Showing 21001 words to 24000 words out of 46406 words

Chapter 8 - HAMDAH part 2 complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

7621

maka kuɗin nan kayi hakuri dan Allah kasan dai yanzu abubuwan sai a hankali,dan Allah
kayi hakuri in sha'Allah zan haɗa maka kuɗin acikin ƴan kwana kin nan,
kakara yimin afuwa".
cikin ɗaga murya Alhaji Mamman yace
"Dakata dan Allah Ni kin ishe ni kullum ke kenan maganar ki ayi miki afuwa ayi miki rangwami,
wai shin kan kuɗin nan in da rangwami da afuwa ake tarashi zai taru ne,
in dai da akwai rangwami acikin tara dukiya da zai taru ne?
nifa kuɗi kawai nake bukata,
shi kuma nake son tarawa,
kin san ta yan da akayi na tara kuɗi na siyi gidan?,
nifa kuɗi kawai nake bukata,
in da ace kin fita tuntini a gidan nan da na tabbata na tara kuɗin da yafi abin da ake tunani dan haka ni kifita min agida kawai babu wani rangwami."
fuskarsa yajuya ta bakin kofa ya ɗaga murya yana faɗin
"Kushigo da kayan Bismillah ga gidan kushigo da su".
kofar da yake kallon na zubawa ido in da naga shima ya fuskanta yana maganar,
wasu mata da ƴan matasa ne suka fara shigo wa da kaya,
suka ta shigowa da shi suna ajiye wa...

Hannu mama ta kuma haɗawa tana cigaba da rokon sa da haɗa sa da Allah da yi masa magiyar in sha Allahu zata biya sa kuɗin a cikin watannan,
yace
"Dai na haɗa ni da Allah ki cuce ni,
na dai faɗa miki babu bulo ɗaya da mijin ki ya ɗaura kan ginin gidan nan,
nariga da na gama magana yanzu bani da hannu acikin wannan gidan na nariga da na bada hayan shi,na karɓi kuɗin sa dan haka fita ki basu gida yanzu nasu ne".
yajuya yaso ma tafiya yana cigaba da faɗin
"Kuɗi na da nake bin ki bawai na bar miki bane kuɗina yana nan a kanki kuma zaki biya ni,
na baki sati biyu ki biyani kuɗi na idan ba haka ba sai nayi miki rashin Mutun cin da baki tunani,
kin san ni a kan kuɗi ko uban waye ma zan iya masa rashin mutunci ko shi mijin naki da muke uba ɗaya bai isa yaci kuɗi na ba tun da bashi ya nemo min ba."
yayi waje yana cigaba da zazzage bala'i.

Bayan sa Mama tabi tana cigaba da haɗa shi da Allah har kofar gida ta bishi,shi ko yaja garen sa yahaye babur ɗin sa yayi gaba.
suko mutanen da yazo da su sai shigo wa da kaya suke suna jibgeshi a tsakar gida,
tuni hawaye yafara sauka a ido na, muna tsaye cirko-cirko har suka gama shigo da kayan.
matan suka dubi Mama sukace
"To mun gama shigo da kaya yazu shirya shi cikin ɗaki ga gurin yafara rufa wa kar ruwa ya sauko ya jika mana kaya."
da sauri Mama ta dubi matar batare da tace komai ba,
Hannuna Mama tarike tana faɗin
"Zo mu fitar da kayan".
cikin zubda kwalla nace
"Mama idan muka fitar da kayan ina zamu kai?".
tace
"Allah bazai hanamu in da zamu kai ba."
Haka mukayi ta fito da kayan mu nuna kai shi can waje kofar gida,
tas muka fito da kayan muka jibgeshi waje duk da dama bawani kayan kirki bane.
muna tsaye a kofar gidan Zainabu ta iso mu hankali tashe tana faɗin
"Mama mai awara yanzun nan yaro yazo yace min yaga kuna ta fitar da kaya,
wasu kuma suna shigar wa ciki, Mama da ma tashi zakiyi shine baki faɗa mana ba?."
Murmushin yake mama tayi kana tace
"A'a mai gidan ne yazuba ƴan haya aciki shiyasa muke tashi muma tashin yanzu ne yasa memu bawai tuntini da ma da shi bane".

