɓata lokaci ba ta dawo rike da kwarya a hannunta tana kusa kan ta cikin ɗakin tayi wurgi da kwaryar da gudu takaraso in da nake durkushe sai kakkkarwa nake narike marata danake jin kamar zai fashe da karfi,sai nanata kalmar Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un nake.
taruko ni tana faɗin
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, taso muje asibiti sannu ƴar nan daure ki mike".
sai kuma ta sake ni tafita da sauri tana faɗin
"Bari na taro mai abun hawa".
tana fita akaci sa'a tasamu a kofar gida yasau ke wata mata ta tsai da shi takomo ciki da tai makon ta na iya mikewa tsaye a duke muka fito,muka shiga napep muka nufi asibitin danake awu,
batare da ɓata lokaci ba suka karɓe ni aka shige dani ɗakin da aka tana da domin masu haihuwa.
nan da nan nurse's suka fara ai kin su,
sai dai har yamma labari bata sauya ba, sai gashi-gashi haihuwa zai zo sai ya tsaya duk wani iya bakin kokarin nurse's ɗin sun yi amma abun yaci tura,har aka kira sallar magriba,
sukace gaskiya yafi karfin su mutafi babban asibiti.
A cikin adai-daita mama narike da ni dan zuwa yanzu karfi na yakare gaba ɗaya,da kyar na buɗi baki nace
"Mama ki mai dani gida kawai ni nasan mutuwa zan yi".
cikin tashin hankalin da take ciki tace
"Ki dai na faɗan haka HAMDAH in Sha Allahu zaki sauka lafiya da yar dar uban giji"....
koda muka isa asibitin aka shiga bani tai makon gaggawa, likitoci mata uku ne a kaina biyu mata ɗaya na mini.
Inaji cikin harshen turanci suke faɗin
"Bazata iya haihuwa da kan ta ba dole sai an mata CS yanzu kuma batare da ɓata lokaci ba".
kuka na fashe da shi ina faɗin
"Wayyo Allah Inna Ummi na wayyo Allah na".
rarrashi na suka shiga yi nan suka nimi ganin miji ko uba domin sa hannu kafin suyi CS ɗin,
sannan kuma sai an ajiye 25k shima ɗin na siyan kayan ai kin da za'a yi amfani da sune kuma cikin gaggawa.
hankalin Mama yakuma mummunar tashi,tace
"Mahai finta ya rasu Mijin ta kuma baya gari amma yaba da izinin ayi mata amma dan Allah kuyi mata yanzu zanje nakawo kuɗin".
Mama tafita cikin tsananin tashin hankali.
Ni da kai na da naji azabar yanin ka na ɗazu nace
"Dan Allah kuyi min kuraba ni da wannan cikin.....★
★★★
2hr ago
★★★
Bayan waɗan nan awan nin
Likitoci suka sami nasarar yimin ai ki wan da duk abun da ake idanuna biyu ina kuma ji, in da suka ciro baby'n sai dai duk yan da suka so na kalli abun da na haifa fir naki dan har lokacin ina cikin jin azabar ciwo duk da kuwa allurar da akamin....!★
*Kukaran ta da hakuri🤦🏻♀️ ban sami damar yin editing ba*
*Saura kuce yayi kaɗan😂 bari ma na fece🏃🏻♀️*
*Nasan ki sarai Rabin jiki maman korafi Allah yasa naji wani magana sai natafi yajin ai ki*🤣
*To oga yace Saturday and Sunday lokacin sane to gashi na ɓantara muku lokacin sa🙈🤣*
*Ƴan HAMDAH FANS 2 sun fiku son na adana oga*🙈😂
Hankali tashe Mama ta isa gida in da ta ajiye asusun da take tara ɗan ribar awara da kuɗin da tabawa Alhaji Mamman yaki karɓa tasaka ciki gudun kada ta kashe,
ta fasa asusun hannunta na rawa tashiga kirga kuɗin data ciro cikin asusun,
naira dubu shida da ɗari biyar ne kacal.
cikin matukar damuwa da tashin hankali tarika juya kuɗin a hannunta wan da bai kai ko rabin kuɗin da ake bukata a asibiti ba.
da sauri ta fita tashiga gidan makotan su bayan sun gai sa da
Kulu mai masa Kulu tace
"Gagurin zama Mama mai awara".
