Showing 1 words to 3000 words out of 46406 words

Chapter 1 - HAMDAH part 2 complete hausa novel

RASHEEDA   

04 Oct 2024

7620

Wani irin kallo yake bin Na'ima da shi yayin da yakejin kwakwalwar sa nawani irin juyawa zuciyar sa kuwa bugu yake kamar zai faso kirjin sa yafito,
System ɗin gaban sa yature gefe kana cikin jan numfashi haɗe da huci yace
"Me kike son faɗa ne kam me kike nufi?!".
baki ta karkata tace
"Ina nufin akan gado na samesu sarkafe da juna suna ai kata baɗala".
ɗan sakai ta maganar nata tayi kana tashiga jan hanci tana matse ido da karfi wasu gun tayen hawayen da suka fito takai yatsa ta sharce kana cikin murya mai kamada mai sonyi kuka tacigaba da faɗin.
"Wlh abun nan ya jima yana dami na, Ni nasan akuyata tayi kuka nasan bani da hakuri amma bazan iya cin amanar aure ba,bazan iya cigaba da zuba ido ana ha'intar kaba bazan iya gani ka karɓi ɗan shege a rashin sani ba,kayi tunani da kyau taya za'ayi cikin wata guda ya zamo naka bayan a cikin watan baka garin kuma ka barta bata da sarki".
da karfi ya furta
"Ya isa!".
ya mike tsaye cikin jin yanda kansa ke juya masa yanufi cikin bedroom ɗin sa.
bayan sa tabi da kallo har yashige yarufo kofar da karfi,
sai ta saki wani murmushi tamike ta koma side ɗin ta tanajin zuciyar ta wasai...

Wani irin bugawa kirjina yayi da mugun karfi acikin baccin da nake wan da nakoma bayan sallar asuba,
afirgice na mike zaune tare da dafe kirjin da yake harbawa da karfi-karfi. jikina na rawa na zamo daga kan gadon na nufi kofa da sauri na fita ta cikin babban parlour nabi nanufi side ɗin sa da sauri na tura kofar bedroom ɗin sa yayin da na dafe kirjina da hannuna guda,
ya na tsaye cikin ɗakin yabai wa kofa baya da sauri na isa na rungumo shi ta baya,tare da manna kirjina da ki bugawa da karfi cikin bayan shi.
"Ya SALEEM".
nakira sunan shi muryata na rawa,
juyowa yayi yaciro ni a jikinsa da karfi tare da watsa min wani irin kallo, fuskarsa ta rikiɗe takoma irin fuskar Ya SALEEM ɗin baya babu wasa ko annuri kan fuskar nasa,
cike da fargaba da tsoron ganin yanayin sana cikin muryar kukan da ya suɓuce min nace
"Ya SALEEM wani mutuwar a ka kuma ko? dan Allah ka faɗa min yanzu ba sai naje gida ba kafaɗa min kawai nima na mutu ko zan huta da azabar da nake ji cikin zuciya ta".
hannuna ya damko da karfi ya janyoni ya nufi kofa dani cikin muryar kuka nacigaba da faɗin
"Ya SALEEM karka kai Ni ka nuna min gawar wani, mutuwa zanyi".
baiyi magana ba bai kuma sake hannuna ba har muka fito cikin parlour'n sa,kana ya saki hannuna cikin fusa tacciyar murya wanda ko a da can baya kafin zuwa na gidan da kuma farin zuwana gidan ban taɓa jin yayi min magana da irin saba yace
"Waye uban sa!!?".
bin in da ya sauke yatsar sa nayi da ido kana naɗa go na kalli fuskarsa da babu ko ɗigon annuri cikin rashin fahimta nake kallon sa.
wani uban tsawa ya buga min tare da kuma faɗin
"Waye uban sa nace!".
wani irin zabura nayi da jin sawan da ya bugamin ya kuma danna yatsarsa da ke kan cikina sosai,nan take abun da ke cikina ya motsa da karfi.
jikina na rawa na kai yatsata sai tin kirjin sa nace
"Gashi nan".
hannuna ya bige da karfi cikin kuma tamke fuska yace
"Raina min hankali zakiyi faɗa min waye shi waye shi da har zai haɗa muhalli da ni!".
kuka na sake da karfi ina faɗin
"Kai ne uban sa Ni bansan wani ba Ya SALEEM dan Allah ka dai na min wannan wasan kai ne uban sa kaine-kaine!".
nafaɗa da karfi.
ida nunsa ya ɗaura cikin nawa kana yace
"Ni abokin wasan kine da zan miki wasa in tan bayeki uban sa kice ina miki wasa akan bakisan uban nasa bane ko..."
da karfi na rufe idanuna batare da na bari ya karasa faɗar abun da zai faɗan ba nace
"Ni ban sani ba, ban sani ba, ban sani ba, ban san kowa ba Ni kai nasa Ni kai ne uban sa".
nafaɗa da karfi cikin muryar shashsheka da toshewar kwakwalwa da gaza fahim tar in da ya dosa.