Ido Zainabu ta waro tare da buga kirji tace
"Ya zuba ƴan haya a cikin gidan bayan da wasu masu hayan aciki,
ban taɓa ganin haka ba,
ba'a taɓa ɗaga ɗan haya rana a saka batare da an bashi lokaci ba sai an bashi kwanaki ya kama gidan da zai zauna kafin a ɗaga shi,
ba irin wannan ɗagawar babu sanar wa ba,
to yanzu ina zakuje Mama kuna da wani gidan da kuka kama ne?".
Mama tace
"Ko ɗaya yanzu dai zamu ni mi wani gidan hayan da zamu zauna".
"Gaskiya kam amma wallahi bai kyauta ba ai ba haka ake yi ba ba'a taɓa ɗaga mai zaman haya haka lokaci guda ba,
sai dai a baka lokaci ka kama wani gidan hayan sai ka tashi ba irin haka lokaci guda ba".
Mama kam murmushin karfin hali yacigaba da yi,
Niko hawaye ne kaɗai ke zuba a ido na naka iya furta komai.
Zanabu tace
"Mama ku tattaro kayan kizo muje ga guri yafara rufawa hadari yana kan taso wa".
ta sun kuya tana tattaro kayan tare da cigaba da faɗin
"Kuyi sauri kada ruwa yasau, ko kuzo muje kutara su a zauren gidan mu kafin ku sami wani gidan".
Mama tace
"To Zainabu".
nan muka shiga kwashe kayan muna kaiwa gidan Zainabu a zauren gidan ta muka tara kayan gaba ɗaya sannan muka shige ɗakin ta dan lokacin tuni ruwa ya sauko...

Tun da aka fara ruwan nan bai tsaya ba har yamma,
har Malam Musa yadawo yazo yasa memu a gidan,
koda yaji labarin bai ji daɗi ba kwarai yace Alhaji Mamman bai kyau ta ba bahaka ake yi ba,sai dai yasan waye Alhaji Mamman karamin ai kin sa ne yin hakan.
Yacewa Mama bari a ɗauke ruwa zai fita yake yataya ta niman gida ko Allah zai sa a samu a yammacin,.
Mama tace ita ma ɗin ruwan take jira yaɗau ke tafita niman gida.
Gidan malam Musa ɗaki ɗaya ne tak a gidan shine kuma wan da suke zaune da matar sa a ciki.
dan haka zaure yako ma yaje ya zauna yabar mu acikin ɗakin,
gaba ki ɗaya Mama a takuri take ganin mai gidan yako ma zaure ya bar mana ɗakin.
wasa-wasa ruwan nan bai ɗauke ba sai daf magriba,
dan haka Malam Musa yace
Abar niman gidan sai gobe tun da yanzu dare yariga da yayi,
a zaure yakwana yabar mana ɗakin...