Mama tace
"A'a Kulu banga ta zama ba HAMDAH na asibiti za'a yi mata aiki da ma aron kuɗi nazo ki bani ko na masa ne dan Allah,
wlh yanzu haka ni ake jira bazata iya haihuwa da kan taba dole sai amma ta aiki kuma sunce cikin gaggawa in ba haka ba za'a iya rasa aɗaya a cikin su ko ɗan ko ita,in sha Allahu zan biya ki bayan suna".
"Capɗi jan".
Kulu ta faɗa tana rike haɓa kana ta cigaba da faɗin
"Ikon Allah haihuwar dai tazo da gardama kenan,
wlh kin gan ni da mayafi a ka gidan mai shinkafa zani wlh tun shekaran jiya take tamin sintiri yau kuwa da sassafe ita ta tashe ni tun ban ɗaura kaskon suya ba yanzu haka kuɗin ta zan kai mata."
cikin matukar damuwa Mama tace
"Dan Allah in kina da wani kuɗin ki taimaka ki ara min
kokuma ki siyi wake na kici gaba da yin awarar kafin a sallame mu".
tace "Wlh sisi bani da shi in ba wannan dubun ba".
taciro gudan dubu daga bakin zanin ta ta nuna mata.
sannan ta cigaba da faɗin
"To kikira mijin ta mana ko a dajin sambisa yake ai zai iya turo kuɗin da za'ayiwa matar sa ai ki, abu na waya yanzu kai yawaye duk duniyar da yake idan ya tura zai iso, yaushe zaki zauna baiwa kanki wuya kune irin iyayen da kuke baiwa mazajen ƴaƴan ku kofar kin yiwa matansu jinya, har yaushe zaki zauna baiwa kanki wuya bayan yana nan da ransa".
da sauri Mama ta juya bata kuma cewa komai ba saboda sabar tashin hankali bata ma fahimtar me take faɗa,
tana fita gidan wata dillaliya tatafi,tace tazo
tasiyi katifar ta.
dillaliyar tace taje zatazo gobe da safe,
Mama
tace
"Dan Allah ki tai maka kizo muje yanzu wlh ƴata ce ke asibiti".
Tare suka taho gida da dillaliyar,
dillaliya ta kalli katifar da ke cikin ɗakin Mama tace
"Nawa kika masa kuɗi".
Mama tace
"To dai kin ga katifar sabuwa ce bataji jiki ba ban jima da siyan sa ba wlh naira dubu 27 na siya amma yanzu nawa zaki siya?".
dillaliya ta kuma dudduba katifar da kyau kana tace
"Na siye shi dubu 8".
Da sauri Mama tace
"Haba ke kuwa dubu 8 gaskiya bazan sai da shi haka ba ki kara dai".
fuska matar ta yaguna sannan tace
"Shi yasa bana son zuwa gidan mutum yin ciniki sabo da bana son dogon ciniki karshe kuma na ɓata kafata a iska,
to ni gaskiyar in da zan iya siyan katifar nan dubu 10 in yayi miki to duk sabon tar sa ai yazama na hanu,
sannan kuma zaki bada kuɗin wan da zan nima ya kai min gida".