"Uban sa shi ne wan da yake sajewa da kayan makarantar su yazo yagama abun da zaiyi yafita, ai rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ce tak na mai kaya".
cak na ji kukan da nake ya tsaya a hankali na juyo in da naji maganar ke fito wa, Na'ima nagani tana tahowa cikin parlour'n cikin isa da izza ta karaso cikin parlour'n tana cigaba da faɗin
"Ai ita da ma haka rayuwa take zaka daɗe kana tsula tsiyar ka rana ɗaya tak a sirin ka ya tonu, baki taɓa tunanin zuwan wannan ranar bako?".
da ɗinbin mamaki nake kallon ta yayin da naji abun dake cikin kwakwalwa ta yana son fin karfin tunanina,kai na na dafe da karfi jin yana min wani irin mugun sara.
maganar ta nakuma sinkayo wa
"Da auren ka karika kawo maza cikin gidan auren ka wannan wace irin rayuwa ce".
zuwa yanzu kam na fahimci duk inda batun nasu ya dosa da sauri na waigo in da take nashiga girgiza kai tare da faɗin
"Aunty Na'ima kiji tsoron Allah me kike son faɗa a kai na".
kugu ta rike tace
"Amma gaskiya yarin yar nan to in banji tsoron Allah ba tsoron ki zanji abun da kike ai katawa ne yau ashirin ki ya toni bazan taɓa zuba ido a haifo ɗan shege cikin gidan nan a matsayin ɗan gidan nan ba, da ma nasan zaki musa dan bakiyi zaton ranar tonon asiri irin na yauba".
kallon ta ta maida kan Ya SALEEM da ya zube kan kujera tare da dafe kansa da hannayen sa biyu tace
"My SALEEM Ina da shaidu kwarara guda uku wan da duk wani abun da ke faruwa a cikin gidan nan suna gani sun ma rigani gani, kuma ko Kotun koli ne zanje da su".
tsayuwar ta ta gyara ta dubi kofa kana ta buɗe murya tace
"Baba Mai gani,Sani direver Habu mai shara".
Da sauri na juyo jin an turo kofar da sallama,
baba mai gani na gaba Habu da Sani suna biye da shi,suka karaso cikin parlour'n kan su a kasa,
a kasa suka zauna taɗan gefe kana baba mai gadi yakuma sunkuyar da kai yace
"Gamu Hajiya". baya tayi ta zauna kan kujerar da ke bayan ta kana ta dube su sannan ta mai da duban ta kan Ya SALEEM,
da har lokacin hannunsa na dafe a kansa idanunsa sun kaɗa sunyi jajirr sannan tace
"Waɗan nan sune shai du na kuma duk kanin su sun rigani sanin abun da ke faruwa amma gasu kaji daga bakin su ranar wanka ba'a ɓoye cibi"..

Bin su yayi da ido har lokacin bai furta komai ba dan yan da yake jin kansa ya zarce tunanin mai tunani.
cikin wani irin bakar yanayi yakuma duban su kana yace
"Wa yake zuwa gidan nan bayan bana nan?".
ganin ya zuba musu ido yasa baba mai gadi gyara zama ya daɗa yin kasa da kai kana yasoma magana
"Allah ya huci zuciyar ka ranka shidaɗe,wata ranar da kayi tafiya da yamma ina zaune a bakin get naji ana ƙwanƙwasa kofa
sai na mike naje na buɗe karamar kofa naleka, sai naga wani ɗan matashi tsaye da kayan makaranta a jikinsa nan nake tan bayar sa lafiya gurin wa yazo yake buga kofa,shine yace min shi ɗan makarantar su HAMDAH ne gurin ta yazo dajin hakan kuma da ganin sa da kayan makarantar nasu sai na buɗe masa kofar yashiga,
to ina dai daga zaune lokacin
tun da yashiga kuma bai fito ba sai daf magriba, washegari yakuma dawowa da littattafai a hannunsa yace min wai zaije koya mata karatu ne ita takira sa,to tun daga ranar ya jera sati yana zuwa da kayan makaranta sai daga baya kuma ya dawo zuwa da kayan gida". yana kai wa nan yakuma yin kasa da kai cikin nuna tsantsar gaskiya.