Washegari da sassafe Mama tafita neman gidan da zamu koma bata dawo ba sai wajen azahar,
tadawo gaba ɗaya a galabaice,
a ɓangaren Malam Musa shima bai jima da dawowa daga niman gidan ba,
Muna zaune a ɗaki
Zainabu ke tambayar Mama Allah yasa anyi sa a an sami gidan.
numfashi mama ta sauke cike da ɗinbin damuwa tace
"Wallahi nagama iya yawo na ban sami gida dai-dai da kuɗin hannuna ba duk gidan da naje niman hayar sa gaba ɗaya sun fi karfin kuɗin hannuna,
azaman yanzu kuma gaskiya masu rangwami sunyi karan ci".
kai Zainabu ta girgiza cike da tausayawa kana tace
"Gaskiya kam yanzu rayuwa tayi tsada Allah yayi mana magani".
Amin muka amsa dashi,
gaba ki ɗaya jikina yagama yin sanyi.
Mama ta mike ta nufi zaure in da kayan mu yake can,ganin ta ɓata lokaci bata dawo ba sai na mike na bi bayan ta,
ganin ta nayi tana shirya kaya cikin ɗan kari min jaka gaba ki ɗaya hankalin ta a tashe,
ta dube ni tare da faɗin
"Zanje garin mu HAMDAH kamar dai yan da na taɓa baki labari ni ƴar Yola ne aure ne ya kawo ni nan,
yanzu rabona da Yola shekara 7 kenan zanje ni na dawo in sha Allahu kwana biyu zanyi na dawo,
zan tafi mana da wasu kayayyakin mu zanje na duba kalar yanayin zaman can idan naje nasa mu matsuguni,duk da dai dama muna da gidan gado kamar yadda na taɓa baki labari yanzu dai zanje na duba acikin gidan gadon mu idan akwai ɗakin da zamu zauna,
zan dawo nazo na ɗau keki mukoma,
kwana biyu kacal zanyi na dawo sai na ɗauke ki mu koma tare".
ta ciro kuɗi naira dubu biyu da ɗari biyar ta mika min
tace
"Ga wannan ki rike a gurin ki ko zaki bukaci wani abun,
kin ga suma nan basu da karfin da zasu iya ɗawai niyar ku duka duk da bawai jimawa zanyi ba kwana biyu ne ka cal,
Amma ki rike zai iya yi muku amfani,ko zaki ga abun da kike so ko su Naseem da Nasmah sai ki siya musu".
numfashi na sauke
jiki a sanyaye dan Mama ta taɓa bani labarin family'n su
Su biyu ne agun mahaifin su ita da wanta na miji,
lokacin auren ta yayan ta baiso auren da wan da take so ba dan lokacin mahaifinsu ya rasu a haka dai akayi auren sam baya so,
shi yasa ko taje gidan ma bata jin daɗi shi yasa takan daɗe bataje gidan ba dan ko taje ma baya sauraran ta,
ko da mijin ta yarasu taje amma yaki yabata fuska tazau na agidan,
sai dai ta alakan ta hakan dan gidan nasa ne yanzu sabo da shi yaci gadon gidan,
abun tun yaranta har yanzu tana ta kan fama,
har yakai ga yanzu shi yayan nata yarasu sai dai matar sa ta ari abun ta yafawa kanta,
ta kanainaye gidan tace gida natane da ƴaƴan ta dan haka babu wan da ya isa ya zauna mata a gida.
dan a lokacin da mahaifin su Mama ya rasu yayan ta shi aka basa gadon gidan in da ita aka bata
gadon gonar mahaifin su...
idan taje gidan matar tarika mata wulakanci da gani-gani shi yasa ma shekaran ta 7 bataje ba...

Hawayen fuskata na share kana nace
"To mama sai kin dawo Allah ya kiyaye hanya amma Mama ki dawo da wuri dan Allah".
tace
"Insha'allahu zan dawo da wuri HAMDAH kwana biyu zanyi da yar dar Allah zanje naga yanayin zaman gurin in yaso ma zan saida gonana da yake can sai na dawo na kama mana gida a nan
ko kuma na kama mana a can Yola sai na dawo na ɗauke ku sai mu koma".
nace
"To Mama Allah ya kai mu ya kiyaye miki hanya"
ta amsa da Amin Amin.

Da azahar ɗin muka fita yi wa mama rakiya ni da Zainabu har bakin hanya muka kai ta yayin da take rike da Nasmah,
da tun dawowar ta daga niman gida ƴar ta nanne mata sai da ta goye ta,
sai da muka tari mai abun hawa kafin ta miko min ita,
kana ta karɓi Naseem tana yi masa wasa shi ko sai wage mata baki yake,
duk yaran sai dariya suke mata itako sai wasa take musu,har sai da mai abun hawa yayi magana kana ta miko min Naseem,
kuka ya saka yana zillo alamun zaije gurin ta,
murmushi tayi tare da lakata kuma tun sa tace
"Mai gidan ka zauna zanje nadawo yanzu bazan daɗe ba zanje na nimo sadaki na kawo maka".
dariya ya saka kamar wan da yasan me aka ce,
Zainabu tace
"Ai kam kine mo da yawa dan yanzu mata suke bawa maza sadaki".
Mama tace
"Ai kam".
kana ta shige abun hawa muna ɗagawa juna hannu yayin da hawaye ke zuba a ido na,
muka juya muka koma gida...!★