Mama tace
"Gaskiya katifar nan yafi haka kodun halin da nake ciki yaci kiduba lamarin kigani".
tafiya dillaliya tasoma tana faɗin
"To shi kenan kya iya nemo wata ta siya nidai daga kan dubu goma babu kari yo ribar nawa zanci ajikin sa".
shiru Mama tayi tana juya lamarin cikin matukar damuwa da tashin hankali.
taduba gabas ta duba yamma batada wata mafita,da yarage ta sai da mata haka bata da in da zata sami kuɗaɗen da ake nima a asibiti bata dasu bata da dalilin su,
ganin tana kokarin fita a ɗakin da sauri tace
"To ki bada hakan".
Nan dillaliya ta caske dubu goma ta bata da fari tace zata cire naira ɗari uku acikin kuɗin ta bai wa ɗan dakon da zai kai mata katifar gida,
Mama tace dan Allah tai maka kada ta cire ko sisi cikin kuɗin ta bita bashi zata bata...
Kuɗin mama ta haɗa da wan da ta ciro a asusu yazamo dubu shashida da ɗari biyar,
ɗakin ta bi da kallo babu wani abun da zata kuma ɗagawa ta siyar wan da zai bata ko da dubu 2 ne bare yacikita ragowar kuɗin,dama katifar ce kaɗai a cikin ɗakin sai ɗan tarkacen ta da ayan zu take ganin basu da amfani tun da bazata sai dasu su kawo mata kuɗi ba.
numfashi ta sauke gaba ɗaya hankalin ta na asibiti da halin da HAMDAH take ciki, tasan tana can tana kan shan azaba.
da sauri ta fita ta nufi gidan Malam Musa mai maganin maciji dan suna mutun ci dasu sosai a tsakar gida da sami Zainabu matar malam musa tana al'walan sarllar isha,
bayan sun gaisa
Zainabu ta ɗan yi dari tace
"Mama mai awara kin biyo bashin awar ki na shekaran jiya ko? kin ga Wlh kwata-kwata na mance da naci bashin awara sai da na ganki na tuno".
Mama tace
"Wlh Ni ba abun da ya kawo ni ba kenan ai nima na mance da ma kin siyi awara,
rancen kuɗi nazo kibani HAMDAH na asibiti za'a yi mata ai ki,kuɗin hanuna basu kai wan da ake nima a asibiti ba dan Allah ki ranta min bayan suna in sha Allahu zan biya ki".
salati Zainabu ta saka tamike tsaye tana faɗin
"Subhalallahi ayya HAMDAH yan da haihuwar yazo mata kenan Allah sarki yanzu an yi ai kinne?".
Mama tace
"A'a ni ake jira nakai kuɗin yanzu sai a mata".
da sauri Zainabu ta shige ɗaki tana faɗin
"Ikon Allah Allah yabamu da sauki".
tafito rike da kuɗi ta mikawa mama tace
"Wlh iyakacin arzikina kenan ɗaka da waje wannan dubu huɗun gashi malam yafita bare musa ran samun wani abu a gurin shi duk da dai shima naji yau yana kokawa".
Mama ta amshi kuɗin tare da faɗin
"Wlh hakan ma na gode zan haɗa dana hanuna na kai musu suyi mata ai kin kafin gobe na nemo musu cikon".
tajuya da sauri tanufi kofa, Zainabu tabita da addu'a da fatan Allah yasa a yi ai kin a sa'a...
Gida ta koma ta ɗauki laidar kayan jariri da take siya da ɗai-ɗai tana ajiye wa idan HAMDAH ta haihu za'asawa abun da ta haifa har na kwana bakwai,wato kala bakwai kenan kayane irin wan da mace da na miji zasu iya sawa,da ɗan sauran kayakin bukatu na jariri a talakance.
tafito ta tari abun hawa tanufi asibitin.
ko da ta isa
ta kai musu kuɗin ta rokesu da Allah kan suyi mata ai kin idan Allah yakai rai gobe zata kawo musu ciko.
Nan suke sanar mata ai ammayi mata CS ɗin sabo da ganin rayuwar ta da abun da ke cikin ta suna cikin haɗari.
wasu nurse's ne guda biyu suka