Sani ya nisa kana yace
"Oga ranar ina cikin wanke mota nima na gansa ya shige cikin side ɗin ta da kayan makaranta a jikin sa, to nima dai kusan kullum sai na gansa yashigo kuma lokacin da kayi tafiyar nan ne, wata rana kuma ina daga cikin parking space na hango su sun fito tana yi masa rakiya sai dai daga bakin kofar side ɗin ta ta tsaya shikuma yafita".
Zama Habu ya daɗa gyarawa kana ya fuskanci Ya SALEEM da kyau kana yaso ma magana yayin da yayi kasa da kansa yace
"Oga lokacin da kayi tafiya kana da kwana 25 ranar ina cikin sharar yamma da sauri dan ranar na makara har gurin ya fara rufawa ina cikin share ta bayan ɗakin ta ta gurin window najiyo dariya sosai na tashi kuma muryar na miji ne, to ban kula ba dai nacigaba da sharana dan a tunani na kunne nane yaji min karya dan nasan dai baka gari,
to can kuma sai narikajin muryar na mijin dai to da nagama sharana har zan wuce sai narika jin wasu ƴan maganganu haka, sai kuma na leka sai naga wani mutum a kan gadon ta abun dai babu kyan gani,
to a lokacin naji muryar Hajiya tana rafka salati shine na zago da sauri".
Sani ya karɓi maganar da faɗin
"Nima ganin Habu da sauri ya shiga cikin side ɗin ta da kuma ihun Hajiya da nake jiyowa shine muka rufa masa baya nida baba mai gadi to shine muka tadda mutumin yana fito wa daga ɗakin ta"...