Mommyn Twins ce



Ranar a zauren malam Musa yakuma kwana ya bar mana ɗakin,
washegari haka na wuni sukuku bani kaɗai ba hatta Naseem da Nasmah idan ka kallesu kasan sunyi kewar Mama,duk da kuwa Zainabu tana jan su ajiki tana yi musu wasa,
Malam Musa kuwa yana iya bakin kokarin sa ya kawo mana abinci sosai Zainabu ta girka mana....
yau kwana biyu kenan da tafiyar mama inata murna da zuba idon ganin dawowar ta dan nasan yanzu kam tana hanya,
ganin bakina yakasa rufuwa Zainabu tayi ta zolaya ta tana yi min dariya.
murmushi nayi nace
"Ai in sha Allahu yau zata dawo".
Ido nayita kurawa hanya dan ganin isowar Mama har yamma shiru babu wani labari,
wasa-wasa har dare yayi zuwa lokacin kam shiru na zauna cikin damuwa jikina yagama mutuwa.
har dare yayi nisa sosai nan ne na cire raina da dawowar mama a yau na sa a raina wata kila sai gobe zata dawo.
goben ma haka shiru yanzu kam hankali na yakai kololuwa wajen tashi,
ba abun da ke damuna kaɗai ba kenan,
duba da gidan da nake zaune duk da Ni basa nuna min wani hali ko kaɗan,
Amma bana jin daɗi badun komai ba,
sabo da ganin shi mai gidan da gidan sa a zaune yake kwana gashi yanzu yanayin damina kusan kullum sai anyi ruwa ga sanyi haka akan taburma take kwana acikin zauren.
gaba ɗa hankali ya ninku wajen tashi,
ace mai gida da gidan sa a zaure yake kwana zauren ma kan taburma ga sanyi.

Yau kwanan mama biyar da tafi babu alamar ta.
da safe na nufi zaure in da kayan mu yake naɗauki akwati na da nazo da shi tuntini na haɗa kayana kala biyar wan da tuntini da ma da su nazo naketa sawa har yanzu sun gama tsufa sun koɗe wasu ma har sun yayyaye sai da aka bisu da ɗin ki,
na haɗa kayan cikin akwati,
na ɗau ki kayan Naseem da Nasmah wan da suka samu a suna kala hurhuɗu sai kuma wan da Mama tasiya tun kan na haihu na haɗa su cikin akwatin,
da ɗan sauran kayan bukata,
nayi musu wanka nima nayi,
Zainabu tazuba min ido ganin inata shiri kana tace
"Naga kina ta shiri da haɗa kaya wai ina zaki ne haka da kaya?".
nayi murmushi tare da duban ta nace
"Zan bi Mama ne dan har yanzu gashi bata dawo ba".
Zainabu tace
"To ke da zaki jirata batace kijirata ba".
nakuma murmushi tare da faɗin
"Eh tace na jira ta amma har yanzu bata dawo ba kawai zan bita can ɗin".
shiru Zainabu tayi kana tace
"To shi kenan amma Ni inaga da kin daɗa kara hakuri ki jirata".
nace
"A'a zan bita kawai".
tace to shike nan.

Bayan nagama kimsa yaran na ɗauki Nasmah na goya na saka hijabi na kuɗin da mama ta tani na ciro sannan na ɗauki Naseem a hannu,
Zainabu ta roko min akwati na har bakin hanya ta raka ni,
na hau abun hawa zuwa tasha ina isa
Na shiga motar YOLA........

Acan cikin garin Bauchi'n Yakubu kuwa zaune Ummi take akan sallaya..........!★



Kuyi hakuri dan Allah wlh sabar sauri ko editing ban yi ba😫



Mommyn twins ce



Wani sassanyan kuka Ummi ta sake dai-dai lokacin da ta sallamar da sallar nafilar da take,
ta ɗaga hannayen ta biyu tana kwararo addu'a yayin da hawaye ke sauka a idon ta,
tun ranar da HAMDAH tasa kafa ta fita agidan kullum Ummi acikin kuka take.
badare barana ko da yaushe acikin yimata addu'a take tana nina mata kariyar Allah a duk inda take.
Wani sassanyar kuka mai matukar taɓa zuciya Ummi takuma sakewa lokacin da take jaddada rokon ta ga mahaliccin mu.
yayin da muryar ta ke fita haɗe da sautin kuka.
Fauzan da yanzu shigo War sa cikin ɗakin da sauri ya isa in da take yadurkusa gaban ta tare da kifa fuskar sa kan cinyar ta,sai ya saki kuka yana faɗin
"Ummi dan Allah ki daina kuka Ummi kullum sai kinyi kuka Ummi ki dai na kuka".
yafaɗa cikin matukar damuwa da ganin halin da mahaiyar tasa kullum take ciki,
kansa ta shafa da hannunta ɗaya yayin da ta ɗago hannunta guda tashiga share hawayen fuskar ta.
a hankali tace
"Taso Fauzan yi shiru na dai na kukan".
tafaɗa cikin sansanin karfin hali da son danne zuciyar ta da ke wani irin muguwar bugawa,
Aduk san da ta nuna da HAMDAH irin yanayin da take shiga kenan sai dai na yau ya ninka na ko yaushe.
yau bugun zuciya ne mai haɗe da ɗinbin tsoro.
da sauri ta kai hannunta ta dafe kirjin ta tare da furta
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un".
da karfi cikin tsananin jin tsoron da ya lulluɓe ta..

