Showing 45001 words to 46406 words out of 46406 words
suka ɗauki naira dubu biyu suka bata suka ce shine albashin ta,
Mama mai awara ta karɓa har hanunta na ɓari tanata zuba musu godiya.
tana komawa gida tahaɗa ƴan kayakin ta tafita sai tasha,
tashiga mota zuwa garin Jos tana isa direct Narkuta ta wuce,
ko da suka iso a bakin titi aka sauke ta kasan cewar ɗan kuɗin da ke hannunta duk yakare a kuɗin mota da kafa tashiga layin unguwar su direct ta ɗau hanyar gidan Malam Musa.
a sakar gida ta iske Zainabu zaune ta yi sallama tashigo, da sauri Zainabu ta mike tana faɗin
"Oyoyo Mama mai awara maraba lale barka da zuwa".
Mama mai awara ta yelwata murmushin fuskarta tace
"Yauwa Zainabu".
Zainabu ta kara buɗe taburman da take zaune a kai tare da faɗin
"Sannu da hanya ga gurin zama".
tazauna gefen taburman nan suka shiga gaisawa kana Zainabu ta mike ta ɗibo mata ruwa mai sanyi cikin randar kasa ta kaso mata.
tasha tana cigaba da mata sannu da hanya.
bayan ɗan gaishe-gaishe da tanbayar bayan rabuwa,
Mama mai awara takuma bin gidan da kallo akaro na ba adadi jin babu wani alamar motsin wani acikin gidan,
ganin yan da Mama mai awara take ta raba ido cikin gidan, Zainabu taɗan muskuta tadube ta tare da yin murmushi tace
"Um sai kawai kiga ɗiyar ki tabiyo ki, fir taki zama fa wai
ita bazata iya zama ba kawai zata biki, HAMDAH kenan ƴar Mama".
Ido Mama mai awara ta waro tare da faɗin
"Wa ɗin wai HAMDAH to ai ni ita nazo ɗauka".
Zainabu tace "A'a ita kuma kika zo ɗauka Mama mai a wara?, to ai HAMDAH kamma tun ran da kika bar nan da kwana biyar tabiki in ban mance ba".
wani irin zabura Mama tayi tare da buga kirji tace
"Tun tafiya ta da kwana biyar tabar gidan nan to ina taje?".
Zainabu tace "Mama kina nufin wai baku tare da ita?".
shiru tayi cike da tsananin damuwa a ranta take faɗin
"To ko ta koma gurin iyayin ta ne".
sai kuma tayi saurin kuma cewa
"Ina baza ta koma ba ko dun gudun ta sana diyyar ta Ummi ta tabar gidan Abba'n ta, ina bazata taɓa komawa gida ba".
cikin tsananin matukar tashin hankali Mama tace
"Ina Zainabu bataje in da nake ba!"
ido Zainabu ta waro tare da buga kirji tace "Bataje ba? nan fa ta shirya tace zata biki nace ta hakura ta barki kidawo tun da kince bazaki jima ba tace a'a zata biki kawai, to ina taje?".
Zainabu tayi maganar hankali tashe.
hankali tashe Mama mai awara ta mike tana faɗin
"Bataje ba Zainabu bataje ba".
tanufi kofa, Zainabu ma ta mike taɗau mayafin ta tabi bayan ta,
duk gidajen da Mama mai awara take tunanin ko HAMDAH zata iya zuwa gidan wato gidajen da suke mutunci da su anan cikin Narkuta.
amma duk in da taje sai suce ai su rabon su da ganin ta tun ranar sunan ta.
batun tashin hankali gun Mama ba'a magana,
tunani tafara tashiga mota taje Bauchi ta tuba ko ta koma can, sai dai bugu da kari batasan gidan su a cikin garin Bauchi ba,ita dai tace mata ita ƴar Bauchi ce amma bata faɗa mata ko awani unguwa take ba,to yanzu idan taje ta ina zata fara neman ta, Bauchi babban gari ne ba karamin gari ba, idan taje ta ina zata fara neman ta....
Ranar Mama mai awara kuka da hawayen ta tayi da shar-shar, tunanin ta bai wuce ina tatafi wani hali take ita da ƴaƴan ta.
kwanan Mama uku ta fara shirin komawa dan tana ganin zaman ta anan nauyi take ɗaura musu, duk yan da taso samun kuɗin mota tatafi batare da sunsan bata da shi ba abun yacu tura, karshe dai malam Musa shi ya bata kuɗin motar komawa.
a haka ta koma taje ta cigaba da rayuwar kunci da bakin ciki acikin gidan su wacce matar yayan ta ta mallake ita da ƴaƴan ta, kullum tana cikin tunanin HAMDAH da ƴaƴan ta da halin da suke ciki,
duk san da tatuna hakan sai ta zubda ƙwalla, sai dai batayi kasa a guiwa wajen yi mata addu'a ba, duk san da zatayi sallah sai ta sanyata cikin addu'o'in ta.....★
wannan kenan
Acan kasar saudi kuwa bayan sati uku da canza Diamond ɗin har yanzu muna cikin masarautar Saudi mun zamo tamkar ƴan gida,
Bappa yace bazamu koma ba sai munyi aikin hajji da yake dumfaro wa yanzu.
wata ranar juma'a bayan mun dawo daga masallaci shugaban kasar mu na Nigeria yakirawo wayar Mahmoud yahaɗa su da Bappa,bayan gaisawar da ya guda na sakanin su shugaban kasar ke magana kan cewa tun ranar da aka tura kuɗin Diamond baikuma jin wani magana ba,
shin akwai wanda za'a basa ATM ɗin bankunan da aka zuba kuɗaɗen ciki nan kasa Nigeria kafin su sudawo?.