Kamar a mafarki haka nake jin maganar nasu sai na rika bin bakin kowannen su da kallo duk wan da yakarɓi maganar sai na zubawa bakin sa ido har sai yakai karshen maganar nasa,
gaba ɗaya ƙwaƙwalwa ta tatsaya cak ta dai na ai ki, bazan iya fasalta yanayin da nake ciki ba sai dai inaji a lokacin in da mutuwa zata ɗauke ni da taga ma yimin gata a rayu.
tabbas na yarda da cewa in kaga kana kuka to shima wata rahama ce da sassauci wa zuciya, idanuna sun kafe sun bushe babu ko ɗigon hawaye a cikin su, numfashi na sai yi yake kamar zai bar jikina da zai tafi da yayi min babbar gata a lokacin.
Maganar Ya SALEEM najiyo a sama
"Meyasa duk waɗan nan abubuwan suna faruwa ba wanda ya taɓa faɗa min? har da kai mai gadi in su tunanin su bai kai nan ba ai kai duk kanin mu ka haife mu kana kallon ɓarna na wanzuwa bazaka sanar a magance abun da wuri ba".
kasa baba Mai gadi yadaɗa yi da kai kana yace
"Allah ya huci zuciyar ka gudun faruwan wata matsalar ce yasa ban sanar ba".
da hannu yayi musu alama da kofa kana yace
"Ku tashi kuje".
da sauri suka mike sukayi waje Na'ima ma ta mike tanufi side ɗin ta.
sai a lokacin na sami damar janyo numfashi na.
idanunsa ya rumtse da karfi kana ya mike zumbur ya damko hannuna cikin tsananin bakar ɓacin rai da kunar zuciya.
kai nashi girgizawa jin yan da harshe na yayi min wani irin mugun nauyi nakasa koda iya matsa shi bare na iya furta wani abu da kyar nakuma iya jan numfashi tare da faɗin
"Wlh Ya SALEEM ban san komai ba ban san komai game da wannan maganar ba wlh na rantse da Allah duk abun da suka faɗa ba gaskiya bane Ya SALEEM cikin nan naka ne kai ma kasan naka ne".
hannuna yakuma damkewa da karfi kana
ya yarfamin wani marin da saida naji jina ya tsaya na ɗan wani lokaci,cikin kakkausar murya yace
"Kada ki sake dan ganta ni da wannan kazamtaccen cikin Ni ba uban sa bane
kada ki yaudari kanki da abun da ke cikin cikin ki kan cewa Ni uban sane". sai kuma ya sassauta murya ya ɗaura idanunsa kan fuskata kana yace
"Akan me yasa zaki hori zuciyata da wannan mummunar horon me na gaza miki da har bayan bana nan zaki kawo wani cikin gidana harkan shin fiɗin mu har ki isar dashi muhallin da ni kaɗai na dace dashi??
Jeki na haramta kaina gare ki,jeki nace!!".
yafaɗa cikin karaji tare da hangizani, nayi tangal-tangal kamar zan faɗi kasa, wani irin motsawa cikina yayi har sai da nakai hannu na dafe cikin,a fusace ya maso ni tare da kuma ruko hannuna yafisgo ni yanufi kofa yabuɗe ya hangizani waje cikin nuna Ni da yatsa yace
"Tafi na daina ganin ki na dai na ganin wannan kazamtaccen cikin na haramta kai na gare ki!".
yakuma nanata karmar haramta kansa a gare ni a karo na biyu,
yana kaiwa nan yaja kofar ya rufe da karfi.
"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un".
nafurta da karfe sai kawai naji wani kuka yazo min da sauri mai haɗe da gudu na juya tare da fashewa da kuka mai tsanani nanufi side ɗina, koda nashiga bedroom rasa me zanyi sai narika zaga cikin ɗakin ina cigaba da kuka nakai tsawon minti 10 ina zaga cikin ɗakin da kuka narasa meke min daɗi me zanyi guda ɗaya,
sai a lokacin na juya na isa gaban wardrobe na tuɓe kayan jikina na ciro riga da zani na atamfa nasa na zura hijabi na janyo akwatin da lokacin rasuwar Inna yakai min kaya a ciki tun da na dawo na aje akwatin ban kuma bi ta kansa ba kayane kala biyar a cikin na janyo
nayi waje.

Ina fita naga Salele tsaye a can gefe yayi jigum ya zubawa kofar side ɗin ido,muna haɗa ido da shi sai ya girgiza min kai tare da share wasu kwallar da suka zubo mishi,juyawa nayi nasoma tafiya in da tafiyar kawai nake amma bana sanin in da nake jefa kafata,
har nafita daga gidan na tari mai a dai-daita ko da muka isa na sau ka nace masa bari naje na amso masa kuɗi ganin yan da nake kuka yasa mai napep ɗin cewa nabar shi Allah ya jikan rai. dan shi a zaton shi mutuwa akayi.
A farfajiyar gida na yar da akwatin ina jin mai gadi yana tanbaya ta lafiya ban ko juyo ba nayi ciki da sauri,
A parlour na tadda Ummi zaune ganin yan da nashiga yasata mikewa da sauri tana faɗin
"Ke HAMDAH menene?".
rungume ta nayi tare da kuma kara sautin kuka na,
a kiɗime Ummi taci gaba da faɗin
"Menene me yafaru??".
ban iya cewa komai ba sai rusar kukan da nake.
Jijjiga ni tayi tace
"Ke HAMDAH ki nutsu ki faɗa min menene menene kuma???".
cikin muryar kuka sosai nashiga faɗin
"Ummi wlh cikin sane narantse da Allah cikin sani".
cikin rashin fahimta da soma shiga damuwa da ganin yan da nake maganar kamar numfashi na zai kwace tace
"Cikin wa? menene ya sami cikin?? kinutsu ki faɗa min".
hannunta na rike da karfi cikin fizgar numfashi nace
"Ya SALEEM Ummi Ya SALEEM Ni ban san komai ba ban san me suke faɗa ba na rantse Ummi ban san komai ba"..
da sauri goggo Hauwa da Aunty Halima suka fito suna faɗin
"Menene me ya same ta?".
Ummi tace
"To ni ma dai ban sani ba ganin ta kawai nayi kamar an jefo ta".
goggo Hauwa ta ruko ni tace
"Ke HAMDAH wani abun ne yafaru a gidan naku?".
kai nashiga gyaɗa mata tace
"To menene".
Nace "Goggo Ya SALEEM ne Ya SALEEM ne".
sai kuka yaci karfina,gaba ɗayan su jikinsu yagama mutuwa cikin hanzari Ummi ta nufi ɗakin Abba kasan cewar yau Saturday ne yana gida,a tare suka fito da shi har lokacin ina rike a hannun goggo Hauwa,tsawa Abba yabuga min yace
"Ke wai meye haka kin bi kin tadawa mutane hankali da safen nan".
kokarin danne kukan nashiga yi dan nasan halin Abba shi ba irin Abbu bane mai jurar rarrashi,karaso wa cikin parlour'n yayi yana kuma faɗin
"In bazaki faɗi abun da ya same ki ba yi waje kije kiyi kukan naki,ina SALEEM ɗin yake?".
toshe bakina nayi da tafin hannuna cikin jan shashsheka nace.
"Yace na tafi ya haramta kaishi gare ni wai cikin ba nashi bane".
na karasa cikin kuka sosai.
wani irin zabura su goggo Hauwa sukayi Ummi kam sai da tayi baya ta zauna kan kujera tare da ambaton sunan Allah,
goggo Hauwa da Aunty Halima suka shiga rafka salati goggo Hauwa ta buga kirji tace
"Ya haramta kansa da ke ya sake ki fa kenan kuma ciki ba nashi ba SALEEM ɗin shaye-shaye yakoma"...