cikin rawar murya mai haɗe da tsoro tacigaba da faɗin
"Ya Allah ka kare baiwar ka aduk in da take a duk halin da take ciki,ya Allah kafini sanin inda take kakare ta da kariyar ka."
Kuka sosai Ummi tafashe dashi ta rungume Fauzan da shima yakara sau tin kukan sa,
kuka sosai Ummi take tamkar karamar yarin ya kuka.
cikin Muryar kuka Fauzan yake cewa
"Ummi kin ce Aunty HAMDAH zata dawo kullum haka kike faɗa gashi har yanzu bata dawo ba,Ummi yaushe Aunty HAMDAH zata dawo?".
hawayen fuskarta tashi ga share wa yayin da take kokarin sai da hawayen da kuma kukan tace
"Ko bata dawo ba Allah zai kare ta a duk inda take a duk halin da take ciki, shine mai kariya buwayar sa ya isa ko ina".
taɗago Fauzan tashare masa hawayen fuskarsa kana taci gaba da faɗin
"Yi shiru kaji a duk inda take tana cikin kariyar uban giji".....



Tun da muka fara tafiya nakejin wani irin yanayi a jikina,
sai dai na kasa fassara kalar yanayin da nake jin kaina ciki,
ina dai zaune cikin matar shiru yayin da Nasmah ke goye a bayana har lokacin Naseem kuma na rike a hannuna,
duk kanin su bacci suke,
daɗa gara rukon Naseem nayi kana na zuba wa titi ido.
sosai motar ke sharara gudu kan hanya sai dai nayi mamakin ganin tulin tafiyar da mukayi mai nisar gaske wai har lokacin bamu iso garin Yola ba,
tashin tun sassafe gamuna har bayan azahar a kan hanya duk da kuwa gudun da motar take.
tun fasinjojin da ke cikin motar suna hira har kowa yayi tsit sabo da nisar tafiyar.
karfe uku da rabi dai-dai muka isa wani gari in da direba yagyara fakin a gefen titi,
numfashi na sauke tare da yiwa Allah godiya a raina nake faɗin
"Kai wannan gari akwai nisa har sai yanzu muka iso gaskiya wannan Yola'n akwai shi da nisa".
bankai ga idda maganar zucin da nake ba najiyo maganar direba yana faɗin
"To nifa iyaka na nan garin bazan karasa can Yola ba waɗan da zasu wuce zasu yi gaba sai su sauka su tari wata motar anan".
Ido na waro da mamaki nace
"Au bamu iso Yola'n bane?".
wata matar da ke gefe na tace
"Eh ai bamu iso Yola ba tukun me mukayi ai da sauran tafiya".
"Ikon Allah".
nafaɗa a fili kana na buɗe marfin motar na fito, direban ya sauke mana kayan mu,
a hankali na koma gefen titi kan wani itace na zauna ina rungume da Naseem daya farka yana shirin yin kuka,
gyara zama ta nayi da kyau nabuɗe jakata na ciro gorar kunu da na ɗura musu,
nabashi yasha kana na kunce Nasmah da naji ita ma tana motsi na bata itama tasha,kana na kara musu da nono, sai da na tabbatar sun koshi sannan na mike na mai da Nasmah na goya ta na ɗauki Naseem...
wata mota ce tasharo kwana daga can dagodu sosai
sai kuma ta rage gudun dai-dai san da tazo daf da Ni taɗan gotani kaɗan sai ta tsaya.

Direban dake tuka motar yazoge glass ɗin motar yaleko ni kana yace
"Tafiya ne?".
Kai na gyaɗa masa kana nace
"Eh". yace "Wani gari".
nace "Yola".
"Ok shigo ai wannan motar Yola can na nufa yanzu".
da sauri na gyara rikon Naseem nasun kuya na janyo akwati na,
da saurin sa yafito daga cikin motar ya karɓi akwatin yabuɗe but yasaka kana yabuɗe min gidan baya nashiga kana ya mai da murfin yarufe yakoma mazaunin sa kana yaja motar muka soma tafiya.
mamaki ne yakama Ni lokacin da naga Ni ɗaya ce cikin motar babu kowa babu ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login