Bappa yace
A'a yarike ATM ɗin a gurin sa dan bayida wan da zai iya cewa abashi sai dai bari yayi wa ita yarin yar magana,
yaji ta bakin ta ko da abun da zatace kan lamarin bari a nemeta aji ta bakin ta.
I na zaune cikin ɗaki ina sakawa su Naseem kaya da yanzu nayi musu wanka, cikin kayan da ɗazu Bappa yabani kuɗi nasiya musu da muke dawowa daga masallaci.
nan yake yimin bayanin yan da sukayi da shugaban kasar mu kana ya ɗaura da faɗin
"Ko akwai wan da kike ganin za'a bashi kafin mu koman?".
nace "A'a Bappa yan da kace ɗin hakan yayi".
yace "To madallh shike nan".
ya mike yafita....
da daddare duk muna hallare a katafaren parlour'n da yake masaukin mu, muna cin abin cin dare Mahmoud ya dube ni sannan ya nisa yace
"Bappa ya faɗa miki yan da sukayi da shugaban kasa ko?".
nace "Eh yafa ɗa min".
kai ya jinjina tare da faɗin "Ok to yanzu kina so a bar kuɗin cikin account banki surika juyawa ne ko da wani abun da zakiyi da shi?".
Bappa yace "Tan bayar da shugaban kasa yayi min ɗazu kenan da nace masa yabar ATM ɗin agurun su,
ni ma dai nayi tunanin ko za'a siyi wasu ƴan kaddarori ne in yaso sai abar sauran banki yarika juyawa".
baki na washe tare da faɗin
"Eh wlh Bapp a siyi wani abu da kuɗin".
Mahmoud yace "To me kike so a siyan".
hannayena biyu na dafe kumatu na, nayi sama da kwayar idanuna ina ɗan jujjuya su, naɗan yi
shuru alamun nazari, sai nakuma washe baki nace
"Bappa kasan me nake tunani kuwa".
kai ya girgiza tare da yin murmushi ganin yan da nayi maganar, Mahmoud ma sai da ya murmusa. cikin muryar dariya
nace
"Bappa kuɗin zai kai yasiya mota da gida?".
nayi maganar ina rufe fuskata da cigaba da dariyar,
Mahmoud yace "Me zai hana shi kai wan har abun da yafi gida da mota ma zai siya, gidaje da motoci ma ba gida da mota kaɗai ba har abun da yafisu ma kuɗin zai siya da shi har yarage".
da sauri nace "Yauwa to kawai a siya motoci irin manyan motocin nan wan da suke loda kaya aciki ana kaiwa garurruwa masu nisa ɗinnan,
da gidan mai".
yace "Gidajen mai dai". nace "To shi da kuma asibiti da masallaci, umm da kuma irin abubuwan sadakatuj'jariyan nan".
Bappa yace
"Rijiya bishiya masallaci bohul makaranta asibiti,da dai sauran su duk sadakatuj'jariya ne".
kai na gyaɗa da sauri nace "Yau wa Eh Bappa".
nakarashe maganar cikin muryar dariya,
yace "Gaskiya kinyi tunani mai kyau abun da yakama ta ayi kenan".
dariya kawai nayi dan ni ban ɗauki maganar da wata girma ba dan ni atunani na mun dai yi sa cikin rahane amma kuɗin bazai iya yin abun da na lissafan nan ba.
Mahmoud kuwa kai ya girgiza ganin yanayin yaranta cike taf cikin maganar tawa......
A daren Bappa ya sanar wa shugaban kasar mu abun da nace ina so ayi da kuɗin,
shugaban mu ya jinjina lamarin matuka yace nayi tunani dan hakan ma ci gaban kasa Nigeria ne kwari da gaske.
za'ayi abun da nace in yaso sauran kuɗin kuma banki sai ta rika juyashi.
bayan sun gama maganar Mahmoud yace to shifa gobe idan Allah ya kai mu zai koma bakin ai kinsa.
Bappa yace "To Allah yakai mu mukam muna nan sai munyi ai kin hajji tukun, idan kaje karika zuwa duba mahaifiyar ka akai-akai gobe ma zaka kuma kirowo min Isa ya hadamu mukuma yin magana da ita".
yace "To ba da muwa Allah yakai mu"....
washegari da misalin karfe 11 Mahmoud yabi jirgi zuwa Dubai in da daga can zai shiga wani jirgin zuwa Nigeria...
★★★★
*After 1 year*
★★★★
🙌🏻🙌🏻🙌🏻🙌🏻🙌🏻🙌🏻😹 *da yar dar Allah anan book 2 yakawo karshe sai mun haɗu a littafi nagaba wato littafi na uku wan da shine zai zamo littafi na karshe da yar dar Allah*
*Zazzaɓin gida-gida yafara kyarkyara ta*
Mommyn twins ce