Abba ma sai da ya girgiza da jin abun da nafaɗa da sauri ya juya yakoma ɗaki.
Number Ya SALEEM yakira yace yazo yanzu-yanzu yana niman sa.
a parlour kuwa zaunar dani goggo Hauwa tayi suma suka zazzauna kowa jikin sa yagama sanyi,a hankali naci gaba da kuka na.
batare da ɓata lokaci ba motar sa yashigo gidan
duk muna zaune a parlour har da Abba yayi sallama yashigo,
gefe da Abba yasamu guri yazauna a kasa kana yashiga gai da Abba da su Ummi, Abba ya nisa tare da gyaran murya yace
"SALEEM wai me ke faruwa ne tashigo ta ɗagawa mutane hankali da koke-koke da wasu magan ganun da babu daɗin ji wai kace ka haramta kanka gare ta da kuma ciki wai ba naka bane ko mene?".
sautin kuka na kuma karawa jin yadda zuciya ta ke tafasa, sawa Abba ya buga min yace
"Zaki rufawa mutane bakine ko sai nazo gun kiyi Mai dalili!".
kai na na jingina da kafar goggo Hauwa ina kukan a hankali.
muskutawa yayi kana yaɗan yi kasa da kansa yace.
"Eh Abba gaskiya ne abun da tafaɗa".
basu Ummi kaɗai ba hatta Abba sai da ya girgiza, goggo Hauwa ta waro ido tare da buga kirji tace
"Kai SALEEM kan ka ɗaya kuwa kasan abun da kake faɗa kuwa?".
Abba ya gyara zama kana yace
"To me yafaru da wannan yanke hukunci haka? An san aure abune mai rai wata kila karshen rayuwar sa kenan, shikuma cikin taya akayi yazamo ba naka ba tana da wani mijin bayan kaine??".
Abba yafaɗa yana duban sa dason jin ba'asi dan shi kan sa yashiga ɗimuwa matuka...


Kafafun sa ya tanƙwashe kana yayi kasa da kansa yace
"Kayi hakuri Abba da abun da zan faɗa".
da sauri na ɗago kai na yayin da naji kukan ya tsaya cak na zuba masa ido babu ko kiftawa.
sai ya kuma yin kasa da kansa kana yacigaba da faɗin
"Lokacin da nayi tafi
naje nayi wata 1 ranar da na bar garin nan tana cikin yanayin rashin sarki,ranar da na dawo kuma na tadda ta bata da lafiya bayan da na kai ta asibiti kuma likita ya tabbatar da tana ɗauke da cikin wata ɗaya gatanan kuma ita shai da ce".
Yafaɗa yana nuna Ni da hannu.
Salati

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login